Showing 102001 words to 105000 words out of 141466 words

Chapter 35 - ZUCIYA kowa da irin tasa Complete Hausa Novel

unknown   

13 Oct 2024

15913

da flask na abinci a hannunta, Nafi ta kalleta haka kawai taji zafin ganin Little da kular abinci.

Ganin kallan da take mata Little tace " Feenah menene?"

Nafi ta share kwallar ta tace " Little me yasa bakya jan dan uwanki a jiki?"

Little ta mata kallan mamaki tace " wani dan uwana kuma?"

Kai Nafi ta girgiza alamar ba komai sannan ta maida kanta kan gado, yau zafin kowa takeji har ita kanta, yanda numfashin Ashraf ke fita da sauri ya kasa barin kunnenta idanu ta runtse cikin kunar zuci tace " Allah ka agazama wannan bawa naka."

Nima nace Amin.


Ashraf nanan a zaune Dan litti ya iso akan babur.

Nan Ashraf ya mike ya matsa daya bangaren shikuma ya shiga.

Kallansa Dan litti yai cikin kulawa yace " me ya faru?"
Kai Ashraf ya girgiza akan ba komai sannan yace " mu tafi office."

Sun isa Ashraf ya shiga office dinsa ya kule kofar tare da ba secretary dinsa umarnin kar abar kowa ya shigo.

Takarda ya d'ako babba ya rubuta.

ABBAS
/ | \
Muktar. | Hashim
\ | /
Rumah

Auwal Mask???

Shiru yai yana kallab takardar kafin yace " komai yayi connecting da Mumy, yayanta, mijinta nada, mijinta na yanzu."

Itama da ita aka dau fansa saboda suna ganin Abba ne sanadiyar mutuwar mahaifinta??

Da sauri ya girgiza kai yace " it can't be, mijinta ne Abba ai."

Shiru yai yana tunani kafin ya mike ya dauko ruwa a fridge a kafa kai, sai daya shanye robar ruwan tas sannan yace " cikin d'ayan biyu, ko da ita akai ko kuma ba a san ranta akai ba."

Waya ya dauka da sauri ya kira Dan litti yace " inaso kamin bincike akan dukiyar Alhaji Hashim inda mukaje rannan."

Dan litti yace " amma tayaya?"

Ashraf yace " zan turo maka number wani dan sanda kaje gunsa zai taimaka ma."

Yana kai nan ya kashe, sai yanzu wani abu ya fado mai, in har dukiyar Dady gaba daya ya sata a cikin wannan dealer din da sukai tayaya ya farfado cikin kankanin lokaci?
A iya saninsa ko makarantar da yake da ita tun daya taso ya santa, sannan tun da ya taso yasan Dady mai kudi ne.


Hmmm Babbar magana.


*#ASHRAFEENAH TEAM*
💞
*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com


*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡




*Wannan Shafin Sadaukarwa ce gareku My Asmy, My Asy Khaleel da Autar Hajiya, May Almighty Allah always guide u through the right path (Ameen)*



*66*


Nafi ganin tana ta kiran number Ashraf amma shiru yasa ta mike tai hanyar waje da sauri, Little ta bita da kallan mamak, me ke damun Feenah?


Kitchen ta nufa da kanta ta shiga shiryama Ashraf abincin safe tana gamawa ta juye sannan ta fito tai bangarensu, wanka tai ta zura wata doguwar rigar abaya ash color anyi kwalliya da stones kalar silver a jiki, tayi kyau sosai.

Little kam mamaki take tace " ina zaki wai?"

Nafi tace " dan Allah so nake in zaki fita skul yanzu mu tafi tare ki ajiyeni a gun aikin yaya."

Idanu Little ta zaro tace " kije kiyi me?"

Tace " gun mijina zanje, hankali na bazai taba dawowa daidai ba sai naga halin da yake ciki."

Little ta rike baki cikin mamaki tace " lalai Feenah kinyi nisa bakyajin kira, amma kina gani yayan bazai fada ba in kika je?ki kirashi a waya tukunna."

Nafi tai ajiyar zuciya tace " da na sameshi a waya ai hankali na bazai tashi haka ba, sannan in ma yamin fadan zuwan ai dai a kalla na ganshi, bazanji haushi ba."

Little ta jinjina kai tace " lalai Feenah wai a 'yan kwanakin nan ne kika mato haka akan san yaya ko kuwa dama can b'oyewa kike?"

Nafi ta mike tare da rataya jaka karama mai dogon hannu tace " Little muje please kafin hankali na ya nemi goshewa."

Tare suka fito Nafi ta d'auko abincin daga kitchen suka tafi.

A hanya ko magana batayi fatanta kawai ta samu Ashraf lafiya, ganin batasan magana yasa Little ma tai shiru.

