Showing 36001 words to 39000 words out of 129540 words

Chapter 13 - ABDUL JALAL Hausa Novel

08 Oct 2024

6684

ma karya take dama dai Neman magana ne ko Shiga abunda ba ruwanta ne yai maganar a zuciyar sa

Yarinyar dasuka hadu dasu Jalal a restaurant ce zaune akan gado Jeje na gabanta a tsaye yana rarrashinta
"Gaskiya Jeje ni bazan iya ba gaskiya zeyi taurin kai ko kallona fa be yiba har na gama surutuna na tashi be kulani ba se abokinsa ne yamin magana"
? Tai maganar tana yatsina fuska
Jeje ne ya Dan gyara tsayuwarsa
"Hanna kiyi hakuri, dama tun farko seda nagaya miki, mugun Dan wulakancine baya saurarar mata Sam amma kicigaba da bibiyarsa kidage Hanna zaki iya"
? "Amma dai kasan bana son wulakanci ko nida maza ke min layi, amma ace ana wulakantani Dan ma dai ya hadune gayen da bazanyi aikin nan ba"
"Kiyi hakuri Hanna seda na duba naga babu me iya min wannan aikin se ke,
Hanna ki dage tunda naga gayen yayi miki"
"Anyway I will try my best ka barni dashi da Hanna yake zancen zan sauke masa wannan taurin kan bani lambarsa"
"That's good Hannah shiyasa nake ji dake"
Jeje yafada yana jin jinamata

Jalila ce tayi sallama da Ummi
Ummi tayimata nasiha da fatan samun nasara
Haka taje islamiyya sukayi sallama da kawayenta da sauran malaman daba dasu za a tafi ba sunata musu fatan alkhairi da fatan samun nasara
Daga nan suka kama hanyar Abuja da sauran dalibai dazasu tafi tare,
Sun sauka lafiya aka basu masauki su huta da la'asar guri ya cika da manyan mutane daga gurare daban? aka fara gudanar da musabaka

Ilham suna parlour da mummy suna hira, mamanta tayi mata waya ta mike tace wa mummy tana zuwa
Daki ta nufa taje ta daga wayar
"Hello Mami ina wuni"
"Ke bar batun gaisuwar nan
Ya akayi yaci abincin"

"Ina fa yaci abincin na kai masa kaman zeci namanta bayacin cous? da ba shi na girka ba da tuni yaci"
"Ke ni yimin shiru tunda beci ba, kina wani shirmen kika dafa abinda baya ci
Yanzu yana ina"
"Yana part dinsa mana"
"To ke kina me ki tashi ki bar abinda kikeyi kije ki tayashi hira mana"
"Maami dan baki san halinsa bane mugun Dan rainin hankaline"
"Kiyi hakuri Ilham, ribarki CE fa da kin aureshi burinmu yacika zan dau fansar abinda uwarsa tayimin, a wuce gurin, in kina yawan zama a inda yake dahaka zaku shaku, in Allah ya kaimiu weekends kizo akwai turaren Dana karbo miki sannan yanzuma ki shafa wancan turaren Dana baki malam yacemin yayi aiki sosai a cikin turaren"
"To maami bari inje "
"Yawwa Ilham koke fa"

Mikewa ILHAM tayi tafara shiryawa tasaka wata doguwar Riga Ja me kama Jiki, ta shafa turare ta Dan Dora siririn mayafi akanta ta fito parlour bakowa a palour mummy ta tashi, Dan haka ta fito ta nufi part din Jalal

