Showing 42001 words to 45000 words out of 129540 words

Chapter 15 - ABDUL JALAL Hausa Novel

08 Oct 2024

6680

gari da safe Jalila ta shirya ta tafi makaranta, Daren ranar addu a ta kwana? tanayi
Ba wai Allah ya sassauta fitinar da ta dakko ba, se dai Allah yasa kar Ummi ta korata kano
? A hanyar makaranta ta hadu da yayan lubabatu data tsokana ranar akayi Sa a ya ganeta, ta Ganshi sarai amma taki guduwa tacigaba da tafiya a hankali,
Zuwa yayi ya sha gabanta
"Ke karamar Mara mutunci ni kika zaga ranan ko waike Yar iska"
"Wallahi kasake ka tabani sena tara maka jama'a nace zaka lalata ni shekara goma sha hudu ce zakayi a gidan yari bayawa"
"Au tunaninki barazanar ki zata hanani in casaki senaga uban da ya tsaya miki"
"Bari kaji in gaya maka idan kana shan kwayarka tagaya maka karya kayiwa mutane hauka, to karkayi gangancin gwada kwayarka akaina,
Dan wallahi sena kulla maka sharrin dazaka kare rayuwarka a prison"
Kafin kace meye wannan Jalila ta ware murya ta fara ihu iya karfinta hankalin jama'a ne yafara dawowa Kansu ana fara taruwa ta silale ta gudu ta nufi makaranta
Abunda yasa ta guduma gudun kar takuma shiga wata cakwakiyar bata fita daga wadda take ciki ba ga Ummi tace zata maida ita gidan su Jawwad da setasaka anmasa duka
? Tana zuwa ajinsu ta tafi taje gurin zamanta ta hakimce ba tareda ta kula kowaba, "Allah ya biya Queen J Dama tunda yarinyar nan tazo kanta yake hayaki, se wani takama take, malamai ma kaman wani tsoronta sukeji segashi kinyi maganinta"
Haka dai seatmates dinta suka dinga zigata ita dai Jalila hankalinta yana kan batun Ummi
Bayan anfita break an dawo ba dadewa Hanan ta shigo ajin tana kallon kowa a wulakance ga malami a ajin amma Hanan batabi takan malamin ba ta tako
Tazo gaban Jalila
"Sannu uwar rashin kunya, dama na miki alkawarin kawo karshen rashin kunyarki,
Yau zakigane kin taba Yar gidan bullet kizo office bullet yazo da kansa"
"Amma kin bani kunya da kikazo da bullet kawai, ai na dauka barikin zaki dakko gaba daya su taho da egwa yadda in sun markadeni baza ageneniba dan dai bullet, ai bullet yayi kadan aga bayana dashi"
Jalila takarasa maganar hade da tsaki"nonsense "
Mikewa Jalila tayi tai gaba ta wuce hanan
Wato Jalila Yar bala'ice babu alamar risina a tare da ita tun tasowar Hanan take taka Wanda taga dama take jefa tsoro a zukatan duk Wanda yai kuskuren shiga hanyarta saboda takamar ubanta wani ne amma yau ta hadu da wadda tafita rashin mutunci
Haka ta bi bayan Jalila suna zuwa harabar ofishin director Jalila sukayi clashing da malama ramatu aikuwa Jalila ta tsaya
"Ita wutar munafiki ko tana karkashin jahannama ne,
Kekam baki dace da malamar makaranta me bada tarbiyya ba kema kina bukatar me baki"
Jalila ta gayawa malama ramatu sannan tai gaba abinta

Tana shiga office din director ta tarar da mutane ba Wanda ta kula kuma bata kalli suwaye a ciki ba ta shige

Share please
More comments more typing.............

=؊??=؊??=؊??=؊??=؊??
[8/31, 8:26 AM] Safiyya:
? ? _ABDUL? JALAL_
? ? ? ? ?? (2020)

? ? ? _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
? ? (Daddy's girl)

? ? ? ? ? ? ? ?PAGE-? 20&21

PART 1

? _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,? ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta? wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar

07063065680
Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din


I want comments not stickers or just thanks=?"?=?"?=?"?=?"?
Your comments give me courage

