Showing 18001 words to 21000 words out of 129540 words

Chapter 7 - ABDUL JALAL Hausa Novel

08 Oct 2024

6694

ina zamu hadu ?"
Yai mata tambayar cike zakuwa

"Inda muka saba haduwa a garden"
"To shikenan kaman karfe Nawa?"
"Da yamma by God will"
"Allah ya kaimu da rai da lafiya"
"I love u Aliyu"
"Love u more my dear"
"Kamin wani Alkawari"

"Wane Alkawari ?"
"Will u marry me?"

"I will me sunan mum insha Allah in dai family dinku zasu yarda dani su bani auren ki, bantaba soyayya ba se akanki, akanki nafara kuma daga kanki nagama insha Allah"
Ajiyar zuciya tayi

"Aliyu ka kwanta karka makara sallar Asuba kaimin addu a lamuran suzo da sauki"

"Kullum inayimana kiyi bacci me dadi zanzo a mafarkinki muje yawo"
Dariya sukayi suka kashe wayar

Kaman yadda tayi masa Alkawari haka tayi kokari seda ta fito daga Gida bawanda yasani

Inda suka saba haduwa yauma anan suka hadu
Se dai sabanin sauran kwanaki dasuka saba haduwa yau fuskarta dauke take damuwa

Kusa dashi ta zauna shiru ya Dan ratsa
Sannan ya kalleta
"Baki da lafiyane?"

Ta girgiza masa kai
? "Ya akai kikayi wannan ramar haka meyake damunki, tell me, meyake faruwa"
Idonta taf hawaye ta kalleshi

"In ka tafi yaushe zaka dawo?"
"Bazan Dade ba insha Allah"
"Dagaske kake zaka aureni?"
? "Am serious ina sonki son da bantaba zaton zanyiwa wani makamancinsa ba bayan Dan uwana I love u with all my heart"
"Aliyu ina sonka Dan Allah in kagama service ka tafi dani garinku ka aureni musulunta zanyi"

Mamakine yacika Aliyu ba maganar da tayine ya bashi mamaki ba illa magana da tayi da harshen Hausa Wanda be taba zaton ko zo tasani da hausaba

" Noor (sunan da yake kiranta dashi kenan)
Dama kin iya Hausa?"

"Na iya Hausa"
Tabashi amsa
"How comes ban taba ji kinyiba"

Wata nannauyar ajiya zuciya ta sauke

"Mamana kiristace babana kuma musulmi ne kuma ba haushe ne family din babana dukansu musulmai ne kuma musulmi suke aure

Baba nane kadai ya auri kirista wadda ta kasance ya mace tilo a masarautarmu yan uwanta duk mazane dan haka ake matukar sonta a cikin masarautar da ta ISA aure ta dage akan wannan musulmi take so akayi? ta hakura taki Dan haka aka kyaleta ta aureshi
? Tunda ta aureshi ya tafi da ita take samun cusgunawa daga dangin mahaifina suka takura mata da kyama da tsangwama a daddafe ta haifeni ta yayeni babanta yece sedai ta dawo Gida a hakura da auren ba za adinga wulakanta masa ya ba a matsayinsa na sarki me fada a aji amma ace ana wulakanta yarsa a gidan aure
Dangin mahaifina suka kwaceni shekarata takwas a hannunsu babana ya rasu a gurin kakata na zauna ita ke koyamin karatun addini shekarata takwas amma na haddace izu ashirin na Qur'ani

Da? mamana taji rasuwar mahaifina ta daga hankalinta akan se an batani ,
An kai ruwa rana seda kakana ya hada da karfin mulkinsa sannan aka karbeni daga dangin mahaifina

A gurin kakannina ni musulma ce na iya abubuwa dayawa kuma na tashi da Hausa a bakina dana dawo nan mamana ta maidani addinin ta sannan tayi Alkawari bazata bari inyi gangancin datayi ba, family dinmu ba a auren Wanda ba yarenmu ba ko kuma ba addinin mu ba? tun daga kan mamana akasaka wannan dokar"

Tana kaiwa nan ta sauke ajiyar zuciya

? "Meyasa tun farko kika boyemin hakan, why"?