Yana kwance da gashi se dogon wando da vest ya kwanta ya lumshe Ido jinsa yake jikinsa Sam ba kwari kaman anyi masa duka
Ilham ce ta shigo parlour ta sameshi a kwance akan three seater yanajin shigowarta amma be motsaba kan kujerar dayake taje ta zauna daga karshen kafafuwansa ji yayi jikinsa ya kuma mutuwa
A hankali ta kai hannu ta dan matsa yatsunsa na kafa taji yayi shiru bece mata komai ba Dan haka ta cigaba da matsa yatsun kafarsa a hankali
"ILHAM"
Taji ya kira sunanta a hankali
"Na'am Yaya Jalal"
Ta amsa masa
"Wane irin turare ne wannan kikasa?"
"Me turaren yayi?"
Ta tambayeshi
"Ji nayi ya kashemin Jiki, kamar ya karamin ciwon kai"
Abun yabata mamaki dataga be hantareta bako ya koreta
Kashe murya tayi cikin shagwaba da iyayi ta fara magana
? "Haba Yaya Jalal turaren da kasanni dashine fa"
Mikewa yai zaune tare da fadin
"No ILHAM this one smells different"
Kusa dashi ta matsa ta kwanta akan kafadarsa
"Kaine dai kaji haka amma ni ban canza perfume ba"
Dan tureta yayi kadan ya Dan kalleta "
dakkomin Wayne a fridge ki hadon da cup"
"OK angama my J"
Ta mike tanata karairaya, tare da mamakin wannan sakin Jiki da Jalal yai da ita haka
Shikam da ido yabita yanajin kaman ba shiba
Wayne din takawo masa ta bude ta zuba a cup ta mika masa ya Sa hannu ya karba itakuma ta dawo kusa dashi ta kwanta a jikinsa
Hannu ya mika ya dakko remote ya kunna Tv
Yana kunnawa yaci karo da fuskar Jalila
Tana murmushi tasha hijjabi blue ga farin glass tasaka ga sufiku a gabanta na karatu gani yayi kamar shitake kallo
Gabansa ne yafadi yaji tsigar Jikinsa ta tashi

Share please
More comments more typing.................


Ina alfahari daku masoya wannan novel
Irinsu
Jamila
Zakiyyat
Ummu hanif
Mabruka
Zainab
Da wannan tsofaffin Fatima zahras
Da duk members Na ABDUL JALAL NOVEL FANS
Wanda na fada da Wanda ban fada ba nasan daku ina alfahari daku

[8/31, 8:26 AM] Safiyya:
? ? _ABDUL? JALAL_
? ? ? ? ?? (2020)

? ? ? _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
? ? (Daddy's girl)

? ? ? ? ? ? ? ?PAGE-? 19

PART 1

? _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,? ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta? wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar

07063065680
Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din


I want comments not stickers or just thanks=?"?=?"?=?"?=?"?
Your comments give me courage

? ? ?
? ? ? ? -My First Novel-

Malamai ne suka jeru suna shirin janyowa Jalila inda zata karanta
Itakam tayi shiru ta kurawa camera ido haka nan taji gabanta na faduwa dukda tasaba zuwa musabuka amma takejinta wani iri

Jalal ne ya kurawa TV ido gani yake kaman shi Jalila take kallo so yake ya tabbatar itace kuwa a jikin allon TV kokuwa kamrun dayasha ce tafara gaya masa karya(giya)
Ita kam Ilham kara shige masa take tana kuma zuba masa Wayne tana mika masa
"Ilham ki kyaleni please"
"Yaya J why?"

Tayi maganar tana kuma kwanciya a jikinsa
Shikam yakoma kaman wani karamin yaro
"Bana so Ilham ki kyaleni kwanciya zanyi kaina ciwo yake"
Dan dagashi tayi ya koma ya kwanta akan kujerar yana kallon TV kasa?
A hankali Ilaham ta mika hannunta tana shafa sajensa
"Sannu Yaya J"
Gyada mata kai yayi

