Showing 93001 words to 96000 words out of 129540 words

Chapter 32 - ABDUL JALAL Hausa Novel

08 Oct 2024

6665

kuma ganinsa"
"Mhmmm" shine kawai abunda Jalila ta ce
"Tunda bazaki gayamin ya yake ba shikenan, ni nakirashi inji, ya Jalal dinki"?
"Jalal dina kuma?"
"Eh mana, tunda bazaki gayamin ya, Jawwad Dina ba, se in tambayeki ya Jalal, tunda bakya iya danne kishinki queen"
Dan dabarbarcewa Jalila tayi
"Kin fiye shirme Hanan, wane irin kishi, ya Mummy da Yaya Abdallah"
"Ya kike kokarin canza maganar ne, anyway kowa lafiya, hau what's app kiga status dina"
"To naji, saura inga shirme"
Hanan ta yi dariya
"Koma dai meye zaki gani"
Jalila ta bude what's app dinta taga Hanan ta turomata messages, ta bude hotunan dasukayine, hotunan sunyi kyau, tana duba dp din Hanan taga hoton Hanan da Jawwad, gashi be iya hade raiba, yayi murmushi, sunyi kyau shida Hanan, Jalila ji tayi kaman ta buga wayar da kasa
Dagaske kishin Yaya Jawwad nake, "yasalam" status din Hanan ta bude hotunan ne dai akan status din nanma ta rubuta kalaman soyayya, akan hotunanta da Jawwad
"Wai dagaske Hanan Yaya Jawwad takeso ko wasa, Hanan karkimin haka mana"
Tana kuma shiga daya hoton setaga hotonta da Jalal, wanda hanan tasata tai dariyar dole, shikuma Jalal yana kallonta Hanan ta rubuta
"perfect Match, Jalal and Jalila"
"Kutmelesi baki da hankali, kinci kai Hanan, Allah yayi min tsari, da mutum irin Jalal,"
Ta turawa Hanan daga nan ta rufe data dinta ta kashe wayar gaba daya
Sakkowa ta yi ta karasa gyaran gadon
Sannan tabar dakin gaskiyar Hanan Jalila kishi take, tarasa meyake mata dadi, harabar gidan ta fito, tana son ganin Jawwad, yau ba ta kaimasa abinci ba rabon data ganshi tun jiya da su Hanan suka tafi,
"Maybe ma Hanan ta kirashi suna shan soyayyarsu" wata zuciyar ta raya mata, tsaki Jalila tayi a fili, tarasa abunyi, kawai ta shiga gayaran flowers din harabar gidan, lokaci? tana tsaki
Abba ne ya fito ze fita yaganta tana gyaran flours, yayi murmushi yakarasa inda take yace
"Barka da safiya, yarinyar kirki, da kanki kike gyaran flowers din"
Murmushi ta yi
"Abba barka da fitowa"
"Yawwa Yar albarka, dakanki kike wannan, akin nasaka a nemo wani megadin daze dinga kulada flowers din"
"Abba dan dai gyaran flowers ai ba wuya koni se indingayi"
"A a baza ayi hakaba inkika fara zuwa school fa, wannan ba aikinki bane,
Yawwa munyi waya da umminki, tacemin tana nan tafe next week insha Allah, zatayi tafiyar nan"
"To Abba nima tagayamin,"
"Masha Allah, Allah yakawo mana ita lafiya"
"Ameen Abba"
Abba ya kalleta
"Ina fatan ba wata matsala zamanki a gidan nan ko"?
" babu wata Matsala Abba"
"Masha Allah, in akwai wani abu dai kimin magana"
"To Abba, Adawo lafiya"
"Allah yasa Jalila"
Daga haka Abba ya shiga motarsa ya fita