Idonta taf da hawaye ta kalleshi
" please Aliyu don't leave me tun randa kukazo da abiola na ganka naji ina sonka kate makamin Aliyu, in kai haka zaka ceceni daga halaka danakee ciki zan samu damar komawa addnina na musulinci"

"Lallai abiola munafiki ne shine ya kyaleni nake ta fama ko Ashe yasan komai"

"Ni nahana shi yagaya maka Dan Allah Aliyu kar kaarabu dani kayi Alkawari zaka aureni"
? Kuka take sosai

"Is OK ai bance miki nafasa ba Dan haka kiyi shiru zansan yadda za ayi zanzo innemi aurenki a gidanku"

Zaro ido tayi tace baze yiwu ba ita dai kawai ya tafi da ita basu saniba

? ? "Idan nayi haka banyiwa iyayenki adalci ba kibari inje kano in dawo zamuyi abinda yakamata"
Haka sukayi sallama kaman bazasu rabu ba

?? Aliyu ya dawo kano cike da tunanin noor (marry) sunyi farinciki da ganinsa, dayake da weekends ya dawo yaita zuba ido yaga Jawwad amma be Ganshi ba

? "Wai INA Dana ne" ya tambayi Usman
"Hmm wallahi wani yaro ya hadu dashi a kusa da makarantarsu, sun likewa juna yaita kuka se an kaishi gurin yaron, shima yaron in aka tashi daga tasu makarantar seyabiyo shi gida direbansa da malaman makarantarsu suyita nemanshi se mun maida shi makarantarsu yayita kuka,
To shine babansa yace Dan Allah da weekends? akai Jawwad kokuma shi akawo shi akawo shi nan"

"wannan wane irin shirmen banza ne kawai Ku dauki da Ku kaiwa mutanen da Baku Sani ba to ni ban yaddaba, akan me kawai ni gayamin inane inje in dakko shi"

"Sannu sarkin azarbabi kai ko kara babu, gidan mutanen kirki ne har nan mahaifin yaron yazo ya roki alfarma yanzu yasakasu a islamiyya daya"
Inna mairo ce take wannan jawabin

"Au saboda wulakanci had da canza masa makaranta haka akeyi kaikuma kana zaune"

? Seda aka gaya masa gidansu yaron yana gadon kaya Yakama hanya ya tafi dakko JAWWAD,
yana zuwa ya tarar an shiryasu me gidan ze fita da su Jawwad da wani yaro da befi sa'an jawwad ba
? Da gudu Jawwad ya tafi ya rungume Aliyu ganin haka yasa shima Yaron ya tafi ya rungume Aliyu, ya rungume su gaba daya
Suka gaisa da mutumin
Aliyu Yace masa

"Dana Nazo dauka"
"Wanne kenan?"
Mutumin ya tambayeshi
? "Jawwad mana"
"To ai har gida na tura aka dakko shi da izinin mahaifinsa"

"To ai nine babansa tafiya nayi ne kuma na dawo abani Dana ban yadda ya dinga zuwa wani guri yana zama ba"
Yayi maganar yana janyo hannun Jawwad aikuwa Jalal ya fashe da kuka ya bisu yana "daddy kace ya dawo min da shi"
Aliyu ba yadda beyi ba adena kai Jawwad gidansu jalal amma abu yaki,
Inma ba akai Jawwad ba za akawo JALAL sekace tagwaye

A yan kwanakin da Aliyu yayi a kano Dan uwansa ya fuskanci akwai abunda yake damunsa saboda Sam baya walwala sosai?

Usman ne yaje ya sameshi adaki yana waya da marry ya jirashi ya gama sannan ya mai tambayar

"Dan uwana me yake damunka ne naga Sam Baka da walwala ko akwai wata damuwa ne"?

" akwai kam yayana"
"Me yafaru?"

Usman ya fada yana kallonsa
Be boye masa komai ba ya gaya masa halin dayake ciki

Jinjina kai yayi
"Gaskiya Dan uwa ka debo da zafi shawarar da zan Baka ka hakura bana tunanin abin nan ze yiwu kasamu wata anaan ka aura"
" a lokacin da ka dakko naka Auren waya hanaka, kamin addu a kawai bana son wanna shawarar taka , tashi kabani guri'"
Aliyu ya fada yana nuna masa hanyar fita

Satinsa daya a kano ya koma kogi state an kai ruwa rana sosai a gidansu marry da aka gano tana soyayya da musulmi kuma bahaushe

Kwanci tashi Aliyu ya kammala service dinsa
Dayazo da maganar auren marry Gida malam yace be yadda ba, ga yayan musulmi nan a garin nan dan haka ya hakura da maganar yarinyar nan.

