Showing 60001 words to 63000 words out of 129540 words

Chapter 21 - ABDUL JALAL Hausa Novel

08 Oct 2024

6685

Abba yayi
"Hakane amma Dan mu tsorata ta ne mun yanke seta kammala wannan ajin da take, sannan zata dawo nan, kasan wasiyyar kanina kenan, gara ta dawo nan maybe sekaga ta nutsu"
"Hakane, to Abba ita ummin fa haka zata cigaba da zama ita ka dai"
"A a Jawwad itama zata koma gurin iyayenta ne, intaje insun karbeta se akai Jalila taga dangin mahaifiyarta, ina ganin in Jalila ta dawo nan bata ganin idon umminta zata dena fitina"
"Hakan yayi kyau Abba Allah yasa mudace,"
"Ameen Jawwad"
Haka suka cigaba da tadi daga baya Jawwad ya fito ya koma gurin Jalal amma da yaje baya nan ya kirashi a waya amma baya dagawa,
Girgiza kai Jawwad, yayi yasan ba makawa Jalal ya tafi mashaya
Aikuwa hasashen Jawwad yazama gaskiya domin kuwa don kuwa bayan abunda yafaru tsakaninsa da Hannah da Jawwad, Jalal yakoma Gida yaji ransa yakiyi masa dadi, ransa yagama baci Dan haka ya fita ya tafi mashaya
Aikuwa Jeje ya takewa Jalal cikinsa da giya yayi mankas ya fita hayyacinsa sannan ya kalli Jalal
"Mutumina wai me yabata maka raine haka naganka some how"
Cike da maye Jalal yafara magana yana tangadi
"Wata usless creature ce take son takurawa rayuwa ta, ga Jawwad shima ya bata min rai mtseww, wai meyasa mata suke da matsala kasan mene ma"?
Murmushi Jeje yayi
"sekafada nawan"
"Kasan wannan kanwar tawa ko? Ilham itama fa hadamin zafi tayi da safe so nayi in tattakata amma Jawwad ya hanani kaga itama wannan banzar da take takuramin wallahi so nake inyi maganinta"
Seda Jeje yakuma banka masa giya sannan yace
"To meye a ciki man Hannah ta kai macen daza a sota she's so beautiful fa" Jeje ya dakko waya yana nuna masa hotunan Hannah da wasu irin kaya a jikinta me bayyana surarta
Ture hannunsa Jaalal yayi yana tsaki
"Kai jeje ni bana sonta bana son shirme aikin banza kaima batamin rai zakayi meye hakane kakeyi"
Jalal Ya mike yana tangadi yana shirin tafiya
Jeje a ransa yace lallai gayen nan akwai taurin kai a bugen ma yana da lissafi amma muje zuwa zaka gane kuskuren ka
A zahiri kuma mikewa Jeje yayi ya riko Jalal in bahakaba ze iya faduwa, Dan baze iya tuki ba Dan sosai yake tangadi