Bayan sun gama breakfast Jawwad ya kalli Jalal yace
"Am going"
"Where?" Jalal ya tambayeshi
"Gida mana ina son ganin Baby, naga kaman tana fushi dani, tun jiya ban kuma ganintaba, yauma ba ita ta kawo min Abinci ba"
Jalal ya mike kafa ba tareda ya kalli Jawwad ba yace
"Laifin me kamata, zatayi fushi?"
"Nima bansaniba Jalal, zan tambayeta dai, na damu da rashin ganinta"
Tsaki Jalal yayi
"Kafiye abun Haushi,"
"Eh naji, nikam se an nima"
"A sauka lafiya"
Daga haka Jawwad ya tafi Gida a harabar gidan ya Tarar da Jalila? ta na gyaran flowers, tabawa gate bata, dan haka batasan ya shigo ba, a hankali ya karasa inda take, juyowa tayi kawai tai tozali da Jawwad, seda ta dan tsorata
Murmushi yayi mata "matsoraciya ga idonki, am sorry nabaki tsoro ko"
Murmushi itama tayi masa ta girgiza kai, kallonsa take ta tuna maganar Hanan
"Kwana nayi ina mafarkinsa yanamin wannan murmushin"
Dan hade rai Jalila ta yi, wata zuciyar ta ce mata "wata kilama sunyi ways da Hanan" kara bata rai tayi,
Karasowa yayi daf da ita ya kalleta
"Baby laifin menayi miki hakane, kike hademin rai, yau duk bana jin dadi ban gankiba"
Rasa me zatace masa tayi dan kuwa babu laifin da yayi mata
"Yayana bakayimin laifin komaiba"
"Are u sure, naga kina fushi dani"
"Bazan iya fushi da kaiba"
"To shikenan kin tashi lafiya"?
" lafiya kalau,?
"Meyasa baki kawomin Abinci ba yau"? dan sunkuyar da kai tayi kasa
"Bakomai"
Maama ce tafito zata fita unguwa ta gansu tare, kallonsu ta yi ta dauke kai, Jawwad yace "Maama fita zakiyi?"
"Ka aikeni ne?"
"A a Maama a dawo lafiya"
Ta amsa da "Allah yasa"
Jalila ma tace "Adawo lafiya"
Kallon Jalila tayi ta dauke kai, taje ta bude motarta, ta shige tai waje,
Jawwad ya dawo da kallonsa kan Jalila
"Baby me yake damunkine naga baki da walwala tun jiya?"
Rasa mezatace tayi kawai setace masa
"Yaya Jawwad, meyasa abokinka bashida kirki? Jiya munje gidansu da daddare Mummy tanata kuka saboda shi Yaya ka dinga yi masa nasiha, ni a ganina tarayarka dashi bata da amfani"
Dan kurawa Jalila ido yayi na wasu sakanni, ya dan sunkuyar da kai sannan ya kuma kallon ta
"Jalila" ya kira sunanta
"Na am Yaya Jawwad" ya mike tsaye sannan yace mata
"Biyoni"
Ba musu ta bi bayansa, har palournsa sannan ya nuna mata guri ta zauna
"Jalila rabuwata da Jalal ba mafita baneba, ina tareda shima kalli halin da yake ciki, inaga inna rabu dashi, babu wasu abokan arziki a rayuwarsa kowa yayiwa dansa kashedi akan mu amala dashi, babu wasu mutanen kirki da yake rayuwa dasu, ko ransa ya baci sune mutanen da suke tarairayarsa, kowa yana kyamarsa shiyasa abune mawuyaci ya rabu da shaye? indai mutanen kirki sukayi karanci a rayuwarsa"
"To Yaya meyasa bazaka masa fada ba ya canza rayuwarsa haka yaga kowa yana yi, babban abun damuwar yadda yake treating mahaifiyarsa, Sam be dace ba" Jawwad yayi ajiyar zuciya
"Abunda yake tsakanin Jalal da mahaifiyarsa sirrine na rayuwarsa, amma dai a da mutumin arziki ne, bahaka yake ba, wani azzalumin aboki ya hadu dashi waishi Jeje shine silar lalacewar Jalal nayi iya kokarina ya rabu dashi, amma yaki, akwai wani mummunan kuduri da Jeje yake dashi akan Jalal Wanda ni kaina ban saniba, yanzu ga wata shedaniyar yarinya data shigo rayuwarsa, wadda nake kyautata zaton bakinsu daya da Jejen wai ita Hannah"
Dan dagowa JALILA tai ta kalleshi "Hannah kuma?"
"Eh Hannah, ta shigo rayuwar Jalal, iatama, Jalal kaman Wanda akayiwa asiri, gashi cutar dashi suke amma baze iya rabuwa dasuba, duk lokacin da nayi yinkurin yi masa nasiha, idan yayi kaman ze dauka seya birkicemin ya dingamin tsawa jijiyoyin kansa su kumbura, wani lokacin seya suma, shiyasa na barwa Allah komai nake masa addu a"
Shiru Jalila tayi wato Jawwad yasan Jalal yana wannan abun
Jawwad yabata labarin nan a dukunkune bata wani gane komaiba amma waye Jeje she needs to know him
Jawwad ya kuma dubanta
"Yana daga abunda yasa bazan iya rabuwa da Jalal ba halaccin mahaifinsa Jalila bayan Abba da Abee, daddyn Jalal yana cikin mutanene daba zan mantaba,Jalal ya kaunaceni tun ina dan talaka na, Jalilalokacin ina zuwa gidansu Jala, y'an fashi suka shigo gidan da daddare, tashin hankalin daddyn Jalal karsu yimin wani abu da sukaga haka se sukai kokarin harbina, Jalal ya taremin harbi, aka sameshi a memakona, Jalal seda yayi jinya a kasar waje, badan ya tureni ba ya tsaya.dani zasu samu "
Zare ido Jalila ta yi, ya gyada mata kai
"Da gaske Baby, idan nafara gaya miki halaccin da yayi min dayawa, dan haka idan na gujeshi nayi butulci, naci amanar kauna da soyayya da yayi min, kitayani yi masa addu a komai ze zama dai? insha Allah"
Nannauyar Ajiyar zuciya Jalila tayi "zan dinga yi masa addu a insha Allah"
"Yawwa baby in kakayi haka kingama min komai"
Daga nan JALILA ta tashi ta koma cikin Gida
Tunani ya hadu yayi mata yawa, Yaya Jawwad be bayyana mata komai sosai ba, yagayamata abubuwan a takaice kuma a dukunkune, ko wazata tambaya
Yana da kyau tasan waye Jejen nan, amma to kuma meya kawo Hannah cikin lamarin nan akwai kanshin bakinsu daya da Jeje kenan
"Kai JALILA karki bari kwakwalwarki tayi bindiga mana kin takurawa kanki akan wannan sha? dabe masa ciwon Kansa ba mutumin da giyarsa tafiye masa komai inyi rayuwata mana, haka Jalila ta cigaba da takura kanta, seta dena wannan tunanin son sanin waye Jalal"