"Ilham karki kuma saka turaren nan inzakizo inda nake banaso"
Yai maganar a hankali
"To na dena"
Tv ya kuma kalla Jalilan ce dai sedai wannan karon annurin fuskarta ya gushe ta dai?ta nutsuwarta aka janyomata inda zata biya
A hankali tayi bismillah tafara karanto Qur'ani cikin sauti me dadi
Ture Ilham yayi daga Jikinsa ya lumshe idonsa jin sautin karatun nata yake yana ratsa ko ina na jikinsa yana saukar masa da nutsuwa Ji yayi kasalar tana sakinsa duk yayinda ya bude Ido seyaga kaman Jalila shi take kallo jinsa yake kaman ba Shiva
Ilham hannu ta kuma mikawa zata taba shi ya daka mata tsawa
"Ke wace irin banzar yarinya ce waima tukuna me kikemin anan gurin ne tashi kibar min daki kafin in zaneki banza kawai"
"Haba Yaya amma
" bazaki fitan ba kenan kalli Tv duk rawar kanta kalli yadda take karatun Qur'ani gwanin burgewa keko sha? baki iya komaiba se hauka get out from my room"
Idonta ta kai duba kan Tv Jalila tagani tana zuba kira'a kaman ba itace me shegen surutu da Neman magana ba, wani abu taji yazo ya tokaremata zuciya wato tun dazu da ya kurawa Tv ido ita yake kallo kenan
Wani mugun kallo taimasa
"To ai gara ni inazuwa Islamiyyar kai...........
Bata rufe bakiba yasaka kafafuwansa ya take nata kafar wani irin ihu tayi da karfi kuma yaki dagawa
" Dan girman Allah kayi hakuri, wallahi bazan kuma ba"
Kara takesu yayi
"Dan ina daga miki kafa ina nan a Jalal dina da kikasani, yanzuma Sa a kikaci da wallahi sena zaneki da belt, tashi kifita wawiya kalli rigar jikinki sokuwa kawai"
Da kyar taja kafa ta fita kafarta se zugi takeyi ta koma dakinta ta hau gado ta kama kuka
Wani uban tsaki ya ja yanemi guri ya zauna
Tashar da suke haska musabakar su Jalika sun tafi talla dan haka
ya dauki cup din giyarsa ya cigaba da sha yakuma zubawa ze sha aka kuma hasko Jalila haka nan se ya aje giyar hannunsa shima ya kuramata ido, yanayin Jalila ne ya nuna kaman bata da nutsuwa
Aka kuma janyomata karatu amma tayi shiru ta tafi tunani ko??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????wa ita yake kallo
Jikinta ne yayi sanyi jitake kaman wani abune ke shirin faruwa, mafarkanta datakeyi yan kwanakin nan ne suke fado mata a rai taji gabanta yacigaba da faduwa.
a hankali tayi ajiyar zuciya ta Dora inda aka janyomata da karatun ta cikin birgewa

Bacci ne yafara fusgar Jalal dan haka anan gurin ya zube ya lumshe ido yana sauraren karatun Jalila har bacci yayi awon gaba da shi

Da safe Jawwad ne yazo ya tarar dashi yana bacci a parlour a kasa kan carpet ga kwalbar giyarsa yasha fiye da rabi
Girgiza kai Jawwad yayi
"Allah ya shiryeka Jalal"
Yasa hannu ya kwashe kwalbar da kofin ya fita dasu ya dawo ya tashi Jalal don yasan be salla ba balle ya karya
Hannu ya kai ze tasheshi yaji kansa yayi zafi, bayansa ya Dan bubbuga a hankali Jalal ya bude ido ya mayar ya lumshe
"Ka tashifa gari yayi haske kayi salla kazo mu karya"
Jalal ne yake tunano abubuwan dasuka faru jiya da daddare gaskene kokuma mafarki yayi ji yai kansa yakuma sarawa

"Kaina ne yakemin ciwo sosai Jawwad"
"Sannu ka tashi in muka karya seka sha magani"
Da kyar ya lallabashi yaje yayi wanka yai sallar asuba, Jawwad ya dakko musu Abinci

