Showing 96001 words to 99000 words out of 141466 words
kasan yace sam baka zuwa gunsa, gashi kullum sai ya tambayeni kai."
Ashraf yai murmushi sannan yace " muje to."
Jikin Ashraf kamar wanda aka zubama ruwa haka yake tafiya, sunje shiga ya kalli Habib yace " dama Dady da Kawu suna shiri??"
Habib ya dafashi yace " me kake fada, ka manta Dady baya shiri da Kawu har bayan auren Mumy."
Ashraf a ransa yace "then y??????"
Jansa Habib yai suka shiga ciki.
Dady na zaune yana karanta jarida yana ganin Ashraf ya mike cikin tsananin farin ciki yace " wa nake gani kamar d'ana da baya nemana???"
Ashraf yai murmushi ya karasa gunsa yace " Dady na sameku lafiya?"
Dady ya zauna tare da nuna ma Ashraf kusa dashi ya zauna, Ashraf ya girgiza kai sannan ya zauna a kasa wajen kafarsa yace " Dady ina wuni?"
Dady ya dafashi yace " Ashraf nida d'ana amma ganinsa ya min wuya?"
Ashraf yai murmushi sai dai a ransa yana kara kallan Dady da tunani kala kala dake yawo a ransa, can yace " Dady kasan aikin namu ne sai a slow."
Dady yai murmushi yace " to ya za'ayi dama komai sai hakuri."
Habib dake zaune yace " wato Dady kaga Ashraf ka manta dani ko? Dama kullum tambayar ka ya Ashraf yake? Wani aiki yakeyi yanzu? Me yakeyi? Wa da wa ya hadu da d......."
Da sauri Dady ya katseshi da dariya yace " kai kuwa ba dole inji halin da dana yake ciki ba?"
Ashraf yai murmushi a ransa yace " shiyasa kake barin Habib ke zuwa kwana akai akai saboda kasan me nakeyi???sai dai akan me? "
Nima nace lalai fa akan me kenan? Soyayyace ta 'yan uwa ko akwai wani b'oyayyen al'amari a kasa????
Hmmmmmmm
*#ASHRAFEENAH TEAM*
💞
*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_
© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*62*
Nafi kam yana fita ta gyara d'akin sannan ta fito kamar munafuka ta nufi bangarensu, a hankali take tafiya taje kwanar da zata shiga part dinsu taji ance " kan bala'i daga ina kike?"
Gabanta ne ya fadi ta juyo a hankali cikin tsananin tsoro, Umma ta karaso cikin huci tasa hannu ta fizgota Nafi ta fadi a kasa.
Umma ta kalleta tace " daga gidan ubanwa kike da safen nan???"
Nafi ta kalleta tace " ba daga inda nake kawai dai na fito ne."
Umma ta nunata da yatsa tace " ke na miki kama da sususu??"
Cikin mamaki Nafi tace " Sususu??"
Umma ta kara hasala tace " badai a bangaren Ashraf kika kwana ba?"
Kasa Nafi tai da kanta da sauri.
Cikin tsananin fishi umma tasa hannu ta mangareta da karfinta tace " 'yata tana can ta kasa bacci tabar mijinta saboda ke, ke kuma kinsamu wannan damar kina neman maye gurbinta."
Nafi ta d'ago ta kalleta, Umma tace "me? Zaki ramane?? Uban me kikaje yi a bangaren 'yata?"
Nafi ta ki dauke ido daga kanta bata kuma bata amsa ba, a zahiri bazata juri dukan nan ba haka kawai ba gaira ba dalili.
Umma ta rike haba tace " ke ni kikema wannan kallon??"
Nafi tai shiru.
Umma ta sa hannu ta kara mangareta tace " dauke idanunki daga kaina."
Nafi kam ko gizau idanun nan nakan Umma.
Takaici ya kara rufe Umma tasa hannu biyu zata rufe Nafi da duka.