Maama kuma tunda ta fita zuciyarta ke tafasa kan wannan kusanci da shakuwa dake tsakanin Jawwad da Jalila, saboda gani take abun nasu na shirin komawa soyayya, idan kuwa tana Raye bazata taba bari hakan tafaru ba, dama gidan wata abokiyar kasuwancinta zataje dan haka tana zuwa a gurguje tai abunda zatayi ta fito ta tafi gidan yayarta mairo
Tana zuwa kuwa tayi Sa a tana Gida dan gantalalliya ce ta innaniha dillaliyace yau tana nan anjima tana can
Ga ta da 'yan mata manya irinsu Sa ada da Naja da sauran mannensu amma har shabiyun rana ko wanke? ba suyiba
Daki suka shige da Maama da Yaya mairo, suka gaisa sannan
Yaya mairo ta kalleta "lafiya dai Zainab naganki haka?"
"Inafa lafiya game da wannan yarinyar ne"
"Wace yarinyar?"
"Jalila mana"
Yaya mairo tayi mutmushi
"Kice Jalila ta gurin arniya, ai jiya Naja data dawo tabani labarin komai, yarinya ta samu sakewar yin abunda taga dama,wai ta dawo gidanki da zama, narasa wace irin macece ke Zainab, ya akayi kika bari ta dawo miki Gida harta samu wannan yancin? Ashe kinshirya ganin ya'yanki sun fara binta coci"
Maama tai ajiyar zuciya
"Ni duk ba wannan ba Yaya, yaron nan fa Jawwad alamu sun fara nunamin kamar Santa yakeyi"
Zare Ido Yaya mairo tayi "ita wa din?"
"Haba Yaya mairo ya zaki dinga tambayata kaman baki San akan Wanda nake maganaba"
Yaya mairo ta jinjina kai
"Tirkashi, se yau na tabbatar da Zainab baki da wayo kina me hakan ke shirin faruwa garin Yaya?"
"Kedai bari duk yadda na kesa musu ido amma alamu sun fara nunamin hakan"
"To yanzu wani mataki kika dauka?"
"To Yaya mairo da na dauki wani mataki ai da banzo nanba"
"Gaskiyane, yanzu abunda ze faru zanzo gidan naku, zan zo in samesu, nasan abunda zanyi"
"To shikenan har na danji sanyi, wallahi"
"Karki damu kibar komai a hannuna"
Da haka sukayi sallama Maama ta koma Gida

