Showing 138001 words to 141000 words out of 141466 words

Chapter 47 - ZUCIYA kowa da irin tasa Complete Hausa Novel

unknown   

13 Oct 2024

15926

Tace " sosai ma dan nasan abinda na haifa zaka koma cema Baby, haka kawai a fara cemin suna ba wani dadewa a canza."

Kallanta yai yace " to amma?" Sai kuma yai shiru kafin da sauri ya kalleta yace " ba wani dadewa? Ya akai kika san haka?"

Kanta ta cusa cikin kirjinsa tace " ya za'ai bazan sani ba bayan lokaci kawai suke jira?"


Idanu ya zaro cikin tsananin mamaki ya d'agota shima ya zauna akan gadon, ya rike hannayenta yace " Baby me kike nufi?"

Harararsa tai tace " sai nayi dala dala? Agunka fa na koyi murda magana."

Yawu ya hadiya sannan ya kalleta cikin wani yanayi yace " Nafisa bana san........."

Kiss tamai a kunci sannan ta kai hannunsa na dama kan cikinta batace mai komai ba.

Kallanta kawai yake kamar a mafarku yakejin abun, da sauri ya jawota ya rungume tsam yace "Nafisa yaushe?"

Tace "sai da mukai tafiya sannan na sani."

Wani irin tsantsar farinciki ne ke ratsashi ya kara kankameta, cikin zolaya tace " kaga banshirya ba na samu ciki sannan gashi ance a satin nan zafa a kafe mana list na makaranta."

Ashraf ya dagota yace " makaranta?"
Kai ta daga da sauri.

Fuska taga ya canza yace " da babyn nawa za'a dinga zirga zirga?salan karatu yasa a ki kulamin da babyna?"

Cikin mamaki ta kalleshi tace " ban gane ba?"

Yace " ki bari dai sai kin haihu."

Kallan tsantsan mamaki tamai tace "yaya mai kake fada haka?"


Dariya taga yasa yace " me? Kinji haushi? Nima ramawa nai ina murnar zanyi d'a ko 'ya amma kidinga min zancen wai karatu? Nima shiyasa na rama."

Hannu tasa tadan bigi kirjinsa tace " yaya harfa ka tsoratani."

Mikewa yai ya daga ta cak yai toilet da ita yana cewa gwara tsoron ya tsaya daga ke karki kaimin shi ciki."

Yana ajiyeta a bathtub ta kalleshi tace " ka gani ko? Dama nasani ina haihuwa zaka daina sona."

Murmushi yai yace "sorry Feenah dan da alama zan daina kuwa."

Haushi ya kamata ta kafeshi da ido, goshinta ya matso ya sumbata yace " in banda abin ki ai soyayyar da muke ma juna ita zamu yi karo karo mu ba babyn mu."

Ta kalleshi tace " hmm gashi nan har ka daina cemin baby, shi yasa ma nace kar a fara."

Shigayai cikin bathtub dib ya sakar musu shaya ya jawota jikinsa ya rungume a hankali yace " Nafisa bansan irin farincikin da nake ba yau lalai ina cikin farinciki mara misaltuwa, ji nake kamar bayani farinciki a duniyarnan."

Murmushi tai ta kara shigewa jikinsa.

Bayan sunyi wanka dakansa ya shafa mata mai sannan ta saka wata doguwar riga baka dake cikin jakarta sannan sukai order na abinci aka kawo musu.

Shi dakansa ya dinga bata bayan ta koshi sannan shima yaci, ya koma kusa da inda take zaune ya jawota suka kwanta a kan gado, a hankali tace " yaya ya kuka kare?"

Nan fa ya zayane mata duk abinda ya faru Nafi kam tasha kuka kankameshi tai tsam taba kuka tace " Yaya."

Murmushi yai yace " karki damu ai komai ya wuce."

Cikin kuka tace " wace irin rayuwa ce wannan ace duk mutanen dake zagaye dakai ba sanka suke ba? Ace mutum ya fifita dukiya akan jininsa"

Ya sake murmushi yace " _zuciyar kenan ai kowa da irin tasa_, wani akan kudi ba abinda bazai iyayi ba."

