Showing 111001 words to 114000 words out of 129540 words

Chapter 38 - ABDUL JALAL Hausa Novel

08 Oct 2024

6719

yadda take ganin kyan dakin Jawwad amma na Jalal ya fishi dayake Jalila bata taba zuwa part dinba, babban part ne, dan seka zata amaryace a ciki, an zuba dukiya a ciki sosai, Suna shiga ta karewa dakin kallo, palournsa katone sosai da dakuna biyu a ciki, akwai kitchen da toilet a palourn, ba laifi ko ina tsaf yake, ga katon tv plasma kusan rabin bango, palourn yasha labulaye da kujeru,sekace dakin amarya, ga kamshin turare yana tashi, kai bakace dakin mashayi bane
Jalal yana kwance akan 3 seater daga shi se wando 3 quarter da vest, yana ta danna wayarsa, yanajin sallamar Jawwad ya amsa a hankali, inba ka kalli Jalal ba bazaka san ya amsa ba, idonsa a lumshe yace,
"Jawwad kai nake jira dama"
"to gani ai, tashi kabani abunda zaka bani"
Jawwad ya amsa suna karasa shiga cikin palourn, Jalal sam be san Jawwad shida Jalila bane, sedayaji Jawwad yace "Jalila, karaso ki zauna mana" Jalal ya bude idonsa ya waiga yaga Jalila ce dagaske, seda gabansa ya fadi, doguwar riga ce a jikinta na material, se karamin mayafi da ta dora akanta, rigar kaman a jikinta aka dinka ta, se yanzu ya kara ganin ta rame sosai se idanuwa, gashi ta danyi duhu amma tayi kyau sosai, dauke kansa yayi daga kanta, be kuma cewa komai ba, Jalila ta shigo cikin palourn ta samu guri ta zauna a kasa kan carfet, kusa da kafar Jawwad, se zumbura baki take, Jawwad yace "Jalal gurinka mukazo fa"
"Ina jinka"
"Ka tashi mana, kaji dame mukazo"
Ba musu ya mike zaune, yana kallon Jawwad, "ina jinka"
"Dama abunda ya farune a Asibiti tsakaninka da Jalila shine mukazo mu baka hakuri, dan Allah kayi hakuri nasan bata kyauta ba, amma gata nan munzo tabaka hakuri"
Wallahi ba dan Yaya Jawwad ba babu abunda zesa Jalila tabawa wani Jalal hakuri kome zatayi masa na rashin kyautawa kuwa,
Jawwad ya kalli Jalila "Jalila kibawa Yayanki hakuri"
Sedata yatsuna fuska, dayake Jawwad baya ganinta, amma tana facing Jalal,
"Dan Allah kayi hakuri, bazan kara ba" Jalal yace
"Hmmm Jawwad kenan, ni nacemaka nayi fushine?"
"A a baka cemin ba, amma bamu kyauta bane, dole mu bada hakuri, da fatan an hakura"
"Se anwa mutum laifine za a bashi hakuri, ai har a tambayi koya hakura"
"Haba Jalal wannan ai gwalewa ne, tunda ta baka hakuri kayi hakuri mana"
Wani mugun hara Jalila takewa Jalal ganin se wani raina musu hankali yakeyi,
Wayar Jawwad ce tafara ringing, Hanan ce ta kirashi, bazeso yadaga agaban Jalila ba, dan yaga Hanan itama muguwar yar rigimace, yanzu setayi abunda Jalila zataji haushi, dan haka yace "please excuse me, Jalila jirani ina zuwa" ya tashi ya fita amsa waya, Jalal ya dora kafarsa daya kan daya, shima yaja tasa wayar, yana dannawa, Jalila se jan tsaki take, wayar Jalal ta fara vibration, ya saka a? kunnensa "Ya JJ ina jinka" Jalila ta dan kalleshi, Jeje in bata mantaba Jawwad ya gaya mata shine farkon lalacewar Jalal,
"Birthday kuma Jeje, ni kuka shiryawa birthday, yaushe kenan"? Ya danyi shiru sekuma yace
"Ok Allah ya kaimu, zanyi shawara ingani, if i can attend" yakuma cewa
"Eh kwana biyunne akwai abunda nakeyine, shiyasa bakwa ganina, amma zanzo very soon"
Jalila a zuciyarta tace
"gaskiya zanso inga wannan Jejen, inga ya yake, kuma meye manufarsa akan Jalal" Jalal ya gama wayar yayinda ta danyi nisa a cikin tunani, kamar an tsunkuleta ta daga kanta kawai sukayi ido hudu da Jalal yana kallonta, cikeda tsiwa, da gadara tace "Meye haka zaka wani tsuramin ido, lafiya?" Jalal yace
"idan kika kuma, zuwa inda nake da wannan dan gyalen, zan nuna miki ba lafiya ba, kalli dan gyalen da kika saka" dan bude baki Jalila tayi da mamaki,
"to ina ruwanka dani, dazaka dinga kallona, ni banason kallo, inma tsirara nake yawo meya shafeka"
"meye abun kallo a jikinki, mummuna dake, kwaila"
Jalika rasa meza tace tayi, dan batayi zaton jin wannan maganar daga bakinsa ba, shi kuma ya dauke kansa ya kunna sigari,
