Showing 33001 words to 36000 words out of 129540 words

Chapter 12 - ABDUL JALAL Hausa Novel

08 Oct 2024

6693


"Ya salam"
ta fada a hankali
"To dagani tunda kin tashi"
"Ummi ki Dan kyaleni mana in gama hutawa ni dama xaki goyani"
Ture kanta Ummi tayi ta mike ta tafi dauro alwala
A hankali taji bugun zuciyarta tana komawa normal
Ringing din wayarta ta jiyo a dakin ta da sauri ta mike ta tafi ta daga wayar lambar siyama CE
"Aminiya ya ake ciki kuwa ?"
"Oho"
"Kaman ya oho ya tafin ne? Kinkuma tambayar Yaya Jawwad?"
"Aminiya mezan tambayeshi ne ?ya rigada yacemin ya tafi se dai kuma addu'a kawai"

" banji dadi ba aminiya
Allah ya kiyaye ya tsare se mucigaba da addu'a amma ina ji a jikina kaman betafi ba"

"Tab wannan uban taurin kan to Allah yasa amma tunda ya furta seya tafi"

"Insha Allah be tafiba gobe in Allah ya kaimu ki shirya da wuri mutafi islamiyya karki jamana dukan makara"

"Insha Allah aminiya"

"Wani irin sha? ne kai jeje why do you failed this mission, after all u know na Dora burina akan wannan tafiyar dazukuyi meyasa?'
a wannan tafiyar naso dawwamar da bakin ciki a zukatan ahalinsa na har abada"?
Mutumin dazune da ya kai jeje airport a motarsa yake maganar cikin fada

"Am sorry sir amma ba laifina bane wannan abokinnasa ne ya hana shi"
"Wa kenan"
Mutumin ya fada cikin fada
"Wannan mayen nasa Jawwad, saboda shi ya fasa tafiyar"

"Jawwad ko? Yayi kyau zan tabbatar masa da ba a shiga hanyata semun bar masa mummunan tabo a cikin zuciyarsa Wanda har gaban abada baze goge ba, dama shine yakemana karan katsaye a al'amuranmu zamuyi maganinsa"
"Hakan shine mafita ayi maganinsa kawai"
Jeje yayi maganar da sauri

Har cikin Gida Jawwad Yakama hannun Jalal yashiga dashi yan gidan duk suna parlour ILHAM.tana zaune? tayi shiru tana tunani
Yayinda mummy keta rusa kuka daddy yana rarrashinta
Jawwad ne yayi sallama gaba daya suka daga kai domin amsa sallamar
Kawai sesuka ga Jawwad tare da Jalal
Jawwad ya janyo hannunsa zuwa cikin palour
"Gashi nan ya fasa tafiyar hankalinku ya kwanta, mummy kukan ya isa gashi ya dawo"
Jawwad ya fada yana kallon mummy
To Alhamdilillah nima ba a son raina ya tafi ba, ba yadda zanyi ne tunda ya dawo se muyiwa Allah godiya
Ita kam Ilham bakinta ne yaki rufuwa
Mummy da gudu ta mike taje ta rungume Jalal tana cigaba da kuka hada sheshsheka

Kunsan d'a da uwa karo na farko bayan lalacewar Jalal da yaji kukanta ba dadi a zuciyarsa
"Kukan ya isa ai tunda gani na dawo
Ki godewa Allah ki godewa Jawwad Bazan iya tafiya in barshi da kewata ba"
Jalal yai maganr yana kallon Jawwad

Mummy kasa magana tayi se daddy da yake kokarin godewa Jawwad
"Haba daddy kar kasa inji kunya mana bakomai "
Nima Jalila ce takara fargar dani abu me mahimmanci Dana kusa mantawa thank you sweetheart Yayi maganar a zuciyarsa

Sannan ya mike yai musu sallama ya tafi Gida
yana zuwa ya dau wayarsa Layin Jalila ya kira domin ya gaya mata Jalal ya fasa tafiyar amma bata dauka ba

