Showing 69001 words to 72000 words out of 129540 words

Chapter 24 - ABDUL JALAL Hausa Novel

08 Oct 2024

6673

gurin Jawwad kowa yarasa ganewa Jalal abinci se Jawwad ya takura masa sannan zeci, baya walwala yadena shiga gidansu Jawwad sam, Jawwad yarasa dalili, Jalal ya dena zuwa ko ina se zaman daki
Yau kusan satin Jalila biyu a kano amma har yanzu Ummi batayi tafiyar nan ba, tun JALILA tana tambayar Ummi har tagaji ta kyaleta,
Jalila tana rayuwa a kano ba yabo ba fallasa, Jawwad da Nana da Abbansu suna kaunarta, yayinda Maama Sam babu ruwanta da ita, bata shiga sabgar Jalila kwata? hakan bayamata dadi amma bayadda ta iya
Tun ranar da Jalila suka samu wannan sabanin da Ilham bata kuma haduwa da ita ba
Jalila tana zaune a palour tana chatting da Hanan, Halima ta fito sanye da hijabi Jalila ta Dan dubeta
"Anty halima ina zuwa haka?"
"Kinga Hajiya ce ta aikeni zan kai kayan nan, gidan wata kawarta"
"Bari in tambayeta se in rakaki"
"To shikenan tambayota semuje"
Dakin Maama Jalila taje ta ganta tana waya ta jirata tagama sannan tace
"Maama naga kin aiki halima zan rakata Dan Allah"
Kallonta Maama tayi a wulakance ta dauke kai
"Ba a karkashina kike zaune ba yadda kika gadama kiyi"
Kallonta Jalila tayi ta Dan girgiza kai, ta mike ta bar dakin ta fito ta tarar da halima,
"Bari insaka mayafi in rakaki"
"To ina jiranki"
Jalila taje ta dakko gyalenta tayi rolling ta fito
Ba karamin kyau Jalila tayi ba doguwar Riga tasa baka tayi rolling da Jan mayafi suna shirin fita Nana suka shigo ita da Ilham
"Wow looking so masha Allah sister kina wuta kinga kyan da kikayi kuwa, ina zuwa haka"?
Murmushi Jalila tayi " bana son zolaya Nana, Halima zanyiwa rakiya"
Banda aikin harar Jalila da kallon banza ba abunda Ilham takeyiwa Jalila
"Gaskiya kinyi kyau, sekun dawo, amma gaskiya ayi a hankali karki hada go slow a hanya"
Nana ta fada tana kashemata ido
"Nana kenan ba kya rabo da tsokana"
Jalila ta Dan kalli Ilham
"Kawata Ilham ba fada me yakawo gaba, fatan kina lafiya"
"Nakasa kika gani a jikina kokuma, a kwance kika ganni kike tambaya ina lafiya"
"Ba ko daya na dai ga kaman u are psychologically abnormal"
Tana zuwa nan a zancenta tanufi hanyar waje, tabar ILHAM a tsaye sororo, tama rasa mezatayi,
Halima tabi bayan Jalila, Nana kam gimtse dariyarta tayi ta kalli Ilham
"Don't mind her please, muje ciki"
"Wallahi Nana badan ina jin kunyarki ba da na Dade da ketawa Jalila rashin mutunci, nizata kalla tace am looking psychologically abnormal"
"Yi hakuri, nidai bazan gaji da Baku hakuri ba, sannan kidena nuna mata kinji haushi
Yanzu dai bar batun Jalila ban labari meyake faruwa ne"
"Mtseww meyema be faru ba kwana hudu kenan banga yaya Jalal ba, idan naje part dinsa a kulle duk na damu, ko yau mukayi aure da Yaya Jalal na azabtu Nana"
"Calm down, Jalal ba karamin yaro bane, maybe yana tare da Yaya Jawwad, sannan tunda ba wata budurwar CE dashi ba ki kwantar da hankalinki, a hankali komai ze wuce, kinsman yanada gaddama"
"Wani irin hakurine banyiba, narasa meyake damunsa, kullum shine tension dina, kina batun bashi da budurwa to yanada ita kuma nasanta indai na haifu senasata tayi danasanin Sanin Jalal da tayi"
Dan zare ido Nana tayi
"Are you serious Jalal yanada budurwa, Dan Allah wace wannan"?
"Ai ba sonta yakeba ita take masa shishshigi, da zarginta nake yanzu na tabbatar da wacece, zan dau mataki na karshe, daze kawo karshen komai"
"Wani mataki kenan?"
Nana ta fada a tsorace
"Just watch, bari inkoma Gida anjima zanzo in tambayi Yaya Jawwad ko yasan Inda yake"
Tana gama fadin haka ta mike tayi waje da sauri
Jawwad be fushi ba yakoma gurin Jalal amma ya tarar ya rufe kofar palour Sa Jawwad yayi iya kokarinsa da rarrashi amma JALAL yaki budewa, gashi tun safiyar ranar beci komai ba haka Jawwad yagaji yakoma gida
Shikuwa Jalal yana ciki yanajin Jawwad yaki bude kofar tabbas Jalila tayi gaskiya yakamata ya bar Jawwad ya huta haka tsawon shekaru yana fama dashi da matsalolinsa
"Wai meyasa nake hakane, meyasa bazan yi rayuwa kaman sauran mutane ba"
Jiyayi zuciyarsa tana tafasa, kaman zata tsga kirjinsa ga wani nauyi da kansa yayi kaman ya fashe yai jifa da Wayne cups din kan karamin table din dakinsa, ya dinga jifa da duk abunda yaci karo da shi ya dinga jifa da abubuwa, da kwalaben giyar da ya shanye
Yakoma ya zauna idonsa suka kara Ja, ya runtse idonsa yanajin kansa yana juyawa
Mikewa yayi zumbur yabi takan fasassun kwalaben nan ya dauki keys din motarsa ya fito a sukwane, motarsa ya nufa ya Shiga ya fisgeta da gudu yayi waje

