Showing 48001 words to 51000 words out of 141466 words
dake cinta, Ashraf ta tuno sanda ya d'auketa, idanu ta runtse kalaman Ferry ta tuna data cemata san Ashraf take, Nafi ta share hawayenta sannan a fili tace " Ina na isa? In kuwa har haka ne lalai ina cikin gararin rayuwa."
Kalamansa na mota ta tuna dayace mata zai saketa in ta samu wanda takeso.
Ta dad'e tana hawaye kafin bacci ya d'auketa.
Washegari da sassafe kuwa Drivern Mumy ya mai da ta makaranta, ko Ashraf bata sa a idanta ba.
Nafi ta dage sosai da ta koma makaranta, ba wai a kan karatu kad'ai ba sai dai kullum suna tare da Ferry tana kokarin canza halayenta.
A wannan zuwa gidan datai lalai ta fahimci abu biyu, na farko Ashraf wasa kawai yake da ita da jawo mata tsana agun mutane bayan ba santa yake ba, na biyu kuwa lalai in har tanasan Ashraf ya fara santa sai ta zama mace daidai shi.
A can kuwa an gama biki lafiya ankai Amarya d'akinta, sannan kowa ya watse.
Anyi hutu amma Nafi ta kira Habib akan zata zauna a gidan Principal ya tambayar mata ita, saboda a lokacin hutun ta samu isashen lokaci na karatu, wannan jarabawar ita tazo ta karshe a aji batajin kuma za ta iya nunama Ashraf wannan dakikantar datai.
Habib ya tambaya, ba tare da wani dogon Nazari ba ta amince, bayan kowa ya tafi gida itama ta koma quaters.
Little taji ba dadi sai dai bayan Nafi ta mata bayani ta waya yasa ta gamsu.
Nafi ta dage sosai......
Shekararta d'aya kenan a makaranta, duk hutu ba ta wani zuwa gida, sai dai duk cikin hutu Little na zuwa ganinta da sakon Provision daga Mumy da kud'in kashewa.
A iya wannan Shekara d'aya ba shakka Nafi ta canza sosai da sosai, ita da Ferry kam sun zama Aminai sosai, sai dai in a b'angaren karatu ne kuma da Jibiya sukeyi.
Yanzu suna S1 Nafi ta canza sosai, bata tunani ko sha'awar zuwa gida duk da kuwa yanda zuciyarta take tsananin rashin Ashraf kamar ranta.
Yanzu sun shiga Ss 2 a a wannan lokacin ne kuma Nafi ta shirya dan zuwa gida, Little tace "wannan karan kam gaskiya sai Nafi tazo gida, dan akwai bikin kawar Little ko ince Aminiyarta da za'ai.
A wannan lokacin shekarun Nafi 18, duk da ba kiba gareta ba sai dai kirjinta ya cika da dukiyar fulani, Nafi ta goge sosai, kamar ba makarantar kwana take ba, komai nata tsaf dan in Little zata kawo mata kaya har da mayuka masu kyau take cewa ta had'o mata.
Nafi tana tsaye kusa da Ferry ga Jibiya a gefensu, Nafi ta kalli Ferry tace " Na nawa kikai?"
Ferry tai d'an tsaki tace " Ai Yaya Yusuf ya rainan hankali wai ta 7 dan tsabar rashin mutunci."
Nafi tasa dariya ita da Jibiya, Ferry ta had'e rai tace " kubarni da abinda ke damuna."
Jibiya ta sake dariya tace " lalai zakisha Fada'a gun Abba dan ni na 2 nai."
Idanu Ferry da Nafi suka zaro, Nafi ta kalleta sannan ta had'a hannayenta ta tafa mata tace " wow! Jibiya kina kasheni."
Ferry ta harareta tace " Zama ta raya ki, ke Feena na nawa kika ci?"
Nafi ta juya kai tace " Secret."
Ferry tai dariya tace " badai irin na last term ba na 12 ba?"
Nafi ta d'an rangwad'a kai cikin tsokana tace " na 8 nai."
Ferry cikin d'aga murya tace " WHAT?"
Nafi tai murmushi tare da ware takardar, murna suka shiga yi sosai, can Ferry tace " Kai naji dadi kin daina cin double number, amma da alama sai na dage kar next term ki dawo gabana."
Suka sakeyin dariya.
Ferry ta kalleta tace " Feena zakizo d'in ko?"
Nafi ta d'an juya ido tace " zanzo insha Allah amma banasan zuwa yayanki nanan."
Ferry ta harareta tace " Gaskiya Feena bazan juri wulakantamin yaya da kike ba, tunda yazo visiting ya nuna yana sanki amma kike wani disgashi, in bakiyi wasa ba har gidanku zan kawoshi."
Nafi ta zare ido tace " wa? Rufan asiri."
