Showing 117001 words to 120000 words out of 129540 words

Chapter 40 - ABDUL JALAL Hausa Novel

08 Oct 2024

6667

suka shirya masa, nasan kwana zasuyi shan giya, nace kar yaje kuma yana neman yayi fushi, seyaje yai tayi ai, am tired da halin Jalal"
Sosai taji tausayin yayan nata, taga kokarinsa ma tsawon wannan lokacin yana tareda Jalal, duk da miyagun halayensa, ga shi da wuyar sha'ani amma haka Jawwad yake tare dashi, kuma tasan wannan fushin na dan lokacine, dole se daya ya nemi daya, ta numfasa tace
"Yaya Jawwad ai be kamata kayi fushi ba fa, tunani yakamata kayi, tsawon shekaru suna tareda shi basu taba cewa zasu shiryamasa birthday ba se wannan karon, kuma ma wai se tsakiyar dare zasu fara, baka tunanin wani abun suka shirya akansa? Bakayi tunanin suna da manufar yin hakan ba? Kn kayi fushi kace yaje yaitayi, kaga sunyi galaba zasu kara janyeshi, shikenan yazama? nasu gabadaya"
Shiru Jawwad yai yana kallon Jalila
Taci gaba da cewa "Kayi tunani yaya na, dan uwanka ne fa, u have to think"
Ajiyar zuciya yayi "Hakane baby kema kinyi magana, amma yanzu me yakamata inyi"
Jalila aranta tace yawwa, nima ga dama ta samu,
A fili tace, "Yaya dole ka shiga cikin lamarin nan, kawai ka yadda da maganar birthday din nan, ka lallabashi kasashi a maida partyn kaman daga karfe ta kwas zuwa goma, sannan dolenka ka halarci gurin domin sakamasa ido, in takama har abokanan ku da yanuwa ku gayyata, hakan ze hana faruwar wasu abubuwan, karfe goma nayi, ka janyeshi daga gurin, yanzu kayi hakuri ka sakko, har ya gaya maka shirye2 da sukeyi, kaima seka san shirin dazakayi, amma inka barshi ya tafi shi kadai jikina na bani akwai dalilin dayasa suka shirya hakan, sun san babu wani dan uwansa daze yadda ya bishi guri irin wannan karfe shabiyun dare"
Murmushi Jawwad yayi, tareda yiwa Jalila salute
"Gaskiya baby kina da tunani me zurfi, hankalina be kai kan hakan ba ni, gaskiya nagode, zan jarraba insha Allah"
Murmushi Jalila tayi
"nifa aikoni akayi, Abba yace kazo yanzu"
"To shikenan ina zuwa"
? A ranar bayan Jawwad yaje kiran Abba, ya je yanemi Jalal suka shirya, yace masa ya yadda, zeje birthday dinsa amma gaskiya zasu gayyaci mutane, dan haka sedai a canza lokacin daga shabiyun dare zuwa karfe takwas, Jalal yace ya yadda.
?? "Jeje wannan ce dama ta karshe dazan baka, a wannan karon banason asamu kuskure, dukda tsawon shekarun nan kayi aiki tareda ni, kamin duk abunda nake bukata to wannan karon, sonake komai ya kare, sonake a wannan lokacin komai yazo karshe, karka bari wannan shirin ya rushe, "
" Oga kb baka da matsala, munyi iya kokarinmu gurin ganin hanyoyin dazamubi domin gabatar da aikin cikin shiri, burinka ze cika, a wannan ranar zamuyi yadda zamuyi muga mun karasa wargaza rayuwarsa, "
Wanda aka kira da oga KB ya gyara tsayuwa yai ajiyar zuciya
" shikenan ina jira zan saka ido inga kokarin ka, a wannan karon, aje acigaba da shiri,"
" Shikenan oga, wannan karon komai zezo karshe"
Daga haka sukayi sallama,
Hannah na gaban dressing mirror tana kwalliya, Jeje ya kirata, seda ya kira sau uku tana kallon wayar sannan ta dauka
"Hannah ina kika shiga ne inata kiran wayarki, ya za ayi mu hadu ne?"
"mu hadu kuma, akwai matsala ne?"
"eh haduwar tamu tanada mahimmanci sosai, akan shirunmune, yanzu haka daga gurin oga KB nake, akwai bukatar mu hadu"
"To zanzo, muhadu inda muka saba"
"To shikenan sekinzo"
? ? ? ??
Ilham se safa da marwa take, a cikin dakinta, ta rasa inda maganganun Jalila suka dosa, tace ita ba son Jalal take ba, amma itama tanada kuduri akansa, kuma inyaci karo da nawa, to tabbas zata rusa nawa, koda tazo nan a tunaninta seda ta zare ido, ta rusa nawa burin saboda nata muradin, to ko ta san menene shirina ne, to amma tayaya zata sani bayan ko Nana bata saniba,
Dakko wayarta tayi, zata kira yaseera, sekuma ta fasa, dole in dau mataki, bazanyi wahalar banza tsawon shekaru ina kallo wata sakarya ta rusamin shirina ba, gara tun yanzu in rusata ita danata shirin, ta mike da sauri ta nufi dakin mummy, tana zuwa ta tura kofar dakin, ta sameta tana waya, taje kusa da ita ta zauna, tana jiranta tagama,