Marry kuwa taita rashin lafiya saboda Aliyu ya tafi ga kuma anki yadda da ya aureta, mamanta ta dena kulata sarki yayi fushi da ita duk da soyayar da yake mata, ita kuma ta kafe tace ita se Aliyu
? Shima nan haka Aliyu yake ta fama da malam amma yaki yadda, inna mairo CE kawai ta goyi bayansa amma malam ya kafe yace be yadda ba sedai ya auri musulma

Da wannan rikicin seda aka shafe shekara biyu ana fafa tawa da wannan rikicin

Marry taje ta samu maman ta tace itafa gaskiya zata tafi kano gurin Aliyu shi takeso bazata iya zama a garin nan ba
A gigice Maman ta taje tasamu sarki ta gaya masa, juyin duniya marry ta kafe tace itafa gaskiya tunda bazasu yadda ba tafiya zatayi,
Dan haka sarki yace to ya sallameta basu ba ita har abada karta kara dawowa, marry tace ta yadda,
Tana kuka mamanta na kuka haka ta hada kayanta ta nufo kano.........

Bayan la'asar marry ta sauka a kano layin Aliyu ta shiga kira bugu biyu ya dauka

"Aliyu kana ina ne?"
ta tambayeshi

"Ina gida"
Yabata amsa
"Kazo ka tafi dani Dan Allah"
"Ahh wai kina ina ne?"
"Aliyu kazo ka daukeni ina kano fa yanzu na karaso"

Zaro ido yayi
"Are u serious?"
"Dagaske nake"
A kidime ya tashi ze fita sukayi karo da Usman
"Dan uwa ina zaka, naganka a kidime haka"

? "Dan uwa marry ce ta biyoni kano"
"What are u serious"
" yanzu mukayi waya da ita ta fadamin"
"Muje tare"
Usman ya fada yana Jan hannunsa suka fice

Kaman yadda ta fadamasa a tasha sukaje suka sameta rungume da akwatinta
Haka suka Dakkota suka taho gida

Suna zuwa Zainab ta karewa marry kallo

"Wannan fa daga ina"?
Tafada a yatsine saboda ta ganta tare da Usman ga kuma uban akwati

" bakuwace"
Shine kawai abinda Usman yace mata suka wuce bangaren inna mairo
Lokacin ana ta kiraye? sallar magariba dan haka suka kaita dakin inna mairo suka tafi masallaci
Bayan inna ta idar da salla ne tare da lazimi
Ta kalli marry tace mata
"Sannu da zuwa"
? "Yawwa mama ina wuni"
Tafada da hausa amma a hausan tata zaka fuskanci ba cikkakiyar ba haushiya ce ba

"Lafiya kalau, amma banganeki ba "
Dan sunkuyar da kai tayi
"Tare muke da Aliyu"

Nan inna mairo ta gane wace ce

Tabata Abinci da ruwa tabata guri ta huta

Se bayan sallar isha'i sannan su Aliyu suka dawo gidan a dakin inna mairo suka hadu suna jiran zuwan malam Imam suji me ze yanke,

Zainab se sintiri take so take taji wace wannan bakuwar dasuka zo da Usman da Aliyu harda su trolley ita dai bata san taba

Akajima se ga malam imam ya dawo yazo ya samesu a zaune jungun? a dakin inna mairo

"Ya akayine na ganku a zaune kunyi shiru, bakuwa mukayine"

Inna mairo ce ta shiga korawa mamalam imam bayani

Ransa ne yayi matukar baci da jin inda jawabin NATA ya dosa, ya tashi ya bar gidan gaba daya
Seda yayi kwana biyu baya shiga harkarsu

Zainab kam ta uzzurawa Usman setaji wace ce yarinyar nan amma yaki gaya mata

A kwana na uku
Aliyu ne yasamu malam a tsakar gida yaje gabansa ya durkusa

"Baba na dama akwai lokacin da zezo kayi fushi dani haka kadena kulani Aliyun ka nefa dan autanka
Kasan bantaba dakko maka magana ba meyasa bazaka yadda da niba"

"Ya raina baze baci ba, seda na jamaka kunne akan yarinyar nan, amma saboda baka jin maganata kaje ka ja jubota ka kawomin ita gida haba Aliyu yaushe kafara dena jin maganata"?
?? Marry tanajin abinda ya faru a hankali ta tako ta karaso gaban malam imam ta zube

"Baba ba laifin Aliyu bane ni na kawo kaina dan girman Allah karka koreni, kafison in koma inda na baro kan addinina na baya?
Baba kaifa malamine kuma ubane dan Allah baba musulunta zanyi, ka auramin Aliyu idan na bar nan bazan koma gida ba wani gurin zanyi in ka koreni bansan inda zani ba,"
Duk wannan maganar da take cikin kuka takeyi
Aliyu ma gaban malam ya durkusa ya rike hannunsa

"dan Allah baba na ka amsa mana ka yadda in auri maryam dan Allah baba inba ita na aura ba wallahi bazan iya auren wata mace ba"
Usman ma gaban malam yaje

" baban mu tun tasowarmu kake sonmu kake kula damu, kake son abinda mukeso, baba ka amince da bukatar dan uwana,
Baba ka girmama son da maryam da Dan uwana kema junansu Wanda yasa ta baro daular da take ciki ta taho gurin mu, inka yadda da auren nan kaman kayi jihadi ne"

Inna mairo ma cewa take

"Malam a duba lamarin nan d'a na kowa ne mukanmu misaline munzo garin nan. Bamu da kowa"

Ajiyar zuciya yayi ya nisa sannan yace........