Ilham CE ta fito tana taka kafa da kyar mummy ta kalleta
"Meyasameki kike taka kafa da kyar"
"Dutse na taka jiya a garden"
"Subhanallah bakiji ciwo ba dai ko?"
"A a banjiba kafar ce dai kawai take ciwo"
"To ko asibiti za a kaiki a duba kafar"
"A'a mummy zata dena ne Insha Allah"
"To shikenan ni zan fita ne zanje ganin likitan Ido, ga breakfast can na gama in wancan Dan zeci yazo ya dauka kema kije ki dau naki"
"To mummy adawo lafiya"
"Allah yasa"
Mummy ta fita

Jalal ne ya dakko wayarsa ze kira daddy yaga message ya shigo wayarsa Dan haka ya bude message din bakuwar lambs ce

? ? ? "Barka da safiya jarumin?? ??
? ? ??? maza fatan kana lafiya? ? ? ?
? ? ?? Zanso ace a halin yanzu
? ? ?? Muna tare ina kallon? ? ? ? ? ? ? ? ? wanna kyakykyawar?fuskar
??? ? Amma lokaci na nan zuwa
? ? ?? Dazamu kasance tare kaji? ? ? ? ? Dadinka masoyina
? ? ? ? ?? ? From ur lovely bae"

Wani uban tsaki Jalal yayi
"Nasan Ilham ce zataci kaniyarta zata gane innin sa,'anta ne"

"Ya dai meyafaru ne kake surutai haka"?
Jawwad ya tambaheshi
"ba komai ci abincinka kawai"
Ya mike ya nufi cikin Gida tundaga parlour yake kiran sunan Ilham amma bata nan dakinta ya nufa yana zuwa ya tarar tana dakinta tana karyawa
A firgice ta dago tana kallonsa

"Uban meye wannan kika turomin a waya wai meyasa ba kyajine Ilham"
Kallonsa tayi cikin rashin fahimta
"Wane sako kuma ni ban turomaka komai ba"
Ransa ne ya kuma baci wato raina masa hankali zatayi gadan? ya nufi inda take da niyyar ya ci kaniyarta
Ta mike tsaye tafara kuka tana
"Wallahi Yaya bansan laifin danayiba"
Yana karasowa Inda take yaji tana warin wannan turaren na jiya kansa ne ya Sara yaji yana Neman ya fadi, da sauri ta taho inda yake
"Yaya menene?"
"Dalla tsaya karki karaso inda nake"
Bango ya daddafa yabi kofa ya fice da kyar ya koma part dinsa Jawwad ne ya ganshi ya rike kai yana dafa bango
"Subhanallah Jalal kanne dai"
Jawwad yafada yana riko JALAL
"Jawwad kaina kaman ze fashe"
"Bari mu tafi asibiti ina key din motarka?"
"Kaga kyaleni bazani wani asibiti ba"
"Meyasa meye amfanin ka zauna a Gida baka da lafiya"
Guri Jalal yanema ya kwanta ji yake duniyar tanata jujjuyawa
? Kai tsaye cikin gidan Jawwad ya tafi ya nufi part din daddyn Jalal yasameshi a parlour yana breakfast
Suka gaisa Jawwad yagaya masa halin da Jalal yake ciki, tare da daddy suka taho gaba? daya part din Jalal
Suka tarar dashi a kwance yanata juyi akan gado ya rike kai Juyin duniya ya tashi su tafi Asibiti yace baza shi ba kunsan mutumin da taurin kai
Se wani likita aka kirawo yaimasa allura se yasamu yayi bacci