Ya tashi ya dakko, giya a fridge ya dawo ya zauna, binsa Jalila tayi da ido, ya bude ya dakko wayne cup dinsa ze zuba, da sauri tace
"Giya ce fa? Kai yanzu baka kunyar ubangiji, baka kunyar kowa, zaka sha giya a cikinka, meye hakane?"
Shiru yamata yafara zubawa a cup
"Wai dagaske shan zakayi,? Mikewa tayi cikin zafin nama, ta nufoshi a fusace daa nufin ta fizge, ko a jikinsa kuma be fasa abunda yai niyya ba
" in kika karaso inda nake zan baki mamaki, stay where u are, wallahi kikazo sekema kinsha, kuma ko a gaban Jawwad ne, se dai ya hadiyi zuciya" ba shiri Jalila taci birki,
"Wallahi tir da halinka, me abun kunya, angirma amma ba hankali, Allah ya tsareni da shan giya, yamin tsari da hali irin naka, gaba daya ka gama bata rayuwarka, baka da wani amfani daza kayiwa kanka ko kayiwa wani, a dai canza hali"
Banza yamata, yaci gaba da abunda yake, yayinda ta cigaba dagaya masa magan ganu son ranta, ganin bashi da niyyar denawa yasata nufi hanyar fita aiko tai karo da Jawwad
" Am sorry na barki kina jira ko, yi hakuri dan jirani kadan ss mu tafi? "
Ranta a bace tace" ni tafiya zanyi gaskiya "
" Me yasa? Ko fadan kuka sakeyi? "
"ni bazan cigaba da zama ana sabon Allah a gabana ba, ko kunya bayaji ya dakko giya yana sha, ni tafiya zanyi," daga hakka fuuuuu tai waje, Jawwad ya kalli inda Jalal yake, tabbas giyar yake sha, jikin Jawwad a sanyaye ya taka ya karasa gurin Jalal, sannan yace" Jalal yakamata kadinga boyewa in zaka sha giyar nan, bayyanar da lefunka ze cigaba da zubar maka da mutunci a idon mutane, bekamata ka sha giya a gaban Jalila ba, Jalal u have to do something good for your life rayuwa bazata tafi a haka ba"
A hankali JALAL ya aje cup din hannunsa ya dan kalli Jawwad
"Jawwad in har banji kunyar ubangiji ba na sha giya, meye kuma abun boyewa wani abun halitta, da bashi da wuta bashi da aljanna, Jawwad i don't know what to do, nasani abunda Jalila take fada gaskiyane bani da wani amfani dazanwa kaina ko nayiwa wani, ban san meyakamata inyi ba, ban san meyake damuna ba, fita kabani guri Jawwad, ka tashi kabarni, leave me alone i want have some rest "
? ? Ilham tana kitchen tana hada tea zata sha, dayake window kitchen a bude yake, kuma kana ganin harabar gidan ta nan, kawai taga Jalila ta fito daga part din Jalal, ta tsaya ta dan gyara mayafinta sannan ta nufi gate, mutsukke idonta takumayi don tabbatar da gaskiyar abinda ta gani, anya kuwa itace, da sauri ta juya ta bar kitchen din
? Jalal yafara fita hayyacinsa, idonsa yafara wannan abun, ga jijiyoyin kansa sun tashi, ya fadi kasa,Jawwad ya zo gabansa ya dutkusa ya dan dafashi "Allah yaye maka wannan matsalar" daga haka Jawwad ya Mike ya fito, dan haka shine samun nutsuwar Jalal, jawwad ya girgiza kai tareda yiwa Jalal fatan samun sassauci a rayuwarsa,
Fitar Jawwad keda wuya, Ilham ta fito daga cikin gida, ta nufi part din Jalal, sam bata hadu da Jawwad ba, tana zuwa kamshin turaren Jalila ya daki hancinta, tana kokarin tabbatarwa ne taga handkchief a tsakar palourn, da sauri takarasa ta dauka, ta kai hancinta ta shinshina, tabbas na Jalila ne, ga Jalal taganshi zube a kasa yana bacci, dora hannu tai aka ta fasa ihu, sekuma tayi saurin toshe bakinta,
"Na shiga uku Allah yasa ba abunda nake tunani bane, Jalal in kamin haka bakamin adalci ba, kaci amanata, kuma wallahi na tabbatar da abunda nake zargi sena kasheka na kasheta wallahi," shikam yafadi a gurin yana baccinsa
Surutu ta cigaba dayi, tana zambarwa a gurin, Jalal besan tanayi ba, tagaji tayi waje ta nufi cikin gida, dakinta ta shige ta kulle kofa, ta dinga zarya, wayarta ta dauka, ta kira malamin su, akayi sa a bugu biyu ya daga
"Malam akwai matsala fa"
"Mastalar mene haka?"
"sonake ka bincikamin, kagani aikin nan kuwa ba a samu wata matsala ba?"
"Matsala kuma kaman yaya, wani abu yafarune"?
"ni dai kawai ka bincikamin dan Allah,"