Jibiya tace " kema kinsan bazata yarda wani saurayin ya bita gida ba saboda sanda takema yayan nan nata."
Tsaki Ferry tai tace " wlh Feena in har kika bari ya gane kin mutu akansa haka lalai sunanki sorry."
Nafi ta tsuke baki tace " Ke nima yanzu ba daina sanshi yaushe rabon ma da inganshi, kila ma ko a hanya naganshi bazan ganeshi ba."
Ferry ta d'aka mata duka tace " ni zaki maida gara? Kullum fa sai kinyi labarin yayan nan naki."
Nafi zatai magana ta hango kamar Little ta fito daga wata zukekiyar mota, tana sanye da sun glass tayi kyau sosai da sosai, Nafi tace " anzo d'aukana."
Nan suka mik'e suka taimaka mata da kayanta, Ferry tundaga nesa tace " Kai Feena gaskiya Little tana kasheni da gayu, ki bari nika inje gida dattin makarantar nan ya fita daga jikina lalai zan tsorata maza."
Nafi tace " Nima ki bari sai nazo gida kin ganni kiga yanda zan kasheki da nawa gayun."
Dariya sukai harda tafawa.
Sun karasa gun, Little ta karaso cikin murna, ta rungume Nafi.
Sunsa kaya a motar sannan Nafi ta leka dan ganin wanda ya kawo Little.
Habib ya sakar mata murmushi yace " Tantancewa akeyi ne?"
Murmushi tamai itama tace " Ai ba sai na tantanceba dama can jikina yaban kai ka kawota."
Nafi kenan ba shakka kim canza wato yanzu bakya kunyar maidamin kalamai na."
Ta d'aga kanta batare da ta amsa mai ba, sannan sukai sallama dasu Ferry ta amshi number Ferry da jibiya tasa a wayar Little.
Nan suka shiga mota, Habib jefi jefi yana kallanta ta glass d'in mota, ba shakka yarinyar nan ta girma, ganin haka yasa Nafi ta matsa daga setinshi ta koma ta can b'an garen.
Little ce tace " Nafi yau ji kad'ai nasan farin cikin danakeyi, nayi missing d'inki sosai."
Nafi tai murmushi sannan tace " nimafa kawai daurewa nakeyi jinake kamar na biyoki inkika zo ganina."
Little ta harareta tace " ba wani nan kedai kawai kinzama 'yar college tafi gida dadi."
Dariya suka d'anyi Nafi ta juya tan kallan window.
Little ta juyo ta kalleta tace " Nafi au Feena baki tambayi ina yaya ba, ko visiting nazo bakya tambayarsa."
Habib ne yai katsal yace " ita meya dameta dashi bayan yayi aure yamanta da ita."
Har cikin ranta Nafi taji haushin maganar Habib amma sai ta daure tace " Ya Habib kenan, dama can ba wani shiri muke dashi ba balle ya nemini."
Little ta kalleta tace " Nafi yanzu kin daina shigar ma yaya ne?"
Ta tab'e baki tace " ni a wa? Dama can bawai shigar mai nake ba kece baki fahimceni ba, ai Yaya Neesa itace zata shigar mai bawai ni ba."
Habib ya saki dariya yace " Gaskiya ne Feena gwara ki fara bayyana musu komai."
Nafi ta kwantar da kanta akan window tare da lumshe ido, tace " Little bacci."
Little ta d'an had'e rai tace " shikenan nayi shiru."
Habib ya kalli Little yace " Ai cewa tai bacci bawai kiyi shiru ba."
"Hmm ai tun da dadewa na gane Nafi au Feena in batasan magana sai tace wai bacci."
Habib ya juyo ya kalli Nafi sannan yace "yarinyar nan ta canza dayawa."
kai little ta jinjina tace " ai naji dadin makarantar nan."
Haka sukai ta maganganunsu itakam tana kwance tana jinsu a cikin zuciyarta take magana " Yaya ba sai ka basar da ni ba, nafi kowa sanin rashin matsayi danake dashi agunka, kila ma inya ganni bazai ganeni ba, ba komai Allah ya kawomin wani mai sona nima inyi kokarin ganin na yakece wannan soyayyar da take one_side."
Nace Uhmmmm zaki iya????.
*THE INNOCENT TEAM*
*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_
©
*na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com
*Wattpad As_AyusherMohd*
{ *32*}
Sun isa gida Habib ya gangara yai parking, sannan suka fito, Nafi ta rataya jakar bayanta uta kuma Little ta ja wo trolly d'in ta.
Habib ne ya matso kusa da ita yace " Gimbiya Feena kawo in tayaki mana. "
Ta kalleshi sannan ta kalli kanta tace " da me fa? "
Nuna mata jakar bayanta yai, tai murmushi sannan tace " ni ai ba kaya na d'auka ba Little ce mai kaya, da alama baka kula ba. " tana fad'a tai gaba.