Su Jalila dake daf da bakin Layin suna tafe suna hira itada halima, sukaga motar Jalal ya dannota a guje, ga uban kura ya tayar ko gane motar ba ayi saboda gudu
"Tab anya Jalal kansa daya, wannan gudun yanzu inya bige wani fa?"? Jalila tayi maganar cike da mamakin wannan mahaukacin tukin na Jalal
"Hmm kema dai kya fada, shi kota ransa ma ba yayi"
"To Allah ya shirya"
"Ameen"
Haka sukaje inda zasuje suka dawo, daf da magariba ne Dan haka suna idar da salla suka Dora sanwar dare
Ana idar da sallar magariba Jawwad Yakoma gurin Jalal yaga ya bude kofar, da sauri ya shiga amma Jalal baya ciki, ya duba bedroom dinsa da toilet baya cikin, se tarin kwalaben giyarsa, ya sha wasu, ya zubarda wasu, ya farfasa wasu kwalaben yayi kaca? da dakin tundaga palour har bedroom
"Ya salam"
Jawwad ya furta ya dakko wayarsa ya fara kiran Jalal amma seyaji wayar tana ringing a kasan pillows akan gado
Cikin gidansu Jalal ya shiga a rude, ya tarar da mummy tana kallo a palour
"Mummy Dan Allah kokinsan inda Jalal yake?"
"Kamarya nasan Inda yake, ai kai yakamata in tambaya, baya part dinsa?"
"Baya can na duba, kamaar akwai abunda yake damunsa mummy tun jiya baya cikin nutsuwa,"
"Ni rabona da shi yau kusan kwana hudu"
Dan zaro ido Jawwad yayi
"Kwana hudu mummy, kuma baki nemeshiba yana part dinsa baya zuwa ko ina, yau kawai yafita kuma be gayaminba"
"To kai kenan daya daukeka da mahimmanci kana sanin inda yake, ni ko inda nake seya ga dama zezo, ina gani kuma Duk inda yaje ze dawo"
Jikin Jawwad ne yayi sanyi jin abinda mummy ta fada,
Da sauri Ilham ta karaso palour da sauri
"Au wai kaima baka San inda ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????yakeba, na dauka kana tare da shi"
Ilham tai maganar a firgice
"Eh amma ki kwantar da hankalinki zanje nemansa insha Allah ze dawo nasan ba nisa yayi ba, ni abinda yafi dagamin hankali dana je na tarar ya farfasa abubuwa a dakinsa"
Zare ido mummy tayi
"Haba dai?"
"Eh mummy shiyasa ma nazo na tambayeki, narasa meyake damunsa"
"Watakila giyar ya sha tagaya masa karya, amma muje bangaren nasa"
Tare suka tafi da mummy da Ilham suna zuwa suka tarar da mugun aika? da Jalal yayi duk wani abu me fashewa Jalal ya fasashi, hankalin mummy ya ta shi sosai
"Na shiga uku Jawwad meyasami Jalal hakane? Be taba irin wannan abunba fa"
Ita kanta Ilham abun yabata mamaki sekace dakin mahaukaci ya farfasa abubuwa
Jawwad ne cikin muryar rarrashi yafara magana