ILHAM tana Shiga daki tayi wani tsalle tare da jefa hannunta sama tace yes key tasaka wa kofar dakin ta sannan ta dawo ta dauki wayarta ta kira layin mahaifiyarta
"Hello Mami"
"Na'am ya ake cikine?"
"Albishirinki"
"Goro"
"Yafasa tafiyar nan dazu Jawwad ya kawo shi Gida yafasa"
"Ke dan Allah dagaske koda wasa"
"Wallahi mami ya dawo"
"Kai amma Jawwad din nan ya kyauta, ya saukaka mana aiki"
"Wallahi kuwa mami"
"To yanxu dai ba sanya zamuyi ba, ki kara dagewa Ilham duk randa burinmu ya cika sekin fini amfana"
"Insha Allah mami zan dage"
"Yawwa yarinyar kirki se na jiki"
"To mami ki gaida mutan gidan"
"Yawwa zasuji"


"Jalila kinga gidan Maman annur ta haihu ban samu na shiga naga babynba zo muje,
Muyi mata barka"
"Ummi wai ita barkan nan dole ce tunda dai bata mutu ba da ranta"
"Ohh ni maryam Jalila mutum ya dau ciki wata Tara ya sauke lafiya tsakanin mutuwa da rayuwa ai aje acemasa barka"

"Ummi naje gobe in Allah ya kaimu yanzu bana jin dadin jikina"
"To Allah ya sawwake miki zo ki rufe kofar gidan"
Jalila tabi Ummi ta rufe gidan sannan dawo cikin Gida ta dakko wayarta ta dawo palour ta Missed call din Jawwad ta gani
"Yasalam yaushe Yaya Jawwad ya kirani ban Sani ba"
Kiransa tayi ya katse kiran sannan ya kirata
"Abunda zan gaya miki ya Riga ya wuceki tunda baki daga wayar ba, se yanzu"
Cike da shagwaba Jalila ta fara magana
"Haba yayana na kaina bangani ba ne se yanzu amma tuba nake ranka ya Dade"
Murmushi yayi
"Sisyna ta wa ni kadai"
"Nanan fa?"
"A'a banda ita"
"Sena gaya mata"
Dariya sukayi gaba daya
"Yayana me yasaka farinciki hakane labarta min"

"Kece Jalila"
"Nikuma"
"Eh mana"
"Ya akayi nasaka farincki"
"Saboda kin tunatar dani abu me mahimmanci
Jalal wani abokinsa ne ya zigashi yayi tafiyar nan Wanda ni da Sam banyi tunanin hakan ba kuma nasan da wata manufar ya zigashi, kuma wai tare zasu tafi
Yanzu dai zancen danake miki Jalal yana Gida yafasa tafiyar ya dawo"
Wata nannauyar ajiyar zuciya Jalila tayi
"Alhamdilillah am glad to hear this from you Allah yakara kiyayewa ya shiryeshi"
"Ameen sisyna muna godiya da gudunmuwarki
Allah yasaka da mafificin Alkhairi ya jikan Abeenmu"
"Ameen dan uwan da babu irinsa"
"Ki gaida ummina"
"Zataji insha Allah na gaida maama,"
Sukayi sallamaa Jalila tace Alhamdilillah
Siyama ta kira ta labarta mata sukayi ta murna tare bakin Jalila yaki rufuwa