Habib ya bita da kallo, gaskiya yarinyar nan tayi, shi dama tun tana yar kauyenta burgeshi takeyi.
Little ce ta karaso tace " yaya mun gode."
Ya rufe ido tare da yin mika yace " Princess na gaji. "
Ta kalleshi cikin kulawa sannan tace " yaya kaje b'angaren su Asim ka kwanta. "
Kai ya girgiza mata yace " a'a gida zan wuce, ai tunda Ashraf yai aure na daina kwana a nan gidan. "
Kanta ta sunkuyar kasa alamar rashin jin dad'i ya matso tare da sa yatsar sa ya d'ago kanta yace " sai munyi waya."
Kai ta d'agamai, ya mika mata key yace " Ungo kiba Ashraf zan d'auki motata nai gaba nima."
Ta d'agamai kai, tana kallo ya koma ya shiga motarsa yai gaba.
Nafi kam tana shiga d'akinsu tai wani ajiyar zuciya tace " Kai nayi Missing d'akin nan. "
Kaya ta shiga cirewa ta d'aura karamin towel sannan ta fara ninke kayan makaranta.
Little ce ta shigo, ta kalleta cikin shagwab'a tace " kina gani Feena har Ya Habib ya tafi? "
Nafi ta karasa ninkewa sannan tasa agun kayan datti ta kalleta tace " Little wani irin so kikema Ya Habib? "
Little tace " so mai yawa wanda yanzu ya zama jinin jikina."
Nafi ta tab'e karamin bakinta tace " Shifa? "
Little ta fad'a kan gado, ta d'an mirgina tace " Shifa haryanzu a kanwa ya d'auken."
Nafi ta girgiza kai a ranta tace " Little nima matsalar dake damuna kenan, gwara kema banaji kinajin rad'ad'in da nakeji in na tuna Ashraf fa mijina ne sai dai yamin nisa. "
Toilet kawai ta shige batare databa Little amsa ba tai wanka.
Ta dad'e tana gurza jikinta a cewarta dattin makaranta ya fita.
Sannan ta fito, bataga Little a d'akin ba hakan yasa ta zauna a gaban madubi ta fara goge fuskarta da cleanser.
Hoda kawai tasa batai wani kwalliya ba, sai dai tayi kyau sosai, ta mike kenan sai ga Little ta shigo ta tiren Abinci, Nafi ta kalleta tace " Little ina kayana? "
Little ta bud'e mata inda ta jera mata nata kayan, Nafi tai murmushi ta sani sarai daba dan Little ba lalai da zaman gidan nan ya gagareta, nan ta zab'o wata atamfa riga da siket, mamaki tayi dataga tana sa kayan da kyar, Little tai dariya tace " ai dole kigafa dad'ewar da kikai bakizo ba, ga yanzu kin kara girma bawai kiba ba ina nufin kin girma ta sama da kasa. "
Nafi ta harareta tace " lokacin girman ne yazo, da alama Little sai kin ban aran kayanki inyaso sai mukai a bud'amin nawa anjima. "
Little tace " ki d'auka mana, sannan kinsan fa yau da yamma zamu kamun Yusra sai ki gwada kayan ko da yake cewa nai a kiki daidai ni kawai dai karya kai nawa fad'i ne saboda nad'an fiki kiba. "
Nafi ta saka wata doguwar rigar material sannan ta zauna suka zuba abinci suka faraci.
Nafi ta kalleta tace " Little ya gunsu Amarya?"
Little ta tab'e baki tace " hmm ke dai bari Nafi bayan kin tafi biki an gamashi lafiya sai dai a ranar da aka kaita sukai fad'a kaca kaca. "
Cikin mamaki Nafi tace " fad'a kuma? "
Little taja wani tsaki tace " Ita wai a dole a daren takesan ya bata wasiyyar mahaifinsa shikuma yace ba wanda ya isa ya sashi ya bada abinda baiyi niyya ba. "
Nafi ta tab'e baki tace " ya suka kare to? "
"Hmm kedai bari Dady ne yaje da kansa ya sasanta yace Yaya yai hakuri gobe ya bata tunda dai hakkinta ne, ita kuma karta kuskura ta sake tambayarsa. "
Nafi ta d'an juya kai tace " Na d'auka tanasan shi dayawa, meye nata na damuwa da abinda baiyi niyyar bata ba? Indai har tana gudun b'acin ransa? "
Little tace " Zigata akai ya Asim da Umma."
Nafi ta d'anyi karamin tsaki tace " san da takemai baiyi nisa dayawa ba kenan indai har za'a zigata akan dukiyarsa."