Tai murmushin takaici sannan tace " yaya wato da rayuwa ta da taka is so similar inaji tamu kaddarar kenan, bamu da kowa sai junan mu, nima daga mahaifina har mahaifiyata kowa rabuwa yai dani saboda san abin duniya."

Ashraf ya kalleta yace " ya akai naga kamar mahaifiyarki?"

Nan ta bashi labarin abinda ya faru, kai ya girgiza cikin takaici yace " Kaddarar da Allah ya daura mana kenan, ikon Allah ne yankaini garinku har na hadu dake, duk da rashin mutanen da ke sona tsakani da Allah a kalla ina alfahari da matata Nafisa na sona tsakani da Allah."

Murmushi tai tare da goge hawayenta ta kai fuskarta saitin tasa sannan tasa hannayenta ta kare bangare biyun idanunta a rufe suke sai ta bud'esu a hankali tana kallansa, shima kallanta yakeyi tace " nima ina alfaharin kasancewa dakai."

Murmushi ya Mata yace " Nafisa tnx alot 4 not living me."

Wani sansanyan murmushi ta saki sannan ta zare hannayenta ta kwantar da kanta akan kafadarsa tace " zaka cigaba da sona duk da banda komai?"

Murmushi yai sannan yace " zaki cigaba da sona duk da yanda nake?"

Idanu ta lumshe tace " duk rintsi bazaka wulakantani ba?"

Murmushi ya sake yi yace " duk rintsi bazaki gaji dani ba?"

Kallan juna sukai suka saki murmushi Nafi tace " yaya amma Little dita fa?"

Ajiyar zuciya yai yace "sai dai kinje."

Ta jinjina kai tace "yaya nisa fa?"

Kallanta yai yace "tana gun tsohuwarta."

Cikin mamaki tace " amma dai ba wai ka saketa bane ba ko?"

Ya hade fuska yace " kinmanta abinda na fada miki? Banda maganin hana daukar ciki datai dani harda ita fa aka hada baki akaina."

Nafi tai murmushi tace " amma yaya kaima ai kasan yanda take sanka ina sanin da kai tana masifar sanka shi yasa kai amfani da ita gun kama Ya Asim? Da kuma ganin akwatin Kawu?"

Ashraf yai shiru bai ce komai ba, Nafi tai murmushi tace " kabarta ma da abinda takeji plx karka saketa."

Hannu yasa ya tureta ya mike tsaye yace " wato ke ko kishi ma bakyayi, a iya sanina murna ya kamata kiyi."

Tasowa tai ta rungumeshi ta baya tace " ni kuwa nake kishinka shine ma yasa na fadi haka, dan ina kishin komai daya shafeka ciki kuwa harda kishin kar idanunka su rufe ka aikata ba daidai ba."


Kanta ta kwantar a bayansa tace" amma yaya nikam maganar wasiyya ta fa?"

Juyowa yai ya kalleta yai dan murmushi sannan ya bata labarin abinda ya faru.

Dariya sosai tai tace " amma dai ai bai kamata Abba yabi maganar wani mutum ba."

Ashraf yai dariya yace " nima da farko na dauka maganar mutumin nan ce ta sashi barin wasiyyar sai dai yanzu na gane ba haka bane, fahimtar dayai su kawu sune sillar halakarsa shine yasa ya mai wasika akan ya janye maganar aurena da Anisa, shi a tunaninsa kawu zai janye, to fatan Abba shine wasiyyar ta isa gun matar da zan aura."


Nafi ta jinjina kai alamar gamsuwa sannan tace " amma yaya kasan akwai mutane masu baiwar haka kuwa? Duk da bance wannan gaskiya ya fada ba sai dai Allah yana hallintar mutane da baiwa kala kala, wasu in basusan ya zasuyi amfani da baiwar tasu ba sai kaga sun koma harkar duba da bokanci da tsubbu."