Ilham ce take ta kaiwa tana kawowa a dakinta tana tunanin me yakamata tayine, dan tayi Alkawarin fitinar Jalal tako ina bazata bari yafara soyayya da wata banza ba, ba itaba Dan hakan dai? yake da rushewar shirinmu ana samun kuskure komai ze lalace, dabara ce ta fado mata
Dan haka gaban mudubi taje ta zauna, ta fara shafa mayuka a jikinta, tareda fara tsara simple make up a fuskarta, dogon wando tasaka skin tied se wata karamar Riga body hook, ta dakko wannan turaren ta shafe jikinta da shi, parking din gashinta tayi ta Dan Dora mayafi akanta ta nufi hanyar fita
Jeje ne yakawo Jalal gida a buge part dinsa ya kaishi ya kwantar da shi
Jawwad da yake kofar gida yaga wucewar motar Jalal koba a gaya masa ba yasan Jeje ne yakawo Jalal, kuma ba makawa a buge yake, girgiza kai Jawwad yayi cikin bacin rai yakoma cikin gida
Bayan jeje ya kwantar da Jalal ne yazo fitowa daga part din Jalal sukayi clashing da Ilham
"Wow so cute, common beb u look so beautiful"
Jeje yai maganar yana mata wani shedanin kallo
"Kai kashiga hankalinka, ka kiyayeni, bani hanya"
"Meyasa kikeso in baki hanya me zakije kiyi masa? Gaskiya na kyasa ya za ayine?"
Wani mugun kallo Ilham tayi masa
"Eh kaman ba gidan ubanka bane nan, meye na tambayata me zanyi masa kai me kayi masa, ka kiyayeni ka fita hanyata, niba Sa arka bace sakarai kawai"
Ta hankade Jeje ta wuce ajiyar zuciya Jeje yayi "gaskiya yarinyar nan ta hadu I have to do something"
Yasa kai ya fice, Ilham har cikin bedroom din Jalal ta shiga ta ganshi kwance yayi dai? akan gado yana bacci. Murmushi Ilham tayi ta shiga cikin dakin ta samu gefen Jalal ta zauna hannu tasa ta Dan shafa sajensa zuwa cikin sumarsa
Dan jijjigashi take
"Yaya Jalal wake up please"

Share please
More comments more typing................



=؊??=؊??=؊??=؊??=؊??
[9/12, 6:02 AM] +234 816 830 7871:
? ? _ABDUL? JALAL_
? ? ? ? ?? (2020)

? ? ? _ STORY & WRITTEN BY AISHAHUMAIRA_
? ? (Daddy's girl)

? ? ? ? ? ? ? ?PAGE-? 27

PART 1

? _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,? ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta? wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar

07063065680
Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din


Gaskiya comments nakeso ba sticker ba kokuma Just thanks in bahaka ba zan dena typing kullum
Special thanks to my group members ina Alfahari daku comments dinku na bani karfin gwiwa

? ?
? ? ?? -MY FIRST NOVEL-

A hankali ya bude idonsa da sukayi jawur, saboda buguwa ya mayar ya lumshe sannan ya fara magana a cikin mayae
"Ni wannan yarinyar bana sonta, narasa meyasa Jawwad yayi min hakane, nace masa bana so amma shi......se wani"
Sekuma yayi shiru, Ajiyar zuciya Ilham tayi tace"munafukan banza daga Jawwad har kanwar tasa, zasu gane kurensu
Matsawa takuma yi ta kwanta a jikinsa sannan ta Dan dago ta kalleshi
"Meyasa baka sonta"
"Mtseww nifa bana son tambaya, bana sonta kawai bata da hankali," ya Dan girgiza kai ya yamusta fuska warin turaren nan yaji da yabaya so
"Itakuma Ilham meyasa baka sonta?"
Dan bude ido yayi ya mayar ya lumshe"wannan fa kanwata ce, meyasa zanyi wani soyayya da ita, kanwata ce kawai"
Shigewa jikinsa ta kumayi sosai
"But I love you, karkayi soyayya da wata bayan ni, Ilham ce kawai take sonka, sauran duk bamasu kaunarka bane, Ilham tana sonka kaima kasota kaman yadda take sonka"
Dukda yana cikin maye setaga yayi murmushi"ka yadda zakaso Ilham"
"Bacci nakeji ki kyaleni da wannan mafarkin"
"Mafarki kake?"
Ya gyda mata kai "ya kusa faruwa a zahiri"
Tai maganar tana shafa gashin kirjinsa ya mutsa fuska yayi ya rike mata hannu"kidena bana so"
"Meyasa bakaso?"
Shiru yayi be ce mata komai ba
"Shikenan tunda bacci zakayi bari in tafi,"
Durkusowa tayi da nufin tayi kissing dinsa se ya juyad da kansa alamun baya so, kallonsa tayi
"Why?"
"Ki tashi ki bani guri nace miki bacci zanyi"
Gabanta ne ya fadi dataji yayai normal magana ba tare da maye ba, kallonsa tayi taga ya bude idonsa fes akanta, sekuma ya mayar ya lumshe yacigaba da bacci Ajiyar zuciya tayi tare da fading"Allah ya temakeni na dauka giyar tasakeshi ne"
Kissing dinshi tayi akan lips dinsa sannan ta mike ta fita ta nufi cikin Gida, me gadi ya hango fitowarta daga part din Jalal
"Kai me yarinyar nan take a bangaren yaron nan a wannan tsohon daren,
Allah ya kyauta bayan shan giya kuma yafara biye? mata, abun kunya kuma da kanwarsa Allah ya shirya"