Alhamdilillah Jalila ita tazo na biyu a gasar musabaka da akayi tasamu kyautuka da dama kuma an karrama malamanta
Ita Jalila duk ba haka taso ba na daya taso tazo
"Duk wannan sakaran ne yajamin haka kawai naita mafarkinsa nazo musabaka ya hanani sukuni"
Haka taita mita suka kamo hanyar dawowa Kaduna suna murna amma ita haushi duk ya isheta
Har Gida motar makaranta takai Jalila, siyama tana gidan tana Jiran isowar Jalila
Ummi tana ganinta ta rungumeta tana murna, amma Jalila tai kicin? da fuska
"Lafiya kuwa babyna?"
"Ummi ta biyu fa Nazo"
Tafada kaman zatayi kuka

"Haba baby Wanda yazo na karshe kuma yace me? Daga na daya fa seke haba babyna"
"Gaskiya aminiya inkakiyi haka baki kyauta ba kullum zakiyita zuwa na dayan, hakan ma mu munyi murna"
"Yawwa ai gara kigayamata siyama, adinga godewa Allah Baby"
Ummi tayi maganar tana dungurewa Jalila kai Dan turo Baki JALILA tayi
Taje tayi wanka suka kule dakii itada siyama suna hira
"Kinsam wani Abu aminiya"
JALILA tai maganar tana kallon Siyama
"A'a sekin fada"
Siyama ta bata amsa
"Wallahi Jiya agurin musabaka naji gabana yanata faduwa ina tuna mafarkin nan danake"
"Kai Aminiya meye kuma na tunawa ABU ya Riga ya wuce kimanta kawai
Bari inbarki ki huta kishirya ranar Monday insha Allah za a koma school"
"Can ta matsemusu bazan komaba senagama hutawa ki gaida umma"
"Aminiya halinki seke tararki za aci fa in baki koma ran Monday ba"
"Hhh tab Tara sedai a ci wasu Tara ba dai niba"
Sukai sallama ta Raka Siyama kofar Gida ta dawo dakinta ta kwanta akan katifa domin huce gajiya


Mummy ce ta dawo Ilham tagaya mata ai Jalal ba lafiya suka tafi part dinsa, yana kwance akan gadonsa yana bacci jijiyoyin kansa duk sun daga dagani baccin ba dadi yakemasa ba, warin turaren Ilham yakuma shaka dukda bacci yake seda ya yamutsa fuska ya juya wani bangaren
A hankali mummy ta kai hannu ta shafa sumarsa tana fadi
"Allah yabaka lafiya son"
ILHAM ta amsa mata da "Ameen"
Se bayan azahar ya farka Jawwad ya shiga cikin gida yace Ilham ta hado tea ta kawowa Jalal,

Jawwad ne gefen Jalal yana masa sannu
"Ya kakejin jikin naka yanzu"?Jawwad ya tambayi Jalal
"nifa har yanzu yanamin ciwo, amma bakaman dazu ba"
"To ai kaima ance muje asibiti kaki ka manne a Gida"
"Ni ba wani asibiti da zanje"
Sakone ya shigo Wayar Jalal, Jawwad ya miko masa wayar

? ? ? ?? "Barka da wannan lokaci
? ? ? ? ?? Lovely am missing ur
? ? ? ? ?? Handsome face wish to
? ? ? ? ?? See u soon
? ? ? ? ?? Love u so much
? ? ? ? ?? From ur lovely bae"
"Mtseww wannan wace irin jaraba ce"
Yana aje wayar tafara ringing an kira yafi sau uku yaki dagawa
"Jalal wayarkace fa ke ringing
Ka daga mana"
"Bazan daga ba in ka gaji da karar kai ka daga"
Girgiza kai Jawwad yayi halin JALAL se hakuri
Hannu yasa ya daga wayar se yaga unknown number muryar mace yaji
"Hello babyna fatan kana lafiya"
"Sorry ba me wayar bane, me wayar baya jin dadi amma wa za ace masa"
"Eyyah shiyasa naji ni bani da lafiya nima ko abokinsa ne JAWWAD"
"Dan uwansa dai"
"To amin afuwa Dan uwansa"
"Eh nine"
"Hannah ce ai masa sannu, ko zaka bani address din inzo in dubashi"
"Ohh no daga nan ma kiyi masa addu'a mungode"
"Anyway Allah yabashi lafiya amma banajin zan iya komai bayan mallakin zuciyata ba lafiya,
Ka gaisheshi please"
"Zeji insha Allah"
Jawwad ya katse kiran ya kalli Jalal
"Mutumin yaushe kafara soyayya ba labari wace kuma Hannah"
"Mtsewww soyayyar banza kai kasanta"
"Easy mutumina adena cika baki wadda takiraka din nan bakaji kalaman data fada tace agaya maka ba"
"Dan Allah ka kyaleni inji da kaina"
"Ohh sorry nadena sannu,
Yanzu za a kawo maka tea"