Da sauri Nafi ta matsa sannan ta kalleta tace " Umma a matsayina na matar Ashraf banaji zan yarda ki cigaba da dukana kamar wata baiwa."
Umma tai sototo tana kallan Nafi, cikin hasala tace " in baki tsaya ba me zakiyi?"
Nafi tace " ni dai ki daina dukana, sannan ni ba bangaren 'yarki naje ba bangaren mijina naje, ba kuma naji nayi laifi dan naje can."
Tana kaiwa nan ta mike davkyar sakamakon jikinta ta cigaba da dingisawa tai gaba, kallan kafafuwanta Umma tai nan danan ta fahimci komai, tsoro da fargaba suka kamata.
Itakam Nafi a hankali ta bud'e kofarsu ta shiga, tana dagowa da niyar ganin Little ko tana bacci, taga Little a tsaye a gabanta daure da towel.
Nafi ta zaro ido ta juya da sauri.
Little tace " da alama nan gaba kadan zaki gudu daga nan tunda yanzu kunfara dan waken zagaye ke da yaya." ta juya tai toilet."
Nafi tadan rufe bakinta sannan ta zauna a gefen gado.
Bayan Little ta dawo Nafi ta kalleta tace " kinga sakon ki?"
"sakon me kenan?"
Nafi ta nuna mata da hannu tace " Ya Habib."
Da sauri Little ta mike ta zanyo jakar, ta hau bud'ewa, turaruka ne da wani lace mai masifar kyau, sai dan kunne da sakarsa silver.
Little tace " jiya yazo?"
Nafi ta daga kai alamar eh sannan tace " do u like him that much?"
Little tai murmushi tace " Ni kaina mamakin kaina nakeyi, amma bakya ganin shima yana sona?"
Tausayinta ya kama Nafi, Nafi tai yake tace " kin fadamai tsakanina da yaya?"
Little ta girgiza kai, Nafi tace " ki fada mai, kar yaji a gari." a ranta tace mayb inyaji ya shiga hankalinsa.
Little ta d'aga kai alamar to sannan ta cigaba da shirin makaranta.
***********
Umma kam a zuciye tai bangaren Mumy, ko gaisawa bata bari sunyi ba tace " Ruma hankalinki daya kuwa?"
Mumy ta kalleta tace " ban gane wannan banzan zancen ba."
Umma ta kara yin hucci tace " wai danki yagama fin karfinki ne? Ko kuwa kin sallamashine yabi duniya?"
Mumy wacce kalaman Umma suka bata mata rai tace " wani irin banzan zance ne wannan, taya zakizo har d'akina ki dinga fadar magana irin wannan wacce batada ma'ana."
Umma ta tabe baki tace " a ido ne kike nuna mana bakyasan wannan tsinaniyar yarinya ko kuwa har ranki?"
Mumy cikin kunar rai tace " har raina mana kema ai kinsani."
Umma tacigaba " to in bakiyi wasa ba zaki samu jikar daji, wanda rabin asalinsa ya kasance kidahumin bafulatanin da ko hausa bai sani ba."
Mumy tace " banasan kunbiya kunbiya me kike san fada."
Umma tace " yarinya ta fara kwana a bangaren Ashraf sannan har jiya ya aikata abinda yakeso, ke wai a sunan uwarsa amma bakisan komai ba sai zaman daki kamar wata gumba."
Mumy ta kara hasala tace " inkin gama zaki iya fita ai ko."
Umma ta juya cikin takaici tai waje.
Zama Mumy tai a bakin gado ta dafa kanta tace " Ashraf!!!!!!"
*********
Shikam Ashraf yau ya koma sabon office dinsa a matsayinsa na Chief Director, Kawu dan ya nuna ma mutane yanasan Ashraf da kansa yazo wai zai tayashi murna.
Bayan ya shiga ya kalli Ashraf yace " Congratulation d'ana."
Ashraf ya kalli Mutanen gun ciki harda Asim sannan shima ya mikamai cikin fara'a, bayan sun gaisa ne Ashraf ya matso kusa dashi yace " thanks but not yet."
