Showing 39001 words to 42000 words out of 129540 words

Chapter 14 - ABDUL JALAL Hausa Novel

08 Oct 2024

6689

masa tea yakemin masifa"
Dan tabe baki Jalila tayi

"Dama yana salla ne se ince ko beyi Azkar ba, to Wanda be salla ba ya za a tambayeshi yayi Azkar ma, kasan in mutum ya nisanta kanshi da Allah komai ma seya sameshi"
Dan kallon Jalal Jawwad yayi yaga idonsa a lumshe se yayi tunanin ko bayajin me Jalila take fada, amma tsaf yaji me tace
"Hmm Adduar ki kawai muke bukata baby"
"To Allah ya shirya ya bashi lafiya, ka kama kansa ka karanta mai bismillah kafa sha Tara se ka biya masa ma tayassara minal Qur'an"

"Godiya muke ya sayyada, Allah yakara hasken makaranta
Brother tashi ka karbi tea din"
Yafada yana Dan jijjiga Jalal
Tashi zaune Jalal yayi ya karbi tea din ya kai bakinsa ya Dan fara sha
"What!! tea naji kace"
"Eh tea zan bashi ya sha kinga yana da dumi"
"Waye ya hada tea din?"
"Ilham ce ta hada masa mana"
Jawwad yabata amsa

Dan tunani Jalila tayi
Meye yasa ta dinga faduwar gaba tun agurin musabaka har yanzu bashi taita ganin Ilham da sauri tace

"What Ilaham kuma? Karya sha tea din nan Yaya Jawwad ka karbe tea din nan"
Tafada cikin karaji

Share please
More comments more typing......

Comments dinku yayi kasa zanyi yajin typing =??=??=??



=؊??=؊??=؊??=؊??=؊??=؊??
[8/31, 8:26 AM] Safiyya:
? ? _ABDUL? JALAL_
? ? ? ? ?? (2020)

? ? ? _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
? ? (Daddy's girl)

? ? ? ? ? ? ? ?PAGE-? 22&23

PART 1

? _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,? ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta? wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar

07063065680
Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din


I want comments not stickers or just thanks=?"?=?"?=?"?=?"?
Your comments give me courage

? ? ?
? ? ? ? -My First Novel-
Not Edited


Jinine ya wanke mata fuska ta fasa kara yarinyar tayi, itako Jalila ko ajikinta, hakan yayi dadi? da isowar class mastern su Jalila hankalinsa ne ya tashi ganin duk saurin da yayi Jalila ta riga tayi aika? be kara tsurewa ba seda ya tabbatar da wadda aka fasawa goshi salati yayi, Hanan Abdurrasheed Yar gidan babban captain din sojan ruwa da aka kawo ranar litinin ita Jalila ta fasawa kai shi kansa ba yadda beyiba ya canzawa Hanan gurin zama saboda yasan me gurin tafi kashi doyi wato queen J,? amma hanan yarinyar akwai izza da jin kai, tace ita dole nan gurin takeson zama,
yanzu yasan ba Jalila ba su Kansu makaranta Ta janyo? musu
"Jalila mene haka kika aikata, wannan wane irin shirme ne, yaushe ma kika dawo ne bansaniba memakon kizo kigayamin seki dauki doka a hannu kalli haukan da kikayi"
"Niba hauka nayiba daba ta mareni ba inaga da hakan bata faruba"
"Shut up zaki gane kuranki ubanta sojane insuka casaki inaga daga yau kindena Neman magana"
"Wai da anyi magana se afara maganar babanta sojane,
Allah sarki mukuma 'ya'yan Allah bani marasa gata, wallahi ko Yar gidan rocket ce bata isa ta mareni in kyaleta ba"
Ya fuskanci babu alamar nadama tareda Jalila Dan ko kadan bata tsorata da abinda tayi ba itakuwa Hanan tuni aka tafi da ita school clinic akaimata dressing daga nan Hanan bata saurari kowa ba ta fice daga makarantar duk yadda akayi a dakatar da Hanan amma tayi waje ta tafi gida
Jalila aka kira office din director
Aka dinga mata fada kowa da abunda yake fada a cikin malamai wasu abun kirkinta wasu akasin haka ciki hadda wata malama ta zage ta dinga zagin Jalila matar a bayan layinsu Jalila take, Jalila ta taba fada da Yar malamar, Dan haka dama tanajin haushin Jalila
"Dama wannan yarinyar ba tarbiyyace da ita ba, bata da mutunci Sam dama ina za a samu wata tarbiyya a gurin Yar mace"
Jalila ce ta daga kai da sauri ta kalleta
"A'a madam adinga hakuri Jalila yarinyar kirkice, tana da tarbiyya ita dai matsalarta da students ne ga tarin alkhairanta ga makarantar mu dabazamu manta ba"
Cewar director
"Hmm yallabai baka San yarinyar nan bane uwatta Sam bata son laifinta ita ta sangarta ta lalace, amma yarinya sekace Yar daba, takama Yar mutane ta fitar mata da jini, dama charity begins at home duk abunda yarinya takeyi to haka taga uwatta tanayi"
"Sir kaimata magana kartakuma zaganmin uwa duk zaginta ta tsaya kaina takuma zagina sena rama, uwa ba tafi uwa ba"
"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun Jalila ta daban ce
Jalila koma class dinku yanzu"
Cewar director ita kuwa Jalila ta mike ta koma ajinsu
"Dan Allah kalli yadda take ikrarin zata zageni yarinyar nan kawai a koreta shine mafita"
Inji malamar dazu
"Korarta ba shine mafita ba yarinya ce me matukar kwazo in muka koreta munyi asara babba"
Cewar wani malami
"Hakane kam wan mahaifinta abokina ne bazan taba korar masa ya ba, kuma duk fitinarta bantaba ganin tayiba se yau yanzu dai mahifiyarta zamu? gayyota tazo mu zauna da ita dakuma wakilinta Dan na tabbatar, Yar gidan sojan nan se sunzo makarantar nan"
"Allah yasa suci kaniyarta sumata dukan tsiya"
"Haba madam in "yarkice fa baza kice haka ba ai shi da na kowa ne addu'a yakamata ayi mata Allah ya shirya Allah kalli dai yasan abunda zata zama nan gaba"
Inji director