"Ki kwantar da hankalinki mummy, insha Allah ze dawo gida, amma yanzu bari in fita in dudduba inda yake zuwa na San tabbas akwai abunda yake damunsa"
Gyada kai mummy tayi tana share hawaye
? Bayan mummy da Ilham sun koma cikin gidane mummy se kuka take "Allah yasa yaron nan ba haukacewa yayi ba,"
"Haba mummy ya kike fadin hakane, insha Allah lafiyarsa kalau"
Ilham ta fada cike da kwarin gwiwa sannan ta nufi dakinta tana zuwa dakin ta kule tasaka masa key
Sannan ta kira mahaifiyarta
"Hello maami"
"Na am Ilham, yakike akwai labarine"
"Eh Mami, Jalal ne ya haukace fa"
"Kamar ya ya haukace ban gane me kike nufi ba,"
"To hauka mana kwana hudu yana kulle kansa a daki Jawwad kawai yake budewa, yau kuma shima din be bude masa ba, ya fita dazu da yamma, amma duk ya farfasa kayan dakinsa bakiga dakinba kamar mahaukaci"
"Ina baze yiwuba, bahaka nakeso ya kasance ba, ba hauka nakeso yayi ba, idan yayi hauka Dan gatan mahaukaci ze zama,
Sonake se yazo hannunmu mun wulakanta hadiza, mun tozarta ta, setayi kuka fiye da Wanda tayi a baya"
"Amma Mami ta Yaya kina gani kullum shirinmu rushewa yake, abinda ya kawoni gidan nan shekara da shekaru mun kasa samu"
"Amma kinsan duk laifinkine da rashin kokari Ilham ni narasa ma zaman me kikeyi abu yakici yaki cinyewa tsawon shekaru"
"Maami dukfa abinda kikasani inayi, amma kinsanshi muguwar gaddama CE dashi gashi jarababbe"
"Hakane amma zankoma gurin malamin nan inji mekuma zecemana"
"To Mami, yadda kukayi kya gayamin, amma da gani nake kawai inyi me gaba dayan nan ina fargabar aikinmu ya lalace"
"Har yanzu kina ganin alamar yana da budurwa ne?"
"Eh mana Mami shiyasa duk na tsorata fa"
"Ki kwantar da hankalinki babu abunda ze faru just focus"
"To mamina nagode, amma bakiga kukan da mummy tayiba"
"Ita tasani ni be dameniba"
Haka sukayi sallama da mamanta
Jalila ce ta fito harabar gidan da parker a hannunta taga Jawwad a sukwane ze bude motarsa, da sauri Jalila taje gurinsa
"Yaya lafiya ina Zaka haka naganka a firgice"
"Jalila Jalal ne banganiba gashi ya farfasa abubuwa a dakinsa bansan inda ya tafiba, shi zan tafi nema"
"To ai dazu da nafita raka halima naga fitarsa a mota kamar ze tashi sama, yana ta gudu a mota"
"Are u serious?"
"Of course naganshi dazu, amma Yaya Jawwad ka nutsu mana, duk ka tayar da hankalinka"
"Jalila, Jalal be taba hakaba bakiga dakinsaba kamar ba dakin Dan Adam ba ya fasa komai"
Gabanta ne yafadi "to ko in raka ka ?"
"No kizauna bari inje"
"To adawo lafiya Allah ya kiyaye, amma kayi driving a hankali"
Gyada mata kai yayi ya shige motar yajata da sauri