Share please


More comments more typing.................



Mss~dyjeer naga rago godiya nake=??
Anty Jamila a soye tabani ta hutaddani suya
Afshan
Rahmatoulaye
Salma
Afshan
Fatima zahrahs (tsofaffi)
And the remaining members
Ina alfahari daku d'd'd'd'd'




=؊??=؊??=؊??=؊??=؊??
[8/31, 8:26 AM] Safiyya:
? ? _ABDUL? JALAL_
? ? ? ? ?? (2020)

? ? ? _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
? ? (Daddy's girl)

? ? ? ? ? ? ? ?PAGE-? 10

PART 1

? _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,? ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta? wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar

07063065680
What's https: //chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL

Is a free book

Ina yinku AbdulJalal novel fans irin=د?=د?=د? da duk sauran masoya wannan novel ina jin dadin comments dinku love u all d'd'd'

I want comments not stickers or just thanks=?"?=?"?=?"?=?"?
Your comments give me courage

Haka suka cigaba da tafiya sunayi suna hira jefi? har suka shiga garin Kaduna
Karfe 4 dai? suka iso kofar gidan su Jalila, suna parking Jalila ta fito bata tsaya bi takan JAWWAD ba balle trolley dinta, ta sakko ta ruga da gudu cikin Gida,
Ummi tana tsakar gida ta idar da salla Jalila ta shigo da gudu ta fada jikinta tana murna
"I really miss you ummina"

"To karyani ki huta sarkin fitina ga yanda kika shigo da gudu kaman an koroki,"

"Bikiyi missing dina ba ko ni duk na damu saboda rashinki a kusa dani amma daga zuwana kin faramin fada"
Ana haka? JAWWAD ya shigo da trolley din Jalila,

"Au shi kikabari da dakon kayannaki? Kekam se a hankali"
Ummi tafada tana ture Jalila daga Jikinta

"Ba komai Ummi naga ta kagu ta ganki ne yasa ta manta da trolley"
Yafada yana murmushi

Murmushi Ummi tayi
Har kasa ya tsuguna ya gaida Ummi ya zauna
Ta amsa fuskata cike da fara'a haka ya zauna sukayi ta hira da ummi,
Ummi tana kaunar Jalal kodan yadda yake son diyarta dakuma yadda mahaifinsa yake tsaye akan lamuransu ita da yarta
Bayan haka kuma JAWWAD yarone me matukar biyayya da hakuri

Sallar la'asar yayi, be wani dade ba yace tafiya zeyi,
"Jawwad tun yanzu"
"Ummi bana son tafiyar dare ne"
"Hakane kam bata da dadi"

To Dan jirani ina zuwa daki ta shiga ta dakko wani turare me kyau tabawa JAWWAD yayi godiya sosai

Yayiwa Jalila alama da ido ta tashi tarakoshi waje
"Sisyna zanyi missing dinki zuwan nan naki yayi min dadi gashi kin dawo kin barmu"

"Allah sarki yayana nima banji dadin rabuwa daku ba "

"Sisyna kiyi karatu kinji nasan ke mutuniyar kirki ce, banda kula kawayen dabasu zuwa makaranta
Banda tsokana da shagwaba"
Ya karasa maganar da sigar tsokana

"Insha Allah yayana"
"Good very good sister, insha Allah very soon zan dawo mukoma"
Dan turo baki tayi batace komai ba

Mortar ya bude ya dakko wani jaka yabawa Jalila
"Thank u very much my brother"
"Shhhhh don't mentioned dear"

"Wish u safe trip brother thank u very much ka gaida min da Nana ta"
"Zan gayamata and karki manta dayiwa yayanki addu a"

"Addu a mekakeso in maka"?
"No bani ba Jalila yayanki Jalal"

"Yaya kaikam narasa wanan kaunar da kakewa Jalal"

"Hmm sisy na kenan zakiji komai insha Allah in kinkuma zuwa kano zakiji dalili"
Yabude mota ya shige yatada mota yana daga mata hannu
Seda ya bace ma ganin Jalila sannan ta koma cikin Gida

"Ummina gayamin me yafaru bayan tafiyata ?"
"Ke dai bari Babyna gidan ba dadi daba kya nan, kawayenki na islamiyya se sintiri suke min, nayi missing dinki sosai daughter na"
Ummi tafada tana shafo fuskan Jalila

Jalila ta riko hannun ummi
"Allah sarki ummina haka kike sona dama?"