Kawu ya kalleshi yace " what du u mean?"
Ashraf ya sake murmushi sannan ya kara matsowa yace " in naje office din Chairman na Company din nan at that time zan amshi taya murnar ta ka."
Kawu ya zaro ido cikin mamaki, ya kalli Ashraf wanda ya sake hannunsa ya karasa ya cigaba da gaida mutane Kamar ba'ai komai.
Asim kam a zuciye yai waje ran nan nasa a b'ace.
Shikam Ashraf ko a jikinsa suna fita ya zauna sannan yasa waya ya kira Dan Litti, ba'a dade ba sai ga Dan Litti nan yazo.
Ashraf yace " Dan Litti inaso daga yau sunanka ya koma Auwal Max, sannan ka fadama mutane hakan sunanka yake, ni kuma yanzu inka fita inaso kaje inda Kawu yake zansa a kiramin kai."
Dan litti yamai kallan mamaki sai dai bai tambaya ba sai yes sir dayace.
Ashraf yace sainya kira ka sau uku zaka amsa.
Yana fita ya shiga neman kawu can ya gashi a sama sai ya wayance da aiki a gun.
Shikuma Ashraf dama dan litti na fita ba dadewa ya tura masingansa akan ya nemomai driver dinsa sunan sa Auwal Max in ya ganshi ya kira sunan da karfi.
Nan masingan ya amsa sannan yai waje.
Dan Litti yana tsaye, gefe kuma kadan Kawu ne tsaye da Asim.
Kawu ya kalli Asim yace " kai wai meke damunka??"
Asim yace " da akai me kenan?"
Kawu ya hade rai yace " ba nace ka dinga kokarin boye emotion dinka ba? So kake kowa ya gane bakasan matsayin da Ashraf ya samu yanzu?"
Asim ya hade rai yace " Abba wai ni haryanzu bakamin bayani ba akan wani dalili ne zaka ba waccan yaron matsayi haka? Baka tsoron abinda zai aikata? Ko kuwa yanzu ka dawo kana bin bayansa ne?"
Kawu ya bud'e baki zai magana yaji ance " AUWAL MAX!"
Cikin tsananin firgice har da sakin takardun hannunsa ya fara waiwaigawa.
Masinja ya kara kwalla kira, Kawu ya rikice yana kalle kalle, Dan litti ya zubamai ido, shikansa Asim sai daya fahimta yace " Abba lafiya?""
Kawu kam sai dudubawa yakeyi baiga alamun wanda yake zargi ba duk ya gama rikicewa, sako ne ya shigo wayar dan litti.
Yana dubawa yaga sakon Ashraf akan kar ya amsa yaje kusa da masinja din kawai su taho.
Haka kuwa akai, Kawu ya duk ya gama rud'ewa dajin wannan suna shikuma Dan litti yaje yaja hannun masinja sukai gaba.
Dan litti ya shiga gun Ashraf ya sanar dashi halin da Kawu ya shiga daga jin sunan.
Ashraf yai murmushi yace "jeka na gode."
Bayan ya fita Ashraf yai shiru yana tunani kafin ya dauko wayarsa ya danna number Dadyn Habib."
Bayan sun gaisa yace " Dadyn nikam dan Allah tambaya, kasan wani Auwal Max?"
Gaban Dady ne yai mugun faduwa duk yadda yaso ya daure sai da muryarsa ta canza cikin rawar murya yace "Auwal Max?"
Ashraf yai dan dariya yace " eh wlh, jiya ne akamin sako akan wai anasan magana dani wai driver din Abba ne Auwal Max, shine nikuma nake tunani kar inje karya yake sannan ni bangama dalilin haduwar mu ba nace bari na kiraka."
Dady yai sauri cewa " Don't meet him."
Ashraf yace ' naam?"