Da safe Jalila tanata shirin makaranta, wata makwabciyarsu bata? wuce sa ar Jalila ba ta shigo tacewa Ummi Dan Allah ta sammata abunda ta girka ita tayi girkin takasa ci dayake tsohon ciki ne da ita
"Allah sarki hawwa'u Allah yaraba lafiya bari azuba miki
Jalila zubomata abinci"
Jalila kam zuwa yanzu Hawwa haushi take bata gani take tsabar kwadayine da iskanci komai bazata iya Ciba sena gurin ummi, Ummi kuma bata taba hanata ba ko kyararta
Jalila tana zumbura baki taje ta zubomata dataga ummi bata kallonta ta dungurar mata da kwanon da kayan tea
"Gashi nan kwadayayyiya seki hada Sa kanki niba Yar aikinki bace"
"Eh naji kwadayaiyiyyar ce ke in naki yazo maga yadda zakiyi"
"Bawani nan komai kidorawa ciki, dayana da baki se yace karya kike masa"
Dariya Hawwa tayi ta hada abincinta ta fara ci suna hira da ummi tana gama ci ta kama aman abincin nan dataci seda ta amayar tsaf
"Kai kekam kin banu sekace akanki aka fara ciki ga rakin tsiya ni bari in bar gidan nan tun kafin nima kisani aman"
Jalila tai maganar tareda daukar jakar makarantarta tayi waje
Girgiza kai ummi tayi indai Jalila ce bazata canza ba

Wajen karfe Tara sannan Jalal ya tashi daga nannauyan baccin da yayi kansa yana ciwo, jiyayi yana warin turaren Ilham tsaki yaja yafara tunanin abunda yafaru wannan wane irin sha? mafarki yayi kuma ma da Ilham (shi a zatonsa abunda yafaru mafarkine)
Mikewa yayi yaje yai wanka ya fito yayi sallar asuba karfe Tara na safe

