Showing 87001 words to 90000 words out of 141466 words

Chapter 30 - ZUCIYA kowa da irin tasa Complete Hausa Novel

unknown   

13 Oct 2024

15902

bud'e an rubuta _Someone! Somewhere is made for u my dearest son_"

Murmushi yai da ya tuna abinda nafi tace da kiss din data mai, hannu yakai kan leb'ensa yace " yarinyar nan kamar ba ruwanta ashe itama killer?"

A haka har bacci yai gaba dashi.

Da safe ya tashi tare da sawa a kiramai dan litti, sunyi breakfast kafin Ashraf ya kalli Dan litti yace "yanzu me kakeyi?"

" Achaba."

Ashraf ya jinjina kai yace "mota fa ka iya?"

Dan litti ya d'aga mai gira yace "ka sanni ai akwai karambani ai zamana a kachako sai da na koya."

Ashraf yace "gaskiya nafa sanka."
Dariya sukai kafin Ashraf yace " zaka koma kauyene?"

Da sauri yace "a ina?ai ni yanzu i am big for them."

Ashraf ya sa dariya yace "u are big?wato baka daina bako?"

Ashraf ya mai alamun zip a bakinsa yace "na daina kai kawai nake san ma."

Ashraf yace "to in ba matsala nafisan ka zama driver d'ina, saboda nafisan wanda zan yarda da shi."

Zaro ido dan litti yai yace " Ashaf kana kasheni in nazama driver dinka ai na zama dan gomna."


Dariya sosai Ashraf yai yace " whoa! Dan litti kai kadai ke sani dariya akai akai."

Dam litti ya mike tare da yima Ashraf salute yace "yes sir!"
Ashraf yai murmushi yace " kaii ban taba ganin mutum irinka ba."

Dan litti ya zauna yace "Ashaf karka damu zan zama mutum mai rike ma amana, dama tunda muka hadu nake sanka bazan taba bari wani abu ya cuceka ba."

Ashraf yai murmushi sannan ya dafashi yace "thanks, amma kanaso kacemin wai baka iya fadar Ashraf bane ko ya?"

Dan litti yai dariya yace "in na cema Ashraf ai mantawa zakai nine d'an littin gayu."

Dariya suka sakeyi kafin su mike su fita.


Makullin motarsa yaba Dan litti shikuma ya wuce b'angaren kawu.

A tsaye ya ganshi shima zai fito, mumy na kusa dashi, wani takaici ya kara kamashi ya matso kusa da kawu ya gaisheshi fuska dauke da murmushi sannan ya gaida mumy.

Bayan sun amsa ne kawu yace "Ashraf ya akai?"

Kallan mumy yai yace "magana nakeso muyi."

Mumy ta kalleshi jiki a sanyaye tai waje, ya matso kusa da kawu fuskarnan a sake yace "naji shiru ne, jiya banga takardar appointment ba."

Kawu ya kalleshi yace "wai da gaske kake?kasan fa matsayin Asim ne ya kakeso inyi."

Wani murmushin rainin hankali yai tare da jinjina kai yace "ahhhh! Na manta ko da yake ba matsala ka barshi a matsayinsa kai sai ka bani naka, dama ai can nawa ne ko ba haka ba???"


Ya fada yana kallan kawu.

Kawu ya shiga hucci, Ashraf yai murmushi sannan ya dan girgiza d'an yatsansa yace "No no no, kawu how can u get angry? Bayan a sama kaga komai?wanda ya sha wahalar yana karkashin kasa?"
Kawu ya kalleshi sannan yai yake yace "ce maka akai raina ya b'aci?"

Ashraf ya d'an kanne idanuwansa yace " why?kunya kake na gano hakan? Hmm ko da yake ba matsala yi zamanka a kujerarka nizansa ka sauka da kanka in har baka ajiye da hannunka ba."
Yana kai nan yai waje,yana fita kawu ya shiga hucci, jakarsa ya cillar can gefe sannan ya zauna a kujera yana maida numfashi kamar wanda yai gudu......