"To shikenan amma kibari seda safe, zan kiraki"
Sukayi sallama da malam, amma fafur batun bacci ya kauracewa idon Ilham se surutai da zage2, kaman ta zare, kai kace mahaukaciya ce, yadda taga rana haka taga dare.
Da safe Jalila dan cin Abinci tayi kadan bata wani ci dayawa ba takoma daki, dan tunda aka sallamota daga asibiti a daki take wuni, seda wani dalili take fitowa, Nana ta tafi gidan kawarta yau, ga Halima taje ganin gida, dama Maama ba shiga sabgarta take ba, tunani duk ya addabi Jalila, ga batada nutsuwa saboda rashin Ummi, ga kuma tunani daya addabeta akan rayuwar Jalal, hankalinta ya karkata kan son zuwa birthday Jalal, domin ganin waye Wannan Jejen,
Tunani duk ya dameta, dan haka ta tashi ta fito harabar gidan, tasamu guri ta zauna, tai shiru tana kallon flowers,
Da safe Ilham ta kuma kiran Malam a waya don tambayarsa ko ya bincikamata, yace
"Na duba, nayi bincike amma ba abunda ya sauya, aikinmu yana nan a tareda shi, aikin da akayivakansa har yanzu yana tareda shi"
Ajiyar zuciya Ilhan tayi, "har naji dadi, nagode sosai malam har naji hankalina ya kwanta"
"Ai bakiga ta kwanciyar hankali ba indai baki kauda wannan yarinyar ba, yakamata fa kisan halin da kike ciki don tabbatar da cikar burunku keda mahaifiyarki, asiri kawai baze tasiri akanta ba dole ki tashi kisan meya kamata kiyi, ina ganin itace zata kawo wa aikin nan matsala, ni nariga nagaya miki yanzu, shawara da dabara yarage naki"
"To shikenan nagode sosai, nikuma zan san abunda zanyi," sukayi sallama ta dakko handkerchief din Jalila ta fito se gidansu Nana, tayi sa a Jalila tana harabar gidan a zaune, gurin Jalila ta nufa, tana zuwa ta kalleta
"Gurin ki nazo zamuyi magana"
Banza Jalila tayi mata, "magana fa nake miki"
"in har zakizo inda nake bakimin sallama ba, banida lokacin saurararki" Ilham tasan inbatayi yadda Jalila take so ba, bazata kulata ba dan haka tai mata sallama
Jalila ta amsa sannan tace "ina jinki"
Ta kalli Jalila ta nuna mata handkerchief din tace mata "wannan kaman naki ko?"
Jalila ta kalli hannunta tace "ba kama bace nawane"
"A ina kika barshi?"
"A inda kika tsince shi" Jalila tabata amsa cike da rainin hankali
"zuwa nayi muyi magana ta fahimta, bata fada ba"
"Inma ta fadan kikazo a shirye nake"
"Jalila meya kai handkerchief dinki dakin Jalal, meye hadinki dashi?, Jalila ina miki kashedi na karshe tun kafin insa ki zubarda hawayenki, inma akwai wani abu a ranki akan Jalal gara ki cire, kishiga hankalinki dan wallahi zan iya illata kowaye akansa, duk wanda yai niyyar hana min cikar burina senasashi zubda hawaye, Jalila wannan ne kashedina dake na karshe, kifita a harkar Jalal, tun kafin ta kwabe miki"
Jalila tai mata kallon tsaf sannan tace
"A matsayinki nawa kike min wannan kashedin haka? Matsayin uwata ko ubana ko wadda ta isa dani? Hmmm gaskiyar dan uwanki dayake cewa bakida hankali, ni kinga wani abu me kama da soyayya tsakanin da wannaan bugaggen dabe maida sabon Allah komai ba,? Ilham ko mazan duniya sun kare ba abunda zanyi dashi, banga abun so a gurinsa ba, Allah ya tsareni son Jalal, bashida kamala da cikar dazesa inso mutum kamarshi, baya jerin irin mazan dasuke birge Jalila, dukda bansan naki kudurin akansa ba, nima ina da nawa kudirin akansa, babu soyayya, ko auren Jalal a kudurina, kuma ki dena wannan tunanin, amma kisani idan har kudurinki yaci karo da nawa akan Jalal to tabbas kisawa zuciyarki sena tarwatsa naki!!! Ban taba sa abu agabana nakasa ba Ilham, ina iya tarwatsa ko shirin uban waye domin biyan bukata ta, wallahi Ilham kinyi kadan kisani kuka, idan harkika sani kuka, nikuma namiki alkawarin zan illataki a inda babu wanda ze gani balle ya miki magani, Ilham zuciyarki zanwa Illa ta har gaba da abada, ganin Jalila kike bakisan wace itaba, tunda kika zabi zaman takun saka dani am ready for you "daga haka Jalila ta fizge handkerchief dinta tai cikin gida, yayinda Ilham ta sandare a gurin