Jalila tana kokarin shiga makaranta taji ana tayimata horn bata waiga ba ta koma gefe akakuma tahowa inda take a fusace tajiyo tana masifa
"Wai meye hakane anyi Horn na canza hanya ankuma biyoni if you like bi ta kaina komawaye"
Bude motar yayi ya fito tana dariya Allah yabaki hakuri Yar baba,
Yayan Hanan ne Abdallah yakawo Hanan makaranta murmushi Jalila tayi
"Au ai bansan kai bane ina kwana"
"Lafiya kalau ya mamanki"
"Tana lafiya"
Juyawa yayi ya kalli motar yace"ke Hanan fito mana kin wani Zauna a cikin mota"
Sannan ya dawo da kallonsa kan Jalila "Yar baba kaman kuwa kinsan daddy yace agaisheki har yabada sako abaki"
Hanan ya kalla wadda se wani cika take tana batsewa
"Hanan bani sakon nan"
A wulakance ta bude Jakarta ta miko masa wata Leda
Ya karba yabawa Jalila
"Kai amma nagode sosai Yaya Abdallah ka cewa baba Yar baba ta gode, Allah yasaka masa da Alkhairi yabashi abunda yake nema duniya da lahira, Allah yabashi ladan kyautatawa marainiya"
Ba Karamun burge Abdallah tayi ba,"zangaya masa insha Allah"
Tsaki Hanan tayi ta wuce abunta cikin school, Jalila ma cikin makaranta ta shige, duk zafin kan Hanan bata kuma kallon seat din Jalila ba balle takuma sha awar zama a gurin,
Zama Jalila tayi ta dakko abunda akabata chocolates ne kala? a ciki murmushi tayi gaskiya mutumin nan yana da kirki
Bayan anfita break Jalila taje seat din Hanan ta zauna a kusa da ita kawata ya kike
Wani mugun kallo Hanan tayi mata ta dauke kai, bude chocolate dinta tayi tafara sha sannan ta kalli Hanan kawas
"Bismillah"
"Abun ya fito daga gidanmu sannan kice insha ke dai da kike kwadayaiyiyya seki sha dama Dan talaka akwai iya shishshigi,"
Murmushi Jalila tayi sannan tace "duba ajin nan akwai yayan Wanda sukafi mahaifinki dukiya, amma abun be baki mamaki ba ina Yar talaka amma nake makarantar yayan attajirai kaman Hanan rasheed, ashema Baku wani Tara ba tunda har Yar matsiyata kamar Jalila Aliyu take a irin makarantar Ku"
Mike kafa Jalila tayi ta Dora a saman bencin
"In ana batun gata Hanan, be kamata kisaka baki ba, Dan baki da gatan da Jalila take dashi"
Jalila se gayamata bakaken maganganu take tana shan chocolate dinta, Hanan tana fargabar ramawa saboda gani take Jalila bata Risina ba zata iya maimaita mata abunda tai mata amma duk da haka ta dake tana ramawa

Jawwad ne yakuma dawowa gurin Jalal amma Jalal yayi masa banza yaki kulashi, haka ya hakura ya tafi ya kyaleshi

Bayan an tashi daga makaranta Jalila ta dawo Gida amma ummi bata nan wani bakin ciki Jalila taji ta tsani ta dawo Gida taga ummi bata nan
Waya ta dakko ta kira ummi
"Ummi ina kika tafi ne?"
"Kinganmu a asibiti Hawwa muka kawo ta haihu Dan ba rai yanzuma Karin jini ake mata"
Zaro ido Jalila tayi
"Wace hawwan dazu fa da safe tazo"
"Bayan tafiyarki tafara nakuda"
"To meyasa akayimata aure yanzu se wahala takesha?"
"Aa seki bari in danginta sunzo ki tambayesu"
"Allah yabaki hakuri itakuma Allah yabata lafiya amma Dan Allah ki dawo Gida"
"Bazan dawo ba din a can zan zauna"
Ummi ta kashe wayar

Seda Jalal ya shafe sati baya kula Jawwad, sekuma daga baya Dan kansa ya sakko, suka shirya
yayinda kullum se Jalal yaje mashaya, Hannah tasamu damar cigaba da cusa kanta, a gefe daya itama Ilham tanata nata kokarin, sunsaka Jalal a gaba, Jalal dai se kara shirircewa yake

Alhamdilillah Neman maganar Jalila daga Islamiyya har boko yayi sauki, ta fara nutsuwa, yayinda mahaifin Hanan keta kyautatawa Jalila, amma Jalila ta takurawa Hanan, kullum tana manne da ita, Hanan ta zageta ta gaya mata bakaken maganganu amma Jalila batajin haushi takance mata"Hanan mahaifinki yana da karamci, yana kyautata min, komai zakiyi min bazanji haushi ba, shiya hadamu kawance kuma ni na karba"
Hanan mulkinta take zubawa a cikin makarantar daga malamai har dalibai shakkata sukeyi,amma banda queen J