Ashraf ya fitowa ya harari d'akin sannan ya juya, jiyai ance "Ya Ashraf."

Juyowa yai ya kalli Anisa wace duk ta dan fada a kwana biyu, ya matso yace" ya akai?"

Kallansa tai tace " yaushe zaka zo ka maidani b'angare na?"

Kafada ya d'aga yace "da nina kawoki nan?"

Kallansa tai tace "yaya ni bazan koma bane harsai ka saki wannan yar kauyen dan pride dina bazai bari in iya kallanta ba, kace ta koma kauyensu."

Hannu yasa ya dafata yace " a maysayinki na wa kenan?"

Tace "yaya!"
Yai murmushi yace " karki damu kiyi ta zamanki a gun mahaifiyarki gani nake zatafijin dadin hakan, nima kuma zan samu saukin bincike min d'aki da akemin."

Yana kainan yai gaba, kallo ta bishi dashi yasan komai meyasa bai taba magana ba????



Mota ya wuce, dan litti ya bud'e mai baya nan ya shiga ya rufe shikuma ya shiga mazaunin driver.






*#ASHRAFEENAH TEAM*

👩🏻‍✈
*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com


*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡

*56*



Ashraf yacema dan litti akan su tsaya a wani babban shago na wayoyi, nan suka fita tare.

Waya ya d'auka kirar Samsung S7+ karamar ta hannunsa, sannan ya kalli Dan litti yace"kaifa wanne kakeso?"

Kai Dan litti ya sosa, Ashraf yace "shikenan in ba ka so."
Da sauri yace " ni kowacce ma ina so."

Ashraf yai murmushi yace "a d'auko mai Iphone 5."

Wani ihu da dan litti ya sake sai dayasa mai wayar ya kwashe da dariya, nan suka sai sim sannan ya kara siyan wani extra sim sannan suka fito.

Suna shiga mota ya d'auko wata yar karamar waya daga cikin jakarsa, yasa wannan d'ayan sim d'in a ciki sannan ya maidata jakar.


Sun isa gun aiki Ashraf ya fito d'an litti yabi bayansa, Asim ne wanda yake tsaye yake jiran isowar Ashraf ya taso da sauri, ya taho gun Ashraf fuskarnan a had'e.

Dan karamin tsaki Ashraf yaja a ransa yace "The fool is here."

Asim na karasowa ya kalli Ashraf yace " Kai bakaji kashedena ba ko? Akan kaba yarinyar nan takardarta ta bar gidan nan ba ko?"

Dan litti ya matso yace " Malam meye hakan?"

Murmushi Ashraf yai yace " barshi magana zamuyi."

Nan Dan litti ya matsa tare da had'e fuska kamar irin shi akama abun nan.

Kallo Ashraf ya maida kan Asim yace " Mahaifinka yace zai bani matsayinka, mai kake tunani?"

Idanu Asim ya zaro tare da kumburo baki yace "matsayina? What do u mean?"

Ashraf ya dafashi yace " what do i mean? Da alama sai ka tambayi mahaifinka da ya dage akan bani matsayinka, mayb kuma ya kula ne u are useless."

Yana kaiwa nan yai gaba, Dan litti yabi bayansa rike da jakarsa yana hararar Asim.

Ashraf ya kalleshi yace " Dan litti kasan kanin mahaifina?"

Kai ya girgiza alamar a'a yace "jiya dai na ganshi sai dai banaji zan iya gane shi."

Ashraf yace "zan nuna maka shi inaso ka dinga kulamin dashi akan abubuwan da yakeyi da kuma wadanda yake gani, sai dai karka bari kowa ya ganka kar kuma asan abinda kakeyi."

Dan litti ya mai salute da hannunsa yace "yes sir."

Hannunsa Ashraf ya ture yace " sorry ba a military muke ba."

Nan sukai dariya sannan suka shiga.
Jakarsa Ashraf ya kaimai sannan ya juyo ya fita.