A bakin company din ta ajiye ta tace " ko inzo in rakaki?"

Nafi ta girgiza kai alamar a'a tace " zanyi tambaya."

Nan Little tai gaba ita kuma ta nufi kofar shiga.

Taje shiga taga wani wanda ba tantama tasan fuskar sai dai a ina?? Shi kam Dan litti kallanta yai sam amma bai ganeta ba, to dama ta ina zai gane Nafi kucaka da wannan?

Tambayar sa tai tace " bawan Allah."

Dan litti har yayi gaba ya dawo, tace " dan Allah office din Ashraf nake nema."

Kallan mamaki ya mata lalai gata kamar mutuniyar arzuki ashe neman mijin wata tazo yi, ya had'e rai yace " ban sani ba, sannan yarinya karama bai dace da ke ba irin wannan rayuwar."

Ya juya yai gaba, kallan mamaki ta bishi dashi bai dace da ita ba kamar ya?

Shiga ciki tai ta sami wani security ta tambayeshi, nan ya mata kwatancen office din Ashraf.

A hankai ta murda kofar ta shiga ta gaida secretary din sannan tace " gun yaya nazo."

Kallan mamaki ya mata yace " yaya wanne kenan?"

Tace " ya Ashraf kace mai kanwarsa ce."

Secretary ya mike tare da knocking din kofar Ashraf, daga ciki Ashraf yace " ka manta nace banasan ganin wani in ba urgent bane?"

Yace " yallabai kanwarka ce tazo."

Ashraf cikin mamaki yace " Little?ba dai wani abun bane ya faru."

Da sauri yace " ta shigo."

Nan Nafi ta karasa tare da murda kofar ta shiga.

Sannan ta maida kofar ta rufe tare da jingina jikinta jikin kofar.

Wani nannauyan ajiyar zuciya ta saki, ganin Ashraf a zaune lafiya kalau.

Kallan kallo suka shiga yi mamaki yake dama Nafisa ce?

Sansanyar murmushi ta saki sannan a hankali ta fara takowa zuwa inda yake.

Kallanta kawai yakeyi yanajin wani sanyi naratsa shi.

Nafi sai datazo kusa da inda yake kadan sannan ta ajiye abincin akan center table cikin shagwaba tace " Nasan ba farin ciki kai da ganina ba, dama lafiyarka nazo dubawa, tunda na gani bari na juya."

Ta fada tare da juyawa, da sauri Ashraf ya taso ya kamo hannunta ya jawota jikinsa ya rungume tsam, sannan ya saki ajiyar zuciya yace " Ban kawo araina zan ganki bane sam."

Tace " A wani hali kake tunanin zaka barni bayan ka amsa waya kamar numfashinka zai fita? Sannan daga baya ka kashe wayar ma gaba daya?"


Ashraf ya dagota tare da rike kafadunta yace " Sry Baby nasan zaki damu in ban daga ba sannan dana daga kuma sai naga kamar zan fi tada miki hankali inkikaji yanayin da nake ciki."

Cikin damuwa tace "mai ya faru wai?"

Murmushi ya mata sannan ya kara jawota jikinsa yace " karki damu ba wani....."

Kwace jikinta tai tace cikin dan zafin rai kadan " yaya baka yarda dani ba ko?"

Jawota ya sake yi ya rungume yace " kema kinsan ba haka bane, kece mutum ta farko dana yarda da ita a duniyan nan."

Har kasan ranta taji dadin kalamansa.

Sake ta yai ya zauna tare da jawo kular abincin yace " Ahhh bari inga mai matata ta shiryamin."

Tai murmushi sannan ta kamar zata zauna a dan nesa dashi.

Harararta yai sannan ya bubuga kusa dashi da hannu yace " nan."

Kallansa tai tace " in wani ya shigo fa?"

Ta fada tare da matsawa inda yake.

Hannu yasa ya jawota ta fada kan cinyarsa yace " anaso ana kaiwa kasuwa."

Baki tadan turo tace " yaushe nace inaso?"

Wani murmushi yai yace " gashi nan waya d'aya ta tada hankalinki gaba daya har kika tsiri kunyar fulani kika biyo mijinki."

Idanu ta dan murza tace " yaya wani abu ya shiga idona."

Dariya yadan yi yace " ko? Bari in duba miki."

Neman mikewa tai tana rurufe ido, hannu yasa ya riko kugunta sukasa dariya a tare.

Kan desk dinshi ta kalla taga take-away kallansa tai tace " wancan fa?"

Yai murmushi yace " wlh abokina ko ince abokinmu ni da ke shine ya damu wai yaga alama banci abinci ba ya kawo min."

Kallan mamaki tamai tace " abokin mu? Ni banda wani aboki namiji."

Yai dariya yace " nima ba wai ina nufin abokinki ba na abota abokinmu dai na aure."