Hanan ce ta shiga tangamemen palour tana kuka wata babbar mace ce zata yi shekaru arba'in da takwas amma Hutu yasa in ka ganta seka zata batafi shekaru talatin da biyu ba, gefenta kuma ga wani babban mutum shima yana shan tea
"Ke Hanan meke faruwane ne yasameki haka a fuska"
Matar Tai maganar cikin iyayi da isa
Mutuminne ya kalli hanan shima
"Auta meyasami goshinki haka meyafaru?"
Hanan kuma fashewa da kuka tayi ta kwashe abinda yafaru da karya ta fada tace Jalila tamata duka ta dinga gwarata da bango tana zaginta
"Amma auta kin bani kunya kamar ba Yar Dana Haifa a cikina ba ki tsaya wata yarinya tamiki duka hada fasa miki goshi kamata yayi insa bulala in zaneki ai"
? "Wannan wace irin magana ce kakeyi haka a dakar min yarinya haka daga shigarta makarantar, wace Yar marasa galihun ce ta isa tayiwa y"ata haka in kyaleta wallahi senaga gatanta a gurin nan senaga uban da ya tsaya mata, se nasa an kulleta daga ita har ubanta"
"No ban yadda ba kinsan ita Hanan din metayi yarinyar tayi mata haka mubi komai a hankali ki bari gobe in Allah ya kaimu da kaina zanje makarantar indai yarinyar ce bata da gaskiya semusan abinda yakamata muyi'
" daddy ance mata baba na soja ne fa amma secewa tayi wai ko Yar gidan bullet ce, Allah yasa Kaine AK47"
Abun ma dariya yabawa baban Hanan
"Lallai yarinyar nan tana da karfin hali"
Itakam Maman Hanan iya wuya ta kulu taso ace baban Hanan ya kyaleta data nunawa yarinyar banbancin civilian da kuma kaki, zata so taga uban daya tsayawa yarinyar nan ko baban Hanan be saniba seta koyawa yarinyar nan darasi seta nuna mata banbancin dake tsakanin yayan farar hula dakuma "ya'yan rainon bullet.
? ? Tun kafin a tashi daga school wannan malar taje gidansu Jalila tagayawa Ummi abunda Jalila tayi bayan haka hadda cewa itama Jalila ta zageta tsaf
Hankalin Ummi yayi matukar tashi da jin abunda Jalila tayi taita bawa malamar hakuri

