Showing 120001 words to 123000 words out of 129540 words

Chapter 41 - ABDUL JALAL Hausa Novel

08 Oct 2024

6688

matsalar mutum ya dinga abunda bashi da kyau kenan wanda ya isa da wanda be isaba sunemi suci mutuncinka"
Bude baki Jawwad yayi ya waigo yana kallonta, dama haka take, tunda ake fadar iya tsiwa na Jalila be taba tunanin ta kai nan ba, rasa bakin magana yayi, shikuwa Jalal ko motsawa beyiba daga inda yake balle ya nuna yasan dashi take, sema tunani da yayi zurfi a ciki, amma yana jin duk abunda take fada, haka motar tai tsit har sukaje jnda zasu sauketa, tace
"Yaya Jawwad ka jirani man in shiga in karbo, semu tafi bannaa son tafiya ni ka dai, kasan ban san kan garin? nan ba"
"gashi kuma ba gida muka nufa ba, zamuje siyayya ne" cikin shagwaba tace " eh naji, ko ina zakuje dai, dan Allah kujirani"
"To yi sauri karkimin kuka" tayi murmushi ta bude motar ta fita"
Jawwad ya dan kalli Jalal sannan yace
"Jalal, Jalila ba karamin mamaki ta baniba, ban taba zaton zata iya haka ba, babban mutum kaman wannan sam bata da tsoro, amma kaima bazan gaji da baka hakuri akan abubuwan datake yimaka ba, kuruciya na damunta, har yanzu yarinya ce"
"Wane kalan kaya kakeso musaka ranan, so nake muyi shiga iri daya"
"A a ya ina maka magana kaikuma kana min wani zancen daban"
"Kasan akwai kaya da daddy ya turo dasu zamuje mu duba, in bamu samu wanda mukeso ba semu siyo wasu, i wish daddy yana Nigeria zanyi birthday" Jawwad ya fuskanci Jalal rainin hankali yakeji, wato baya son wancan zancen da sukeyi, dan haka ya rabu dashi.
? Bayan barin Alhaji kabiru gurin nan, ya dinga tunanin wace wannan yarinyar haka, wace ce ita, mene alakarta da Jalal haka, wayarsa ya dakko ya kira lambar Jeje, bugu biyu Jeje ya dauka,
"Allah ya temaki, oga KB"
"Jeje tambayarka zanyi"
"to Oga Allah yasa nasani"
"akwai wata yarinya danagani a gurin Jalal, ko kasan wacece dinsa"
"ya take oga?"
Ya fasalta masa siffar Jalila, jeje yace gaskiya be santa ba amm ze bincika masa.
Jalila ta fito, tazo ta bude motar ta shiga, Jawwad yace "har kinfito"
"Eh Yaya banason bata muku lokacine"
Jawwad ya kunna mota, suka hau titi, suna hirarsu da Jalal, aka jima se cewa tayi
"waimu ba za a gayyacemu bane?"
Jawwad yace "mu mun isa dole a gayyace ku mana"
"hadasu Nana, da Ilham"
"Eh mana hadasu" shidai Jalal bece uffan ba, baze so zuwan Jalila gurin nan ba dan yasan tabbas setayi surutu intaga abunda be mata ba, kuma yasan dole ayi shaye2 a gurin, meyasa Jawwad ya amsa mata suje gurin nan, a titi suka sauketa, sukuma sukayi gaba, ta dade tanajira sannan ta samu napep ta karasa gida, a palour ta tarar da Maama da Abba ta kaiwa Maama kayan, Abba yana mata sannu da zuwa, Maama ta bubbude kayan ?an kunnaye da sarka masu matukar kyau,
Jalila tace "Maama bari in daukesu a waya a tura social media, za a samu costumers tunda new design ne" dayake a gaban Abba ne se Maama ta sakar mata fuska,