Watarana anayiwa wata Yar ajinsu Jalila birthday a aji, kunsan yayan masu kudi aka dinga jijjiga champaign suna sakinta a sama, suka dauki turare suka dinga fesawa a ajin sun ware kida suna cashewa
Hanan ce ta nufo ajin ta shiga tana shiga wannan kamshin turaren da akasaka ta shaka nan take ta fadi kasa dama tanada asthma, da sauri Jalila taje kanta tana jijjiga ta
Yan ajin tsayawa sukayi suna kallon Hanan data ke ta fama da numfashi,
Jalila ta dinga jijjigata "Hanan meyafaru, ki tashi"
Jalila taga hakan bazeyiba tasa ta dago Hanan ta rungumeta zata fita da ita amma jikinta yariga ya saki yan ajin suna kallo ba Wanda yabi takan Hanan saboda rashin mutuncinta balle ayi tunanin me temakamata
Jalila ce kawai taketa kici? da hanan, ana haka Sega siyama
"Jalila meyasameta?"
"Nima bansaniba amma kaman asthma ne,"
Jalila da siyama ne suka kama Hanan suka kaita school clinic akaimata abunda yakamata amma babu wani cigaba duk ta fita hayyacinta
Aka kira gidansu hanan aka sanar dasu, sukace akaita wani asibiti private anan likitan dayake duba hanan yake,
a motar makaranta aka saka hanan Jalila tana rungume da ita tana mata fifita
Suna zuwa aka karbeta aka fara yimata abunda yakamata har tasamu bacci
"Likitan ya kalli Jalila yace sister din kice"
Gyada masa kai tayi
"Ya akayi bansanki ba kuna kama sosai"
Banza? Jalila tayi masa tacigaba da kallon hanan har cikin zuciyarta ta kejin ba dadi halin da hanan ta shiga, saboda bata manta lokacin da hakan yafaru da ita a kanoba lokacin da Jalal ya duramata sigari, ta sha wahala amma condition din Hanan yafi worst
Se da baccin Hanan yayi nisa sosai, ga lokacin ta shi yayi Dan haka Jalila ta mike ta tafi Gida aka bar Hanan da wata malama a harabar asibitin taga daya daga cikin motocin gidansu Hanan ta shigo,
Ba ta tsyaba tayi tafiyarta Gida,
Ummi ke tambayarta ina ta tsaya tagaya mata abunda yafaru
Dan kallonta ummi tayi taga duk ta damu a ranta tace Allah sarki baby halinki halin abbanki ba kya riko sam,
"To Allah ya sawwake yabata lafiya"
"Ummi zakije dubata?"
Hararar Jalila tayi ta cigaba da aikin ta,
Washe gari da safe Jalila ta shirya ta dama kunun gyada ta zuba a flask ta tafi asibitin da aka kwantar da hanan, room din da Hanan take taje ta bude kofar ta shiga, mum Hanan ce a zaune tana ta fama da Hanan taci abinci taki, "ina kwana"
Jalila ta gaida Maman Hanan
"Ke mekikazo yi nan"?
"Hanan nazo dubawa"
"Waya nemeki, munji mungode, jeki Allah yabada lada"
"A a mummy dubanifa tazo, shigo kawata"
Hanan tayi maganar tana kallon Jalila,mikewa Jalila tayi taje gefen gadon Hanan ta zauna
"Sannu Hanan ya jikin baki"?
" da sauki Jalila, yau za a sallamemu ma"
"Allah yabaki lafiya, ga kunun gyada na kawomiki ni zan tafi makaranta"
"Jalila nagode sosai da abunda kikayimin jiya,"
"Bakomai manta kawata, Allah yabaki lafiya"
Jalila ta mike ta kalli mummy Hanan
"Mummy se anjima"
Dauke kai mummy tayi batace komai ba, Jalila na waigowa zata fita taci karo da Abdallah abakin kofa a tsaye, yaga duk abunda yafaru gaisawa sukayi ta ratseshi ta wuce
Bakin gadon Hanan yaje ya zauna"sannu autar mummy "
"Yaya kasan wani ABU?"
"A a sekin fada"
"Yanzu nakejin ban kyautaba abunda na dingayiwa Jalila a baya ba, bakaga yadda ta dinga kula dani jiyaba, kaman Yar uwata, ban tabajin naji babu dadi ba saboda na wulakanta mutum ba se akan Jalila"
Murmushi yayi"auta kinga illar wulakanta mutum ba, yanzu dai kwanta ki huta"
Tsaki mummy tayi ta tashi tabar dakin
? Tundaga wannan ranar Hanan ta sake da Jalila har ziyara take kaiwa Jalila, ga kyautatawa da mahaifin Hanan yake yiwa Jalila, a sanadin Jalila Hanan ta dena wasu daga cikin halayenta marasa kyau

