Showing 54001 words to 57000 words out of 129540 words

Chapter 19 - ABDUL JALAL Hausa Novel

08 Oct 2024

6682

da yatsaya mata ta dokarmin yarinya"
"Ohhh my God mum Abdallah kinfiye rikici fa, wallahi ba Yar wani bace ba kawai dai she's so kind, yarinyar and she regrets what she did, ni yarinyar ma tausayi tabani wallahi mamanta duk ta damu, gashi kuma kanwar abokin Abdallah ce"
"Kaga ya isa haka bana bukatar jin wani abu ya isheni haka, ko uwar abokin Abdallah ce senasa an koyamata hankali balle wata kanwar aboki, in kai ka hakura ni ban hakuraba wallahi...
" Enough "
Ya daka mata tsawa nan take ya juye ya koma sojansa fuskar nan kaman be taba dariya ba
"Idan kika kuskura kikayi wani abu akan yarinyar nan kinsan meze biyo baya kinsanni sarai"
Yayi maganar cikin tsawa sannan ya fice ya bar mata dakin

"Wai Jawwad meyake damunka ne tun dazu ka kasa zama, ka kasa tsaye se zagaye kakeyi"
Jalal ne dake kwance akan gadon Jawwad yai maganar yana kallon Jawwad
"Ta yaya zan iya zama bansan wani hali akeciki ba ko sojan da Jalila ta dakarwa yarinya ya hakura, bansan me ake cikiba nakira wayoyinsu gaba daya basu daga ba Allah yasa dai lafiya, Allah yasa basuyi mata wani abun ba"
Jawwad yai maganar cikin damuwa
Dariya Jalal yayi "to meye abun tada hankali in suka karairayota se ka tafi Kaduna jiyya"
Jalal ya karashe maganar yana dariya
Tsaki Jawwad yayi Wanda yayi dai? da ringing din wayar Jawwad
Da sauri ya dakko wayar yadaga a zatonsa Abbana
"Hello hey Aliyu yakake"
"Ina lafiya Alhamdilillah , amma ban gane me magana ba"
"A Rasheed ne"
Aka bashi amsa
"Ohhh Abdallah ban dauki muryarka bane, kuma bani da wannan lambar taka"
"Wallahi kuwa na canza layine"
"Allah sarki ya kake ya mutan gidan"
"Kowa lafiya Alhamdilillah, yau naga kanwarka"
"Kanwata wacce kenan ai Nana tana kano"
"Ba itaba wata Jalila"
Gaban Jawwad ne yafadi
"A ina kaganata ya akayi kasan kanwata CE?"
"Sabani suka samu da Hanan mummy ta daga hankalinta mukaje nida daddy, har muka hadu da abbanku"
Ajiyar zuciya Jawwad yayi sanan yace
"Alhamdilillah Abdallah ya ake ciki Dan Allah kuyi hakuri kabawa daddy hakuri,"
"Karka damu, ai ba abunda yafaru daddy yace "yarsace itama, kanwartaka ce Yar daruce Aliyu bata da tsoro"
"Nagode sosai Abdallah,"
"Ba komai Aliyu, nima kanwata CE, kuma wani abun mamaki suna matukar kama da Hanan din"
"Allah sarki Dan Allah kayimin godiya agurin daddy"
"Ba komai Aliyu girmankane "
Sukayi sallama, nannauyar ajiyar zuciya Jawwad yayi tare da fadin
"Allah gatan bawansa, kaga abun mamaki Jalal, Allah ya tsallakar min da baby, basuyi mata komai ba, Ashe kanwar abokina CE sukayi rigimar da ita, kanwar A rasheed CE yarinyar"
Dariya Jalal yayi
"U escape this time around, se Ku kiyayi gaba, Dan ba kullum ake kwana a gadoba"
"Eh munji, for now we are safe, se dariyarka ta koma ciki"
Jawwad yayi maganar yana kallon JALAL yai murmushi tareda shafa sumarsa