"eh hakan yayi kyau, in anjima dan Allah ki mikawa mummy, dama saboda ita nasa aka karbosu tacemin ana so"
"to shikenan bari inyi salla" harta mike zata tafi, Abba ya kirata ta dawo
Yace "daukar muku, keda Nana kowa biyu, se a gayamin kudin"
"to Abba mungode Allah yasaka da Alkhairi, Allah yasa afi haka"
"Ameen ya Allah, Allah yayi Albarka" Jalila ta tashi ta tafi dakinsu, yauma Nana bat nan, Jalila tayi salla taci Abinci, ta kwanta tana hutawa, ta dau wayarta tana ta tura kayan nan social media a haka har bacci ya dauketa
? Jawwad sun sha yawo, shida Jalal se kusan la'asar sannan suka dawo sun gaji matuka, sallar la'asar sukayi, sannan Jawwad ya kira Jalila a waya yace dan Allah akai musu Abinci, ji tai kamar tace A a saboda batason yawan zuwa inda yake tunda mahaifiyarsa bata so, amma Nana bata nan Halima ma haka, badan haka ba da bazataje ba,
"to Yaya gani nan zuwa, bari in kawo"
"to shikenan muna jira"
Jawwad ya kalli JALAL, bari in shiga in dan watsa ruwa kafin ta kawo abincin" Jalal yace
"to kifi, sarkin ruwa seka fito" befi 3min da tafiyar Jawwad wanka ba Jalila ta shigo da kayan Abinci, tai sallama amma Jalal ya mata banza dama bata sa ran ze amsa ba, ta ajiye Abincin, harta juya zata fita taji muryarsa
"Ke zo nan" kutmelesi wai ke, juyowa tayi da niyyar yi masa rashin mutunci, kawai taga yamata wani mugun kwarjini, gashi ya kafeta da ido,
"gani mene?" tazo kansa ta tsaya tana zumbura baki, hannayenta ya janyo da karfi seda ta durkusa akan gwiwoyinta, seda ta danyi kara ta dago ta kalleshi tareda fizge hannunta, saboda taji zafi
"Idan na kuma kiranki, kikatsaya min aka, kamar itace sena miki abunda zaki karye, mara kunya kawai" kallon up and down ta masa ta dauke kanta
"Ubanwa kike cewa nusari dazu, wait tukuna ma, uban wayasa kiyiwa mutumin nan rashin kunya, ke yayiwa koni, meye alakarki dani da zakiyi wa babban mutum kamar wannan rashin kunya, inkinyi dan ki birgeni ne, to baki birgeba dan JALAL bayasin shishshigi"
Murmushi Jalila tayi wanda yai matukar yi mata kyau, "wayace maka saboda kai nayi, aini birgeni yayi da yayi maka haka, kasan wanda yasan darajar dambu shike zuba masa mai, duk inda naji ana cin mutuncin iyaye koba nawa bane raina baci yakeyi, saboda karya zarce da zagin daddy shiyasa nai magana domin dakatar dashi, ba wai dan kai ba, kwakwalwarka ta dinga lissafa maka dai2 mana" kuramata ido yayi baya ko kiftawa, sekuma yayi dariya
"Karya kikeyi, idonki ya nuna abunda kike fada? a yanzu karyace kawai,
Sekuma ya hade rai
" Zan miki wani kashedi, idan kika kuskura kikazo gurin birthday na duk abunda yasameki kekika jiyowa kanki, danban gayyaceki ba, tashi kbmibani guri, mummuna uwar magana kawai" mikewa tayi ta danyi gaba sannan ta waigo ta kalleshi
"wallahi senaje, ai ba dan kai zaniba, saboda yaya Jawwad zani, tunda shi yace inje, dayake abun na rashin gaskiyane shine wai ba a gayyaceniba, to wallahi senaje, inyaso in naje a dakeni, ragon maza kawai nusari.