Ilham ta dawo daga makaranta amma har taje ta dawo bata fuskanci komai ba, kamar yadda Daren jiya batayi bacci ba tunda Jalal ya nuna mata messages din wayarsa da yake tuhumarta akai, hankalinta yaki kwanciya tun jiya take takura kwakwalwarta domin kokarin gano wadda ke turowa Jalal wannan sakon amma takasa tuna komai, a iya saninta ba ya muamala da mata, to ta Yaya? wacece wannan take kokarin rusa nawa shirin ita ta kafa kanta,
Jikinta a sanyaye taje tayi wanka amma takasa cin abinci "ko gurin Nana zanjene ko zata tayani gano wacece ta, tambayi kanta
Kodayake yanzu ta dawo daga makaranta kar in takuramata koma inje tana wayar da wannan sha? Yar uwatta ta
Da sauri Ilham ta mike JALILA tafada a fili, tabbas JALILA ce itake turomasa wannan sakonin dan babu Wanda yakewa Jalal shishshigi in ba itaba iya sanina Jalal baya kula mata ko a family
? Amma indai na kara bincike na tabbatar Jalila ce sena yi maganinta babu wata "ya mace data isa tayi takara dani a soyayyar Jalal, wallahi JALAL nawane ni kadai, duk macen datayi yinkurin yin takara dani senaga bayanta
se yanzu nagane wato duk wannan shishshigin da take masa Ashe sonsa take
To ba ta isaba wallahi

Koda aka tashi daga makaranta Jalila hankalinta kwance ta taho gida tare da kudurcewa a zuciyarta setaje gidan malaman nan data ce mata 'Yar mace ta mata warning dan bata hakura ba,
Gida ta tafi ta shiga da sallama amma Ummi bata amsa mata ba dan haka kai tsaye dakin Ummi ta nufa
Ummi nakan sallaya ta idar da salla tana lazimi Jalila ta wuceta ta canza kaya zuwa towel taje tai wanka tai salla tasaka uniform din islamiyya amma still Ummi bata kulata ba
"Ummi wai baki ganni bane, yau ko sannu dazuwa bakice minba se fushi kike wai mena mikine?"
Still Ummi batace mata komai ba gaban Ummi taje ta zauna
"Ummi wai meyene"?
Janyota Ummi tayi gabanta ta zuba mata kyawawan maruka guda biyu
" wato Jalila duk kokarin danake akanki inkika fita abinda zuciyarki tagaya miki shi kikeyi,
Kin fasawa Yar mutane goshi, kinzagi malamanki wannan itace tarbiyyar danayi miki ko?
To yanzu zankira Abban Jawwad in aka kashe case din nan gobe in Allah ya kaimu,
Koshi ko Jawwad wani yazo ya daukeki sukoma can kanon dake,
Lokaci yayi dazan koma dangina kema kikoma hannun wan ubanki tunda ba kya tausayina,
"Yar gidan babban captain fa na sojoji Jalila me nake dashi da Zan iya wannan rigimar dakika dakko, kano zaki koma nagaji, gaskiyar mahaifinki kafin yarasu da yace tarbiyyar mace seda tsayayyen namiji bazan iyaba Jalila nagaji"
"Har anzo angaya miki karya da gaskiya kekuma kin yadda ko Ummi to walla.....
" rufemin baki Dan ubanki"
Da sauri Jalila ta kalli Ummi bata taba jin Ummi tayi zagiba
"Akan kujerar zama ko? kikayi wannan aikin ko ubankine ya sassaka kujerar kokuma akai na? haifeki dazaki daki Yar mutane akai kujerar banza,
Kuma saboda baki da kirki ki dubi malama ramatu Dan an miki magana ki zageta ko Jalila"
Se yanzu Jalila ta gane malama ramatu CE tazo tagayawa Ummi
"Wallahi Ummi malama ramatu munafuka ce bafa haka..
" Ai bazaki canza ba, hali indai nakine bazaki canza ba agaban nawa ma kuma zagin malamar ki kike ko?
"Wallahi niba malama ta bace yan primary take koyarwa bata taba koyamin uwar komai ba"
"Yayi miki kyau ina fada kina fada"
"A'a Ummi Dan Allah kiyi hakuri karkiyi fushi bazan karaba"
"Aini nagama yanke hukunci Abbanku zan kirawo azo a maidake kano, nima gurin nawa dangin zan koma"
"Ummi wai dagaske kike, dan girman Allah kiyi hakuri nace mikifa bazan karaba ni wallahi bazan koma kano ba"
"Sekuma kiyi ai tunda ni kin rainani gara kikoma gaban Zainab itace daidanki"
"Na shiga uku wallahi Ummi kafata kafarki ko bangon duniya zaki tafi ko a kafa sena biyoki, wallahi bazan kuma ba dan Allah Ummi, wallahi banason zuwa kano"
Banza ummi tayi mata ta dakko wayarta tana kiran Abba yayinda Jalila ke gabanta tanata faman kuka