Bayan Ummi ta dawo ne ta lura da farin cikin da Jalila take sewani walwala take
"Waime ya farune naga kinata wannan farincikin haka baby gayamin mana"
Dariya Jalila tayi
"Hajiya Ummi ba komai kawai tsintar kaina? nayi cikin farin ciki Mara misaltuwa"
"To Allah yasa alkhairine"
"Ameen ummina"
Haka Jalila tayi kwanan farin ciki Allah ya temaketa yau batayi mafarkan ba balle a tsorata ta
Lokacin tafiya islamiyya yayi yan matan sun dau guga a cikin dogayen hijjaban makaranta suna tafe suna hira yau fuskar Jalila fes ba wata damuwa Dan haka yau ajinsu suka tabbatar ta dawo banda hira da surutu ba abinda sukeyi ana hirar yaushe gamo wasu na mata tambayar meyasa randa tazo bata walwala kwanakin nan sunyi missing dinta
Hayaniyar ce ta ishi malam Naziru ya fito Dan ya tsawatar musu
Yana zuwa Jalila yayiwa kashedi
"Yau malam baya nan balle ya ceceki wallahi naji surutu a ajin nan babu ruwana ke zan zanewa jikinki"
Befi yan mintuna da tafiya ba Jalila tabasu sabon topic suka barke da hira hada shewa itakuma ta silale ta gudu ta bar ajin ta nufi babban aji
Malam Naxeeru ne yakuma komawa domin casa yan ajin kuma ya kudiri takan Jalila ze fara
Yana zuwa ajin ya nemeta yarasa ya tambayi tana ina sukace basu saniba aikuwa suka sha jibga yayinda uwar gayya ta fece sun daku ragwaye na kuka, yayinda masu karfin hali kena zuci Dan malam Naziru ya iya bulala,

"Tsinanniyar yarinya ta jamana duka ta gudu shegiya azzaluma wallahi ban yafe ba"
Cewar wata daliba aikuwa a fusace siyama ta juyo

"Allah ya isanki ta biki haba lubabatu ai ba matsa bakinki tayi tace kiyi magana ba kuma Jalila ba shegiya bace"

"Nafada wallahi ban yafe ba"
Lubabatu ta maimaita
"Ke nima ba yafewar nayi ba wallahi wannan azabar dukaa itakuma ta gudu"
Wata dalibar tayi magana Siyama na kokarin tarewa Jalila wasu suka hayayyako mata ana haka Sega Jalila ta dawo gaba daya sukayi tsit saboda sunsan hali indai bakine Jalila akwai baki
Ba'a kada ita a fanni surutu
"Yanaji ana surutu amma ina shigowa naji anyi tsit"
"Aminiya ba komai hira kawai mukeyi,
Amma fa malam Naziru yace yau in yakamaki kashinkj ya bushe"
Siyama ta fada tana dariya
"Hh base ya ganni ba ai bazan bari mu haduba indai yaune"


Ilham ce ta sha kwalliya kaman ka saceta ka gudu se karairaya take ta shirya abinci a Warmer's ta nufi part din
Jalal ba kowa a parlour dan haka ta aje a parlour ta karasa bedroom dinsa
Dogon wando ne ajikinsa se vest ya na gefen gadonsa yana ta busa shisha
Sallama tayi da mamakinta taji ya amsa, a hankali ta tako gabansa cikin iyayi tafara magana
"Yaya dama mummy ce tayi girki tace in kawo maka"
"Ina abincin"?
Yai maganar kaman ba yaso
"Yana parlour"
Gyada kai yayi
"Thank you"
"Amma zakaci ko?"
"Maybe"
Shine kawai abinda yace seda ta juya zata tafi ya daga kai ya kalleta
Ganinta yayi kamar wata balbela, gashi se wani kariraya takeyi sam bata da wani shape se tsawo amma fara ce tas
Murmushi yayi a ransa yarinya Karama amma ta iya wannan shirmen ya Dan ja tsaki
Itakam fita tayi tana addu'ar Allah yasa yaci abincin nan


Kamar yadda Jalila tafada har aka tashi bata hadu da malam Naziru ba sunyo ayari guda yan ajin su daba yan ajinsu ba kowa na kokarin bin hanyar gidansu,
Anzo layinsu lubabatu suka tarar da yayan lubabatu a bakin hanya da abokansa se shan sigari suke ga tarin karnuka a gabansu kaida kagansu kaga yan daba
Jalila tare suke tafiya da su lubabatu seda sukazo dai? inda matasan nan suke Jalila secewa tayi
"Tab Siyama kinsan wani abu
ga irinsu Jalal da gayyar abokanan Sa baki kullum cikin hayaki, kalli yadda bakin yayan lubaba yayi saboda zukar taba lebensa duk ya zazzage,
Ni bansan ya akayi bakin Jalal bezama haka ba wai shantu"