Share please
More Comments More Typing..............................




=؊?? =؊?? =؊?? =؊?? =؊??

? ? _ABDUL? JALAL_

? ? ? _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
? ? (Daddy's girl)

? ? ? ? ? ? ? ?PAGE-? 51
PART 1

? _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,? ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.

A har kullum ina jinjina da godiya ga masoya wannan novel nawa, comments dinku da addu oinku ina jin dainsu matuka, ina godiya kwarai dagaske,
Domin sharhi, gyara, kokuma shawara a nemeni ta what's app akan wannan lambar wayar
07063065680

? ? ? ? ? ? ?? _My First Novel _

Tana gama fadin haka ta juya tai tafiyarta, dan girgiza kai Jalal yayi, ya cigaba da danna wayarsa, Jalila na komawa taga Maama tafito daga kitchen "Ke daga ina kike?" "Yaya Jawwad ne ya kirani yace in kaimasa Abinci" tsaki Maama tayi sannan tace "inkinyi sallar magariba, ki mikawa Mummy kayan nan" "to zan kaimata Insha Allah" Maama ta wuce, Jalila kuma ta shige dakinsu tana zuwa ta tarar Nana ta dawo, "Nana Ashe kin dawo, sarkin kawaye" "bawani sarkin kawaye, zumunci dai"
"hhh to naji, ya kika baro su" "suna lafiya amma naso tare mukaje, ke kullum kina gida" "ai bayan tafiyarki nima na dan fita Maama ta aikeni" "inyee kinfara gane gari" "sosai makuwa" sukayi dariya sannan Jalila tace "Nana wai ranar Saturday za ayi birthday din Jalal" "Are you serious, ya akayi kika sani?"
"Yaya Jawwad ne yagayamin"
"Amma ya haka duk shekara tare sukeyi fa" "nima bansaniba, guri zasu kama amma muma zamuje"
"dan Allah ai basu gayyacemu ba"
"Injiwa Yaya yace zamuje muma"
"kai amma naji dadi Jalila dama an kwana biyu banfita wani outing ba"
"Haka kika iya sarkin yawo"
?? Bayan Jawwad sun gama cin Abinci suka fito suna hira, a harabar gidansu Jalal suka koma suna basket ball, se magariba suka bar gurin, bayan sallar magariba Jawwad yacewa Jalal, yazo suje gurin Mummy "muje muyi mata me?" "yakamata dai muje kwana biyu ban ganta ba bamu gaisa ba" "kaje kai kadai mana, ba dolene se naje ba" "Jalal ba shawararka nake nema ba, ka tashi mu tafi" Ganinda Jalal yai Jawwad ya hade rai sosai, shiyasa shi mikewa, "tashi muje" Jawwad ya tashi suka tafi cikin gidansu Jalal, Jalal ne a gaba Jawwad yana binsa, Ilham ce kadai a palourn kwance akan three seater tana daddanna wayarta, mikewa zaune tayi tareda fadin "sannunku da zuwa" Jawwad ne ya amsamata, "yawwa Ilham, ina Mummy ne?" "tana dakinta, inaga salla takeyi bari inje in kirata" ta mike ta nufi part din Mummy, Jalal dai se cika yake yana batsewa sekace wanda akayiwa wani laifi, ba a dadeba sega mummy ta fito, Ilham na bayanta, ta karaso ta nemi guri ta zauna a palourn, dan risinawa Jawwad yayi "Mummy ina wuni" "lafiya kalau Jawwad kwana biyu ya gida, yasu Maaman"
"tana lafiya" "Kwana biyu bamu hadu da ita ba, ina jira zata aikomin da kaya" "eh dazu naga an karbo, amma zata aikomiki ne" "Yayi kyau" shidai Jalal bece uffan ba, sema mike kafarsa da yayi ya kashingida, Jawwad yace "Mummy ranar Saturday yakama birthday din Jalal fa" "ina sane Jawwad, wannan karon ba tare zakuyi ba" "eh mummy, nashi zamu farayi tukuna, nace bari agaya miki" "Assalamu Alaikum" gaba daya suka amsa sallamar tareda waigawa, ko be juyoba yasan muryar Jalila ce, karasowa tayi cikin yanga, ta kalli Jawwad tai masa murmushi sannan ta durkusa kasa tace "Mummy ina wuni" "lafiya kalau 'yan mata kwana biyu, kin buya bana ganinki" murmushi Jalila ta kumayi "ina nan Mummy bana fitane kawai" "amma baki da lafiya ne, naga kin rame haka?" Jawwad yace Mummy ta danyi rashin lafiya kam""Allah sarki ba labari, Allah ya sawwake" suka amsa da Ameen banda Jalal da Ilham dan tunda ta shigo Ilham ke mata kallon banza
Mummy tace "Jalila yi hakuri bari in dan saki aiki, jeki dakina akwai drowern mirror dina akwai, key ki dauka ki bude wardrobe dina, zaki ga akwai wani kit kibude ki dakko kudin ciki
Ilham seda ta kalli Mummy dan sam Mummy bata sata harkar kudinta, amma yau ta tura Jalila har bedroom dinta ta dakko kudi, seda Jalila tayi Jim kaman bazata ba sannan ta mike, ta nufi dakin Mummy,
"Yawwa Jawwad ina jinka, yi hakuri na tsaya surutu" "bakomai Mummy dama cewa nayi, ko zaki halacci gurin birthday din nasa" Jalal ne ya dago da sauri yana wa Jawwad wani mugun kallo, shikuma ya dauke kai kaman besan me yake ba, murmushi Mummy tayi "waceni Jawwad, Allah ya temaka, ya raya Jalal sannan ya shiryamin shi"