Jawwad ne ya dawo daga makaranta ya gaji matuka kaya wanka yayi yai salla ya tafi gurin Rabin ran nasa wato Jalal
"Dan uwa ka dawo daga makarantar kenan sannu da zuwa"
"Yawwa bros Sannu da hutawa"
Jawwad yafada yana Neman gurin zama
"Nagaji sosai Jalal,"
"Nagani a idonka ai yau kukayi tests din ko?"
" eh yaune Alhamdilillah test din duk se godiyar Allah sunyi sauki sosai kuma hada jajircewar ka da addu'arka proud of you dan uwana rabin jiki"
"Kajika kaifa kake karatunka bani nake maka ba wannan kan naka akwai ja mutumina i wish nike da kwanyarka"
"Amma fa ka zageni Jalal, kasan ban isa inyi karatun dakayi a bayaba in kana waje wayake Neman irinmu, Jalal wai yaushe zaka koma makaranta ne kai?"
"Zan koma amma ba yanzuba, bana son wannan zancen zomuje muci abinci"
"A ina kuma ga abinci can a Gida zuwa nayi muje mu ci"
"koma inane muje daganan kasha ice cream ka dan huta, ka huce wannan gajiyar "
"Kaikake koyamin kwadayi fa"
Dariya sukayi gaba daya
"Kasan wani abu Jawwad?"
"A'a seka fada?
" wallahi wata mayyace take uzzurawa rayuwata gashi tayi hiding number balle insata a black list, kullum seta kirani kota turomin messages ni na rasa yadda zanyi, wallahi na gane wacece setayi Dana sanin wannan gangancin da take min"
Dariya sosai Jawwad yayi
"To kai meye abun damuwa aciki, dan ance ana sonka"?
"Mtseww kai kafiya shirme Jawwad ni bani da lokacin wannan shirmen, inyi rayuwata ni kadai ya fiyemin, duk yayinda ka gayyoto mata cikin rayuwarka kamar ka gayyatowa kanka matsalane"
Dariya? Jawwad ya dingayiwa JALAL seda Jalal yafara jin haushi sannan ya dena
"Jalal wayagaya maka mata matsalane, mata ni'ima ne, tabbas akwai daga cikinsu masu matsala, amma akwai na kirki sosai, soyayya akwai dadi mussaman in kayi dace da mosoyi na kwarai, bazaka gane hakan ba seka fada tarkon soyayya"
"Hmm mata duk matsalane indai irinsu Ilham ne duk matsalane"
"Hmm bazaka gane ba Jalal"
"Eh naji bazan ganeba"
"Lokaci ze ganar da kai ai"
"Eh naji mutafi"
Jeje ne yakira Jalal yana son su hadu Jalal
Shikuma yace masa ya fita shida Jawwad bazeyiwu su hadu yanzu ba
Gurin cin abinci suka tafi shida Jawwad
Bayan sungama cin abinci ne suna hira aka kira Jawwad lambar Ummi yagani ya kara nutsuwa ya dau wayar
"Salamau alaikum Ummi barka da rana"
"Yawwa barka Jawwad ya kake ya mutan gidan"
"Kowa lafiya Ummi ya Jalila"
"To lafiya kalau za a ce meyasamu lambar abbanku nakira bata shiga"
"Inaga inda yake ne ba network, amma lafiya Ummi"
Ajiyar zuciya Ummi tayi ta kwashe kaf abunda yafaru tagayawa Jawwad
"Yasalam Ummi kiyi hakuri insha Allah komai zezo da sauki, yanzu bana Gida idan na koma zanwa Abban bayani insha Allah, kiyi hakuri Ummi dan Allah kinsan har yanzu yarinya ce"
"Ba batun yarinta? Jawwad tsabar rashin hankaline kawai
" adai yi hakuri Ummi "
Haka dai sukayi sallama Jawwad ya dafe kai
"Ohhh my God sisy ba dai rigima ba"
"Ya dai meyafarune?"
Jalal ya tambayeshi, Jawwad ya kwashe komai ya gayawa Jalal,
Dariya Jalal ya dinga yi kaman wani tababbe
"Kan bala'i wannan yarinyar Yar bala'ice wallahi, kaga zancena ko Jawwad, nagaya maka mata matsalane, mussaman irin wannan kanwar taka zama da ita seda panadol"
"Hmm haba Jalal kaima kanwarka ce, Jalila bata son raini bata yadda da wulakanci ba nidai fatana Allah yasa kar baban yarinyar yayi mata wani abu"
Wata dariyar Jalal yakumayi
"Kamar ya kar yayi mata wani abu "yarsa fa ta Daka, aigara suko yamata hankali yadda gobe bazata kuma ba,"
Yayi maganar yana dariya
"Haba Jalal Yar gidan Abee ce fa, in duniya da gaskiya bekamata kace haka ba"
"Hakane Jawwad kaima kace wani abu amma kasani bataji, in mutum yana rashin kunya in besamu dai? da shiba baze dena ba