Little tai ajiyan zuciya, Nafi tace " yanzu fa? An bata ai nasan hankali ya kwanta. "
Little tace "Hmm Yaya wai cewa yai wasiyyar dama mahaifinsa ne yace aba matar sa ta farko million d'aya ko ince wai ya ajiye kud'in a banki, to Yaya yabata kud'in sai dai Umma tace itakam gaskiya bata yarda wai kud'i kawai akace ba."
Nafi ta had'e rai tace " shi kuma yayan me yace? "
"Uhm bai kulasu ba kinsan shi ai. "
Nafi ta kara tab'e baki tace " Allah ya sauwake. "
Little ta amsa da Amin sannan ta d'aura da cewa " kigama muje ki gaida Mumy sannan kije kiga b'angaren Amarya. "
"wa? Bada ni ba, inje in musu me? " sukasa dariya a tare.
¤¤¤¤¤¤¤¤
A b'anagren Ashraf kuwa ya nemi aiki yanda kowa yake nema ya kuma samu ba babban aiki bane sai dai yanajin dad'in yanda yake fahimtar matsalolin ma'aikatansa tundaga kasa, yana kuma fahimtar abinda ya cancanta da zai musu bayan ya amshi company d'in.
Sai dai su Asim da Kawu kam shar take a gunsu, Asim kam gani yake kamar saboda Aneesa ne ya hakura da mukaminsa, sai dai shi kawu haryanzu yana tunanin da wani abu a kasa.
Kamar kullum yau ma ya dawo gida daga gun aiki, yana zuwa daidai saitin kofa yaji maganar mutane da karfe, da alama ma musu sukeyi, kai ya dafe cikin tsananin takaici sannan ya kwankwasa tare da murd'a kofar.
Aneesa ce zaune cikin kawayenta su uku, sallama yai sannan suka kalli inda yake, Aneesa cikin kissa ta taso da sauri tazo ba kunyar mutane a falon ta rungumeshi tare da manna mai kiss a kunci, Ashraf ya d'an zareta kad'an sannan yace " Bari in shiga ciki.."
Hannunta ta sakala cikin nasa sannan suka fara tafiya, shidai takaici ma hanashi magana yai.
Yana shiga d'akinsa ya kwace hannunsa sannan ya kalli d'akin yanda ya tafi ya barshi haka dai ya dawo ya sameshi, ya kalleta cikin takaici yace " Anie mekenan? Ba nace ki gyaramin d'aki na ba? "
Ta shagwab'e tare da kwantowa jikinsa tace " kana fita su Laila suka zo ni ko tunawa ma banyi ba. "
Ya kalleta cikin takaici yace "yau kwanan d'akin nan uku kenan a haka kullum da abinda kike cewa, wasa wasa ma falo da mai aiki bata zuwa ta gyara haka nan zaki barshi da sunan kinada abinyi ko? "
Aneesa ta kara shagwab'ewa tace " Hubby kayi hakuri zan gyara. "
Wani mugun kallo ya mata yace " banaso fitarmin daga d'aki. "
Zatai magana ya nuna mata kofa da yatsarsa sannan ya had'e rai sosai, jiki a sanyaye ta fito, sai dai dankar kawayenta su gane ta saki fuska.
Shikam tana fita ya sawa kofar makuli tare dajan wani tsaki yabi d'akin da kallo, ko sanda yana shi kad'ai baya barin d'akinsa haka amma yanzu ji d'akisa?
Gadon ya gyrara sannan yai wanka ya kwanta a kai, bai dade ba bacci ya d'aukeshi.
Bacci yai sosai harya makara sallar la'asar sai karfe 5 ya tashi, da saurinsa yai alwala ya fito masallaci.
Sukam su Nafi ganin anyi sallar la'asar suka shiga yib kwalliya dan tafiya gidan biki, saboda kawar Little ce sosai, sunaso suje da wuri dan a gamama Amarya kwalliya su tafi da ita gun biki.
Anko suka saka, light purple d'in wani yadi ne, shiba lace bane sannan ba material bane, riga sukai da siket sannan sai head shima kalar kayan, sunyi kyau sosai da sosai, balle abin kan nasu Little ce ta d'aurama Nafi sannan ta d'aurana kanta, Nafi tace " amma ankon yayi kyau. "
Little tai murmushi tace " kawayenta ne kawai zasu sa wannan ragowar atamfa ce. "
Nafi ta jinjina kai sannan tace " Farin mayafi zamusa? "
Little ta girgiza kai tace " a haka zamu. "
Nafi ta kalli kanta sannan ta kalli Little tace " taya zamu fita a haka? "
Little tace " haka ake yi ai in ma mun d'au mayafin sai dai mu rike a hannu. "
Nafi ta jin jina kai sannan ta zaro wani mayafinta karami golden color tace "ni dai da wannan zani. "
Little tace " to. "
Sun fito abin sha'awa dan hatta takalminsu iri d'aya ne, sai dai ba kyan kwalliya