Seda mummy tagama waya, sannan ta kalli Ilham tace
"Ilham ya akayine, naganki wani iri haka kaman mara lafiya"
Fashewa tayi da kuka, ta fada kan cinyar mummy
"Mummy wallahi nakusa mutuwa, in har yaya Jalal be aureni ba, zan iya mutuwa, Mummy ina sonshi, dan Allah asaka ranar aurenmu,"
"Yi shiru kiyi hakuri, kinji nima naga kamatar yin hakan, kila in kika aureshi ma ya shiryu sanadin haka, yanzu kidena kuka, bari daddynku ya dawo, muga me yakamata ayi, amma karki kuma zance zaki mutu saboda shi, aini na miki alkawari, indai ina raye Jalal shine mijinki, indai nina haifeshi baze taba auren wata mace inba keba, kidena kukan nan haka ya isa"
Wata irin nannauyar ajiyar zuciya Ilham tayi, tareda yin murmushi a boye, a fili kuma tace
"dan Allah mummy asaka da wuri, ina tsoron ya auri wata baniba,"
"ki kwantar da hankalinki, shi kinga alamar ma zeyi soyayya da wata, ko kina tunanin akwai wadda zata aureshi a haka, aini kingama min komai da kikeson Jalal a haka, dan haka bari daddyn sa ya dawo, zamuga yaushe yakamata asaka"
Ilham ta riko hannun mummy,
"Nagode sosai, mummy"
"bakomai, kidena kuka"
?? Hannah zaune akan fararen kujerun dake? gurin, fuskarta dauke da wani arnen glass dayake barazanar cinye fiye da rabin fuskarta, ga barima da tasaka a akan dogon hancinta, se tauna chew gum take, tana fuskantar Jeje,
"Hanna daga gurin oga KB nake, kuma yace lallai wannan itace damarmu ta karshe akan Jalal, yazama dole muyi yadda zamuyi mukammala aikin nan," hannah ta dan nisa ta cire glass din fuskarta, sannan tace
"Idan ban mantaba shekaru uku zuwa hudu muna aikin nan, duj wani salon makirci, da kisisina ba wanda banyi ba, tunda nafara bariki, bantaba ganin dan bala'i ba kamar Jalal, ban taba haduwa da mutum me azabar taurin kai ba kamar Jalal, babbar nasarar dana samu a rayuwa akansa shine, a labarin daka bani, bayan sauyawar Jalal, ina cikin jerin matan daya sake dasu, har yake shiga harkata, amma naiyi iya kokarina alakarmu ta wuce haka amma yaki yadda, ni yanzu bani da wata dabara,
Nagama nawa, bansan meye shirinka ba"
"Hakane Hannah, nasan kinyi mana aiki, kinyi iya yinki kinmana kokari, abaya a koda yaushe ina galaba akan sa amma yan shekarun nan, nafara ganin sauyi a tareda shi, koda nagama aikina akan Jalal, sena tabattar da nayiwa Jawwad babbar illa shima, saboda tsawon wannan shekarun shiya hana cikar burin mu, Jalal yanajin maganar Jawwad fiye data uwar data haifeshi, wadda ita ta haddasa komai, "
" Baka ganin ina aka cutar da Jawwad ba a masa adalci ba, shi meye nasa aciki "
" yana da laifi Hanna kuma dole ya karbi hukunci, yanzu ki tsaya ki saurareni"
"ina jinka"
"a gurin birthday din damuka shirya masa komai ze kare," hannah ta kalleshi sannan tace
"bangane mekake nufi ba"
"zaki gane ne Hannah, nagama shirya komai, kinsan meze faru?"
"No seka fada"
"kamar yadda muka shirya, shabiyun dare zamu fara gabatar da taron, a cikin cake din dazamu bawa Jalal ke zakiyi wannan aikin, zaki saka kwaya, a dai2 inda za a bashi, saboda sonake ya bugu ya fita hankalinsa yadda baze iya komai ba, za sakama a lemon da zs sha, da zarar ya fita hayyacinsa zamu dauke shi, mu kaishi wani gurin, kekuma zaki gabatar da aikinki"
Dan tsaki Hannah tayi
"Ni gaskiya ba a haka naso aikin yazo ba"
"to ya za ayi se hakuri, tunda shi dan taurin kaine, zamu nuna masa munfishi iya bariki"
Wayarsa ce tafara ringing, jeje ya kalli Hannah "Dan halak shike kirana"
Tai murmushi tace
"Pick it"
Dagawa yayi yasa a hands free
"Allah ya temaki, mazaje, namijin duniya sha gwagwarmaya, namjin damusa bakason raini"? Jalal yace
"Kai Jeje ya isa haka, magana nakeson yi maka akan maganar partyn nan"
"ok inajinka"
"Munyi magana da Jawwad, dan haka dole a maida shi eight Jawwad yace baya son ya kai karfe shabiyu in bahakaba baze attending ba, dan haka ina so amaida shi eight pm, saboda inason Jawwad ya kasance a gurin"
What!!!!!!! Jeje yafada da karfi yana mikewa tsaye