"Hmm Jalilana a duniyar nan a yanzu wanake dashi bayan ke kin ko son soyayyar dake tsakani da da uwa, da baki tambayi haka nakesonki ba"

To amma ya akai tsakanin Jalal da mummyn Sa basa jituwa shi bayajin wannan soyayyar ta mahaifiyarsa a ransa, Jalila tai maganar a zuciyarta

Da daddare bayan Ummi da Jalila sunci Abinci
Ta je ta dakko trolley din ta, ta dakko? kyautukan da ta zo dasu ta nunawa Ummi sannan ta dakko Wanda ,Jawwad yabata

Katuwar teddy ne Ja da kuma manyan kwalin chocolate kusan guda biyar
"Allah sarki yayana Allah ya karemin Yaya Jawwad har yanzu be manta abinda nake so ba "
Ummi kallonta ta tayi tai murmushi
"Hmm Jalila kenan, Jawwad ya biyewa shirmenki hada siyamiki teddy da girmanki"

"To ni ummi har wani girma nayi
Yawwa Ummina tambayarki zanyi"

"Allah yasa nasani"
" Naga nabaki abunda akabani a gidansu Jalal baki tambayeni waye Jalal ba ko kinsanshi ne?"

"Eh nasan yaron koba makotan su Jawwad ba"?

" Ummi shine, amma kinsan yazama dan shaye? bashi da tarbiyya Sam bakiga yadda yakewa mamansa ba ya akayi kika sanshi?"

"Allah sarki Jalal da ba haka yake ba daga baya yazama haka abokin Jawwad ne tun suna yara kanana
Daga baya yakoma haka saboda wani abokinsa ko wayake oho?
Amma naji ance hada laifin mahaifiyarsa amma bansan ya akayi ba nikam"
"To Ummi ya akayi mahaifiyarsa tabari yazama haka"

"Ke rabu dani nima ban saniba sarkin tambaya meyasa baki tambayesu a can ba ni rabu dani bacci nakeji"
"To shikenan Ummi "

Har sun kwanta bayan wasu mintuna da kwanciyarsu,
Jalila ta nisa
"Ummina"
"Na'am Jalilana"

"Yaushe zaki kaini garinku inga yan uwanki?"
"Jalila meyasa kikayi min wannan maganar,? so kike ki hanani bacci ko rigimar zakimin daga dawowarki ko baby, bana so yi baccin ki kawai nasan kingaji"
"Ummi bazan iya bacci ba sekin Sa ranar dazaki kaini garinku ni wallahi ko wasu irine ina so inje in gansu Dan Allah Ummi koba Sa sanmu ni inasonsu a haka Ummi kitemaka"
Jilila ta karashe magNar tare da rike hannun Ummi tana hawaye"

Fizge hannunta Ummi tayi
"Nemi gurin kwanciya kafin in wanka miki mari"
Ummi ta daka mata tsawa haka Jalila ta kwanta ta juya wa Ummi baya tana kuka
Har cikin zuciyarta Ummi takejin kukan Jalila tareda tausayinta.

Tayi rigingine tana tuna abubuwa da dama dasuka shude

*********
Aliyu Imam Habib shine cikakken sunan mahaifin Jalila su biyune kawai a gurin iyayensu shida? yayansa Usman Imam Habib (babansu Jawwad)
Mahaifansu sun haifi yara dayawa sun rasu su biyune suka rage asalin iyayensu Fulanin Adamawa ne ne akayi wata rigima yan fashi suka je rigar fulanin? aka karkashe wasu, yawan hare? da ake kaiwa fulanin ya tilasta wasu suka watsu a Sassan Nigeria an kashe musu yan uwa da dama malam imam da shi da me dakinsa mairo sukayo hijira zuwa kano.
? an kashe musu yan uwa dayawa, wasu daga cikin yan uwan Nasu kuma basu San inda suke ba abinda suka tsira dashi bashi da wani yawa, duk da kasan cewar su masu arziki a rugarsu amma haka suka siyar da abinda ya rage musu suka taho kano (ta dabo jalla babbar Hausa kodame kazo an fika)

Zuwansu kano a lokacin duniya tana kwance , a lokacin in akayi baki masarautar kano zamanin sarki Ado

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login