Wata ashar yayan lubaba yasaki yayo kan su shida abokanansa tareda karnukan kankace meye wannan ayarin yan makaranta sun watse ba kowa a hanyar
Jalila ta dinga dariya yan mata manya da kanana sun zage sun kwashi gudu
Sukace gaskiya gobe insha Allah se mun kai karar yarinyar nan gurin malam aja mata kunne
"Jalila lafiya kike ta haki haka ?"
"Bakomai Ummi karnukan bakin anguwane suka biyomu"

Jalal ya bude Warmer's dinda Ilham ta kawo yaga cous? tsaki ya ja lallai ma yarinyar nan tasan bayacin wannan abun amma shine aka kawo masa rufewa yayi ya tafi gidansu Jawwad Dan samun abinda zeci a can
Ya tarar Jawwad yatafi masallaci dan haka ya nemi guri ya zauna yana jiran dawowarsa

Wayar Jawwad ce ta dinga ringing ta cikawa Jalal kunne Dan haka yaje ya dauka da nufin fadawa me kiran me wayar baya nan
Ya daga wayar yasaka a kunnensa

"Hello yayana "
Shiru yayi be amsa ba
"Yaya Jawwad yanaji kayi shiru bakajine?"
"Bashi bane"
Ya bata amsa a takaice
"Au Ashe Kaine ya akayi kafasa tafiyar,
Kacigaba da rashin ji kana biyewa abokan banza wataran se sun jaka inda zasu kasheka"

Share please
More comments more typing........


=؊??=؊??=؊??=؊??=؊??
[8/31, 8:26 AM] Safiyya:
? ? _ABDUL? JALAL_
? ? ? ? ?? (2020)

? ? ? _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
? ? (Daddy's girl)

? ? ? ? ? ? ? ?PAGE-? 18

PART 1

? _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,? ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta? wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar

07063065680
Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din


I want comments not stickers or just thanks=?"?=?"?=?"?=?"?
Your comments give me courage

? ? ? ? ? ? ? -My First Novel-

"Da kasake ka tafi da yanzu ka gane illar hawayen iyaye"

"Kinmanta kashedin danayi miki game dani ko? Har yanzu baki fasa min shishigi ba ki ji da rayuwarki, ba ruwanki da rayuwata"
Ya katse wayar ya aje tare da fadin
"Jarababbiya kawai, ko ina ruwanta dani oho, zan sauke mata wannan taurin kan"

Jawwad ne ya dawo ya tarar dashi
"Yunwa fa nakeji, find something for me to eat"
"Kamar me kake so"
"Komeye ma amma banda tuwo
Yarinyar nan ta kaimin abinci nazata wani abun kirkin ne ashe wannan abinne dabana ci saboda tsabar ta rainani aikuwa zan koyamata hankali"

"Ai kai abunda baka ci dayawa wanne daga ciki"
"Kaga ni abar wannan maganar me kukayi yau"
"Nima banci abincin ba alala sukayi yau"
"What alala kuma,"

Ya Dan girgiza kai
"Kasan itama bana ci"
"Anyway bari in canza kaya muje restaurant se muci"

"Kar ka kaini inda za abani abunda za bata min ciki kasan bana son jagwal gwalo"
Murmushi Jawwad yayi

"Jalal kaima yakamata ka canza kayan nan kasaka manyan kaya"
"Nifa bana son wannan kayan nauyin isa ta suke da zafi"
"Please dan Allah kasa manyan kaya"

Jawwad ya fada yana Ciro masa wata hadaddiyar Shadda coffee colour yaita lallaba shi har ya yadda ya karba ya canza kayan yasaka shaddar nan,
Ba karamin kyau Jalal yayi a cikin kayan nan ba manyan kaya ba karamin fito da kamalar namiji yake ba Jawwad yaita koda shi, yana masa hotuna yana yaba masa yayi kyau,
Haka suka shirya suka tafi restaurant cin abinci