? "Wow tauraro a cikin taurari kaina mussaman ne ban taba tunanin kana dariya haka ba, bakaga yadda dariya kemaka kyauba"
Gaba daya suka waiga domin ganin me maganar Hannah ce budurwar dasuka hadu da ita wancan karon, tayi maganar tana karasowa inda suke guri tanema ta zauna
"Jarumin maza meyabaka nishadi kake wannan dariyar haka ka fi ko yaushe kyau ko dan uwan ne yake baka nishadi"
Ta karasa maganar tana kallon Jawwad
"Uban wa yace kizo inda nake, me kike Nema a gurina ne kin uzzuramin kindami rayuwata meye hakane, waima wayagaya miki ina nan da kike bina"?
? Wani kasaitaccen murmushi Hannah tayi
"Call me by my name Hannah, or any special name u choose,
Kasan ita zuciyoyin masoya kaman wireless ne, our hearts and souls are always connected, dan hakazuciyarkace tagayawa tawa zuciyar kana nan shiyasa nazo kuma nayi sa'a nasameka zuciyarka kawai nake bukata Jalal, in har kabani zaka huta da nacina, akasin haka kuwa zan cigaba da hanaka sukuni cikin dare ko rana har sekabani abunda nakeso"
Wani wulakan taccen kallo Jalal yai mata ya watsar da ita bece mata komai ba
Jawwad ne ya danyi gyaran murya
"Kinaji Hannah already Jalal akwai wadda takeson Sa kanwarsa ce kuma kinga.....
Dagawa Jawwad hannu Hannah tayi
" haba dan uwan masoyina meye laifina anan dan ina kokarin cikawa zuciyata burinta, kowa iya allonsa ya wanke, tayi nata kokarin nima inyi nawa wadda tai galaba ta kafa soyayyarta a zuciyarasa shikenan, ni Hanna babu macen data isa tayi takara dani akan soyayya,
Jawwad son danakewa dan uwanka ko matansa hudu sena kori biyu ya aureni saboda space din daya yamin kadan,
Kar ace rashin adalcin nawa yayi yawane da se ince seya kori kowa ya aureni saboda shidin nawane ni kadai"
Saroro Jawwad yayi yana kallonta
"In kagama jin tatsuniyar kazo mutafi inada abunyi" Jalal yafada yana mikewa
Hanna ma mikewa tayi tazo gabansa kaman zata shige jikinsa se wani irin fitinannen kamshi take
"Babyna kabani dama ko sau dayane in gwada maka yadda nake sonka mana, kuskurewa bukatata shizesa incigaba da uzzura maka har gidanku nasani zaka iya ganina a kowani lokaci, karkayi mamaki nasanka farin Sani a yadda kake a haka nake sonka, zan iya komai akanka, kagayawa kanwarka ta janye kudirinta na sonka ta barmin kai in bahakaba"
Ta kashe masa ido daya daga nan tai tafiyarta,p babban abunda yabawa Jalal mamaki dayakasa yimata komai
Jawwad ne ya janyo hannunsa suka hau motarsu suka nufi Gida
"Jawwad ka yadda mata matsalane, abunda zuciyarsu ta raya musu kawai shi sukeyi, yanzu ga haukan da wannan tayi min, amma zan dau mataki akai"
"Kabi komai a hankali Jalal, kasan in mutum yana kan ganiyar so makancewa yake so ba karyane ba, ka dena wulakanta Wanda yace yana sonka kai baka san a ya zaka fara taka soyayya ba,
Amma wannan Hannah ka nemi tsari da sharrinta because Dana kalli cikin idonta ya tabbatar da she mean what she said"
Haka suka cigaba tattaunawa har suka iso gida
Bayan sallar isha'i Jawwad yaje part din Abba ya tarar dashi shi ka dai, yagaya masa abunda ya faru jinjina kai Abba yayi
"Hmm Jalila iya rigima, halin mahaifinta ta dakko bata son raini Allah ya kaimu goben, zan San yadda za ayi"
Da asuba Abba ya taho kano be gayawa maama abunda ya faruba ya dai cemata zeyi fitar asuba zashi wani guri

? Still wannan Daren ma messages din Hannah suka dinga shigowa wayarsa seda yagaji ya kashe wayar

Washe

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login