Showing 117001 words to 120000 words out of 141466 words

Chapter 40 - ZUCIYA kowa da irin tasa Complete Hausa Novel

unknown   

13 Oct 2024

15922

tunanin mun wani abuba."

Mumy taja wani numfashi tacigaba, a sanda suka hada plan din halaka mahaifinka matar Dady taji komai, sanda aka kawomin hoto ina kokarin kiran Abbas matar ya hisham ta kirani nan ta sanar dani komai.
Cikin rikicewa na kira Abbas na sanar dashi sai dai alokacin yana mota, bayan yayi hatsari ne ya sanar dani inyi a hankali da muktar lalai zai iya yimaka illa."

Ashraf jin Mumy tayi shiru yasa yace " naji na kuma fahimta sai dai tambayata anan shine ta yaya hotunan nan suka je gun Kawu?"

Tace "Dauka yai da ina asibiti."
Ashraf yace " menene dalilin dayasa kafin Abba ya rasu ya bar zama dake kullum sai dai ya zauna dani?"

Kallan Ashraf tai cikin wani yanayi tace " Ashraf wlh sharri akamin, Muktar ne ya d'aukoni daga gidan Ya hisham sai yace yanada abinda zai kai Tahir Guest palace shine muka shiga, ni a mota ma na tsaya ya shiga ya fito amma bansan ya akai ba wani ya dau hoto ya turama Abbas, tundaga lokacin naga ya daina shiga harkata sam nikuma ban kawo komai a raina ba, sai bayan yayi hatsari ya sanar dani dalili."

Kallan rashin aminta Ashraf ya mata sannan ya mike tsaye yace " kinsan yana sanki akan me zaki yarda har ya daukoki? Sannan akan me zaki aureshi bayan kinsan shine ajalin mijinki?"

Kuka Mumy tasa sosai tace " Ashraf bazaka taba fahimtata ba, Na auri Muktar ne dan na kareka, na auri Muktar ne dan na kare yayana na auri Muktar ne dan kare dukiyar da mahaifinka ya tara da guminsa."

Ba tare da ya zauna ba ya mata kallan mamaki.

Mumy kuka take sosai tace " Muktar shi yaba Ya hisham shawarar a halaka Abbas sai dai ya Hisham shine ya sanar da Driver din Abbas, wanda ashe cikin shirinshi ne ya dau recording din maganar Ya hisham a sanda yake bada umarni, bayan anyi sadakar bakwai ya kawomin ya bani naji yace bazai kuma yadda da kashemai dan uwa da hisham yai ba, sai dai alokacin banida evidence da zai nuna hardashi, shi kuma yanada wanda inyakai kotu kama ya Hisham ba wani abu bane."

Ashraf ya kalli Mumy baice komai ba.
Tacigaba " Ashraf."

Idanunsa ne suka ciciko da kwalla yace " what about me?" cikin wani yanayi yake maganar, yace " nifa? Wanda baki taba ba kulawa ba, baki taba sanin matsalata ba? Nifa?"

Hawayenta ya tsananta sosai da sosai, sai dai ta kasa magana, Ashraf ya daki inda zuciyarsa take yace " yanda baki taba kula da halin da nake ciki ba banaji kinsan matsalar mahaifina, tunda har shima zai dauke miki kafa amma baki tambayeshi dalili ba, wace irin rayuwa kuka jefa Mahaifina a ciki? Ke da kike matarsa bakisan matsalarsa ba kamar yanda bakisan ta danki ba, shi da yake dan uwansa yana neman illatashi, kamar yanda yake neman illatani."

Ya juya cikin wani yanayi ya fara tafiya yana hard'e kafa saura kiris ya fadi yaji an rikeshi.

A hankali ya dago ya kalleta, kuka take sosai, ta taso da niyyar zuwa gaida Mumy taji maganar Ashraf cikin b'acin rai daga bakin kofa.

Kallan ta ya tsaya yi zuciyarshi na tafasa, dagewa yai yana neman maida kwallarsa, Nafi kuka take sosai idanunta na kansa.