Asim kam yana gama magana da Ashraf yai office dinsa kamar zai fadi saboda sauri, yana zuwa ya ture takardun kan desk dinsa da hannayensa biyu, ciki hucci yace " ni zakama haka Abba?"


Kawu kam yana zuwa office yasa aka rubuta takardar ragema Asim matsayi aka aika mai.

Asim yai shiru yana kallan takardar, can cikin takaici ya yaga takardar sannan ya mike cikin fishi yai office d'in kawu.

A zaune ya ganshi shi da manager suna magana, nan ya tsaya suka gama, manager din ya fita sannan ya shiga.

Tsayawa yai a kan mahaifinsa yace "ban yarda da ragemin matsayin nan ba."

Kawu yace " kasan complain din da ake kawomin naka kuwa?in ban rage ma matsayi ba mai kake tunani mutane zasu daukeni?"

Mamaki ya kama Asim yace " wa zaka ba matsayina? Ashraf?"

Kawu ya juya kai yace " haka shareholders da director's suka yanke."

Dariya Asim yasa yace " ko kuma ka tsara ba?"
Kawu ya had'e rai yace "kai ni kake fadama haka?"

Asim cikin hucci yace " ni dai na fada kar a kuskura a ragemin matsayina in ba haka ba zan iya tona abubuwan da na sani."

Mikewa kawu yai tare da dukan desk dinsa da hannu yace " me zaka tona?"
Yai dariya yace "abubuwan da kai, kana tunanin in Ashraf yaji zai barka?wato yanzu tunda kaga Anisa batada matsayi a gunsa shine kake neman juya mana baya ka koma gunsa ko?"

Kawu a zuciye ya d'aga hannu ya kai mai mari, Kallansa Asim yai sannan yai waje rai a b'ace."


Kawu ya bi bayansa da kallo sannan ya zauna tare da rike kansa.


Asim sama yahau cikin takaici yahau hucci tare da kara, ko aure bai taba kawowa ba saboda yanasan ya gaji Company din nan, shine yanzu mahaifinsa zai fara juyamai baya??"


************


Nafi kam bayan ta gama aikin gyara musu d'aki ta zauna tare da daukan qur'ani tana karatu.

Mumy ce ta aiko a kirata, nan ta mike gabanta na faduwa tai waje.

B'angaren Mumy ta nufa ta zauna tare da zama a kasa.


Mumy ta kalleta tace " jiya ina kika je?"

Nafi kanta na kasa tace " Gidan wata kawata da mukai makaranta."

Mumy ta kalleta tace " ina sanki a natsayinki na yarinyar da aka taimaka amma ba wai a matsayinki na matar Ashraf ba."

Nafi ta d'ago a hankali ta kalli Mumy.

Mumy ta cigaba "Ashraf bai samu kulawa daga gareni ba sai bakin ciki dana dinga kunsa mai, mahaifinsa ya rasu hankali bai gama shigarsa ba."

Idanun Nafi suka ciciko, Mumy tace " sai dai hakan ba yana nufin zan yarda ya auri mara ilimi ba alhalin aiki babba yana gabansa, yana bukatar matar datasan gari sannam takeda ilimi at least degree, shine wanda zai gaji mahaifinsa."

Nafi tai kasa da kai hawaye suka zubo mata, Mumy tace " kije kiyi tunani in har kina san Ashraf to kiyi tunanin menene abinda zaifi amfanarsa a rayuwar nan."

Nafi ta mike a hankali tana share hawayenta, b'angarensu ta nufa, da gudu mai gadi ya karaso yace " yallabai yace wai ki mai abincin rana zai dawo da anyi la'asar."

Kai ta d'aga sannan ta koma ciki.

Ana azahar ta fito tai kitchen ta fara mai girke girken Asabe na tayata.


*********

Umma da Anisa kam suna zaune abin duniya ya damesu, Anisa can ta nisa tace " duk laifinku ne Umma, meyasa kuka hanani haihuwa dashi?"

Umma tace "mene?"

Anisa ta cigaba" da yanzu akwai zuri'a a tsakaninmu ko baya sona ai nasan halin Ashraf bazai wulakantani ba."