Share please

Dan Allah kuyimin afuwa rashin jina akan lokaci, dakuma karancin pages din wasu lokutan, ayyuka ne sunmin yawa, in baku mantaba a baya kullum nake mumu posting, yanzu abubuwa ne sukamin yawa amma ina neman afuwar ku,
Ina alfahari daku, kuma ina sonku irin sosai din nan masoya, muje zuwa kucigaba da bina a sannu domin jin yadda zata kaya a cikin wannan novel
Taku har kullum
Daddys girl =?
?=?
?=?
?=?
?=??



More Comments More typing..............................


=؊??=؊??=؊??=؊??=؊??=؊??
[9/23, 10:27 AM] +234 802 426 7634:
? ? _ABDUL? JALAL_

? ? ? _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
? ? (Daddy's girl)

? ? ? ? ? ? ? ?PAGE-? 49
PART 1

? _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,? ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.

A har kullum ina jinjina da godiya ga masoya wannan novel nawa, comments dinku da addu oinku ina jin dainsu matuka, ina godiya kwarai dagaske,
Domin sharhi, gyara, kokuma shawara a nemeni ta what's app akan wannan lambar wayar
07063065680
Ina godiya matuka Allah yabar kauna

Ina amfani da wannan dama, domin?????
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
 mika ta a ziyyata ga yan uwa mutanen zazzau da dukkanin al ummar musulmi, na rashin sarkin zazzau
Alhaji shehu idris, ina fatan Allah ya jikansa yasa mutuwa hutuce, dashi da dukkanin al ummar musulmi da suka gabacemu
Allah ya rahamshesu in tamu tazo Allah yasa mucika da imani