ILHAM kam wani tunani tayi this is another opportunity for her to use that medicine again
Tunda wancan lokacin be Ciba a abinci yanzu tasan zesha a tea
da rawar jiki Ilham ta mike taje ta nufi kitchen ta hada tea ta zuba wani maganin a ciki ta juye tea din a flask ta doro cups akan plate ta nufi sashin Jalal

A cikin bacci Jalila taji kirjinta ya tsanan ta bugawa Ilham kawai take gani a mafarkinta a hankali ta bude ido gabanta ne yacigaba da faduwa meke Ilham ke shirin yine nake ganinta a bacci na
"Laila ha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin"
Shine abinda Jalila taita maimaitawa kamar wadda aka tsikara tayi zumbur ta? mike zaune ta dakko wayarta


Sallama Ilham tayi tana kokarin shigowa
Jalal ne ya Daka mata tsawa
"Tsaya a nan malama karki karaso inda nake"
"Haba Jalal wai meyasa kai ba a maka gwaninta ne"
Saroro Ilham ta tsaya tana kallonsu
"Eh naji ba amin gwaninta amma karta shigomin nan"
Mikewa Jawwad yayi ya karbo tray din hannunta
"Kiyi hakuri ILHAM kinji zedena ne nasan ba kyajin dadin abunda yake miki, nan gaba in ance yayi koda kudi baze miki ba"
Gyada masa kai kawai Ilham tayi tabashi tray din kayan tea ta koma
Gaban Jalal ya dawo ya zauna
"Bross Ilham kanwarka ce yadda kake treating dinta Sam be dace ba"
"To mekakeso in mata indinga goyata ko kuma in zauna ina mata dariya a hakanma kana ganin rashin kunyar da takemin har ta kalleni tace ni take so sa'anta ne ni?"
"Jalal Ilham itama yarinya ce, kuma so ba karya ne ba bazaka gane hakan ba se ranar da yai maka kamun kazar kuku"
"Naji labarin ya isheni haka, hadamin tea in sha"
Jawwad na cikin hada masa tea dinne Jalila takira wayar Jawwad
Murmushi yayi sannan ya daga wayar
"Sisyna am sorry nayi laifi ban kiraki naji yakike ba yau hankalina ne ba a kwance baya musabakar?"
Seda ta tura baki kaman tana gabansa
"Yaya Jawwad ta biyu fa nazo"
"Kai amma nayi murna, dole inzo Kaduna muyi celebrating"
"Wani celebrating bafa ta daya Nazo ba wai ta biyu"
"To ai kinyi kokari baby meye kuma na bata rai? Aini a hakan ma kinfiyemin Wanda yazo na daya"
? "Dan Allah ka aje wayar nan, ko kabani tea din in hada da kaina"
Jalal yai maganar a fusace

"Ohhh sorry bari in hada maka"
Jawwad yai maganar yana kashewa Jalal ido
? "Yayana kaida waye ne?"
Jalila ta tambaya
"Nida yayanki ne bashi da lafiya tun jiya yake fama da ciwon kai an masa allurai amma har yanzu kan bedena ciwo ba, shine zan hada

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login