Lumshe idanunsa yai ya bude su ya kalleta yace " Nafisa ya akeso inyi da rayuwata? Me yasa ba wanda yake fahimtar kuna da radadin da zuciyata keyi?"

Kuka takeyi cikin kuka tace " Yaya Allahn daya hallacemu yafi kowa sanin halin da kake ciki kuma shi zai kawo maka mafita."

Murmushi yai sannan ya zare hannunta daga jikinsa ya mike yai waje.

Mota ya fada yai waje da gudu, tafiya kawai yake, babban burinsa bai wuce yaga Nafi a jikinsa ba tana lallashinsa sai dai ya zai yi?

Ya fahimta Mumy ba da ita akai komai ba sai dai bazai taba fahimtar selfishness dinta ba na kin kula da mijinta da danta ba.


***********

Mumy kam yana fita ta tsugunna tana kuka, cikin kuka tace " Ashraf nasani sarai laifinane sai dai tsoro nake in nuna maka soyayya kishin Muktar ya motsa ya nemi halakamin kai."


Nafi ta kalleta tace " Mumy na fahimceki sai dai duk da ba hurimina bane zance abu daya, rashin nuna soyayyarki ga Yaya bai hana Kawu tsanarsa ba da san halakashi, wannan dalilin shi zai sa Yaya ya kasa fahimtar dalilin ki na kin nunamai kulawa."


Tana kainan tai waje tana share hawaye.


D'akinta ta nufa ta zauna ta bude wani shafin kukan, ya zatai da Ashraf? He is soo pitiful, ita tsoronta ma kar wani ciwo ya kamashi.

Jitai gefen cikinta ya rike, ta san matsalar sarai rashin cin abincine sai dai ta ina zata iya tauna abinci bayan yanzu tasan yaya ko ruwa bataji zai iya hadiya a halin daya tsinci kansa?"



*#ASHRAFEENAH TEAM*

💞
*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com


*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡



_Maman Shaheed wannan shafin sadaukarwace gareki, Allah ya kareki a duk inda kike Ameen_

*75*


Ya dade a waje kafin zuciyarsa ta daidaita ya dawo gida, har ya kusa isa gida ya kira Anisa, ta d'aga cikin tsananin farin ciki, yace " Nisa kina ina?"
Tace " ina nan gidan su Zee."

Yace " bari nazo na daukeki."

Wani dadine ya kamata suna kashe waya ta saki wani ihu na farin ciki gaskiya yanzu ta aminta da san da Ashraf yake mata, nan Zee taita tsokananta wai ta dinga ja mai class, itakam ita kadai tasan abinda ta gani da yanda taji asanda ya juya mata baya.

Ashraf yai shiru bayan sun gama waya har yanzu yana mamakin kawu, ya sani sarai mutum ne mai tsananin ambition sai dai bai taba tunanin haka b'oyayyun halayensa suke ba, da har zaiyi threatening din mahaifiyarsa da yakeso akan laifin da yayanta dashi suka aikata akan ta aureshi, shiru yai yana tunani kafin yai gwafa sannan ya kira Dan Litti, bugu biyu ya daga.

Ashraf yace " Dan Litti ka nutsu sosai ka ji mai zanje maka."
Nan ya shiga mai bayani da ni kaina bansan me suke cewa ba sai dai sunkai kusan minti 20 suna waya kafin daga bisani Ashraf yace " Ka fahimceni?"

Dan Litti yace " yes sir, yanzu zakama Lawyer din maganar ko inje?"

Ashraf yace " karka damu kai dai ka samo mutanen da zamu yarda dasu wanda kuma baza'ai suspecting dinsu ba."

Nan suka karasa bayanansu sannan sukai sallama.

Gidansu Zee ya wuce ya d'auko Anisa tana ta zubamai sakalci a hanya shidai sai kokari yake kawai yana biye mata.

Nafi na zaune a barandar b'angarensu tana jiran taga shigowar Ashraf dan sam hankalinta ya kasa kwanciya ganin yanayin da ya fita.