Share please
More comments more typing.......................
Inajin dadin comments dinku, kuna comments ina muku typing
Am proud of you all
d'd'd'd'

=؊??=؊??=؊??=؊??=؊??
[8/31, 8:30 AM] Safiyya:
? ? _ABDUL? JALAL_
? ? ? ? ?? (2020)

? ? ? _ STORY & WRITTEN BY AISHAHUMAIRA_
? ? (Daddy's girl)

? ? ? ? ? ? ? ?PAGE-?32

PART 1
Share please

? _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,? ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta? wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar

07063065680
Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din


Special thanks to my group members ina Alfahari daku comments dinku na bani karfin gwiwa
ABDUL JALAL NOVEL FANS
Love u all guys d'd'd'd'd'

? ? ? ? ? -MY FIRST NOVEL-

Jawwad ya ja motar yabar cikin gidan, fara zagawa yayi clubs din da yasan Jalal yana zuwa amma be sameshi ba, tun bayan magariban nan yake yawo amma be samu ganinsa ba, Gida ya koma yabar motarsa a bakin layi yakoma part din Jalal ya dakko wayar Jalal ya koma inda yabar motarsa, ya shiga ya zauna cire wayar yayi daga key dayake yasan password din, call log dinshi ya duba yaga kiran Hannah dayawa amma be daga ba lambar Jeje itace ta karshe da aka kirashi dashi kuma shima be amsaba,
Dafe kai Jawwad yayi "ohh my God Jalal ina kashiga ne karka yiwa kanka Illa mana"
Lamabar Jeje ya kira, yai Sa a kuwa Jeje ya daga
"Ina Jalal yake?"
"Kamar Yaya?" Jeje ya tambayeshi
"Kamar yadda na tambayeka"
Jawwad ya bashi amsa
"Ohhh in ka damu da shi seka zagaya mashayar da yake zuwa kaneme shi,"
Jeje ya kashe wayarsa
Girgiza kai Jawwad yayi ya kuma kunna motarsa ya marasa ina ze dosa Neman Jalal
Haka ya dinga zaga clubs har gurin goman dare, club din dayaje da farko ya koma Wanda nan Jalal yafi zuwa, Jawwad ya duba ko ina amma bega Jalal ba,
Yazo ze fita ya hangi motar Jalal a can wani guri da sauri ya fito ya nufi inda motar Jalal take, bude motar yayi da sauri Jalal yana zube a cikin motar ya fita hayyacinsa sosai, gashi nan dai shiba sumamme ba kuma shiba me bacci ba
Dagoshi Jawwad yayi yana jijjiga shi
Da sauri Jawwad ya koma ya bada ajiyar motarsa gurin masu gadin club din ya shiga motar Jalal ya jata ya nufi Gida
? Jalila kam tagagara yin bacci tunda Jawwad ya fita tana palour a zaune tana jiran dawowarsa tun suna hira da Halima har Halima ta tafi ta kwanta tabar Jalila a palour
Karfe sha dayan dare taji motar Jawwad ya dawo
Da sauri ta fito setaga motar Jalal, tana nan tsaye taga Jawwad ya fito daga motar
"Yaya lafiya kuwa naga ka Dade?"
"Baby da kyar Nagano Jalal, yanzu dare yayi bari inkira Me gadin gidansu Jalal ya kama minshi in kaishi part dina"
"To shike nan"
Jawwad ya juya da sauri, Jalila takarasa bakin motar ta leka, Jalal yana kwance Kamar gawa, ba a dadeba Sega Jawwad sun dawo dame gadi