Umma ta mike tsaye tace " Anisa meke damunki?"

Anisa cikin dan fada tace " wlh ni duk ku kuka cuceni, da ace na haihu dashi ai da d'ana shine zai zama yanada gadon dukiyar Ashraf amma dayake ba ni kukeso na gaji dukiyar ba shi yasa ba wanda yai wannan tunanin."

Tana gama fadar haka ta mike tai cikin d'aki tare da bugo kofa da karfi, Umma ta bita da kallan mamaki.


*******



Karfe hud'u da rabi Ashraf ya dawo, b'angarensa ya nufa, shima dan littibya wuce nasa.

Zama yai tare da d'aukan waya ya kira Little, yace "kin dawo?"
Tace eh yaya.

Yace "ki turomin Nafi."

Ta amsa sannan ya kashe.

Nafi ta kalla wacce tai wanka tai kwalliya cikin atamfa riga da siket, bata d'aura d'an kwalli ba kanta ba kisto sai dai ta tifkeshi da ribon.

Kan nan yayi gwanin sha'awa.

Little ta kalleta tace " Yaya na kiranki, da alama dama shi kike jira."

Nafi ta harareta tace " ni wai ina mutumin ki? Naji shi shiru kwana biyu.

Little tace "tafiya yai wlh amma gobe zai dawo."

Nafi ta zari d'an kwalinta tai waje.

Kitchen ta nufa ta d'auko tiren data jera mai abincinsa sannan tai b'angarensa fuskarnan fal take da farin ciki, dukda dai kalaman Mumy suna kara yimata yawo a zuciyarta.

A bud'e taga kofar hakan yasa tasa kai tare da sallama, Ashraf wanda ke zaune akan kujera ya kalleta fuskarnan d'auke da murmushi, dinning ta wuce ta ajiye sannan ta tsaya daga gun tace "ka taso."

Hannu ya mata alamar tazo nan tad'an yi kasa dakai sannan ta make kafada tace " naki ni dai ka taso."

Murmushi yai ga mamakinta sai taga ya taso ya nufota, jingina tai da jikin dinning din tana kallansa fuskar nan d'auke da murmushi.

Ya karaso kusa da ita batai zata ba sai jitai ya rungumeta.

Murmushi tai sannan tace " Yaya ka dawo lafiya?"

" Hmm lafiya lau, jiya yaushe kika tafi?"

D'agowa tai ta kalleshi tad'an mai hararar wasa tace " ba bacci kai ka shareni ba."

Idanu ya zaro yace garin yaya?"

Ta turo baki tace "Allah yaya indai ina zuwa gunka kana min bacci ko?"

Bakin data turo ya d'an sumbata hakan yasa ta maida shi da sauri, yace " me za amin?"

Kallansa tai tace " kazo kaci abinci."

Murmushi yai sannan ya saketa ya ja kujera ya zauna tare da nuna mata kujerar kusa dashi.

Nan ta zauna ta zuba mai, kallanta yai yace " muci."

Tace " am full."
Idanu ya kafeta dashi hakan yasa ta mike ta d'auko wani spoon din ta zauna.

A hankali suke ci sai dai ya kamo hannunta na hagu ya rike.

Bayan sun gama ne ta zubamai juice ya sha sannan suka mike.

Hannu yasa a kugunta ta kalleshi tai murmushi a haka suka karasa ya zauna akan kujara tare da jawota kan cinyarsa.

Kallansa tai tace " yaya inada nauyi fa."

Dariya yai yace " indai kinada nauyi to lalai Afra ma tanada nauyi."

Cikin shagwab'a tace " Afran?""

Ya d'aga mata kai sannan ya d'auko ledar dake gefensa yace " Gift."

Kallansa tai ta amsa zata bud'e yace " ba anan ba sai kin tafi kya bud'e, yanzu dai tukuicina zaki bani."