Shigowar motarsa ce yasa ta saki ajiyar zuciya tare da mikewa tana kallo yai Parking sannan taga ya fito.

Murmushi ta saki ganin fuskarsa dauke da fara'a, sai dai me? Anisa taga ta fito ta d'aya b'angaren ta matso kusa dashi ta sakala hannunta cikin nasa, kallan juna taga sunyi suka sakarma juna murmushi.

Jitai wani abu ya tokare mata a makoshinta da sauri tai ciki tana kokarin kakaro numfashi.

Da kyar ta samu numfashinta ya daidaita kafin ta saki wani irin kuka, tace " ni ina nan hankalina ya kasa kwanciya saboda kai amma kai kana gun matarka kuna soyayya? Yaya ya kakeso inyi da rayuwata?"


Wajen karfe shabiyu na dare taji ta kasa bacci wani irin ciwo cikinta yake mata, dakyar ta iya daukan waya ta kira Little.

Little ta dauka da sauri tace " Feenah tun dazu nake nemanki, yau bazan dawo gida ba ina hostel, gobe 7 zamuyi text ga malamin ba shida sauki."

Da kyar Nafi ta iya cewa "to"

Ta yarda wayar tanaji Little na kiranta sai dai azaba ta hanata dauka.

Little da sauri ta kashe ta kira Yaya, wanda shikuma alokacin suna kwance da Anisa ya samu dakyar ya lalabata tai bacci wai ita adole sai sun gwada ko ya warke, da kyar ya samu ya shawo kanta ta hakura.

Yanajin ringing din wayarsa ya zare jikinsa daga nata yai falo, ya daga cikin mamakin ganin number Little.

Cikin rud'ewa Little tace " Yaya inaji Nafi bata da lafiya dama tun jiya na kula ba tacin abinci sai ruwan zafi to yanzu kuma ta kirani naji muryarta ba dadi."

Cikin rud'ewa yace " kedin kina ina?"

Tace " makaranta."

Tsaki yaja sannan yai waje da sauri ya manta ko kaya bai canza ba, yana zuwa ya bud'e kofar yajita kuwa a bude da alama ta barma Little kofar ne inta dawo.

Da sauri ya shiga ciki ya bude kofar d'akin.
A durkushe ya ganta a kasa tana murkusus, da sauri ya karasa gunta a kid'eme ya d'agota cikin tsananin firgice.

Nafi kam azaba kawai takeji, hannunsa ta rike kam tace " yaya cikina."

Kara rud'ewa yai yace " Nafisa? Me yasamu cikin? Bakici abici bane?"

Kasa bashi amsa tai a rude ya dawo falonsu ya hada mata tea mai kauri ya dawo gunta ya kwanto ta jikinsa ya fara bata, sha kawai takeyi dan bazata iyamai musu ba, haka yai ta bata har ta shanye sannan ya d'auketa ya maida ita kan gado ya kwantar tare da ja mata bargo.

Kanta ya shiga shafawa a hankali bacci ya dauketa.

Ido ya kura mata cikin wani yanayi na dana sani da yakeyi, idanunsa ne suka kada sukai jaa a hankali yace " Am sry Nafisa, it's all my fault."

Ganin kamar baccin ya fara nisa yasa ya mike a hankali zai tafi, hannunsa ta riko, wanda hakan yasa ya tsaya ba tare da ya juyo ba.

Nafi ta bud'e ido a hankali tace " Yaya ina rokon Allah ya kawomin cuta a kullum indai har hakan ne kadai zaisa inganka a kusa........."

Saurin matsowa yai gunta yasa hannunsa ya toshe mata bakinta yace " Nafisa me kike fada haka? "

Lumshe ido tai ta bud'e sannan ta zare hannunsa daga bakinta tace " in har hakane zai sa inganka zan iya horar da kaina da abinda yafi yunwa ma."


Kallan mamaki ya mata yace " Kada ki kuskura ki sake dan kuwa bazan yafe ma kaina ba inhar wani abun ya sameki."