Share please
More Comments More typing.............................

Akodayaushe kuna raina masoya comments dinku ke bani karfin gwiwa da sani nishadi, amma in naga ba kwa comments sosai, se inji kamar inkoma posting duk sati =??=??=??=??=??
Ina godiya da adduoi Allah yabar kauna




=؊??=؊??=؊??=؊??=؊??
[9/24, 8:35 PM] Ayshercool:
? ? _ABDUL? JALAL_

? ? ? _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
? ? (Daddy's girl)

? ? ? ? ? ? ? ?PAGE-? 50
PART 1

? _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,? ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.

A har kullum ina jinjina da godiya ga masoya wannan novel nawa, comments dinku da addu oinku ina jin dainsu matuka, ina godiya kwarai dagaske,
Domin sharhi, gyara, kokuma shawara a nemeni ta what's app akan wannan lambar wayar
07063065680

? ? ? ? ? ? ?? _My First Novel _

Jalal yace "Lafiya naji kana wani what, ko baka gane menace bane?"
"Amma meyasa zakayi manaa haka Jalal, mun riga mungama shirya komai, sannan kace wai se a maida shi eight, haba Jalal dan Allah, dolene se Jawwad yaje gurin, mene a ciki dan munyi iyamu da abokanmu yanzu....
" Kaga Jeje ba dole ai bani na rokeku ba dama tun farko dan haka, inbazaku canza lokacin ba bazan zo ba" yana zuwa nan ya kashe wayarsa, jeje ya daki tabur ya zuba ashar,
"kingani ko Hannah wallahi dole a hukunta Jawwad, a koda yaushe shi ke bata mana shiri,"
Hannah tace
"Kaga kaifa fushi banaka bane a yanzu, ka yadda kawai, in ba hakaba wannan damar ta wuce aiki ze kuma komawa baya, gara ka kirashi kace ka yadda" , jinjina kai Jeje yayi
"Shikenan amma Jawwad seyaga abunda zanmasa"
Haka jeje ya kira Jalal, yace masa sun yadda,
Washe gari babu zato babu tsammani, Daddyn Hanan sukazo shida Abdallah, suka duba Jalila, taji dadi sosai da zuwansu, dukda ba wani dadewa sukayiba, dayake hanan? gaya masa abunda yasamu Jalila, daga bauchi suka dawo suka biyo suka tsaya a kano domin dubata, Daddyn Hanan yace Insha Allah shima ta bangarensa zesa aimasa bincike game da batan Ummin, sannan yaita rarrashin Jalila tareda yimata nasiha,
Daddyn Hanan yacewa Abba
"gaskiya wataran zanzo kabani Jalila, mutafi da ita bauchi, gurin kakarsu Hanan, itama taga wannaan kamannin nasu, daga bata labarin Jalila se magiya take dan Allah akaita ta ganta, dayake ta tsufa bata iya fita aida da ita zamu taho"
Abba yace
"Allah sarki insha Allah randa kuka shirya kuzo ku kaimata ita"
"To shikenan, nagode kwarai da karamcinka Alhaji usman"
Sukayi musu sallama suka nufi kaduna
Kwanan su Abdallah biyu da zuwa, su Jalila suna cikin farin ciki, sun samu admission a BUK daga ????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? ita har? Nana, ranar litinin zasu fara zuwa makaranta, Abba yayi musu nasiha sosai game da rayuwar dazasuyi a cikin Jami a, ita Nana
mass communication zatayi, itakuma Jalila catering craft zatayi, da farko Jawwad yaita mata mita akan mezatayi da wani catering duk kwakwalwarta, itakuma tace shi takeso, dan tana son harkar girke2 da sanao'in hannu.
Anata shirye2 birthday Jalal, Yanzuma Jalal ne da Jawwad a harabar gidan akan fararen kujeru, suke zancen yaya birthday din ze kasance, Jalila ta fito zata fita,