Ashraf yace " haka ne, amma bakya ganin ya kamata mu maida Inna gun mijinta ta nemi yafiya?"

Nafi tai shiru, Ashraf ya dagota yace " karki damu ba abinda zai faru, iya kaci inyace baisan aurensa da Inna sai mu dawo da ita nan gida."

Kallansa Nafi tai sai dai batace komai ba, tana matukar tsoron Datti gani take bazai taba yafema Inna ba tunda ta satar mai saniya.


Da yamma sun taso sun iso garin kano, ya kuma sanar ma Mumy hukuncinta, a da taso ta zabi zaman gidan yarin dan gani take bata kyautama Ashraf ba a rayuwa, sai dai shi da kansa yace gidajenta za'a saida a bada rabi shi zai bada rabi a biya kudin, sai dai sam tace bata yarda ba, sai dai a saida duk kadararta a bada bazata taba yarda ya biya kudin laifin data aikatamai ba.


Sun isa gida inda Nafi ta shiga gun Little da sauri, a kwance ta ganta a d'aki ita kadai su Afra suna falo suna kallo, Nafi da sauri ta karasa gunta ta rungumeta tsam a jikinta a tare suka saki wani kuka, kuka suke sosai kafin daga baya Nafi ta shiga ba Little hakuri.

Little tace " Nafisa da wani ido zan kalli Yaya? Da wani ido zan kallu Ya Habibda mumy?"

Nafi ya rike hannayenta tace " Little bakiyi komai ba fa, baki san me ya faru ba, ta yayya zaki daura wa kanki laifin da baki aikata ba?"


Little hawaye na zubo mata tace " ta ya zakice ban aikata ba bayan mutuwar Abban Yaya itace sanadiyyar haihuwata?"

Kai Nafi ta girgiza mata tace " karkiyi sabo Little kaddarace ta riga ta faru fatanmu Allah yasa mu gyara."

Da haka Nafi tai ta ba little baki harta kwantar da hankalinta, nan ta jata bangaren Mumy.

Little na zuwa ta fada kanta tana kuka.


Asim kam tunda ya isa ya samu abinci agun Umma ya hau ci ba kakkautawa, Umma kam tausayin dan nata takeji ganin yanda yake tutura abinci kamar zan cinye har kwanon, sai da ya koshi sosai ya tam sannan tace yaje yai wanka.


Yana fita ta saki kukan takaici itakam ina zata sa kanta, basuda komai sai gun zaman nan yanzu in har Ashraf yace su bar gidan nan fa shikenan tasu ta kare.



**********


Da daddare Ashraf yana zaune ya bugama Nafi waya, ta dauka tare da mikewa daga gun su Inna da Mumy da take, cikin rada tace " yaya ya akai?"

Yace " wai bazaki taho gun mijinki ba?"

Tace " gun mijina?"

Yace " da kina so kicemin a gun Little zaki kwana?"

Tace " naga da acan nake kwana?"

Yace "da kenan yanzu ai kayanki zaki tattaro ki dawo bangaren mijinki."

Murmushi tai tace " ni dai kunya nake ji gaskiya."

Yace " kunya ko? To ni bari nazo na daukeki."

Yana kaiwa nan ya kashe wayar.

Dariya tai tace " in zaka iya kenan ba."

Ta koma suka cigaba da hira, batai minti 10 da zama ba suka ji sallamar Ashraf.

Little tai kasa da kanta, shigowa yai ya zauna kusa da Little tare da dagota yace " kanwata ko neman Habib kike ne?"

Dagowa tai da sauri tace "ni kuma?"

Murmushi yai yace " to ni kike nema?"

Kasa tai da kanta tana murmushi, Ashraf ya harari Nafi yace " malama tashi ko?"


Nafi ta zaro ido ta kalli Mumy da Inna cikin tsananin mamaki, wai keke damun Ashraf? Abinda tafada kenan a ranta.

Mumy tai murmushi tace " Ashraf bafa inda zataje."

Kallan Mumy yai cikin mamaki.