Jalila CE da umminta se Abban Jawwad a parlour
"Inaga lokaci yayi dazaka cika wasiyyar mahaifin JALILA, ka dauketa ta koma gabanka, nima in koma Gida, JALILA ba ta jin magana, kullum cikin Neman magana take, bataji Sam abunda zuciyarta ta raya mata shi takeyi, ayi mutum ba hakuri kullum cikin Neman magana"
"Haba ummina tun jiyafa nake baki hakuri ashe baki hakura ba
Nace fa bazan kara ba"
Jalila tayi maganar idonta taf hawaye
"Yi min shiru bazan hakuranba, ke banda Allah yasa mutumin kirki ne baban yarinyar nan da yanzu wani zancen ake ba wannan ba,
Ke ba Yar uban kowa ba, amma har kina ikrarin ko Yar gidan bullet ce ko,
Kanaji har wallet ya Yar ta dauka, da sunyi bincike suka ganota a gurinki sunanki barauniya, wannan halin naki in kika cigaba a haka to wahala zaki sha, ayi mutum fada kaman kura"
Abba ne ya nisa ya danyi murmushi sannan yace
"Haba ummu Jalila, babynki fa ba haka kwai takeyiba,
Kin manta marigayi shima haka yake baya daukar raini, gashi na jama'a kinfi kowa sanin halinsa ba wasa"
"Amma be kai wannan yarinyar ba, JALILA fa da kudinta seta saka ta sai rigima koda uban waye,
Duk rigimar Abu Jalila mutumne simple kuma yana da kawaici, amma ita sun raba hanya da hakuri"
"Ummu Jalila kenan kin manta biyuce ta hadarwa Jalila, kefa jinin sarauta ce akwai wannan izzar ta sarauta a jikin Jalila, haka zalika mahaifinmu, babansa shine sarkin Fulani a rigarsu, kinga ba yadda za'ayi Jalila ta yadda, da raini Jinin sarauta na zagayawa a jikinta
Mikewa Jalila tayi ta bar dakin ta koma dakinta ta kifa akan katifa tana kuka, bataji sallamar Siyama ba saboda kukan da takeyi se kawai ganinta tayi a gabanta, dafa Jalila Siyama tayi
"Aminiya meya faru? Garinya haka ta faru a school? Jiya da yau banjeba bana jin dadi dazu ake gayamin abunda yafaru tsakaninki da hanan nasanta babanta abokin Abba ne Sam bata da kirki Yar gadarace"
Siyama tayi maganar cikin damuwa
"Kinga ni ba itace agabana ba
Aminiya kinji wai Ummi sena koma kano gidansu Yaya Jawwad nikuma wallahi bazan komaba bana son zaman garin nan"
"To aminiya saboda me? Meye a ciki Dan kin koma?"
"Au haka zakice ko? Dama ba kya sona, hmm Dan bakisan abunda dangin Maman su Nana din nan sukemin ba, ga wannan mugun abokin Yaya Jawwad din, Siyama bana son rabuwa da Ummi wallahi tun jiyafa nake bata hakuri amma taki hakura yanzuma zancen takeyiwa Abba fa"
"Ki kwantar da hankalinki aminiya, nasan kawai dan kin bata mata Raine amma bazata bari kikoma yanzu ba"
Mikewa Jalila tayi ta dakko wayarta ta fara kiran wayar Jawwad
Lokacin Jawwad ya tafi masallaci yabar wayar a dakin
Dan haka Jalal ya duba wayar cwt sisy ya gani akan screen din wayar
Tsaki Jalal yayi, ya daga wayar amma yayi shiru bece komai ba
"Yayana dan Allah ka kira Ummi kabata hakuri, tun jiya nake bata hakuri amma taki hakura, tace sena dawo kano, dan Allah yayana, ka tayani bata hakuri maybe kai inka bata hakuri ta hakura wallahi nadena sata magana, bazan iya rayuwa babu ita ba "
Tai maganar cikin sheshshekar kuka
Bece komai ba ya kashe wayar
"Fitinanniya kawai yanzu ma kin kira danki kuma daga masa hankali, shikuma duk yabi ya wani rude ya biyemiki, kina son ummin kike daga mata hankali "
Yai maganar cikin mita bayan h ya katse wayar, kuma kira Jalila tayi amma yayi rejecting kiran ya kashe wayar gaba daya,
Jalila ta dubi Nana
"Nana Yaya Jawwad yayi fushi dani, yaki cewa komai, kuma ya kashe wayar Sa"
Share mata hawaye Siyama tayi
"Calm down Aminiya, seta yiwu beji dadin abunda kikayi bane, amma shima ze huce"