Jalila ce a office din malamai ta inda suka shiga ba ta nan suke fita ba suna mata fada akan rashin ji
Saboda ankawo kararta akan jiya ta tsokanowa yan uwanta dalibai yan daba, masu zaginta sunayi irinsu malam Naziru, masuyi mata nasiha sunayi ita dai Jalila shiru tayi batace komai ba? suka gama ta tashi ta koma aji tanata cika tana batsewa
? Ba a jima ba malam Naziru ya shigo ajinsu da hanzari yana kiranta
"Jalila zancen musabakar nan ne ya taso wadda za ayi a Abuja? sati me zuwa insha Allah"
Wani irin mugun kallo Jalila tayi masa tai masa banza
? "Jalila da ke nake fa kije ki jadadda hadda abun yazo mana a bazata dukda nasan bani da damuwa akanki"
"Ba inda zani kunemi me zuwa karkuje inja muku magana, yaza ayi kamata taje musabaka "

Tafada tana hade rai
Sekuma ya Dan sha jinin jikinsa
"Wai meye hakane Jalila ana magana kina wani zance daban ina miki magana"
Mikewa tsaye tayi tare da kara hade rai

"Nace fa bazani ba anemi wasu suyi ni bazani ba,"
Ta dau Jakarta ta bar ajin
Office malam Naziru yakoma yana mita
"Kajimin ja'irar yarinya nizata cewa bazata je musbaka ba wai anemi me zuwa"
Malam Yusuf ne yace
"Banga laifinta ba nan kuka sata a gaba da fada bama kai se yanzu kuma bukatarku ta taso kuce tazo tayi muku,
irin wannan yaran nasiha ake musu ba zagi ba duk abu suna da irin baiwarsu"
"Hmm ni ba wannan ba tunanin mafita nake kasan ta da taurin kai abune me wahala taja ga malam baya nan"

Jawwad ne ya tashi ya tafi amsa waya yayinda Jalal ya dukufa yana cin abinci saboda yunwar dayake Ji
"Masha Allah"
Wata budurwa ta fada, mikewa tayi daga inda take tazo kujerar gaban Jalal ta janyo ta zauna
"Sannu dai barka da wannan lokacin"

Dan dagowa yayi ya kalleta, ya maida kai ya cigaba da cin abincinsa
"Ehmm nace ba Dan Allah magana nakeso muyi da kai"

Still shiru yayi mata yaki magana haka tacigaba da surutun ta ko kallonta yakiyi
Jawwad ne ya dawo yasamu guri ya zauna
"Sannunku da fatan ban takura muku ba"
Jawwad yafada yana murmushi

"Mtseww kaga ci abunda zakaci mutashi mu tafi ni nagama kasan bana son kallo"
Jalal yayi maganar a fusace

"Dama yana magana?"
Budurwar ta tambaya
Dariya Jawwad yayi

"yanayi mana, gashi kuwa kinji"

"Amma nayi masa magana ya shareni"
Se Jawwad yai niyyar tsokanar Jalal
"Au be kulaki ba, aikuwa yana magana, haba bros ya zata na maka magana ka shareta"

Wani takaici ne ya tokare wa Jalal shi Sam baya San sabga da mata dan haka banza yai musu
"Au bazakayi maganar ba kuwa"
"Inaga nidin ce baze kulaba, ba komai nagode"
Ta mike zata tafi
"Kiyi hakuri fa Dan uwan nawane se a hankali"

Murmushi tayiwa Jawwad sannan ta mike ta bar gurin
Wani uban tsaki Jalal yayi yana hararar Jawwad
Sunkuyar da kai Jawwad yayi yana dariya Jalal ji yayi kamar ya naushi Jawwad
Haka Jawwad yagama cin abincin suka nufi Gida