Mumy tace " Nafisa tana bukatar wani shagalin biki dan a kara shaida auranku, mutane dayawa basu san matarka bace, ita kanta kunya ya hanata sanar da kawayenta."



Cikin tsantsan mamaki ya kalli Mumy yace " to ai...."

Mumy ta hade rai tace " mun yanke hukunci da mahaifiyarta nan da sati d'aya za'ai ko yar walima ce sannan ta tare."

Haushi ya kama Ashraf yace "har sati?" ya fada yana kallan Nafi.

B'oyewa tai bayan Little tamai gwalo, haushi ya kamashi ya mike yace " hmm amma da ina tunanin gobe zamuje kauye tare da Inna dan ta nemi yafiyar Datti."

Mumy tace " hakan yayi kyau, inyaso sai Little ta rakaku."

Yace " amma mu biyu ma....."

Mumy ta katseshi zan ma Habib magana shima kila zaiso yaje kauyen kaga sai kuje da armashin ku sai ku dauki babbar mota, gashi Afra nan ma xasuyi rakiya."


Haushi ya kama Ashraf yai waje cikin takaici, bangarensa ya nufa ya kalli yanda ya tsara musu bangarensu yace " har wani sati? Sannan goben ma baza'a barmu mu biyu ba???"



**********



Washegari haka suka shirya suka dauki mota babba, Little, Inna,Nafi, Afra da Amra, Dan Litti Habib da Ashraf suka nufi kauyen su Nafi.

A hanya Ashraf yai musu siyayya sosai duk da Habib ne ya sashi dan shi gani yake bazai iya kaima Datti komai ba, haka suka isa kauyen

A kauyen su Dan Litti suka fara sauka aka saukeshi mutane sai kallansu sukeyi, sannan suka wuce rigar Datti.

Sun samu ba kowa a gidan gidan ma a rufe yake nan fa hankalinsu ya tashi sai ga wani yazo wucewa nan ya sanar dasu ai yana gidansu.


Nan suka shiga mota suka gangara, Datti na kwance a karkashin bishiya shi kadai abin duniya duk ya isheshi yana ganin mota ma ta tsaya amma ko alamar mikewa baiyi ba, mutane suka zagaye motar, nan fa su Nafi suka fito ba wanda ya ganesu gwarama Inna yayan Datti na ganinta ya ganeta.

Sai da aka musu iso suka zauna a ciki sannan yayan datti ya aika a kirashi.

Ba'a dade ba sai gashi nan, nan yaga inna sai dai maimakon masifa gani sukai ya saki kuka yana ce mata " innar Nafi mun shiga uku na saida ma masu yankan kai Nafi."

Kuka yake sosai wanda saida yasa Nafi ma kuka, Ashrad ya kalleshi yace " baka gane ni ba baffa?"

Kallansa yai yanasan gano fuskar sai dai ya kasa, Ashraf yai murmushi yace " mijin Nafi ne."

Nan fa aka dau salati, nan Ashraf ya zayyane musu komai, Inna ta nemi yafiya shima datti ya nemi yafiyar ta data Nafi.

Sun dade kafin daga bisani suce zasu tafi,Datti yace ai auransa nanan da matarsa, jin matsalar data sameshi yasa Ashraf ya ciro kudi masu yawa ya bashi yace ya sai wasu dabobbin, sannan suyi shawara in sunfisan zaman nan to in kuma sunfisan birni sai ya turo a daukosu.


Nan ya musu sha tara ta arziki suka fito, kowa sai sha'awar Nafi yake, nan Hanne ma dataji labari tazo taganta alokacib itakuma 'ya'yantama 2.


Su kadai suka taho dan dan litti yace sai yayi kwana biyu, zai dai dawo lokacin bikinsu da Nafi.


***********


Duk yanda Ashraf yaso su kebe da Nafi abin yaci tura har ranar zagayowar sati, Nafi tayi rabon Iv gida ya cika sai dai Anisa da Umma sukam suna zaune a bangarensu ko fitowa ba sayi.

