Showing 21001 words to 24000 words out of 141466 words
na rawa baka kunyar nuna mai. "
Shiru Asim yai baice komai ba.......
_A Gida_
Nafi bayan ta gama komai tai wanka dama Little ta fito mata da kaya hakan yasa ta saka ta fito domin zuwa kitchen yin aiki.
Ta d'anyi tafiya kad'an taji ance "Ina Zaki? "
Tsayawa tai cak ta kasa juyowa, shima bai sake magana ba hakan yasa ta daure ta juya a hankali, daga gefe ta ganshi zaune akan d'aya daga cikin kujerun gun, gani tai ba kallanta yake ba hakan yasa tad'an kuramai ido, duk da bai kalleta ba jitai yace " Kallan fa? "
Da sauri ta d'auke idanta tace " na fito ne kawai"
Ya kalleta sannan ya mata alama da hannu akan tazo, a hankali ta karasa inda yake, ya kalleta yace " So nake kimin wani abu. "
Cikin mamaki ta kalleshi tace " Me kakeso yaya? "
Ya bud'e baki zai magana sai ga Aneesa ta karaso cikin salon tafiya da yanga, tana zuwa ta shagwab'e murya tace " Cwt Yaya kaifa nake nema. "
Ashraf ya kalli Nafi sannan ya kalleta yace " Anie ya akai?"
Baki ta turo tace "ni dai banasan Anie kacemin Neesah na. "
Kunne yad'an sosa sannan ya kalli Nafi wanda da alama zaman gun ya isheta yace " Nafeesa jeki kawai. "
Wani kasalalen kallo tamai wanda ita kanta batasan ta iya ba, so take ta tambayeshi me yakeso tamai? Ga Aneesa agun ita kuma duk ta rasa mai zatace, Aneesa ta maka mata harara sannan tace " Nafi yace kije zamuyi magana ne. "
Kamar tai kuka haka ta juya ta fara tafiya, me yake so? Abinda ke mata yawo kenan.
Itakam Aneesa zama tai ta shiga mai salo, wani abun ya biyeta wani kuwa ya juya kai kawai.
Nafi kam duk aiki take amma hankalinta nakan Ashraf har suka kammala girki, nan Goggo tace "A d'au na Ashraf akai mai. "
Da sauri Nafi ta amshi tiren tace "bari na kaimai. "
Goggo ta kalleta tace " kinsan b'angarensa ne? "
Haka kawai tasamu kanta da yin karya tace na sani.
Nan Goggo ta bata.
Fitowa tai tana ta kalle kalle, nan Allah ya had'ata da Amrah murmushi tai ta karasa gunta tace "Amra inane b'angaren Yaya? "
Nan Amrah ta nuna mata, karasawa tai tana tafe tana tunani da fatan Allah yasa yana nan.
Knocking tai a hankali, Ashraf dake kwance akan doguwar kujera yana kallo a falo yace "in abinci ne ajiye zan d'auka."
Nafi ta kalli kofar kamar tai kuka har ta ajiye zata tafi sai kuma ta koma gefe ta zauna a kasa.
Shikam ya dade kafin ya taso ya bud'e kofar, mutum ya gane a zaune ya jingina da bango cikin mamaki yace "lafiya? "
Da sauri Nafi ta mike ta kalleshi, kallan mamaki ya mata yace " kece? "
Kai ta d'aga kawai, yace " D'auko abincin ki shigo. "
D'auka tai sannan tabi bayansa, tana shiga ta tsaya a bakin kofar, ya karasa kan kujera yace " turamin kofar. "
Rufe kofar tai sannan ta kalleshi, da hannu ya mata alama akan ta ajiye abincin a dinning, nan ta kai sannan ta kara tsayawa tana wasa da hannunta, ya kwanta ba tare da yace mata komai ba, itama shiru tai dan batasan me zatace ba.
Shikam kwanciyarsa yai yana jiran tai magana, sun dade sosai a haka shikam bacci ne yai gaba dashi.
Nafi tana nan a tsaye jitai kafarta ta fara amsawa, a hankali ta d'an matso kad'an cikin in ina tace "dama d'azu ne.... "
Sai kuma tai shiru, Jin shima baice komai ba yasa ta kara daurewa tace "naji kace zan ma abu? "
Nan ma shiru, lekashi tai kad'an, gani tai bacci yake, a hankali ta matso inda yake ta kuramai ido, a ranta tace "na sashi yai bacci baici abinci ba. "
Kallansa ta karayi, itadai haka kawai tun sanda ta ganshi takesan taga tana kallanshi, batasan sanda murmushi ya bayyana a fuskarta ba ta juya tai waje.