Suka fito da Jalal suka shiga dashi suka kwantar da shi akan gadon Jawwad
Jalila ta kalli Jawwad "yaya wai meyasameshi? Bashi da lafiyane"
"Wallahi ban saniba Jalila inaga giya ya sha dayawa"
Dan zare ido Jalila tayi
"To se yaushe ze tashi"
"Se lokacin data sake shi, amma akwai abunda yake damunsa a rai, Wanda bansaniba"
Jawwad yafada cike da damuwa
"Yaya kalli yadda yake numfashi ko bashi da lafiya, kalli jijiyar kansa fa duk sun daga"
Jawwad ya kai hannu goshin Jalal yayi zafi sosai
"Da alama kansa yana ciwo ma"
Kafarsa Jalila ta kalla ta mike da sauri
"Yaya Jawwad kalli kwalabe sun fasa masa kafa"
Da hanzari Jawwad yazo ya duba kwalabe duk sun shige kafarsa
"Ya salam inaga bari in fita akwai wani abokinmu likitane, bari inga in yana nan yazo ya duba shi inba ya nan kuma, inzo in kaishi asibiti"
Ya Ciro wayar JALAL ya ajiyeta akan side bed
"To kayi sauri danni tsoro nakeji palour zan koma danaga ya taso in zura da gudu"
"Jalila da hankalinsa ba haukacewa yayiba kinji, ki zauna a parlour kiji rani"
Gyada masa kai tayi, ta fito parlour ta zauna shikuma Jawwad ya fita lokaci? Jalila seta leka dakin taganshi a kwance yadda a aka barshi, motsi taga yafarayi a hankali yana yamutsa fuska yana surutai cikin maye
"Hannah meye hakane, bakida hankaline,? Mtseww nace miki bana so fa, bana son yimiki rashin mutuncine amma ba kya ganewa"
A hankali Jalila ta Dan shiga dakin tana kallonsa
"To wace kuma Hannah,"
Jalila tayi maganar a zuciyarta
Cigaba yayi da surutai idonsa a rufe ya cigaba
"Nifa Jeje giyar nan yau kaman ba irin wadda nasaba sha bace kamar akwai wani abu a ciki, mtseww, nii ban San meyake damuna ba Jawwad baya son giyar nan danake sha fa"
Jalila ta kalleshi
"Kai ni dalla ka isheni ka cikamin kunne, kayimin shiru, nina aikeka ka sha kalleka Dan Allah, mutum har mutum amma ba hankali, ko kunya bakaji kake shan giya kai ko tsoron Allah bakaji ma bana tunanin kayi sallar isha'i, kana kwance kana maye, kasa Yaya se wahala yake in bakayimin shiruba nida kaine"
Jalila se rashin M takewa Jalal shikam baya hayyacinsa, yacigaba da surutansa
"Ko wace kuma Hannah oho masa"
Wayar Jalal ce tafara ringing ta kalla sunan Hannah ta gani a kan screen din wayarsa,
"Hmm kishiyar Ilham ce Ashe"
Tayi banza da wayar takoma palour, wayarce ta cigaba da ringing ta cikawa Jalila kunne Dan haka ta mike ta koma bedroom din ta kai hannu ta daga wayar
"Dan Allah baiwar Allah kiyi hakuri, me wayar kin ganshi a kwance, tunda kika kira be dagaba ai seki hakura ko, saboda shirme a tsohon Daren nan haba, kinkira ba adagaba sekace mayya duk kincikamin kunne"
Jalila tai tsaki ta kashe wayar ta kai hannu zata aje wyar ya rike hannunta gam ya bude Jajayen idanuwansa fes akan JALILA
Kwalalo ido Jalila tayi ta firgita matuka
"Meye haka kacikamin hannuna"