Kallan mamaki ta sake mai, zatai magana ya matso saitin kunnenta yace " ya? Muyi skipping din aikin yau ne?"

Hannu tasa ta rufe mai baki tace " aikin fa?"

Yadan sosa kai kadan yace " yau so nake nai spending din whole day din dake."

Tai kasa dakai tace " kar mu tafi azo nemanka."

Yace " karki damu muje kawai."

Abincin ya dauka da kansa ta kwace tace " barshi ni zan dauka."

Yai murmushi shi ya fara fitowa ya kalli Secretary dinsa baisan mai zaice dan bai iya karya ba, ganin yana sosa kai yasa Nafi tai murmushi tace " zamuje dubiya bazamu dade ba."

Yace " okay sir adawo lafiya."

Ashraf ya kalleta sannan yai gaba, tabi bayansa, gudun ma kar asan inda zasu yasa suka tari mai adaidaita.
Ta kalleshi tace " ka taba shiga?"

Kallanta yai yace " ke dai muje."

Ita ta fara shiga sannan ya shiga ya kalli mai adaidaita yace " Shagari Quarters."

Kallansa tai mai alamar tambaya yadan matso bakinsa yace " akwai gidana acan na Abba."

Kai ta jinjina sannan sukai gaba.

Kafin su isa ya kira mai gadi ya sanar dashi zuwansa.


***********



Yau Datti ya tashi cikin tsantsar farin ciki saboda jiya da yamma Mairo ta kawo mai shinkafa da miya abinda rabon dayaci shinkafa har ya manta, ga shi harda kaza a ciki, ya gama sannan ta bashi lemo mai dadi ya sha.

Sai dai fa tundaga shan lemon nan bai farka ba sai yanzu, agoggon hannunsa ya kalla yaga wai karfe 9 na safe.

A firgice ya mike zaune yace tun hudu da rabi na yamma nake bacci?"

Mikewa tsaye yai yana kwalla ma Mairo kira, sai dai me? Shiru yaji kamar ba kowa ma agidan.

Nan ya fito waje yana kiranta, babu ita ba alamarta.

Da sauri ya shiga nemanta sai dai ina sam batannan.

Yai dariya yace " da alama wata kazar aka tafi siyomin yau ma zansha dage dage."

Garkensa ya nufa da niyyar ganin halin da dabobinsa suke ciki.

Idanu ya zaro ganin kofar a bud'e.

A tsorace ya karasa ciki....


Jama'a mai Datti zai gani??????


Kaf an kwashe komai dake cikin garken ba komau a ciki sai kashin dabobbi.


Wani irin kara ya kwalla da karfi....

Wanda ya razanani yasa na yarda biro na.



*#ASHRAFEENAH TEAM*
💞*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com


*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡




*Gaisuwa tare da godiya gareku Miss Softie, Mum Farhan da Fatima Lawan Jet.Nagode kwarai da kaunar da kukema Littafin nan.*
_Datti na gaisuwa Softie....Lol_


*67*


Datti kam daga wannan ihu shikenan ya zube ya zauna a gun kamar gunki, sam ya kasa ko da magana na ne.

Gashi a bayan gari suke hakan yasa ba wand ya shigo, sai can wajen azahar yayansa ya biyo dan yanasan datti yazo ya duba mahaifiyarsu dake kwance ba lafiya.

Can ya ganshi zaune, yai tsaki yace " kaji asara wlh kazo kasa dabobbi a gaba kana kallo, ni can na bazama ina nemanka kai ko jina ma bakai ba."

Ya karasa maganar tare da karasowa inda Datti yake.

Ganin kamar baima san me yake cewa ba yasa yayan ya tabashi da hannu tare da kallan garken.

Shikanshi tsorata yai, ya kalli Datti cikin tsananin firgici yace " Datti ina dabobbin?"

Datti kam ba magana yai dif kawai sai kallan turkensa yakeyi.

Ganin kamar ba a hayyacinsa yake ba yasa yayan ya d'agashi dakyar yai waje dashi, a taburma ya zaunar dashi sannan ya shiga mai fifita.

Datti kam haryanzu baya hayyacinsa ganin haka yasa yayan yai waje da sauri dan neman mai magani kafin matsala ta afku.


*************


A b'angaren Ashraf kuwa sun isa gidan suka sauka daga kan adaidaita nan ya bada kudi suka nufi gidan.

Mai gadi ya bud'e tare da gaidasu.

Suna shiga falon Ashraf ya rungume Nafi ta baya yace " ahhh finally we are alone."

Ta zare hannunsa daga kugunta sannan ta kama hannun ta zaunar dashi kan kujerar dinning sannan ta ajiye kular tai kitchen ta dauko plate da spoon.

