Showing 30001 words to 33000 words out of 141466 words

Chapter 11 - ZUCIYA kowa da irin tasa Complete Hausa Novel

unknown   

13 Oct 2024

15898

Aneesa kafe Ashraf kawai tai da ido jitake kamar zata mutu dan tsananin kishi.


Kawu ya kalli Ashraf rai a b'ace yace " Wani irin iskanci ne hakan Ashraf? "

Ashraf ya mike daga zaunan da yake ya kallesu ga mamakinsu Murmushi sukaga ya saki, ya jinjina kai sannan yace" tunda maganar Asim itace gaskiya banaji inada abin cewa. "

Yana kai nan ya nemi hanyar fita, Umma cikin kuluwa tace "lalai kuwa Alhaji yarinyar nan dole ne ta bar gidan nan, inshi ba'a isa dashi ba ai ita kam karya take. "

Ashraf ya juyo ya kalleta sannan ya kalli Aneesa da ta ke zaune kamar gunki ya bud'e baki zaiyi magana yaji Mumy tace " Gaskiya nima Alhaji yarinyar nan bata kwanta min ba."

Fuskar Ashraf ce ta canza, yanzu kam ransa ya b'aci sosai, bai damu inkowa ya mai abu ba amma ya tsani yaga mahaifiyarsa na goyon bayan masu mai abu.

Kawu ya kalli Asim yace "Ai ba sai anja da tsauri ba, yanzu nan za'a kirata tabar gidan nan. "

Ashraf ya had'iyi wani abu sannan ya d'auke idansa daga kan Mumy ya maidashi kan kawu, ya kalli Kawu yace " Kawu banasan abu yaji da zafi sai dai in aka kaini bango banajin kowa zaiji da dadi a gidan nan. "

Yana kai nan yai waje, Mumy ta dafa kanta, tanaji Umma na cewa " Allah wadaran nakaa ya lalace, sam yaran nan yafi karfin kowa a gidan nan? "

Kawu yai shiru shikansa ya kasa magana.

Ashraf kam yana fita ya kira number Habib, bugu biyu Habib ya d'aga yace " Buddy yau kuma soyayyarce ta tashi? "

Ashraf yai tsaki yace " Habib dan Allah makarantar Abbanka wace iri ce? "

Da mamaki Habib yace "lalai Ashraf kana nufin bakama san me Abbana yake ba? "

Ashraf yace " Malam dole ne sai na sani? Ba gashi ina tambayarka baa yanzu? "
Habib wanda baiji dadin kalaman Ashraf ba yace " Primaryce da secondary."

Ashraf yace " day ce ko boarding?"
Day ce mana.

Ashraf yad'an shafi kansa sannan yace " Habib boarding school nakesan asa Nafisa gashi kasan tayi girma ba ilimi na rasa ya zanyi. "

Habib yai shiru can yace " karka damu Aminin Abba matarsa itace principal ta makarantar kwana dake nan minjibir, sai a d'an yi mata ciwa ciwa ko Js3 ne a sakata. "

Ashraf ya d'an saki fuska yace "yauwa Habib hakan yayi."

Habib yai dariya yace " bazaka gode min ba? "

Ashraf yace " in komai ya kammala zan gode ma, but please ka tambayi Abban yanzu dan inasan ta tafi a satin nan. "

Habib yace Shikenan.


Yana kashe wayar yai ajiyar zuciya sannan ya makama inda ya fito wani mugun kallo na takaici, yai gaba.



¤¤¤¤¤¤¤¤


Su kam a ciki sai tada zancen suke yi, mumy kam duk ranta ya gama da gulewa rai b'ace ta fito daga falon tai b'angaren su Little.

A zaune taga Little a kan gado ta zuba tagumi, Nafi kuma ta ra kub'e a gefen gado ta cusa kanta cikin cinyoyinta, abu d'aya ke yawo a ranta tajama Ashraf fada ita abinda ke damunta kenan.

Muryar Mumy ce tasata ga d'ago, mumy ta tsaya a kusa da Little tace " Nafi ta fadamiki abinda ya faru? "

Jikin little a sanyaye tace " Mumy bakisan Nafi bane, kome ke damunta bazata taba fad'amin ba. "

Mumy cikin fada tace " ai kuwa yau dole ta fada tunda gashi can ta jama Ashraf cin mutunci. "

Nafi wacce jin hakan yasa ta mike cikin tsoro ta matso kusa da Mumy ta tsugunna a gabanta tace " wlh Mumy ba abinda Yaya ya sani, bai ma san nice naje d'akin ba. "

Mumy tace " mene? "
Nan little ta fad'a mata ita yace taje ita kuma batada lafiya shine Nafi taje, jikin mumy ne yai sanyi ta kalli Nafi tace " to akace kina d'akinsa? "

Nafi ta share kwalla tace "Mumy bashida lafiya fa? "

Idanu mumy ta zaro ta kalli Nafi jiki a sanyaye, Nafi wacce idanta ya rufe dasan kare Ashraf tacigaba " Mumy wlh tun safe bashida lafiya kuma wlh yana jin jiki, ni a ganina bai kamata ma ace kaf gidan nan ba wanda yasan halin da yake ciki ba........"