Ko kyafta idonsa bayayi akanta gashi ya riketa gam ko motsa hannun bata iyawa, idonsa tsoror yake bata
"Na shiga uku nika cikani, dama ance watakila ka haukace"
Kara karfin rikon yayi mata
"Wai meye hakane"
Setaga hawaye na bin gefen idonsa can yayi wani yunkuri se yafara amai kumface kawai take fita daga bakinsa, yasaki hannun Jalila a hankali
Zare ido tayi dataga irin aman dayakeyi
"Nikam ina Yaya Jawwad ya tsaya haka"
? Itakam Hannah mamakine ya cikata wace ta dauki wayar Jalal a Daren nan, OK ko Itace kanwar tasa da Jawwad yake fada, to me take masa a wannan lokacin haka?
"Tabdijan to wallahi da sake akwai matsala"
Jalila ta koma bakin kofa ta zuba masa ido Dan tarasa meya kamata tayi can jimawa Sega Jawwad ya dawo shida wani
"Sorry Jalila kinganni ban dawo da wuriba, seda naje Asibiti na dakko likitan"
"To gashi can dai wani irin amai yakeyi yana surutai"
Da sauri Jalal da likitan suka shiga cikin dakin
Likitan ya kalli bakin Jalal duk wannan kumfar fara
"Subhanallah" ya furta yasaka abu ya goge masa kumfar yayi masa wasu allurai
Jalal ya dinga aman abunda yaci
Likitan ya kalli Jawwad
"Jawwad Jalal wasu miyagun kwayoyi yasha Wanda besaba shan irinsu BA, suke nema suyi masa illa"
"Bayan giyar kuma hada kwayoyi"
Jalila tafada cikin mamaki
"To gashi nan dai, kuma da alama ya Dade beci abinci ba"
Likitan yabata amsa, girgiza kai kawai Jawwad yayi, Jalila ta koma palour
Shida likitan suka gyara gurinda Jalal yai aman suka canzamasa kaya zuwa Jallabiya
Kafar Jalal aka ciremasa kwalaben daya taka, sannan yasa masa drip, ya rubuta magunguna yacewa Jawwad da safe yaje ya siyo masa,
"Yaya ni Bacci nakeji seda safe"
"To baby mungode sosai, kiyi bacci me dadi"
"To Yaya kaima ka kwanta haka dare yayi"
Ya gyda mata kai likitanne ya kalli Jalila
"Baby ni baza ayimin sallama ba?"
Dan murmushi tayi
"Seda safe tafada a takaice"
Jawwad kam Dan hade rai yayi, ya kalli likitan "muje in maida kai"
"Jawwad dan Allah wannan babyn fa nifa na faller wallahi, Yar gayu da ita ga iyayi"
"Ina ruwanka da wacece, nifa banason irin wannan abun salis, muje in saukeka ni"
"Tuba nake sirikina amma nikam naga guri"
Fusata Jawwad yayi "kaga wuce muje"
Haka suka tafi ya maida doctor, se bayan karfe daya sannan Jawwad yasamu nutsuwa lokacin drip din jikin Jalal ya kare ya cire masa, sannan ya kwanta
? Bayan sallar asuba Jalila take gayawa Nana a gidan Jalal ya kwana, yanata a man kwayoyin da yasha
"Tab to indai wannan ne sun saba, amma iya sanina baya shan miyagun kwayoyi, sedai giya da taba, watakila Suma yafara watsa abunsa wayasani, kice hadake akai jinya"
Nana tafada Dan Neman magana
"God forbid indai Dan ta shine, yaje ya karata ni Yaya Jawwad ne abun tausayi wallahi"
"Mutane dayawa na mamakin kaunar da sukewa Juna, Allah ne ya

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login