Tunda Jalila ta koma gida sedata shafe kwana uku bata zuwa makaranta
Ummi tayi? tagaya mata meyasa bata zuwa makaranta amma taki, kullum seta ce mata bata da lafiya,
Seda malam Naziru da wasu malamai suka biyo Jalila har Gida akan takoma makaranta saboda batun musabaka
Ummi tace musu ba komai indai Jalila ce zataje musabakar insha Allah sukayi mata godiya suka tafi
Ta dawo Gida taitama Jalila fada meyasa zatace bazatayi musabaka ba har malamanta su biyota Gida suna lallabaki
Dan tsuke fuska Jalila tayi
"Ummi bakiga abunda sukayimin ba suka dinga min masifa kuma se yanzu yawani zo wai inje musabaka wallahi Dan kinsa bakine kuma Dan malam babba zani wallahi da bazanje ba"
"To yanzun ma kice bazakiba mana in dai za a biyewa halinki ai kullum se an zanekima ba fada ba"

Kayan da Jawwad yabashi yasaka ne duk suka isheshi da zafi Dan haka suna dawowa gidan su ya wuce domin ya canza wasu kayan zuwa kananan kayan daya saba sawa
Yana bedroom dinsa yana kokarin canza kaya yaji motsin Ilham a palour zata kwashe Warmer's din data kawo masa abinci, bubbudewa tayi taga baici ba
Fitowa parlour yayi ya tsaya a bakin kofa Dan dago kai tayi ta kalleshi masha Allah wani irin kyau taga yayi me daukar hankali kayan sun masa kyau sosai ta Dan kura masa ido
"Ke me ye haka uban me kike kallo, saboda tsabar kin rainamin hankali kika kawomin wannan abincin, kuma kinsan banacin wannan abun amma kika dakko kika kawomin yaushe nafara wasa dake dazaki min wannan rashin mutuncin"
Yasalam ta manta baya cin cous?
"Am...am wallahi Yaya namanta....."
"Shut up kwashe su kibarmin daki sokuwa kawai komai kin manta shiyasa kike dakikiya both islamiyya da boko kanki Sam baya Ja fita ni"

Ai garani ina zuwa kaifa
Ta fada a zuciyarta ta kwashe kayan tana zumbura baki tana kunkuni
"Ke ni kikewa kunkuni na tattakaki wallahi kinsan halina sha? kawai"
Sum? ta bar dakin

"Indai zaka biyewa mata se Jininka ya hau"
Yai maganar a fili tare da yin tsaki

Jalila ta dage da tilawar haddarta malam Naziru se kuma lallaba Jalila yake saboda yana son taje musu musabaka Abuja
Kullum dare se tayi waya da Jawwad se suyi kwanaki basuyi waya da Nana a wayaba, amma kullum suna manne da Jawwad a waya
Yauma yana dakin Jalal suna hira Jalila ta kira waya in suna wayar nan Jalal bata masa rai sukeyi? Jawwad kuma yaita biye mata
"Yayana saura kwana uku insha Allah zamuje Abuja musabaka"

"Masha Allah, badaban inada lectures ba ranar dase nazo garin Abuja naga yadda kanawata zatayi musabaka in bata kwarin gwiwa"

"Koba ka nan kalamanka zasu bani karfin gwiwa, kasani a addu'arka Dan Allah"
? "Addu'a kullum cikin yimiki nake Insha Allah zakiyi nasara"
"Godiya nake yayana ka gaida mutan gidan"
"Zasuji insha Allah, muna tare da yayanki Jalal zan gaya masa shima ya yi miki aduu'a"
Jalila dariya ta kwashe da ita tare da kashe wayar

"Jalal kanwarka zataje musabaka Abuja ranar Juma a insha Allah kasata a addu 'a"
Jawwad yafada yana kallonsa
? "Kanwarka dai kasan ni bana kalen dangi"
"Kanwa tawace kalen dangi Jalal? kaima kanwarka ce Jalila ce fa"
Shiru Jalal yai be kuma cewa komai ba
Dama wannan yarinyar har wani karatu ta iya zata je musabaka kil

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login