Koda Jalila tashiga taga part din Mummy ma ya tsaru, katon palour ne, me dauke da kayan alatu, se tangamemen kofar bedroom dinta, ya tsaru matuka, kaikace a kasar wajene, Jalila ta nutsu ta dau abunda aka sata ta fito.
Jawwad ya gyara zama sannan? yace "Mummy in bazakije ba ga Ilham, ko yan uwa ai yakamata sumana kara suyi attending" Jalal ji yake kaman ya make Jawwad, shi bayason gayyar surutu, amma Jawwad se gayyato masa tarkace yake Ilham tace "Jawwad aini ko ba ku gayyaceni ba zuwana gurin birthday din yayana dolene, dan haka zanje nida kawayena" wani uban tsaki Jalal yayi, duk suka juyo suka kalleshi, Mummy tace "kagani ko Jawwad, nikam Allah yakawo silar shiryuwar Jalal, yanzu a haka kake tunanin inyi attending gurin birthday dinsa, ya dizgani a gaban abokansa, Sam baya ganina da mutunci"
Ai kuwa Jalal a fusace yace "kagani, nidama bance tazo gurin birthday na ba, seda nace bazanzo ba amma ka janyoni kaga har zata faramin korafi sek....... Sekuma sukaji yayi shiru, ya koma ya kashingida, fitowar Jalila taji Jalal yana wannan masifar suka hada ido, ta girgiza masa kai, alamar ya dena, shine abunda yasashi yin shiru, yakoma ya kashingida, duk abun nan ba wanda ya lura dame ya faru se Ilham, wadda taji kaman an dakko dutse an sakamata a zuciyarta.
Jalila ta karaso ta durkusa tabawa mummy kudin, Mummy tace "tafi dasu, kibawa Maama kice kudin wancan kayanne, ban mata transfer bane saboda wayata, ta dan samu matsala" "to zan gaya mata Insha Allah, seda safenku" Jawwad yace "bazaki jirani ba" "a a yaya, seka taho"
Ilham ce tafara mikewa ta tafi dakinta, sannan Jalal, shima tashi yayi ya bar dakin, dan Jawwad yagama bata masa rai, Jawwad kuma ya tsaya, yaita rarrashin Mummy kan halayen Jalal, sannan yai mata sallama ya tafi.
Koda Ilham ta koma dakinta ji tayi kaman ta dora hannu akanta ta fasa ihu, wannan wace irin masifa ce, tunda take a gidan nan, mummy bata shigar da ita cikin sha anin kudinta, amma yau da kanta ta tura Jalila kan kudinta, kuma karewar abun takaici wai hartayiwa Jalal signa ta hanashi abu, kuma ya hanu, lallai akwai sauran aiki, meyasa wannan yarinyar ta shigo rayuwarmu tayi kane2 haka, me yakamata inyine, kozan yi yawo tsirara se burin mahaifiyata ya cika, amma ta yaya? Wata zuciyar ta tambayeta, shiru tayi zuwa can kuma tayi wani irin shu'umin murmushi, tareda jinjina kai, "muje zuwa, Jalila kin tara kin samu, senayi sanadiyar da mujiya seta fiki farinjini a cikin al umma"
? ?? A satin ranar Monday su Jalila suka fara zuwa makaranta, Abba ya daukar musu driver saboda Kar a dorawa Jawwad nauyi dayawa shima ga nasa karatun, Jalila taji dadin fara zuwa makaranta, in ka ganta kai kace irin salihar nan ce, dan ko magana batayi sosai, wanda yana cikin halin Jalila in taje guri seta karanci kowa tsaf sannan zaka san wacece, ko magana bata fiyeyi ba, sannan bata yadda tayi kawa ba har yanzu, a satin nan tunda tafara zuwa hijjabi take sakawa har kasa, se farin glass, yauma uban dogon hijjabinta dark blue har kasa ne a jikinta, se jakarta data rataya, sunfito daga lectures tana jikin wata bishiya inda suke haduwa da Nana, taji? wasu suna zundenta wai ga ustazan jami a, gigin secondary ne ta shigo a ustaziyya kafin afita kuma anyi clean, irinsune mugayen tantiran makaranta in suka waye, itakam ko ta kansu batabiba, dan ko kallo basu isheta ba, a ranta tace "kucigaba karku fasa, ku bari in zama yar gari, zaku gane baku da wayo dan ba ruwana da wata jami a, mutun yayimin senayi masa, but now kuci karenku babu babbaka" tana tsaye nan Nana ta karaso, suka nufi motarsu, a hankali Jalila take gane halin yan ajinnasu, da yaran masu kudi, dana talakawa masu dorawa kansu karya, yan rainin hankalin lecturers, da masu iyayi, kowa tana ankare da halinsa, tana ganesu, amma still ba ruwanta da kowa, wasu suyi gulmarta a gabanta wasu a bayan idonta, seta nuna musu ita magana ma abun wahala ce a gurinta,
Nana kam hartayi kawaye daga zuwanta, yayinda dabi un Jalila suka tafi da imanin kawayen Nana, ta iya gayu maganarta kawai abun burgewa ce balle tafiyarta da sauran
mu amalarta, sedai suna mata kallon me girman kai, saboda gani suke kaman wulakanci take musu, inba Nana ba bata kulasu, dan ta yanayin shiga da mu amala tana iya gane, mutanen banza dana kirki, Jalila kenan me abubuwan ban mamaki