Dady yace " hmm karka yadda Ashraf ku hadu da mutumin da baka sani ba, wayasa me zai maka? Ko mugu ne??"
Ashraf ya jinjina kai alamar gamsuwa sannan yace " nima abinda nake tunani kenan, shiyasa nace bari na kiraka."
Dady yace " yauwa Ashraf kayi tunani mai kyau."
Nan sukai sallama, Ashraf ya kankance ido tare da yin hucci yace " How can u do this to me???? Tayaya duk a cikin mutane ace kaii!!! Har da......"
Kasa karasawa yai ya sa hannu ya rufe fuskarsa.
*ASHRAFEENAH TEAM*
💞
*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_
© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
_*MY INTIMATE FRIEND AISHA MUHD UMAR*_💞
*As it's a special day for My Intimate Friend, i just can't express how happie i am today, It's ur wedding day, the day 5th August have become a memorial day for us.*
*Allah ubangiji ya baku zaman Lafiya da zuri'a dayiba Ameen suma Ameen*
*63*
Ashraf yana fita ya wuce gidan su Ferry, yayi sa'a kuwa a lokacin Mahaifin su Ferry ya dawo.
Tare suka shiga gidan bayan sun gaisa Isma'il ya kalli Ashraf yace " banyi tsammanin ganinka da wuri haka ba."
Ashraf ya dago cikin wani yanayi mai wuyar fassarawa yace " Kasan komai ko kuwa kaima bincike kakeyi??"
Isma'il yai murmushi yace " Bansan komai ba sai dan abinda ba'a rasa ba."
Ashraf yai dan huci kadan yace " Auwal Max a ina zan sameshi??"
Kai ya girgiza yace " bansan inda yake ba, tun wannan ranar, in fact banmasan ko yana raye ba ko ya mutu, sai dai nasan abu d'aya tabbas shine wanda yaja Alhaji a wannan ranar sai dai abin zargi shine sun fita daga gida tare amma daga baya danai bincike sai naji Alhaji ne kawai a cikin motar sannan a bincike nane na gano Auwal Max mai gadi yana kallansa sanda ya shiga kasan mota, hasashe na ne yasa nasan yayi wani abu bawai proof gareni ba."
Ashraf ya matse hannunsa da karfi, tare da runtse ido yace " Shi Abban a ina ya san Auwal max din?"
Isma'il ya kara girgiza kai yace " bansani ba, sai dai tun da nasanshi tare nake ganinsu, sai dai a koda yaushe inaji kamar bawai zuciya daya yake zaune da Abbas ba ganin duk wani plan indai mukai kafin mu aiwatar sai muji shi a gari ance Muktar yayi, shi kuma Abbas ba ya kara tada zancen."
Ashraf yace " Daga bangaren mahaifiyata akwai wani abu da kasani na gaba ko wani abun a tsakaninsu??"
Isma'il ya dan shafi goshinsa sannan yace " akwai case daya faru wanda ya jawo asarar dukiya mai yawa daga bangaren matar Abbas."
Idanu Ashraf ya zaro yace " case?? Wani iri kenan?"
Isma'il ya girgiza kai yace " i can't tell u, sai dai kai ka nemo menene."
Ashraf yai shiru yana tunani, sun danyi shiru kafin daga bisani Ashraf yamai sallama.
Yana fita ya shiga mota tare da sa kansa a sitiyari wani irin zafi yakeji zuciyarsa namai.
Ya dade kafin ya daure ya tada mota yai gida.
**********
Nafi kam yau sam bata fita ba tana kwance a d'aki gani take kamar in ta fita za'a gane abinda ya faru daren jiya.
Bayan magrib tai sallah tana zaune ita da Little sukaji ana knocking.
Little ta tashi ta bud'e, Mumy ce ta shigo fuskarnan tata a b'ace.
Little tace " Mumy ya akai?"
Bata kulata ba ta karasa gun Nafi wacce cikinta har ya duri ruwa, Mumy tace " Ki shirya gobe zansa a maidake garinku."