? ? ?
? ? ? ? -My First Novel-

"Meyasa kikace kar ya sha"
"Nidai kawai kahana shi sha kar ya sha tea din nan"
Jawwad ji yayi gaba daya ta firgice masa
"Amma meyasa kikace kar ya sha?"
Sekuma tarasa mezata ce masa
"Am...emm.. Idan ya sha ze iya yin amai gara kaimasa tofi na ayoyin Qurani ya sha kafin kabashi abinci in Bahaka ba, ze iya bashi matsala eh..m.. In...nima malaminmu ne yafada mana a Islamiyya"
? Da Jawwad yaji haka da sauri yasa hannu ya karbi cup din tea
Daga hannun Jalal
Jalal ne ya kalleshi
"Meye haka kuma?"
"Kanwarka tace karka sha tukuna, Dan huta ina zuwa"
"Kaga ni bani yunwa fa nakeji yaushe zan tsaya biye maka yarinya Karama tana juya ka"
ya yunkura ze karbi cup din tea daga hannun Jawwad yaji kansa ya kara nauyi dan haka ya koma ya zauna yana jujjuya kan
"Sannu bros"
Jinjina kai kawai Jalal yayi
Kamar yadda Jalila ta gayawa Jawwad yaje fridge ya dakko ruwa ya karanta ayoyin Qurani ya busa masa a ruwan yazo ya tsiyayo a cup ya bashi
Hannu yasa ya karba ya shanye ya ajiye kofin, ko minti biyar beyi da shan ruwan ba ya mike ya???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? tafi bandaki ya dinga wani irin bakin amai
Jawwad ne ya bishi yana masa sannu ya kwashi mintuna yana amayar da wani bakin abu
Seda Jawwad ya Dan tsorata

"Jalal mutafi Asibiti your condition is getting worst jin ciwon nan nake kaman a jikina"
Ture Jawwad yayi ya tafi ya kwanta gaba daya jikinsa ya mutu ga wani mugun Jiri dayakeyi
Jawwad ya biyo bayansa, Dan kura masa ido yayi yaga jijiyoyin kan Jalal duk sun mike fuskarsa tayi Ja
Gefen gadon ya zo ya zauna yasa hannunsa akan Jalal yana masa karatun Qurani a hankali
Wani baccin wahala ne ya kuma awon gaba da Jalal abun mamaki a cikin baccinsa ya dinga Jin sautin karatun Jalila Wanda ya dinga jin nutsuwa tana saukar masa

Jawwad ne ya mike ya nufi gida don tafiya masallaci lokacin salla la'asar yafara gabatowa
Cikin Gida ya shiga ya tarar da Nana tana video game maama kuma ta Dan kwanta a akan kujera tana kallon Nana
Sallama yayi suka amsa gaba daya
"Maama sannu da Gida"
"Yawwa ya jikin Jalal din"?
"Da sauki maama"
"Allah ya sawwake"
"Ameen"
Ya amsa
"Nana babu abunda kika iya se shirme,
Jalila tana can tayi abun arziki ke kam shirirtarki ta fiye miki"
Attention dinta gaba daya Nana ta bashi
"Allah Yaya me Jalilan tayi"
"Gasar karatun Qurani sukaje abuja jiya, tazo na biyu, amma se rikici takewa Ummi wai ita na daya take so"
"Dan Allah Yaya dagaske amma naji dadi, ga fitina ga kwanya Allah sarki Jalila Allah yakara hasken makaranta"
"Ameen kema se ki dage kidena wannan shirmen"
Duk abun nan maama bata ce uffan ba
? "Amma shine ko ta gayamin amma kai ta gaya maka dani take zancen"
Nana tafada tana Dan bata rai
"Aini kullum se munyi waya da ita"
"Ai Yaya dole muje Kaduna we have to celebrate the victory of my great sister bari Abba ya dawo"
Nana tai maganar tana murmushi
?? "Karki fara, kwata? yaushe ta bar gidan nan kike zancen, wani zakuje to babu inda zaku, nasake naji kin tambayi abbanku zakije sena bata miki rai sha? kawai,
Kaikuma naga zakewarka akan yarinyar nan yafara yawa ka kiyayeni? Jawwad in bahakaba daga kai har ita senaci mutuncinku,"
Maama ce tayi wannan maganar cikin fada da fushi gaba daya suka bita da kallo
Ajiyar zuciya Jawwad yayi ya dan girgiza kai
"Allah yabaki hakuri ya huci zuciyarki za a kiyaye insha Allah"
Ya Fita yabar parlour itakuwa Nana zunbura baki tayi itama ta barwa maama parlour
"Lallai in ban dageba maganar Yaya mairo na shirin zama gaskiya zakuci kaniyarku sena raba Ku da yarinyar nan"