Kallansa tai tare da daura kanta kanta kan cinyarsa a hankali tace " Yaya ban iya san abu ba, in har nai nisa asan abu jinake bazan iya rayuwa ba tare da abun nan ba, tunda nake a rayuwata ban taba san abu ba kamar kai, juyamin bayan dakai jinake kamar duk duniyar ta juyamin baya, sam..........."


Matsowa yai da kansa batai auni ba taji bakinsa cikin nata,lalai sunyi missing din juna, jiyai sam ya kasa tsaida hankalinsa nan kowa ya shiga nunama dan uwansa tsantsar rashin junansu da sukai.........


Sai bayan komai ya kammala sannan bacci mai nauyin gaske yai gaba da ita bayan sunyi wanka, kura mata ido yai yanaji a ransa shifa yafi santa akan yanda takeji akansa, shikadai yasan ya zuciyarsa takeji inya ganta.

Ya dade a gunta sai wajen karfe 3 sannan ya fito daga d'akin yai bangarensa.


*************

A kwance ya tada Anisa da alama ma ko farkawa batai ba kallanta yai yanajin tsantsar tsanar mahaifinta na kara ratsashi.

Falo ya fito ya kwanta yadanyi bacci kadan kafin asuba.


Nafi kam tunda ta tashi taji ciwon cikin ya tafi sai wani tsantsar farin ciki da takeyi, idanunta a rufe ta fara shashafa gado dan jin masoyinta, jin ba alamunsa yasa ta farko baki ta turo ganin ba ya nan, a ranta tace "mayb masallaci yaje."

Sallah tai sannan tadan kishingida, wani bacci ne ya kara gaba da ita.


**********


Asim yaje shiga office yaji wasu mutane daga gefensa suna magana.

"kai amma na tausayama Zakari, yanzu duk girman company din nan nasa haka zai saidashi da arha?"

D'ayan yace "nikaina tausayinsa nakeji, to ya zaiyi duk kadarar tasa ta karye."

Matsawa kusa dasu Asim yai yace " wani Zakarin?"

Wanda ya fara magana yace " Yallabai Zakari dai mai company din sabulai da mayuka na jiki, lotion da sabulu."

Asim yace " garin yaya?"

Mutumin yace " wlh karayar arziki ce ta sameshi komai nashi ya kare sai company din gashi dansa ba lafiya."

Asim cikin zakuwa yace " kuma nawa zai saida?"

Mutumin ya danyi shiru kafin yace " million 190 dai naji ana cewa, shiyasa kowa yake tausaya mai ganin guri ne babba mai kyau ga kayan aiki da komai a kalla gun nan yakai million 250 amma mutumin nan ya karyar da shi."

Asim yai shiru kafin daga bisani ya shiga office dinsa, shiru yai yana tunani kafin yace " in nasai company din nan lalai ba karamar garabasa zan samu ba, yanda zan nunama Abba nima na fara abin kaina ba wai dashi na dogara ba."


Ya danyi murmushin mugunta yace " gaba ko Ashraf ya kwace company dinsa nidai inada makafa" wayarsa ya zaro ya duba account dinsa, million 30 ne a ciki kansa ya dafa cikin takaici yace ina zan samu kudi bayan ko rabi bandashi?"

Sauri yai ya kira Anisa yace " kanwata wannan takardun haryanzu sunanan a inda suke?"

Ta mike tare da dubawa tace " eh."
Ajiyar zuciya yai yace " guda nawa ne ma?"

Ta fito dasu tace " da alama ma ya kara wasu a gun da guda biyar ne yanzu kuwa sunkai 8."

Yace " ganinan zanzo yanzu in amsa."

Tace " amma yaya....."

Yace " karki damu bazai gane ba, inma ya gane sai musan karyar da zamuyi ko kuma yau da yamma kiyi kuka ki kirashi kice barayi sun shigo."

Tace "to."