Abun duniya duk ya ishi Ilham tarasa abunda yake mata dadi gaba daya wani mugun kishine yake damunta akan Jalal, se yanzu take tabbatarwa kanta tafada soyayyar Jalal fiye da yadda take tunani,
Dan haka bayan an tashi daga makaranta gidansu ta wuce taje tasakawa maminta kuka ta gaya mata abunda ke faruwa
"To kekam meye na damuwa duk kin daga hankalinki kalli yadda kika rame fa, naga dai Soyayyar ta wucin gadi ce burinmu na cika shikenan"
Mami a gurinki ce soyayyar dan lokaci ce se yanzu nagane dagaske soyayyar Jalal ta Huda zuciyata bana tunanin zan iya rabuwa da shi ILHAM tai maganar a zuciyarta
A fili kuma tace
"Mami duk da soyayyar wucin gadi ce amma kuma in shirinmu ya rushe fa?"
"Inkinga shirinmu ya rushe to sakacinkine, indai kika dage komai zezo dai? da yadda muka tsara, kedai kicigaba da amfani da magungunan danake karbo miki, sannan duk abunda zemiki na wulakanci kidena fushi kici gaba da binsa,
Randa ya shigo hannunmu kuma"
Bata karasaba se wani Murmushi da mamin tayi
"Kiyi kokari ki gane wadda take turamasa sakonnin, itama zamuyi maganinta"
gyada kai Ilham tayi cike da kwarin gwiwa, Aranta tace "da kaina zanyi maganin ko wace, Jalila kinyi gangancin fara soyayya da abunda nakeso zakiga tsiya"(nikam nace Allah sarki Jalila bata San anayi ba)
Haka Ilham ta shirya ta nufo hanyar gida, harta wuce part din Jalal kawai ta dawo ta nufi hanyar part dinsa tana zuwa kofar bedroom dinsa ta tsaya tana tunanin me yakamata tayi

Shikam Jalal Yana kashe wayar Jawwad shikuma tasa wayar tafara ringing lamba ce amma ba suna dan haka beyi tunanin komai ba ya dauka

"Oughhh baby tun safe banji muryarka ba ina kewarka sosai
A ina zamu hadu ne please, am missing you so badly, said something please, ko muryarka inji mana"
"Waike wace irin mace ce Mara kamun Kaine? Ki rabu dani nagaya miki meyasa kike min shishshigi ne bana son yi miki rashin mutunci fa"
? Wani murmushi Hannah tayi cike da kissa ta kara kashe murya cikin shagwaba tace
? "Babyna komai zaka kirani dashi fa bazanji haushi ba, ni komai naka burgeni yake, ko da zakamin duka ne a gaban jama'a, I wish halinku daya Da Jawwad da komai yazomin da sauki, nasan da shine ze tausayamin halin danake cikin amma a yanzu ma karkayi tunanin zan karaya, yanzu ko ka fadamin inda kake ko inkira Jawwad in tambayeshi, kuma ko inane biyoka zanyi"
"Karki fara Jawwad daban ni daban, Jawwad ne yake lallabaki, kuma shi yahana tun farko in nuna miki waye Jalal, kishiga hankalinki, wannan shine gargadina dake na karshe
Ilham dake bakin kofa kuwa daskarewa tayi
Ya tabbata Jalila ce Wato dama Jalila ce kenan, itace take son Jalal take turo masa messages haka, gashi yana cewa yana kyaleta saboda Jawwad, lallai Jawwad ma munafiki ne
Wani baking kishine ya ciwota Bata San lokacin data karasa dakin ba tasa hannu ta fizge wayar daga hannun Jalal tayi jifa da ita tana wani irin huci wayar ta tarwatse a gurin

Share please
More comments more typing..................