"Yaya barka da yamma"
"Yawwa baby ina zuwa haka?"
"Maama zan karbowa kaya, a jambulo"
"Bari mu tafi tare, semu ajiyeki dama fita zamuyi"
"To yaya, bari inje waje in jiraku"
Jawwad ya kalli Jalal, "Dakko motar, bari inje insaka kaya"
Jalal ya fito da motar waje, Jalila bata shiga motar? ba tana tsaye a waje har Jawwad ya fito, suna shirin tafiya sega wani abokinsu Jawwad yazo wucewa, tsayawa yayi suna gaisawa, dayake? tsohon abokinsune kuma sun dade basu hadu ba,
Jawwad yace "kai faruk ba a ganinka ko a gari, ina ka shige haka ne?"
Wanda aka kira da faruk yai dariya "ina nan Jawwad, makaranta ce munata fama, kasan yanzu ina ABU zaria bana zama sosai a kano, yanzuma wani filin baba mukazo gani unguwar taku, Jalal nema bana ganinsa sam" Jalal ya kalli Faruk ya danyi murmushi, sannan yace
"Nima ina nan haduwa ce dai tai wuya, ya karatun? "
"Alhamdilillah Jalal, y garin, ya karatu ko har yanzu baka koma makarantar ba" Jalila dai na tsaye jikin mota tana jinsu, Jalal yace
"Gari gamu a cikinsa, makaranta kuma bana zuwa har yanzu"
Jawwad yace, "Faruk, yana Jalal yana shirin komawa makaranta kwanan nan insha Allah"
"To Allah yasa"
Jawwad yace "au Jalal nayi mantuwa, bari inje in dakko wayata, ka karbi lambar faruk mudinga gaisawa"
Jalal yace "Ok seka fito"
Jawwad ya shiga gida, faruk ya kalli Jalal, yace "Jalal wannan kuma wacece?" jalal ya dan kalli Jalila sannan yace
"gata nan tambayeta mana"
"Hmm Jalal halinka yana nan dai" faruk ya kalli faruk "y'an mata yakike? "
"Lafiya kalau" faruk yakuma cewa "Jalal ban san wannan ba, kanwarka ce kota Jawwad, kokuma.... Jalal ya katseshi ta hanyar cewa
" kai faruk, kaima surutun nan naka yana nan da shegen son mata" dariya sosai faruk yayi, ana haka sega wata mota tazo wucewa, amma akayi parking mutumin ciki ya fito, babban mutum ne, ya tunkaro su a fusace da farko faruk be ganshiba seda gabaya, dan bude baki yayi ya zaro ido, mutumin yana zuwa ya kalli Jalal sannan ya kalli faruk,
"Kai faruku, ban hanaka kula wannan dan iskan yaron ba, danayi sa a na rabaka dashi, shine yauma kakuma lallabowa, gurinsa ko, sekaima ka lalace kamar sa, kai ko kyamarsa ma bakayi, dubeshi kana kallonsa kaga mutumin banza wuce kabar nan gurin ko in kifa maka mari, "
Faruk ya fara in ina" A a Bab... Baba, dan Allah kayi hakuri, gaisawa kawai muke
"Zaka wuce ko sena marekan, nahanaka hulda da yaron nan, inkuma kaima kafara shaye2 ne kaima se inji, ba Shiri faruk yai gaba, yana waiwayensu
Jalal dai bece komaiba ya sunkuyar da kai yai shiru, Haka nan se Jalila taji ba dadi, mussaman da Jalal ya sunkuyar da kansa bece komai ba,
Mutumin ya juyo ya kalli Jalal, ya nunashi da yatsa
"kaikuma bakai ba dana, idan nakuma ganinka dashi wallahi hukuma ce zata rabamu da kai, dana ba lalatacce bane ba kamar kai, ni dana kamiline, baze yiwu ka koyamasa shaye2 da rashin tarbiyya ba," Jawwad ne ya kawo kai ya fito ya tarar da cin zarafin da akewa Jalal, tsayawa yai cak yana kallon ikon Allah, mutumin ya cigaba da bala'i