Se bayan magariba Jalal ya kuma ta shi wannan karon seya jishi sakayau babu ciwon kan se rashin kwarin jiki
Wanka yaje yayi ya rama wasu daga cikin sallolin dabe ba ya bar wasu Jeje ya kira a waya yaji yana ina yagaya masa
Kaya ya canza ya dauki motarsa ya bar gidan kai tsaye club din da yake haduwa da Jeje ya tafi kamar kullum yauma club din cike yake da "ya'yan da suka rasa mafadi maza da mata kowa na sharholiyarsa matan nan wasu sunyi shiga half nicked wasu na rawa yayinda wasu suka kama daki suna shagalinsu
Jeje naganinsa ya washe baki yana masa sannu da zuwa gaisawa sukayi Jalal yasamu guri ya zauna Jeje ya tafi kawo masa mutuniyar tasa wato giya
Duk gigin matan gurin nan basa zuwa inda Jalal yake saboda sun San halinsa basa gabansa shidai ze sha giya yayi mankas amma be yadda yayi zina ba
Jeje ne yasamu guri ya kira Hanna
" kina ina ne?"
"Ina Gida mana"
Hanna taba shi amsa
"Muna tare da mutuminki fa yanzu haka"
"Dan Allah dagaske dazu Dana kirashi abokinsa yace min bashi da lafiya"
"Ke dalla rabu da wannan sakaran kilma karya yakeyi"
"I wish in samu dama in fito yanzu inzo in ganshi"
"Ke rufamin asiri yanzu ma abu zan karbo masa ke dai kicigaba da kokari"
"Karka damu kaman yazo hannuna ya gama ne"
"That's good seda safe"
Sukayi sallama da jeje ya tafi bar domin karbo giya
Bayan ya karbo ne yazo ya nemi guri ya zauna ya Tarar da Jalal yanata salansa yana bawa sama hayaki tabarsa kawai yake sha
Jeje ne ya tsiyayawa Jalal giya a cup ya tura masa gabansa
Wayar Jalal ce ta fara ringing ya Dakota seyaga unknown number seyaki dagawa ya cigaba da abunda yake haka wayar taita ringing
"Maza wayarka fa ake kira"
Sedayaja wasu seconds sannan yabawa Jeje amsa
"Nagani"
Dan tabe baki Jeje yayi yacigaba da shan giyarsa
Messages ne suka dinga shigowa wayarsa
Tsaki yayi ya dau wayar yafara duba messages din
? ? ?? "Haba fitilar rayuwata? ? ? ?? meyasa zakamin rowa, just want hear your sweet voice
I really care for u, bazan iya bacci ba in banji muryarka ba love u baby
? ? ? ?? From your lovely bae"

Ire? wannan messages dinne ake ta turomasa tsaki yayi sannan ya danyi shiru yana zancen zuci anya kuwa Ilham ce take turo masa wannan messages din, wacece ta kira dazu sukayi waya da Jawwad?
Ya tambayi kansa still wayar ce tafara ringing da Sauri Jalal ya yinkurin dagawa domin yiwa ko wacece rashin mutunci seyaga Jawwad ne yake kiransa dan zaro ido yayi sannan ya daga wayar
"Jalal kana ina?"
Jawwad ya tambayeshi
"Na dan fitane"
"Hmmm daga samun saukinka harka fita ko ka tafi gurin Wanda sukafi kowa mutumci a idonka shikenan seda safe"
Jawwad ya katse kiran mikewa Jalal yayi yadauki mukullan motarsa ze fice
Jeje ya kalleshi
"Ya dai ba dai tafiya zakayi ba?"
"Tafiya zanyi mana dama bana jin dadi Jawwad yaje bana nan naji ransa a bace dole in tafi inje ba shi hakuri"
Wani bakin cikine ya tokarewa jeje ji yayi kamar ya rufe Jalal da duka,
Yadda Jalal baya son bacin ran Jawwad da iyayensa yakewa haka da ya dace
Anya ba asiri Jawwad yayiwa Jalal ba jeje yayi maganar a zuciyarsa
Shikam Jalal besan yanayi ba dan tuni ya bar gurin

Ilham ce ke ta safa da marwa a dakinta tare da fatan Jalal ya sha tea din nan da se tafi kowa farin ciki gajiya tayi da tunane? dan haka ta yanke shawarar ta dan fita taje gurin Nana
A daki ta tarar da Nana suna waya da Jalila dan haka ta nemi guri ta zauna daga baya data fuskanci Nana da Jalila take waya seta wani hade rai
"Naji kaman kinyi bakuwa se anjima"
Jalila tayi maganar
"Ba wata bakuwa ceba Ilham ce fa"
"Hh kice Juliet ce, to kice mata a dai dinga sassauta masa adena wahalar dashi"
Dariya Nana tayi tare da fadin
"To Ilham kinji dai sakon Jalila"
Tsaki Ilham tayi dan yanzu ta kara tsanar Jalila mussaman akan abunda yafaru shekaran jiya Jalal ya dinga zaginta