Nafi ta zaro ido cikin tsananin mamaki ta kalli Mumy, Little ta matso tace "Mumy wai meyasa kike haka ne? Matar yaya ce fa....."
Tsawa mumy ta mata tace " fita."
Little mamaki ya kamata ta fita da sauri, bangaren Ashraf ta nufa tana zuwa tahau bugawa, shiru da alama bai dawo ba gashi ta bar wayarta, jiki a sanyaye ta dawo nan ta hangoshi daga nesa.
Da gudunta ta karasa gunsa, Ashraf ya kalleta yace " Little!"
Cikin haki tace " Yaya Mumy ce."
Yace "Mumy?"
Ta daga kai tace "Nafisa...."
Ai bai jira ta gama ba yai bangarensu da saurinsa.
Yana zuwa bakin kofar dayake a bud'e yake yaji Mumy na cewa " Me zaki iyama Ashraf da har kike tunanin zamq matarsa? Ban yarda da wannan auren ba dan haka dole ne gobe ki koma kauyenku."
Nafi kam hawaye ne kawai ke zubo mata.
Muryar Ashraf ce ta daki kunnuwansu yace " Inji wa kenan?"
Mumy ta juyo har zuciyarta sai dataji dan tsoro sai dai ta dake tace " injini ni mahaifiyarka."
Ashraf ya karaso ciki yace " Do you hate us that much? Ni da Mahaifina nake nufi?"
Idanu Mumy ta zaro cikin mamaki tace " me kake fada haka?"
Yai murmushi yace " me? Ba tsantsar tsana bace yasa kike bakin cikin ganin farinciki na? Na sanar dake matatace, na dauka uwa mai san danta zataso farin cikinsa."
Ya girgiza kai cikin takaici yace " sai dai me? Ban taba gani kinso abinda nakeso ba tun da na mallaki hankali na, in har nace gabas nake san yi to burinki kice kekuma yamma kikeso nai."
Cikin murya mai zafi ya karasa maganar da cewa " inkinsan da haka meyasa kika auri Abba har kika haifine??"
Nafi da sauri ta taso tazo kusa dashi ta dan turashi baya, idanunta na zubar da hawaye tace " Yaya me kakeyi hakan?"
Mumy kam gaba daya jikinta ya gama mutuwa kamar wacce aka kwarama ruwan sanyi, Nafi ta cigaba da turashi zuwa waje tanacewa " please Yaya ka bari, kar kai fada da Mumy saboda ni dan Allah."
Ashraf ya rike hannunta idanunsa suka kada sukai jajawur kamar jan gauta, ya kalli Mumy yace " na tabbata sanda mahaifina ya rasu kina daya daga cikin masu farin cikin faruwar hakan."
Nafi kai kawai take girgizawa tana kuka, Ashraf na gama fadar haka ya fara jan hannun Nafi, har sunje bakin kofa ya juyo yace " in har baso kike nabar gidan nan ba kar ki kara shiga harkar matata."
Ya ja hannun Nafi sukai waje, zubewa Mumy tai a gun ta rike inda zuciyarta take jin tana mata zafi ta saki wani irin kuka mai kuna.
Ashraf kam jan Nafi kawai yake sunje yin kwana sai ga Anisa ta sha gabansu, ya buga mata wani kalli dan yanda yakejin zuciyarsa tayi sa'a ka da bai mareta ba, itama harararsa tai tace "anji kunya wlh kwartanci da ranar Allah, to wlh baku isa ba naga uban da zai maye min gurbina."
Ashraf ya kalleta cikin tsananin bacin rai yace " gurbin inaji nine nake rike da ragamarsa ko? To mai zai faru in na sallami mai gurbin?"
Idanu Anisa ta zaro tace "mai kake nufi Yaya?"
Yace " zaki matsa ko sai na fahimtar dake abinda nake nufi??"
Da sauri ta matsa ya ja hannun Nafi sukai bangarensa, bai saketa