*THE INNOCENT TEAM*
*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_
© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com
1⃣4⃣
Sai yamma Little ta dawo, abinci kawai taci suka shiga bubud'a kaya nan Little ta ware mayafai da jaka suka had'a kayan da za'a kai d'inki.
Nafi sai murna take a ranta zataga cikin gari.
Driver d'in mumy ne ya d'aukesu, a hanya Nafi sai kalle kalle take can ta tuno tahowarsu a mota itada Ashraf murmushi ta saki wanda Little ta kula dashi.
Little ta d'an harareta tace "Nafi na kula yau dai a farin ciki kikeyi."
Murmushi ta sake sannan ta kalli Little tace "Little dan Allah tambaya. "
Inaji kawai little tace sai dai ta maida hankalinta kan Nafi, Nafi tai kasa dakai cikin alamun kunya tace " in mutum yace yanaso kamai wani abu, me zai kasance? "
Dariya sosai Little tai ta dade kafin ta tsagaita tace "Hala Ya Ashraf ne ya fad'a? "
Nafi ta d'an turo baki kadan tace "shine to menene kike dariya ?"
Little tai d'an karamin tsaki tace "in kikaji yaya ya fad'i haka wallahi aiki yakesan saki. "
Nafi ta kalleta tace "aiki shine yanasan inmai wani abu? "
Little ta girgiza kai tace "Tab bakisan mutumin nan ba, amma duk da haka nayi mamaki dan ni kad'ai yake sawa aiki ni kuma ba abinda na tsana a rayuwa irin inji yaya yace zan mai wani abu. "
Nafi ta d'an jujuya kai sannan tace " Meye abin tsana? Nikam dadi zanji inya sani aiki ma. "
Little ta mata wani kallo na yarinya da sauranki tace "Nafi bakisan waye Ya Ashraf ba, duk aikin da zakimai bazai tab'a burgeshi ba sannan bazai tab'a cemiki ko sannu ba. "
Nafi ta d'an tabe baki tace " to mezai sa sai yayi miki sannu bayan ke kanwarsa ce? "
Kallan mamaki Little take ma Nafi itakam Nafi ina ta sani cigaba tai da cewa " Sanna? N da alama ba a mai aikin yanda yake so ne. "
Duka little ta kai mata,Nafi tai saurin sa hannu agun, Little ta rike hab'a tace "Lalai ashe kina magana haka? "
Nafi tai murmushi batace komai ba, Little ta kalleta tace "Naji ni kanwarsa ce sannan naji d'in bana mai yanda yakeso, ke tunda kinanan sai ki mai yanda yakeso ki kuka tabbatar yacemiki sannu. "
Nafi murmushi kawai tai batace komai ba, Little tace "Kinga da Ya Habib ne? Wayyo Allah na. "
Da mamaki Nafi ta kalleta tace "Ya Habib? "
Little ta saki wani fara'a yacigaba "D'an yayan mumy ne yanazuwa gida sosai ya dad'e yanzu ma na tabbata kila karshen satin nan ki ganshi. "
Nafi ta maida kanta titi kawai, Hannu little tasa ta juyo da ita tace " Nafi kinsan me? "
Kai Nafi ta girgiza alamar a'a, Little ta cigaba cikin zakuwa "Ya Habib ko Opposite d'in Ya Ashraf ne. "
Nafi da mamaki tace "Oppo? "
Little ta dafa goshi tace " Kinsan me? Kinga Ya Ashraf bai da san magana shi kuma ya Habib akwai surutu, sannan Ya Ashraf akwai zafin rai shikuma Ya Habib Saukin kai gareshi. "
Nafi ta d'an bata fuska tace "Zafin rai? "
Little tace " naji ba zafin rai ba, sannan kinga Ya Habib akwai san wasa da mutane, ga mutunci. "
Nafi wanda ta rasa dalilin jin haushi Little datai tace "Little da wa kuka fi kusa? "
Cikin rashin kulawa tace "Ya Ashraf. "
Nafi tai shiru batace komai ba jitai Little tace "Amma Ya Habib zan aura. "
Juyowa tai cikin tsananin mamaki ta kalleta, Little ta harari Nafi ta juya.
Nafi kam ta kasa magana sai shiru tai.
Tanaji Little ta d'aga waya suna hira da wata kawarta akan Lesson d'in da suke zuwa, saboda shirye shiryen Exam d'in Qualifying da zasuyi, ga makarantarsu anyi hutu kuma suna komawa za'a fara jarabawa.
Nafi kam sai kallan sha'awa take mata, har suka isa gun d'inkin.
An gwadata sannan suka bada kayan akai sai nan da sati d'aya za'a amshi wasu daga baya sai a zo a amshi sauran.
_A gida_
Ashraf ya dad'e yana bacci kafin ya tashi, wanka yai sannan ya ci abinci, ya gama kenan Amra ta shigo tace Mumy na nemansa hakan yasa ya mike yai waje.