"Kinga ni na tafi nazo gurinki kina rainamin hankali"
Ilham tai maganar tana mikewa
Nana tayi saurin rikota tare da kashe wayar
"Ke bakisan wasa ba indai Jalila ce wataran se ta saki kuka"
Da Sauri Ilham ta kalleta "kamar ya?"
"Eh mana ai ita yayinda taga ba kyason abu to lokacin zata dinga yimiki dan tabaki haushi"
"Wallahi nafi karfin kamata wata Jalila ta Sani kuka"
"A'a dai yadda kike da saurin fushin nan Lokacin daza tasaki kukan ma baki Sani ba
Amma abunda yake burgeni da ita shine akwai kwanya musabaka sukaje Abuja fa tazo ta biyu"
"Ai nasani"
Ilham tabata amsa
"Ya akayi kika Sani?"
"Ke ni mu bar wannan zancen Nana damuwata kullum karuwa take akan Yaya Jalal amma gani nake ba wadda tsana kamar ni"
Ta karasa maganar cike da damuwa
Nana ta dafa ta
"Ilham ba tsanarki yai ba kinsan shi kawai miskiline baya son shiga sabgar mata mazan ma kinga ba kowa yake kulawa ba Sam baya son mutane watakila fa a ransa yana sonki, inaga Ku da haka naku labarin soyayyar ze fara"
Nana tai maganar cike da kwarin gwiwa
"Dagaske Nana kumafa se hakan yakasance ko?"
"Sosai makuwa wannan ai ba abun mamaki bane"
"Shiyasa kike burgeni Nana bakiji yadda hankalina ya dan kwanta da maganganun nan nakiba"
"Ai irin miskilan mutanen nan abune mawuyaci kagane inda sukasa gaba da wuri karkiyi mamaki sonki yana nan fal a zuciyarsa"
"Allah yasa haka Nana"
"Ai hakanne ma insha Allah Mrs. Jalal to be"
Haka Nana ta dinga ziga Ilham tana kwantar mata da hankali Akan abunda bata da tabbas akai

Jalila tana daki tana gugar uniform zasu koma makarantar boko Ummi kuma tayi bakuwa
Jalila taji kaman ana harbe? a waje da sauri ta fito tsakar Gida
"Ummi bakiji karan bindiga ba"
Bakuwar Ummi tace
"Wani captain ne na sojoji yake tarewa a anguwar nan bakiga wani kerarren Gida ba da aka gama kwanan nan ai nasane wallahi gidan ya keru kaman a kasar waje "
"To shine kuma za a zo a cikamana kunne da karar bindiga saboda shirme, ni gidan ma nakeso in gani inga iya keruwarsa"
"Allah yabaki sa'a kije Neman magana duk yadda zasuyi dake se dai suyi dan ba abunda zan iya indai sojojine zaki yabawa aya zakinta"
Ummi tai maganar cikin bacin rai shiru Jalila tayi ta koma daki

Jawwad ne yakema Jalal fada akan fitar da yayi daga samun saukinsa
Yayinda Jalal ke bashi hakuri
"Ai gani dai na dawo ban zauna a can ba hankalinka ya kwanta"
"Bawani hankalina ya kwanta kabata min raine ka dinga sassautawa kanka wannan abubuwan dakake durawa cikinka"
Hade rai Jalal yayi "naji kuma ina nace kayi hakuri "
"Haka ka iya ai saura ka kara fita"
Jawwad yayi maganar da alamun gargadi
Dariya Jalal yayi
"Sorry yayana bazan kuma fitaba a yau insha Allah"
Murmushi Jawwad yayi sannan ya fita
Bayan fitar Jawwad
Jalal ya saka wayarsa a caji ya mike yatafi cikin Gida part din daddy yaje suka sha hira
Cikin hikima daddyn yake masa nasiha
"Daddy nima bana jin dadin abunda nake amma kacigaba dayimin addu'a wataran zakaga kaman banyiba"
"Nima ina fatan hakan yaron kirki"
Se kusan shabiyundare Jalal ya fito daga part din daddy shima mummy ce taje part din daddy shiyasa ya fito
Ilham tana kwance akan kijerun parlour tana kallon Bollywood
Waiwayawa tayi taga Jalal
"Sannu Yaya ya jiki?"
"Da sauki"
Rannan a hade Yabata amsa ya fice
Yana zuwa dakinsa ya tarar missed calls kusan takwas
Da wannan unknown number din
Tsaki yayi yaje yayi wanka yazo ya nemi gurin kwanciya ya dakko wayarsa hotonsa ne da Jawwad akan wallpaper dinsa kallon hoton yayi sunyi kyau a hoton matuka murmushi yayi ze bude what's app dinsa message ya shigo wayarsa budewa yayi