My group members inajin dadin comments dinku da addoinku nagode sosai Allah yabar kauna
Kuna comments ina muku typing=؃?=؃?=؃?
Kuna bari ina lalaci >?q?>?q?>?q?=? ?=? ?


=؊??=؊??=؊??=؊??=؊??
[9/12, 6:02 AM] +234 816 830 7871:
? ? _ABDUL? JALAL_
? ? ? ? ?? (2020)

? ? ? _ STORY & WRITTEN BY AISHAHUMAIRA_
? ? (Daddy's girl)

? ? ? ? ? ? ? ?PAGE-? 25

PART 1

? _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,? ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta? wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar

07063065680
Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din


Gaskiya comments nakeso ba sticker ba kokuma Just thanks in bahaka ba zan dena typing kullum
Special thanks to my group members ina Alfahari daku comments dinku na bani karfin gwiwa
Dama dukkan masoya wannan novel ina alfahari daku d'd'd'
? ? ?
? ? ? ? -My First Novel-

Not Edited

Kallonta Jalal yayi da mamaki ya kalli inda Ilham ta tarwatsa masa waya ya dawo da dubansa kanta
"Baze yiwu ba Yaya Jalal, kana wahal dani kana garani kawai dan nace inasonka amma kalli yadda wata take bayyana maka soyayyarta baka dau wani mataki ba amma ni kalli yadda kake wulakantani sau daya baka taba kallona da idon tausayiba
Meye laifina dan nace ina Sonka?"
Shi mamakima ya hana shi magana be ce mata kala ba ya durkusa yana tattara pieces din wayarasa, ya tattara ya nufi waje ze bata guri tazo ta sha gabansa
"Magana fa nake maka Yaya Jalal, let me tell you something wallahi kai nawane ni kadai babu wata Jaka data isa tayi takara dani wallahi kowace sena kauda ita gefe"
Hawayene ke fitowa daga Idonta wani irin kallon baki da hankali yayi mata ya kuma zagayeta da niyyar ya fita
Janyo shi tayi takuma tsayawa a gabansa ta kalleshi ido cikin ido cikin masifa tace
"Jalal baka isaba ina magana ka maidani mahaukaciya zaka tafi ka barni, I mean what I said wallahi, zan iya komai akan cinma burina, gara tun wuri ka gargadi zuciyarka kattayi gangancin fara soyayya kaidin nawane"
Bata rufe baki ba ya sauke mata maruka biyu masu kyau,
"Har kin isa ki tsaya a gabana kina gayamin maganganun dakika ga Dama, kin fasamin waya na kyaleki be isheki ba shine zaki tsaya a gabana kina gayamin abunda kika gadama ko yaushe ma nafara wasa dake, da kika iya tsayawa kina gayamin wannan haukan,"
"Wallahi kozaka kasheni na dena boye soyayyata a gareka koni ko ita wallahi"
Hannu yadaga ze kuma marinta
"Jalal meye haka kakeyi"
Jawwad ya karaso da sauri ya rike shi
"Haba Jawwad ba girmanka bane dukan mace, me tayi maka haka, kake dukanta"
Dawo da kallonsa yayi kan Ilham
"Ilham koma cikin Gida yi hakuri banni da shi tashi kikoma Gida"
Wani mugun kallo tayiwa Jawwad a ranta tace munafiki ai kasan komai amma a zahiri ta mike ta nufi cikin Gida tana kuka
"Haba Jalal me kayi hakane abunda kakewa Ilham yafara yawa gaskiya, koba komai kanwarka ce kuma mace ce, kadena dukanta hakan baze canza komai ba Fa"
Nunawa Jawwad wayarsa yayi
"Kalli abunda tayimin be isheta ba, ta tsaya a gabana tanamin hauka"
"Dukda haka kadinga hakuri, halin mata sekana hakuri, kasan shi so makahone waima tukuna, waima ya akayi wayarka taje hannunta har hakan tafaru?"
"Mtseww manta kawai"
Shine abunda Jalal ya fada kawai ya bi hanyar fita waje
Itakuwa Ilham tana zuwa cikin gida taga mummy a palour jikin mummy tafada tana kuka
"Ilham lafiyarki kuwa me akayi miki kike kuka,?"
"Mummy Yaya ne baya sona kwata? ya tsaneni, ni kadai nake sonshi mummy kiyi wani abu akai Dan Allah, zuciyata zata fashe"
Tausayinta ne Yakama mummy
"Is OK my dear, yi hakuri kidena kukan, Insha Allah Jalal bashi da matar data wuceki insha Allah, komai ze wuce"
"Mummy me nayiwa Yaya Jalal ne dabaya kaunata baya so naje inda yake"
"Bikiyi masa komai ba Ilham, haka dai halinsa yake na rashin son mutane, ya za ayi yace baya son mace kamarki, karya yakeyi, kidena kukan haka kar kanki yayi ciwo"
Haka mummy tai ta kwantarwa da Ilham Hankali