Can kuma yace " a'a ba haka ba yau da daddare zansa a shigo gidan sai ki bar kofar a bud'e muyi kamar yan fashi ne suka zo."

Tace "yauwa hakan dai yafi."

Shiru yai yana tunani dole duk da haka yana bukatar wasu kudin ya tabbata wannan bazai isheshi ba, fitowa yai ya samu Secretary dinsa yace " yana bukatar account book na Company din nan."

Nan yai waje dan amsowa, Asim yai murmushi yace " ko na dau kudin Company ba abinda Abba ya isa ya min."


Nace hmmmm

*********


Nafi kam sunyi waya da Ferry tace " Little ta kaimata kudin, harta je kasuwa ma ta siy musu."

Nafi tace "to ina amarya?"

Ferry tace " tana gun dangin mamanta taje sallama."

Jin ance mamanta yasa jikin Nafi yai sanyi, haka dai sukai ta waya har suka gama, Nafi tana kashe wayar ta kwantar da kanta kan kujera tace " ko ina ni tawa uwar?"







*#ASHRAFEENAH TEAM*

💞
*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com


*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡



*_Gareku 'yan Group d'ina The Queen Bee & Ayusher Fan Club.....Really luv u ol ❤_*

*76*


Ashraf na tasowa daga gun aiki ya wuce ban gareb Mumy, bai sameta a falo ba sai Afra ce tace mai tana d'aki tun jiya batajin dadi, nan ya wuce d'akin.

A kwance take sai dai jin kwankwasawa yasa ta mike ta bud'e, Ashraf ya shigo tare da zama a kasa ya gaisheta, ta amsa a hankali sannan ya kalleta yace " Mumy tambaya nazo da ita."

Gabanta ne ya fadi dan itakam tsoron tambayoyin Ashraf take, ya kalleta yace " gidajen Dady na waye?"

Kallansa tai bakinta yadan motsa kadan tace " wasu nawa ne wasu kuma nashi ne."

Kallanta ya sakeyi yace " asibitin Dady ya akai shima yaje hannunsa?"

Gabanta ne ya fadi ta kallu Ashraf cikin dan rawar murya tace " Mahaifinka ne........"

Katseta yai yace " sanda Abba yaki taimakama Dady har abin yazama ajalin Mahaifinki bakiji haushin Abba ba?"

Kallansa tai sai dai ta kasa magana, Murmushi yai sannan yace " Kince bakyasan kawu saki yai kika aureshi a dole saboda Dady meyasa kina aurensa kika hada zuri'a dashi bayan a fadarki ba sanshi kike ba ga haushin ya yi sanadin mijinki?"

Idanunta ta runtse a hankali hawaye ya zubo mata, Ashraf ya mike tsaye yace " no matter what i can't understand u Mumy, ke kanwar Dady ce, sannan matar Abba ta da sannan matar Kawu ta yanzu, duk inda na duba kina tsakiya."

Mikewa yai jiki a sanyaye yai waje har yaje fali ta fito da sauri tace "MUHAMMAD."

Tsayawa yai jiki a sanyaye idanunsa sun rukid'e, tace " zo."

A hankali ya koma d'akin ta zauna a bakin gadi shikuma ya zauna kusa da ita a kasa,Mumy tace " Ashraf duk na fahimceka sannan koma wanene dole ne indai yanada zarfafa tunani yai mamakin wad'an nan abubuwan."

Ashraf cikin zafin rai yace " bayan mahaifinki ya rasu ba shine dalilinki na fara kula Kawu ba har ya jawo zargi tsakani........."


Batasan sanda ta mareshi ba, bai dago ba sai dai yana ji dole ne ya fada mata abinda zai kona mata rai ko dan ta sanar dashi abinda ke b'oye.

Mumy ta share kwallarta tace " Kana nufin da aure na nai tarayya da kanin mijina? Dan kawai in rama abinda yamin kome?"

Ashraf a ransa yace " kiyi hakuri nima maganar ba har raina na fada ba."
Jin yayi shiru tacigaba " Tunda nake ban taba

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login