Jeje ne ya kalli Hannah,
"Hanna akwai bukatar kara himma akan Jalal, idan mukace zamu cigaba da bin komai a hankali muna lallabashi to aikin nan base yiwuba"
"Nima nayi tunanin hakan amma me kake gani za ayi?"
"Birthday Jalal saura wata daya, a wannan lokacin nakeson mu kaddamar da komai, ko ya rayu yayi abunda mukeso, ko kuma...................

Ilham tana kwance ta lumshe ido, da alama tana son yin baccine, wayarta ta fara ringing, yamutsa fuska tayi takai hannu da niyyar yin rejecting kiran taga sunan malam Wada a jikin screen din, da sauri ta tashi zaune taje tasawa kofar dakinta key ta dawo ta daga kiran
Suka gaisa, sannan yace
" dama batun Yarinyar nan da kikayi min magana akanta ranan ne"
"Nagane Jalila kenan"
"Yawwa ita nayi bincike akanta amma akwai Matsala............


Share please
More comments more typing..........................


=؊??=؊??=؊??=؊??=؊??
[9/12, 6:02 AM] +234 816 830 7871:
? ? _ABDUL? JALAL_

? ? ? _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
? ? (Daddy's girl)

? ? ? ? ? ? ? ?PAGE-? 42
PART 1

? _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,? ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.
Ina me neman afuwarku masoyana, kwana biyu banyi typing ba wayata ta dan samu matsalane
Sannan ina kuma neman afuwarku bazan samu dinga yi muku posting kullum ba saboda zan koma lectures online, Nagode da kulawa

? ? ?? _My first novel_

Sassauta murya Ilham tayi sannan tace
"Malam matsala kaman yaya?
" eh nayi bincike akan yarinyar nan, amma abune mawuyaci asiri yayi tasiri akanta, zanyi kokari inga aikin dazanyi akanta amma kema sekin dage danaki kokarin domin samun nasarar kawar da ita gefe"
Ajiyr zuciya Ilham tayi,
"to shikenan malam nagode"
Sukayi sallama Ilham ta yi shiru nawani lokaci sannan tai kwafa
"indai makircine Jalila tasamu daidanta, nasan abunda zanyi"