Maman Hanan ce hakimce akan kujera dauke da remote a hannunta, yayinda Hanan ta kwanta akan cinyarta tana kallon TV
Sallama Abdallah yayi yayan Hanan
Sannan yasamu guri ya zauna
"Da girman kujerarki mum barka da Gida"
Ya mutsa fuska tayi ta nisa
" "Yar uban waye ta dakarmin yarinya kunje kaida daddyn Ku amma ba wani mataki daya dauka, waye ubanta a garin nan"
Kallonta Abdallah yayi da mamaki
"Ohh I think dad has already closed this case, meyasa kike kokarin dawo da maganar nan, an sulhunta komai"
"Dalla yimin shiru, a gurina be wuce ba tambayarka kawai nayi Yar inace waye ubanta?"
Tai maganar cikin fushi
"Amm Mum Dan Allah kiyi hakuri zancen nan ya wuce wallahi kanwar abokina CE, kuma mum dinta tabada hakuri sosai, tundaga kano Wan babanta ya taho yau duk Dan subada hakuri fa, to mu suwaye daba zamu hakura ba"
"In kaga ma yimin nasihar tashi kabarmin parlour"
Be kuma cewa komaiba ya fice
Hanan ce takuma fashewa da kuka "mummy ciwon zafi yakemin kaina se ciwo yake wallahi ni ban hakura ba"
Tayi maganar tana kuka
"Yi shiru mana sannu, nima ba hakuran nayiba ai, ai jininki baze zuba a banza ba nasan matakin dazan dauka"

Abbane ya fito ze tafi, Jalila tafito da sauri daga dakinta tana kallonsa domin jin wani hukunci aka yanke akanta
Siyama ce tabiyo bayanta itama
"To se yadda ta yuwu, ummu Jalila ki hada mata kayanta in Allah ya kaimu sati me zuwa koni ko Jawwad zamuzo mu tafi da ita, tunda bata jin magana"
Abban Jawwad yayi maganar yana kallon Ummi
Kuma fashewa da kuka Jalila tayi
"Ummi nace na dena fa bazan kuma ba Dan Allah kiyi hakuri"
Girgiza kai Abba yayi
"A a senaga kindena din tukuna, a yanzu dai ban yaddaba zuwa sati me zuwa insha Allah in kin canza halinki, shikenan ta fiya kano bayan zuba"
Gyada kai tayi tana goge hawaye itakam Ummi banza tayi mata taki kulata
"Abba insha Allah bazata karaba ta dena"
Cewar siyama
"Anya kuwa wannan kawar taki batta kawai akwai rashin ji"
Abba yafada yana nuna Jalila
Haka Jalila ta cigaba da kuka tana magiya akan suyi hakuri
Abba yayi musu sallama ya koma, kano yayinda still Ummi taki kula Jalila
Abun duniya ya ishi Jalila, Jalila tayi trying lambar Jawwad har tagaji amma akashe
"Haba Yaya Jawwad kaima Fushin kake dani haka, shikenan kowa ya tsaneni"
Haka dai Jalila ta cigaba da sake? aranta tana kuka