? ? "Haba baby at least ko sau daya yakamata ka dau wayata kasan kuwa yadda zuciya ta takeyi I feel u in my every heart beat, nayi missing innocent face dinka gashi kaki yadda ko muryarka inji help me baeb na damu da kai
? ? ? ? ?? From ur lovely Bae"
"Wai wannan wace irin Jaraba ce haka, wace ce wannan take Neman yimasa kutse haka a cikin rayuwarsa shi baze iya wannan shirmen ba wannan soyayyar duk haukane da bata lokaci"
Yana cikin wannan mitar ne wayarsa kuma takama ringing unknown number din ce dai
Dagawa yayi a fusace
"Waike wace irin mahaukaciyace karfe nawa yanzu nibana wannan haukan ki kyaleni tun kafin ta kaimu ga bata miki rai"
? ? ? ? ?? "Wow komai naka birgeni? ?? yake baby jin muryan nan taka kawai ta isheni bacci me dadi,
Mark you ba abunda zakamin Wanda ze batamin rai
Love u.......
Katse wayar yayi ya kasheta gaba daya ya jefa wayar kasa nonsense yafada a hankali

Washe gari bayan sallar asuba Ummi taga Jalila ta koma bacci
" ke baby ba ankoma school ba kwana biyu da komawa amma kina nade a Gida tashi ki shirya yau makaranra zaki tafi"
"Ummi bangama shiryawa ba in nagama zan koma"
"Aikuwa sekin koma yau din nan"
"Ummi bani da socks fa, kuma ni sekin canzamin school bag zan koma"
"Kibari inzo gurin nan baki tashi kinyi shirin makaranta ba ni da kene"
Ummi ta fita daga dakin Ummi na fita Jalila tacigaba da baccinta har kusan karfe bakawai Ummi tazaci Jalila ta tashi amma tana zuwa ta tarar da ita a cikin bargo
Ran ummjne ya baci ta yaye bargon ta Dala mata duka tashi dan kaniyarki dama baki tashi ba tashi kisa uniform kitafi
"Ummi dan Allah kiyi hakuri,? banga socks dina bane"
Girgiza kai Ummi tayi
"Allah ka shiryamin yarinyar nan, ai tunda baki gadama ba nasan bazakiba zakiga tsiya"
Wunin ranar Sam Ummi taki kula Jalila
Ta dinga binta tana bata hakuri tana mata magiyar ta saimata wata jakar daga karshe seda Ummi ta bata kudin Jaka da socks din hankalinta ya kwanta
Amma Ummi tace bazata fita ba seda yamma

Washe gari se bayan sallar la'asar sannan Jalal ya kunna wayarsa amma yana kunnawa sakonine sukacika masa waya wasu na bin wasu
"Wannan wane irin Jaraba ce haka"
Sakonta na karshe ya duba? "Baby in baka bude wayarka? ? ba zanzo har inda kake, tun safe nakasa nutsuwa ko har yanzu baka da lafiya ne?
Na damu da kai baby
? ? ? ?? From your lovely Bae"

"Wannan wace irin Jarababbiya ce da take uzzurawa rayuwata ne"
Yana cikin wannan tunanin Sega Ilham ta shigo da kayan abinci ta samu guri ta ajiye
"Yaya ga abinci inji mummy
Harta mike zata fita ya kira sunanta
"Ilham"
"Na'am"
"Zo nan" seda cikinta yayi kara gabanta ya fadi Allah yasa ba wani abun nayi masa ba jiki a sanyaye ta nufi inda yake guri ya nuna mata kusa dashi ta zauna wayarsa ya dakko ya shiga messages din nan ya nunamata
"Ke kike turomin wannan shirmen ko?"
Gabanta ne yafadi ita ba tuhumar dayake matane ta sata faduwar gaba ba se fargabar wace wannan take shirin yi mata kutse
"Tambayarki fa nake"
Jiki a sanyaye ta daga kai ta kalleshi
"Bani bace ba"
Jawwad ne ya shigo
"Inyee yau zumunci ake jine Yaya da kanwa"
Basu kulashiba ya karasa ciki ya zauna yaga ran Jalal a bace Yana ma Ilham magana

"To waye?"
Jalal Ya tambayeta
"Ya za ayi in sani yaya, nidai nasan bani bace"
Tabashi amsa

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login