Hanan tacigaba da kiran Jalila tana takuramata akan Jawwad, in Jalila taki dagawa tabita what's app, duk Yadda Jalila taso ta dinga kokarin danne kishinta amma takasa, itakuma hanan kaman Jalila tana zigata, ta dage ita Jawwad takeso.
Wajen karfe shadaya na safen yau yaya mairo tazo gidansu Jawwad, tunda matar nan tazo gaban Jalila yake faduwa, dan tasan yau ranar cimata mutuncine, tunda yaya mairo bata kaunarta,
Aikuwa tunda tazo take bakaken maganganu, ita dai Jalila ta makale a daki taki fitowa
? ? Jawwad sun gama breakfast dinsu, suna hira da Jalal, Nana ta kira Jawwad a waya
"yaya kana ina? Nazo part dinka baka nan?
"Nana ya akayine? Muna tareda Jalal"
"Yaya Jawwad, yaya mairoce take nemanka fa"
Gabansa ne yafadi
"Nana nikuma, me yafaru? Wani abun nayimata?
"wallahi bansaniba, se faman fada take niban san akan me take fadan ba, tace lallai kazo"
Ajiyar zuciya yayi
"to gani nan, ina zuwa"
Ya sauke wayar a hankali, Jalal ya kalleshi
"ya akayine?"
"wai yaya mairoce tazo tana nemana bansan me nayi mata ba, banason fadan? nan nata"
Tsaki Jalal yayi
"ni wallahi kana? bani mamaki, to dolene sekaje ai ba dole bane,"
"haba Jalal itama kamar uwa take a gurina fa, ya za ayi takirani naki zuwa"
"to haifarka tayi, sekayi tayi, tashi muje, akwai abunda zanyi a dakinka"
Jawwad ya Mike suka fito, suka tafi gidansu Jawwad, Jalal yayi part din Jawwad shikuma Jawwad yai cikin gida, Jawwad yana zuwa ya tarar da Yaya mairo, A palour Maama na kusa da ita, ya shiga cikin palour ya tsaya daga bakin kofa, ya durkusa yana gaida yaya mairo
"shigo mana kawani tsaya daga bakin kofa, kaman mara gaskiya, dama ba gaskiyarce da kaiba"
Karasawa yayi gabanta ya zauna ya da n risinar da kansa, sannan yace
"Nana tace kina nemana"
"eh ai naganka, takanas nazo gidan nan domin in maka Jan munne, Mahaifiyarka taje har gida ta sameni akan taga take2nka na shigewa wannan yarinya, yar gidan arniyar nan, to bari kaji kaf zuriarmu babu arna dan haka bazamu hada zuria dasuba jan kunne nake maka, karka kuskura kasawa zuciyarka zamu bari ka aureta, bamu shirya ganinka tsakanin massalaci da coci ba"
Dagowa yayi ya kalli yaya mairo
"haba Yaya, Jalila fa ba arniya bace kuma koba komai itama kanwata ce, kuma batada wani aibu"
Maama ce ta kalleshi
"au Jawwad abun har ya Kai ana maka magana kana mayarwa"
Yaya mairo ta kalleta
"ai shiyasa nace kinyi sake zainab,"
Jalila kam ga gaji da zaman daki ga shi ko karyawa batayiba, cikinta yafara kullewa ga sauran aikin gida, dazatayi, dan haka ta mike ta fito
Aikam karaf miyagun maganganun Yaya mairo suka fara dira a kunnuwanta
"muna da ya'n mata a dangi ga su Naja nan da kannenta ka duba a ciki, kasamu matar aure amma ka kiyayi kanka da fara soyayya da wannan yarinyar arniyar ragowar titi, suda basu san abun kunyaba, Allah ka dai yasan mazan da take bi, ni muslincin nasu ma ban yadda dashiba"
Gani sukayi ya kurawa kofar corridor ido suna juyawa, sukaga Jalila a bakin kofar tana hawaye
Yaya mairo ta tabe baki
"to almira da kika tsaya kina mana kuka ai ba karya nayiba"
Maama tace "to tama ce karya kike mana, aikowa yasani, nidai fatana a kyalemin yarona, ato bana son wannan shishshigin da ake masa"