" ni banyi sake ana ya lalace ba dan haka bazan bari ka lalata min shiba, niba nusarin ubane ba kamar ubanka, daya bari ka lalace kalleka, kowa ya ganka yaga dan iska mara tarbiyya sha3" harzuka Jalal yayi, ya kura ma baban faruk ido, amma abun mamaki still Jalal yaki cewa mutumin nan uffan
"Shima baban nasa bashi ya saiwa kansa ba, kuma ba laifi yayiwa Allah ba ya jarrabeshi da fitinanne yaro ba, haba baba, a haka gaka dattijo amma aji wannaan maganganun suna fita daga bakinka, to in Allah ya doramaka ya zakayi? Akan wani dalilin zaka dinga zaginsa dan kawai ya gaisa da danka, shi Jalal din shi yaiwa kansa, ka gayamin wanda akayi shawara dashi kafin a halicceshi, ko kaddara abunda ze faru a rayuwarsa"
Gaba daya ido suka zuba mata baki bude, suna kallonta, tsagwaron bacin raine kwance a idonta, bil hakki take fadan maganganun da take, kana kallonta kasan har zuciyarta ranta ya baci, Jawwad ne yai yunkurin cewa
"Jalila meye haka, ba kya ganin babban mutum ne? Baba kayi hakuri insha Allah Jalal baze kuma...
" Wai yaya Jawwad laifin me akayi masa kake bashi hakuri, ABDUL JALAL ne ya taka kafa yaje inda dansa yake kokuma shi yakawo kansa, baba irin wannan abubuwan da akewa mutane irinsu Jalal shike kara lalatasu, yazama bame jansu a jiki, kowa se kyama da tsangwama, danka da kake fada akansa ma mutum ne, kuma baka isa ka hana Allah ikonsa akan shiba, in Allah ya jarrabeshi shima, yazakayi a ganina in bakayimasa addu a ba bekamata ka zage shi haka ba, da kake cemasa mara tarbiyya kazagi mahifinsa da ya dau mataki akanka fa, kasan a hakan nan se ya zageka tsaf bazaka iya masa komai ba, kuma kaga hakan baze maka dadi ba"
Jawwad yace na shiga uku, halin Jalila yana nan ashe, bata canza ba, shiru2 da take na kewar Ummi ne ashe, yayinda Jalal yai shiru yana satar kallonta, Jawwad yace
"Ke kiyimin shiru, meyasa kike haka, sa ankine"
Baban Faruk yace, "Kyaleta i like her confidence, kin birgeni sosai yarinya at least, kin tunamin abunda na manta, nagode sosai" ya kalli Jalal yace
"Am sorry my son, nasan na bata maka rai, kayi hakuri" yajuya ya wuce ya hau motarsa ya tafi
Jalal be taba tunanin tsiwar Jalila ta kai haka ba, babban abunda yabashi mamaki yadda ta zakakalkale haka, bayan itama rashin mutunci takemasa, juyawa tayi ta bude bayan mota ta shige abunta kamar batayi komaiba, Jawwad yacewa Jalal "taho mu tafi" ba musu Jalal ya bishi, amma Jawwad ya zauna a mazaunin direba, Jalal yana kusa dashi, Jawwad dan waigo ya kalli Jalila sannan yace
"Baby ya haka, abunda kikayi kin kyauta kenan? Babban mutum ne fa, haba baby dama baki canza ba?"
"ka taba ganin an haifi mutum da hali ace ya canza, in tsoho beji kunyar hawa jaki ba jaki baze ji kunyar kada tsohoba, a matsayinsa na babba abunda yayi ya dace kenan, kozakayiwa mutum rashin mutunci karka hada da mahifinsa, shima daganinsa kaga criminal idonsa kawai zaka kalla kasan ba mutumin kirki bane"
Shi Jawwad Jalila ta dena bashi mamaki tsoro take bashi
"Ke Jalila ya akayi kikasan criminal ne, karki kuma, baban wanine koba komai ya haifeki"
"Yaya nifa ba karya nayiba bakaji yadda yake magana ba ne? Shima wannan nusarin Jalal din yanaji ana zaginsa yai shiru, inkaga yana masifa to akan Matane, yadinga wani muzurai,

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login