Yana ganinsu Asim da kannensa a zaune d'auke kai yai kamar bai gansu ba yai gaba, yana wucewa kuwa sukaja tsakin takaici.
Sun gaisa da Mumy sannan ya gaida Kawu, shiru ne ya biyo baya kafin kawu yace " Ashraf dama maganar auranka ne da Aneesa. "
Kallan Kawu yai sai dai baice komai ba, Kawu ya cigaba "saura wata biyu a d'aura auren shine nakesan jin ra'ayinka akan abubuwa guda biyu."
Ganin Ashraf bai da niyyar magana yasa yace " Da farko inda zaku zauna, anan kake so ko kuwa a d'aya daga cikin gidajen mahaifinka zaka duba d'aya? "
Ashraf kam tambayar ta d'an b'atamai rai sai dai bai nuna ba kawai cewa yai "A tsarin mahaifina yafisan inzauna anan cikin 'yan uwana. "
kawu yai murmushi yace " yauwa haka ake so dams banasan tauyema hakki ne, tambaya ta biyu maganar aiki fa? "
Ashraf ya kalli Kawu ga mamakinsu murmushi sukaga ya saki, Mumy ta daure tace "Ashraf me kenan? "
Kallan Kawu yai yace "Kawu so kake in fara aiki? "
Gabab Kawu yad'an fad'i badai yaron nan yasan basaso ya fara aiki ba?
Mumy ce tace "wani irin zance kakeyi haka? "
Bai amsa mata ba sai maganar sa ta d'azu daya maimai ta "Kawu so kake na fara aiki? "
kawu ya saki murmushi yace "in banda abinka Ashraf tun yaushe nake cema ka fara aiki? Ga mahaifiyar ka nan duk ta damu akan rashin aikin ka."
Bai kara magana ba kawai kansa ya maida gefe, Mumy kam abin nan na damunta ganin zata sake magana yasa Ashraf yai saurin cewa "Kawu zan shiga ciki akwai abinda zanyi. "
Kawu ya kalleshi sannan ya kalli Mumy wanda jikinta yai sanyi, bai jira amsarsu ba yai waje, Umma dake tsaye a kofa tanajin me ake cewa sam batasan Ashraf zai fito ba tana ganinshi ta shiga borin kunya, ko kallan ta baiyi ba yai gaba, duk ransa na dadi.
D'akinsa ya wuce ya d'au waya ya kira Little, nan ta sanar dashi sun dawo gasunan shigowa, yace "kuzo keda Nafeesa. "abinda ya fada kenan ya kashe wayar.
Little ta girgiza kai tare da kwaikwayan abinda yace, Nafi tace "to me kikeso yace? "
Little tace "Inkun iso to kuzo ke da Nafisa ina nemanku. "
Nafi ta juya kai tace "meye marabar hakan da yanda ya fada? "
Little ta harareta tace "Lalai nafi na kula bakyasan indinga kushe yayan nan nawa."
Nafi ta kalleta kawai batace komai ba, Little tai murmushi tace "ko da yake dole ne ganin yanda ya taimakeki. "
Sun isa ko bangarensu basuje ba suka wuce bangaren Yaya, a zaune sukaga su Ya Asim hakan yasa suka rusuna suka gaidasu, harsun yi gaba Asim yace "Ke yar kauye? "
Nafi ta juyo cikin tsoro alama ya mata da hannu kan ta matso, a tsorace ta matsa inda suke.
Asim cikin izgilanci yace "Nemanki yake ne? "
A tsorace tace wa?
Dariya yasa irinta rashin mutuncin nan ya kalli kannensa yace "kun yadda Ashraf haka kawai ya kawo ta nan ba da dalili ba? "
Nafi cikin mamaki ta kalleshi dan bata fahimci inda ya nufa ba.
Dariya suka kara mata d'aya daga cikin su yace "amma wannan kwailar? Kalli fa kirjin? "
Dariya suka kara sawq hrda tafawa, Nafi kam yanzu tafara ganewa, kasa tai da kanta a hankali hawaye suka zubo mata.
Little ce ta matso wacce batasan me suke cewa ba sai dai ganin suna dariya ya nuna mata iskanci suke mata.
Tana karasowa tace "Ya Asim yanzu Ya Ashraf ya kira muje ko ince mai ka tsaida ita? "
Hararar Little din yai sannan ya kalli Nafi yace dalla bani guri.
Nan Little ta kamata sukai gaba, tambayarta tai meya faru? Kai kawai Nafi ta girgiza alamar ba komai, haushi ya kama Little tace "to na fadama ya Ashraf inyaso sai ki fadamai. "
Da sauri Nafi ta rike hannun Little tace "Maryam karki fad'amai dan Allah. "
Da mamaki Little ta kalleta, Nafi ta goge hawayenta tace "dan Allah mubar maganan nan in yaji ransa ne zai b'aci. "
Little tai shiru sai dai tana jinjina hakuri irin na Nafi.