Ilham ta gayyaci kawayenta gurin birthday din Yayanta kuma masoyinta wato Jalal, se wani rawar kai take tana shirye2, ta gayyaci su yaseera da sauran kawayenta, se shiri takeyi, taje sabon gari ta sha kitso, tayi booking din make up, hatta shigar da zatayi sabon kaya ta siya.
Jalila ma nata shirin takeyi, saboda mugayen mafarkan da take da Jalal, dan haka da shirinta, zataje gurin birthday din nan, tanason tayi taka tsan2 sosai a gurin nan dan ita sam bata yadda da wannan birthday dinba, tana so taga suwaye abokan Jalal ne, mussaman Jeje, dakuma wasu abubuwa da take shirin yi a gurin, tanason tabattar wa Ilham Jalal baya gabanta, Bangaren Jeje ma shidasu hannah da abokan shaye2 sun shirya tsaf domin gudanar da mummunan kudirinsu akan ABDUL JALAL.
Ranar juma a da daddare, wanda yakama jajibir din birthday din Jalal, Jalila ta tafi Dakin Jawwad domin tana son magana dashi, tai sa a kuwa shikadai ta tarar a palourn, taje tasamu guri ta zauna, Jawwad ya kalleta"Babyn Yaya Jawwad, ya akayine?"
"gurin Yaya nazo" "to Yar gidan Yaya, ina jinki"
"Yaya Jawwad , gaskiya abokinka tunda mutane masu hankali zasuje gurin nan, dan Allah ka kaishi a rage mai gashin kansa, sannan kar kabari yasaka sarkan nan dayake sakawa sekace wani kare, ga wan..... Kai tsaye ba sallama sukaga Jalal ya shigo, hade rai Jalila tayi" a dai dinga yin sallama" banza Jalal yai mata, ya kalli Jawwad "kai gurinka nazo" Jawwad yace"ai gani, Allah yasa lafiya" wayar Jawwad tafara ringing "excuse me bari in amsa waya" yadaga wayar yasaka a kunnensa tareda yin sallama "Assalam Alaikum"
Muryar Hanan Jalila taji "wa alaikum salam barka da yamma Taurarona fatan kana lafiya?"
"lafiya kalau Hanan, ya gida, yasu Abdallah da daddy?" "suna lafiya, nice dai bani da lafiya" "yasalam meyasameki" "kewarka mana, itace take damuna, yanzu yaya queen take, naga kwana biyu haushina takeji" "tana lafiya, yanz... Juyawa yayi da nufin yabawa Jalila wayar, yaga Jalila ta cika ta batse, ta hade rai sosai, fasa bata wayar yayi, yace
" Queen dinki tana lafiya" "Masha Allah ina sirikata Nana, kodayake ita muna waya, dan Allah Yaya Jawwad yaushe zakuzo Kaduna ne, inaso inkuma ganinka, kullum senayi mafarkinka fa" Jalal dake gefe ya kalli fuskar Jalila kawai ya kwashe da dariya ganin yadda ta hade rai, Jalal ya tashi ya fita daga palourn, yana kuma yin dariya, ba karamin kyau Jalal yakeba idan yana dariya, Jawwad seda ya sha jinin jikinsa yakuma kallon Jalila, muryar Hanan ya kuma ji "my Haidar bakace komai ba, dan Allah yaushe zakuzo?" mikewa Jalila tayi ta fice daga

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login