Yai maganar yana mata wani kallo, itakam in Yaya na mata irin wannan abun mamaki takeyi dan a iya saninta da gani take mutum ne wanda bashida sakin fuska, sai dai ferry dama ta fada mata maza duk daya suke indai a harkar so ne, kenan shi yana santa da gaske."

D'an kwalin kanta ne ya zame, kanta ya kurama ido, a hankali yakai hannu ya shafa yace " i like this."

Murmushi tamai sannan tai kasa da kanta tace " tukuicin me kake so?"

Nesa dashi ya nuna mata yace zauna, nan ta tashi ta zauna a gun, zatai magana taji ya kwantar da kansa kan cinyarta yace " a gajiye nake, so nake inji ya bacci yake a kan cinyar matata."

Kallansa tai tare da sa hannunta kan fuskarsa tace " amma ai kana kwanciya akan cinyar yaya Nisa."

Yai murmushi bai ce komai ba sai idanunsa daya rufe.

Murmushi tai sannan tasa hannu ta fara shafar kansa.

Ta ina zata iya rabuwa da Ashraf?


Bataji zata iya, in kuwa tai to gaskiya rayuwarta ta gama karewa.



*#ASHRAFEENAH*
💋
*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com


*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡




*Thanks alot My Wattpad fans, i really appreciate ur luv and support.*


57


Tun daga idanunsa take bi da kallo fuskarta sai murmushi ke bayyana, lalai soyayya da dadi amma batajin in har da wani ne zataji dadin soyayyar nan.

Ashraf kam bacci ne ya daukeshi, jin yanda Nafi ke shafa masa kai.

Bud'e kofar falon yasa ta kallo gun da sauri tana san ganin wanene ya bud'e kai tsaye.

Ganin Anisa yasa ta zaro ido sai dai bataji zata iya d'aga Ashraf daga jikinta saboda Anisa.

Itakam Anisa tun daga bakin kofa ta tsaya tana musu wani kallo, wani irin zazzafan kishi ne yake damunta, kitchen ta wuce direct ta debo ruwa cikin bokoti ta nufo Nafi.

Itakam Nafi ganin tayi kitchen yasa ta saki numfashi na farin ciki, tare da kallan Ashraf, batai auni ba kawai sai ruwa sukaji akansu.

A firgice Ashraf ya farka tare da mikewa tsaye, kallan mamaki ya shiga yima Anisa wacce ta shiga yin huccin masifa.

Ya maida kallansa kan Nafi wacce dama kanta ba d'ankwali saboda dazu ya cire mata tun daga saman kanta har jikinta duk a jike yake jarab.

Yaso yama Anisa magana amma ganin Nafi cikin wannan hali yasa ya wuce dakinsa da sauri ya d'auko towel sannan yazo ya rufa mata.

D'aga ta yai ko kallan Anisa bai kuma yi ba ya wuce da ita cikin d'akinsa.


Nafi kam tayi lamo har suka shiga ciki, ya kalleta yace " kinji haushi ko?"

Kai ta jinjina alamar eh, yai murmushi yace " kinsan......"

Ta katse shi da cewa " haushi na d'aya kana bacci an tasheka."

Kallanta yai tare da murmushi ya jawota jikinsa, sannan ya kamo hannunta sukai toilet.

Kallanta yai ya mika mata towel, ta amsa sannan tace " ka fita to."

Baya ya juya sannan yace " ki cire a haka dan ba inda zani, ai ba kallanki nake ba."

Ta ce " taya zan yarda bazaka juyo ba?"

Yai murmushi yace " in ma na juyo ai abuna na kalla ba na wani ba."

Juyawa tai da sauri cikin kunya.

Da kyar ta cire kayan ta d'aura towel din sannan ta sa kayan a bokiti, tace kazo ka cire naka sai in wanke mana."

Murmushi ya mata sannan ya sa wani takalmin ya shiga toilet din.

Juyowa tai zata fita ya riko hannunta.

Nan ta tsaya ba tare da ta juyo ba, yace " ina zaki??"
Kallansa tai da sauri tace "naam?"

Yace "

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login