Sun kwankwasa sai dai jin muryar mace sukai tace ku shigo, ba sai an fada ba sun san wacce.
Fuskar Nafi ce ta canza, a falo suka ganta ta baje a kasa tana cin abinci shi kuma yana gefenta amma a saman kujera yana kallo.
Jin sun shigo yasa ya kallesu itama kallansu take ganin Nafi yasa tace "me take anan?"
Ashraf yace "d'akinki ne? "
Cikin shagwab'a tace "Amma ai ya kusa zama nawa. "
Idanunsa akan Tv yace "sai kijira inya zama naki sai ki fad'i haka. "
Mamaki ne ya cika Nafi wai haka itakam saurayi yake ma budurwa magana? Jiya da suka dawo sai taga kamar bada wannan zafin yake mata magana ba to ko abin zuwa yake?
Ashraf ne ya katsesu da cewa "so kuke inta d'aga murya? "
Nafi kam bata fahimceshi ba, Little tace " mu shiga. "
Sun karasa Little ta zauna kusa da Aneesa tace "Yaya Neesa nan kika gudu cin abincin? "
Ta kalli Ashraf tace "nafisan inci abinci a plate din dayaci tunda bayasan muci tare. "
Kasa Nafi tai da kanta da sauri, Ashraf ya kalli Aneesa sai dai bai ce komai ba.
Little ta kalleshi tace "Yaya munkai."
Gud kawai yace, Little ta kara cewa "Gamu to. "
Nafi ya kalla yace "Nafeesa so nake gobe ki gyaramin b'angare na. "
Murmushi tai sannan ta d'ago ta kalleshi tace "Toh. "
Little tai kwafa aranta tace "kiyi murmushi da kyau. "
Aneesa ce ta harareta hakan yasa tai saurin maida kanta kasa, kanta ta maida kan Ashraf tace "Ya Ashraf yanzu me wannan zata maka? "
Cikin rashin damuwa yace "to ko zakiyi? "
Da sauri tai shiru dan ba abinda ta tsana irin aiki, Ashraf ya kallesu yace "Little kuje."
Little wacce dariya ta kusa kamata da yaba Aneesa amsa ta mike itama Nafi ta mike, har sun fara tafiya Nafi ta juyo tanasan tambayarsa.
Kallanta yai yace "d'azu yaushe kika tafi? "
Aneesa ta kalla cikin tsoro tace " ban dade ba ai. "
Kai ya d'aga kawai, ta daure tace "Goben karfe nawa zanzo? "
"Sanda kika gama abinda kike.
"
Juyawa tai bayan ta amsa da to.
Aneesa ta rakata da hararar tsana....
Suna fita ta shagwab'e ma Ashraf wai ya dizgata a gaban nafi.
Murmushi yai yace "kinsan banasan irin tambayoyin nan ai amma naga in bakimin ba bakyajin dad'i.
*THE INNOCENT TEAM*[5/5, 1:06 AM] +234 703 962 5239: *ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_
© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com
*Sry jiya nayi mistake zansa 16 nakara sa 15.*
*Nagode kwarai da tunatar dani.... LYSM*
1⃣7⃣
Kwanaki sun d'an tafi yau kwanar Nafi 10 sai dai abubuwa dayawa sun canza, sam yanzu Ashraf yadaina mata magana tundaga wannan ranar ko gaisheshi tai kai kawai yake d'agawa, tana zuwa gyaramai d'aki duk bayan kwana biyu sai dai daga ta shiga yake fitowa, wannan abu na damun Nafi iya tsanani, gida ya mata zafi ga Little yanzu suna jarabawa ba zaman gida take ba, sannan cikin gida kowa zancen biki ne a gabansa, shiyasa yanzu zamanta yafi yawa a kitchen, sosai ta fara iya abinci dan yanzu tana nata iya kokarin.
Kamar yanda ta saba yau ma a ka'ida zataje ta gyara b'angaren Ashraf suna gama aiki a kitchen tai wanka ta d'au abincinsa tai gaba, ya bata makuli saboda wani sa'in in bayannan hakan yasa data kwankwasa taji shiru kawai tasa makuli ta bud'e, karfe goma ne shiyasa kanta tsaye tai d'aki ta d'auka ya fita, me zata gani?
Ashraf ta gani kwance ya dukunkune jikinsa da bargo, lekawa tai cikin tsoro idanunsa a rufe suke hakan yasa ta karasa kusa dashi, numfarfashi yake fitarwa sama sama, Nafi ta