Hannah ce take ta trying lambar Jalal taki shiga tayi messages din ba adadi amma shiru
Layin Jeje ta kira
"Da girman kujerarki, gimbiya sarautar mata farar mace Alkyabbar mata, Zara acikin mata, daya tamkar da goma, tauraruwa me wutsiya ganinki ba alheri ba"
Murmushi Hannah tayi da jin wannan kirari da jeje yake mata
"Jeje ya akayi ne dazu muna cikin waya da Jalal naji ta dauke nayi trying tun dazu wayar bata shiga"
"Wow har ya fara yadda ya amsa wayarki kice tarkon ya fara kamashi"
"Ina fa da sauran aiki Ja wallahi, shammatarsa kawai nake naji ya daga wayar, yanzu dai yana ina ne?"
"Nima bansan inda yake ba rabona dashi tun last week, wannan mayen ya hanashi zuwa inda nake"
"Allah sarki simple dashi abokin nasa da akansa zanyi aikin nan da yanzu nakusa nasara, shikam taurin Kaine dashi"
Dariya jeje yayi
"Lallai baki San Jawwad ba zahirinsa kika gani, tsawon shekaru shiya hana aikinmu tafiya yadda ya kamata anyi masa barazanar amma, bashi da niyyar hakura duk abunda kikayiwa Jalal, kai tsaye kamar kinyiwa zuciyar Jawwad ne"
"Tab amma gaskiya yana kaunar JALAL, yanzu dai ka bincikomin inda Jalal yake, inason zuwa"
"To bari in jarraba"

Jawwad ne yabi bayan Jalal
"Yanzu dai kayi hakuri zomuje se a siyo wata wayar"
Bece komaiba yabi Jawwad sukaje suka siyo sabon waya, yabada wadda Ilham ta tarwatsa aka gyara, domin ya kwashe abubuwansa masu mahimmanci na kan wayar, wayar ta daku, Dan karfinta Ilham tasaka ta buga wayar,
? Jawwad ne ya dakko wayarsa don kiran Abba yaji koya dawo, seyaga wayar tasa akashe, be tunanin komaiba ya kunnata Abba ya kira yaji ko yakaraso, yace masa yana hanya.
Ya kashe kiran kenan message ya shigo wayarsa
Jalila ce ta turomasa message,
?? "Yaya kaima fushi kake dani?
? ?? Shikenan kowa yatsaneni
? ?? Abba yayi fushi, Ummi ta? ? ?
? ?? Dena kulani, Dan Allah kai
? ? ? Kar kayi fushi dani"
"Allah sarki sisyna ni Sam bana fushi dake"
Jawwad yai maganar a fili Jalal da yake driving ya Dan kalleshi ya basar
Jawwad ne yaketa kokarin kiran Jalila amma taki dagawa, be fushiba haka ya dinga kiranta har daga karshe ta daga tana daga wayar sautin kukanta yaji
"Yaya? Jawwad kaima fushi kake dani ko? Nakiraka dazu ka daga kaki magana daga baya kuma ka kashe wayarka"
"Nidin Jalila? Ni na isa in miki haka sedai matsalar network, a duniya banga laifin dazakiyi min in ki daga

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login