Jawwad yace "haba Maama harda ke?"
Maama a tsawace tace "dalla rufemin baki,"
Yaya mairo ta juyo ta gyara zama sosai ta fuskanci Jalila
"ke ki bude kunnenki da kyau kijimu, gida dai gashi nan kinzo kin zauna, amma Jawwad karki sakawa ranki zamu bari ya aureki dan Zainab tace kusancinku da kuma zakewar dakike yayiwa kashedi nake miki yanzu, kisani 'yar dangi' yar cikakkun musulmai zamu aura masa, yar asali yar dangin uwa da uba ba wadda take da raunin nasaba ba, ba wanda yasan uwarki daga ina tazo ya akayi suka....
Juyawa Jalila tayi cikin kuka ta koma dakinsu, bazata iya jure wannan maganganunba, dan inta cigaba da tsayuwa za a iya samun matsala, Jawwad yabi Jalila da kallo, yana jin kukan Jalila har cikin ransa ya dawo da kallonsa kan Yaya mairo
"haba Yaya mairo, be kamata kisata gaba kina cin zarafinta ba, babu wanda Allah yayi shawara dashi lokacin da ya shiryamana kaddararmu, meye laifin Jalila anan"
Maama ce tace "wallahi ka kuma magana sena mareka, mu zaka gayawa abjnda ya dace muyi, kaika haifemu? Koka fimu sanin abunda ya dace da kai"
Yaya mairo tace
"kyaleshi ya dakeni, se insan kaji haushi"
Halima tana daga dakinta amma tana jin duk abunda akeyi, ranta ya baci matuka, bataji dadin abunda akayiwa Jalilan ba, cin mutuncin yayi yawa,
Ita kam Jalila tana zuwa dakinsu da kuka ta shiga, Nana tasan Yaya mairo ce tayi mata wani abun, dan girgiza kai Nana tayi ta Mike ta fito palour
Itama tazo ta tarar yaya Jawwad ya sunkuyar da kai yayi shiru Yaya mairo tanata? surfa masa fada hadi da cin mutuncin Jalila da mahaifiyarta, ita kanta daba ita akayiwa ba seda taji ba dadi, dakinsu ta koma ta tarar da Jalila tana kuka hada sheshseheka zama tayi tana rarrashinta, amma Jalila taki yin shiru
Seda yaya mairo tayi me isarta Maama tana tayata, Jawwad ko kai bekuma dagoawa ba balle yace zece wani abu seda sukagama sannan yace "Allah yabaku hakuri za a kiyaye Insha Allah" daga nan ya tashi ya fita
Yaya mairo ta dawo da kallonta kan Maama sannan tace "to kema bazama zakiyi ba ki mike tsaye ki tsaya akan yaranki ki tabbattar kin rabasu, ba ruwanku da ita in tagaji ta tattara ta koma inda ta fito, baze yiwuba ankawo miki arniya an ajiye tana mjamala da yayanki ba"
? Jiki a sanyaye Jawwad ya shiga dakinsa, yasamu guri ya zauna, ya kashingida a jikin kujera ya lumshe ido, Jalal dayasaka systems agabansa yana dannawa ya dan dago kai ya kalleshi ya maida kansa kan abunda yakeyi, Jalal gani yayi Jawwad bashi da niyyar yin magana, Jalal ya dan gyaran murya
"Me yafarune, me kayi mata?"
Seda Jawwad yaja wasu seconds sannan ya dago ya zauna sosai ya kalli Jalal
"Jalal narasa me Baby tayiwa Yaya mairo ta tsaneta haka ba"
Dan tabe baki Jalal yayi "Maybe Rashin kunya take mata"
"No Jalal, Jalila ba abunda tayi mata ta tsaneta, yanzu ma kiran datakemjn wai Maama taje ta sameta akan wai Jalila tana zakemin, wai kar insa ran zasu bari in aureta, babban abunda ya Kuma bata min rai, kiran Jalila da suke da arniya, me raunin nasaba, kuma Jalila taji, amma matar nan takiyin shiru tacigaba da cin zarafinta, ina jin kukan Jalila a cikin zuciyata"
Dan kurawa Jawwad ido yayi sannan

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login