? ?? ? ? ? ?? _My first novel_


Jalila na zuwa dakinsu ta kife akan gadonsu,
"Nikam Jalila nashiga uku, wace kaddara ce ta kawoni kano har nasan Jalal ne, wanda har rayuwarsa take neman hanamin tawa nutsuwar, Ummi dan Allah in kina raye duk inda kike ki dawo, nagaji da zaman nan ina cikin damuwa, Allah ka temakeni, kabani ikon jarraboyina na rayuwa"
Ta karasa maganar tan zubda hawaye, tayi me isarta sannan ta mike ta duba wayarta ta kira Hanan, seda ta kusa katsewa sannan Hanan ta daga, tana dagawa tace
"Tace afuwan ranki ya dade, ina wankane, ya jiki Jalila?
" Da sauki Hanan, ya Baba na dasu Abdallah "
" Baba baya gari yana bauchi, Yaya Abdallah ma haka dagani se mummy, ya jikin kinji sauki"
"jiki Alhamdilillah na warke ganima a gida"
"masha Allah, nakira Jawwad nace ya hadani dake amma se yacemin ba kya kusa, siyama ma takiraki bata shiga ki kirata dan Allah"
"zankirata Insha Allah"
Hanan ta ce
"nikan Jalila meyasameki haka har ya kai ga kisamu stroke ko wani abu na damunki ne?"
Se Jalila taji kaman Hanan ta sosamata inda yake mata kaikayine, batasan lokacin da hawaye yafara fita daga idonta ba
"Hanan ni meye ma baya damuna, ko kinsan cewa a halin yanzu sati biyu kenan, bansan inda ummi takeba ko a raye ko a mace ban saniba"
"Kamar yaya baki saniba, naje gidan fa ranar dazata taho kano, tacemin zatazo kuyi sallama zata wuce garinsu, kuma kice bakisan inda take ba"
"Hanan tunda Ummi ta tafi, mukayi waya da ita, wayanta be kara shiga ba anyi trying har angaji, karshe aka kira Abba aka gayamasa, wai wani me mota ya bigeta, kuma ya dauketa ya tafi da ita, bawanda yasan ina ya kaita, kotana raye kota mutu bamu saniba"
"Innalillahi wa inna ilaihi raji un, Jalila meyasa baki gayamin ba tunda wuri, kuma angayawa"yan sanda"?
"Hanan Abba yana iya kokarinsa amma har yanzu ba labarin Ummi ni harna hakura na fawwalawa Allah komai"
"kiyi hakuri Jalila, nasan abun da wuya a gurinki, amma mucigaba da addu a, insha Allah za a ganta, in daddy ya dawo zan sanar masa koda wani abu da za a iyayi akan matsalar, kiyi hakuri, Jalila insha Allah ummi tana raye za a ganta". Hanan ta ke rarrashin Jalila yayinda itama take zubarda hawaye, har cikin zuciyarta takejin matsanancin tausayin Jalila,
"Addu a ina nan inayi hanan, sedai kuma ina bukatar taku adduar"
"Insha Allah zan tayaki addu a, kinji kidena damuwa sosai, kar wani ciwon yakamaki"
"Karki damu kanwata na fawwalawa Allah komai, shi ze bani mafita"
"Masha Allah haka akeso queen muzama masu karbar kaddararmu a duk yadda tazo mana," domin kokarin kauda damuwar Jalila, se tace mata "nace ya gidannaku, ya mutuminki?"
"waye kuma mutumina?"
"kinfini saninsa Jalal mana"
"Yana gidansu"
"kai queen har yanzu kina masa rashin mutunci ko?"
"ko jiya ma seda mukayi, yau kuma wannan mahaukaciyar kanwar tasa tazo zatamin hauka, wai ita alallai son Jalal nake, wai in ban fita harkar saba seta sani kuka kiji fa,"
Dariya Hanan tayi, sannan tace
"queen J nasanki da kafiya, dan Allah karki bari Ilham tayi nasara, kizama silar shiryuwar Jalal, u can do it, kibata mamaki, kamar yadda kika bani"
"ke nina fara gajiya, gashi jarababbe, ga taurin kai gashi mugu, itakuma gani take sonsa nake ko uwar me zanyi da wannan makakken, dan wahala daga ita harshi"
"A a dai, banda cika baki, daga baya kizo kina zare ido akansa"
"Kut me kike nufi, mezanyi da wannan Allah ya rufamin asiri"
"Oho dai inda rabon an jone ne.... Jalila bata bari takarasa ba ta kashe wayar tareda fadi" ji muguwa zatamin mugun baki, ta Allah ba taki ba"
Daga haka Jalila ta Mike ta fito palour don samun dan abunda zata ci, Maama tana palour a zaune tana kallon Aljazeera,
Jalila tace "Maama sannu da gida"
Kallon Jalila tayi ta dauke kai ba tareda ta amsa mataba, har Jalila zata wuce kitchen, Abba ya shigo, ya dawo da wuri yau, da alamu ko mantuwa yayi, Jalila tace
"Abba sannu da zuwa"
"yawwa Jalila ya jiki ya gidan,"
"lpy qalau Abba"
Maama tacewa Abba "Sannu da zuwa"
Banza yayi mata da nufin shigewa dakinsa, Jalila tai farat tace "Abba, Maama na maka sannu da zuwa fa, bakace komai ba"
Abba ya wayance da "Yawwa maman Yara, yi hakuri banji bane" ya wayance kar Jalila ta gane, sannan

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login