Nafi da kanta ta sai kusu kayan da zasu sa a cikin kudin dake katin da ASHRAF ya bata.

Ta aikama Anisa da umma.


Hall aka kama, ga innarta ta zo itada mahaifinta da hanne, dama ta shirya musu dinkuna.

Su ferry da Little amara kirjin biki kenan sai hidima sukeyi, duk inda Little ta wuce Habib binta kawai yake da ido, sosai guri ya cika Abdulkadir wanda ke kula da dan siyasan nan shima yazo dan yanzu ya zama babban mutum Ashraf ya bude mai shago babba anan titin Zoo road inda yake saida kayan masarufai yanzo ko motar da yake hawa ka kalla sai ka kuma kallo, tunda ya iso shikuma ya kyalla ido yaga ferry hankalinsa ya tashi, sosai ta birgeshi.


Anyi shagalin biki sosai mutane kowa ya tayasu murna, sai dai Nafi tunda ta zauna Ashraf ya hanata tashi, ko kiranta Dj yai sai yace a mata uzuri haushi duk ya isheta datai magana sai yace wai bazai yarda a wahalar mai da baby ba.

Haka aka gama taro aka watse, Little da Ferry sune suka kai Amarya Nafi bangarenta inda Little tai ta mamakin sanda aka canza komai na bangaren.


Duk yanda Habib yaso suyi magana da Little abin ya faskara, haka suka kai Nafi bayan sun ajiyeta Little ta juya zata tafi Habib yai saurin binta suna fita yace " Little haka zamu dawamma ko magana babu?"

Kallansa tai tace " yaya da wani idon kakeso na kalleka bayan mahaifina shine sillar lalacewar rayuwar Dady?"

Habib ya kalleta yace " amma wannan ba ya wuce ba?"

Kai ta girgiza mai tai gaba zata wuce, hannu yasa ya rikota da sauri ta tsaya cak gabanta na faduwa yace " Little bantaba tunanin ina sanku haka ba sai bayan faruwar wannan abun."

Juyowa tai ta kalleshi tace " nifa?" tafada hawaye na gangaro mata, tace " nifa da nake sanka tun ina yarinya?"

Wani irin kallo suka shiga yi ma juna.......


Ferry kam da Abdul bansan ya akai ba can na gansu tare suna hira mamaki ya kamani nace hmmm lalai......


Shikam Ango ana watsewa ya yaye mayafin dake rufe a fuskar Nafi yace " su Amarya am gama gudun?"

Tai kasa dakai wai kunya, dariya yai yace " au abin Amaren gaske zakimin?"

Ta turo baki tace " ba amaryar bace?"

Yai dariya yace lalai su Amarya bari in kaiki ciki in gwada ingani ko Amarya ce da gaske."

Zatai magana taji ya sureta..........


Washegari da safe taga bangarenta sosai taji dadi sai dai tace ya dawo da Anisa, ya aminta da shawarar sai dai yace sai dai a gyara mata wani bangaren dake cikin gidan dan kuwa inhar ta zauna dasu gaskiya itace a wahale dan kuwa bazai iya adalci ba zai kuma sanar da ita hakan.


Da zai fita zuwa gun Anisa ne ya zaro takarda ya mika mata yace " uwar gida ga wasiyyar ki."

Yai gaba

Kan kujera ta kwanta a hankali ta bude takardae.


_Zuwa ga sirikata_

_Bansan me zance miki ba, ban kuma san dalilina na yin wasikarnan ba sai dai nasan abu d'aya shine ke rinjayata, dan Allah ina rokonki da kularmin da wannan yaron nawa, amanace na baki kisoshi saboda Allah bawai dan dukiyarsa ba, ki nunamai kulawar dazaisa yamanta shi marayane, wannan ita kadaice rokon da zan iya miki a rayuwa._

_Ga nawa gudun mawar na auranku, ba yawa sai dai wannan nine nake daburin baki ba wanda yasan da zamansu sai ni sai ke sai Lawyer na Salim, nagode

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login