Kallo kawai yake binta dashi yana murmushi, ta kawo ta ajiye mai sannan ta bud'e abincin wani daddadan kamshi ne ya daki hancin Ashraf ya lumshe ido tare da kallanta.

Dankalin turawa ne aka mai hadi cikin kifi da vegetable ta zubamai a plate sannan ta mikamai spoon tace " a taimaka a ba cikina abinci."

Kallanta yai cikin tsananin so yace " nima ko ba'a fadaba nasan nawa cikin yana bukatar abinci."

Tai murmushi sannan tace " to ya za'ai kenan? Nima nina zubama nawa cikin abinci baka ganin kaima aikinka ne ka kula da naka?"

Murmushi ya saki wanda har fararen hakoransa suka fito, hannunsa ya nuna mata alamar tazo.
Ta dan turo baki ya kara nuna mata hannunsa, nan ta mike cikin shagwaba ta karaso gunsa kujerar kusa dashi ya jawo mata ta zauna ya kalleta sannan ya matso cikin rada yace " muci tare gwara na tabbatar da yawan abincin da zakici dan inaji a jikina nayi a jiya a cikina."


Kallansa tai cikin mamaki sai dai bata gane mai yake nufi ba, tace " ajiya?tame kenan?"

Yai murmushi tare da sa yatsarsa akan bakinsa yace " sirrine."

Harararsa tadanyi sannan ta d'auko spoon suka fara cin abinci a plate daya.

Suna gamawa ta kwashe kwanukan tai kitchen dasu, cikin tsautsayi garin ajiye cup na tangaran ya fadi kasa.

Ashraf dake falo jin kara yasa yace " Baby menene?"

Idanu ta zaro duk ta rikice batasan ko kadan ta jawo abinda zai batama Ashraf rai, tana kokarin matsawa dan ta bashi amsa sai jiyai ta dan yi kara.

Da sauri ya mike ya nufi kitchen din a rikice.

A zaune ya ganta ta rike kafarta ga jini sai zubowa yakeyi a tafin kafarta.


Cikin rudewa ya karaso tare da kallan cup din daya fashe.

Ya zagayo inda take ya d'aga cak yai falo da ita.

Kan kujera ya zaunar da ita ya kalleta da niyyar yi mata fada akan rashin kulan da takeyi sai dai ganin yanda tai raurau da ido yasa yai shiru.

Hannu tasa ta dan rike kunnenta tace " Yahkuri."

Kallanta yai tare da rufe ido sannan ya kalli kafarta, mikewa yai ya dauko tissue ya ciro kwalbar sannan ya goge jini, sai dai yana gogewa wani na zubowa.

Kallanta ya kumayi yace " sai dai mujibko chemist ne."

Tace " ta yaya? A adaidaita fa muka zo."

Ya kalleta cikin fada yace " Akan me ma tun farko bazaki dinga kula ba? Abu ya fashi kuma kin gani, mai zai sa bazakibi a hankali ba ki zagaye gun?"

Yar kara ta saki tace " Yaya zafi."
Ya sani sarai ta fadane saboda ya daina mata fada.

Mikewa yai ya sungumeta yai toilet da ita.

Ruwan dumi ya tara a dan roba sannan ya zuba dettol ya fara wanke mata.

Rike rigarshi tai tana dan rakinta, bayan ya gama ya kalleta yace " zaki iya tashi?"

Kai ta girgiza alamar a'a, yadan yi murmushi kadan yace " to yanzu ya za'ayi?"

Ta dan kara shagwabewa tace " kadaukeni irin na d'azu."

Baisan sanda yai dariya ba yace " naki, tunda bazaki dinga kula da kanki ba."

Rigarsa ta rike, ya juyo ya kalleta tadan karkatar dakai cikin shagwaba tace " in nai kuka fa?"

Kallanta yai batare da ya bata amsa ba, tace " Allah zanyi kuka, bakasan zafin da nakeji ba."

Murmushi ya karayi sannan ya d'agata, d'aki ya kaita ya ajiyeta a kan gado sannan ya zauna a gefenta yana kallan yanda take murmushi kasa kasa, ya kura mata ido yace " me kike saka wa?"

Mazewa tai ta kalleshi sannan cikin sanyin murya kalar tausayi tace " ruwa nakesan sha kuma bansan ya zan ba."

Kallanta yai yace " ruwa?"

Kai ta daga da sauri, ya mike yai waje, tabi bayansa da kallo, yana fita tadanyi dariya.

Bai dadeba sai gashi da ruwa ya bata ta amsa ta sha, yace " ni danazo dan karamin honeymoon kin maidani mai kula da mara lafiya."

Kasa tai dakai tace " ya hkuri yaya nima ba asan raina naji ciwon ba."

Ajiyar zuciya yai sannan ya matso kusa da ita, cinyarta ta nunamai tace " kwanta

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login