Haka lokacin ya dinga tafiya Jalal ya cigaba da fuskantar barazana a cikin rayuwarsa ga Hannah tasashi gaba, gefe ga Ilham da itama take uzzurawa rayuwarsa danma ita Ilham yanacin kaniyarta, ga Jeje da yake ta kuma rusa rayuwar Jalal, lalacewa har tafi baya, danma Jawwad yana kokari akan Jalal
Lokaci? Jalila takan yi miyagun mafarkan data sabayi da Jalal
Abun yana damunta sosai a rai,
Duk mafarkan da take dashi se dai taganshi a mawuyacin hali.

Yaune ake taron iyaye da yan uwa na kimanin dalibai arba'in na set dinsu Jalila, taron ya kunshi manyan mutane da iyayen dalibai, taro yayi taro inda aka karrama dalibai da dama, can na hango Jalila cikin graduation gound tayi kyau matuka takara girma tayi wani irin kyau, Jalila tana cikin dalibai naga ba da aka karrama da iyayenta, ta karbi kyautuka da dama sunyi hotuna da malamai da dalibai yan uwanta, mussaman Hanan da siyama ga Jawwad da Abba gefe ga ummi sunji dadin yadda sukaga ana ji da Jalila a cikin dalibai, a matsayinta na shugabar dalibai tayi speech me matukar ma'ana, ta birge mutane da dama, sunyi kukan rabuwa da dalibai sakamakon shakuwa da sukayi, haka taro ya tashi farin ciki fal zukatan dalibai
? Bayan sunkoma gidane Jalila da Jawwad suka tafi yawo cikin garin Kaduna yayinda Abba da ummi suke tattaunawa akan makomar rayuwar Jalila, Jalila taji dadin fitar da sukayi da Yaya Jawwad sunsha yawo sosai tare da hira
"Baby naji dadin ganin yadda aka karrama ki gashi kinkara kyau kin girma u look so beautiful"
Murmushi Jalila tayi
"Yayana na kaina, jajircewar Abba ce tasa na taka duk wani matsayi a yanzu bazan manta karamcin Abba ba Allah yasaka masa da alkhairi"
"Ameen baby?"
"Amma Yaya Jawwad,Ina Jalal?"
Subucewa maganar tayi taji ta fito ba tare da ta shirya ba
Kallonta Jawwad yayi
"Meyasa kike tambayarsa bayan ba kyayimasa addua"
"Kawai tambaya nayi amma ina yimasa addu'a"
Gyada kai Jawwad yayi
"Jalila al amuran Jawwad se a hankali abun nasa sedai addu a kawai
Yana nan yadda kika sanshi, yama fida"
"Kuma har yanzu kana tareda shi?"
"Eh muna tare Jalila bazan iya rabuwa da shiba"
"Amma meyasa?"
"Kin manta alkawarinmu sekinzo kano zan gaya miki"
Gyada kai Jalila tayi sannan suka nufo Gida
Bayan sunkoma ne Abba da Jawwad suka tafi, tun bayan tafiyarsu Jalila ta fuskanci ummi bata da walwala tana cikin damuwa sosai lokaci? takan share hawaye
"Ummi wai meya farune me akayi miki, meyasa ki damuwa haka, kona bata miki Raine?"
"A a Jalila lokacine yayi

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login