Hannu tasa ta rufe bakinta, me take fada? A ranta tace " amma ai Anisa ta sani.

Mumy tai shiru a hankali ta juya tai waje batace komai ba, little ta kalleta tace " lalai Nafi dama kin iya zakewa haka? "

Nafi ta kalleta tace " Maryam bakisan halin da yaya yake ciki bane sannan ace dake kanwarsa da mahaifiyarsa ba wanda ya sani? Na d'auka in bashida lafiya Mumy ya kamata ya fara sanarwa? "

Little tai wani sansanyan murmushi tace " Nafi kenan, bakisan komai ba a kan harkar rayuwar gidan nan. "

Nafi ta mata kallan mamaki, little tace " karki damu zan sajar dake komai gobe, in kikaje zaki gane dalilin dayasa Yaya baya shiga harkar Mumy. "

Nafi tai shiru batace komai ba....





*THE INNOCENT TEAM*
*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com

2⃣2⃣




Mumy ta fito jiki a sanyaye kanta sai sara mata yake yi, a waje ta hango Aneesa ta taho kamar zaki rike da wata zungureriyar waya tana tafe Umma na mata magana amma da alama bata ma jin me ake cemata, Mumy tana tsaye a kofar su Little har Aneesa ta karaso, idanunta sun canza.


Da mamaki Mumy ta kalleta tace " Neesah meye hakan? "

Aneesa wacce sai hucci take ta kasa magana sai neman cusa kanta ciki take, Mumy tasa hannu ta riketa tace " Neesa meye hakan wai? "

Umma ce ta karaso cikin kinibibi tace" Yauwa gwara da kika riketa wai Nafi zataje ta zane. "

Mumy takaici ya kamata tace " in kuma Ashraf d'in yajiki kice me? "

kallan Mumy tai kamar mai shirin kuka tace" Mumy amma kina ganin..... "

Mumy tace " Laifinkine, in har Nafi ta fiki sanin meke damun Ashraf, ke da zai zama mijinki amma ace ba kece ke kula da shi ba. "


Umma tace " wace irin magana kikeyi haka? Haba Amina ya zakisa yarinya a gaba wacce ranta yake a b'ace ki kara b'ata mata."

Mumy ta kalli Umma sai dai takaicin abinda yake faruwa yasa ta kasa tanka mata.

Umma ta juya kai tace " haba Amina _wace irin zuciya gareki?_ace ke kawai d'anki kika sani? "

Mumy ta juya batare da ta sake magana ba.

Aneesa ta kara zuwa wuya gani take kamar saboda Nafi itama Mumyn take mata haka.
Hannunta ta fizge daga gun Umma tai ciki a zuciye.

Nafi kam ta d'auro alwala isha'i kenan, ta zauna a bakin gado ta rasa abinda ke mata dadi, taji an banko kofa da karfi kamar za'a b'ala, da sauri ta kalli kofar.

Little dake zaune akan kujera ma ta d'ago da sauri.

Aneesa a zuciya ta shigo d'akin, Nafi dake tsaye ta shiga kallanta cikin tsananin tsoro, Little ta mike tace " Ya Neesa meye kuma hakan? "

Aneesa ta buga mata wata muguwar harara sannan ta nufi kan Nafi gadan gadan Umma kuma ko kunya tana tsaye a baya.

Da karfi Little tace " Wlh Ya Neesa kika daketa sai na fadaki da Yaya. "

Cikin kuluwa Aneesa ta wurga mata kallo, Little ta kalleta tare da d'aukan wayarta tace " Wlh kika daketa yanzu zan kirashi."

Aneesa kam ta kulu fam kamar zata fashe, Umma ta matso ta gaurama Nafi mari iya karfinta sannan ta kalli Little tace" ni ki tabbatar kin fadamai inyaso ya zo ya rama mata. "

Tana kai nan ta fizgi hannun Aneesa tai gaba.


Nafi kam ko kuka batai ba dan ganin zabgegiyar bulalar dake hannun Aneesa yasa batama ji zafin marin sosai ba.


¤¤¤¤¤

Mumy kam ana idar da sallah tai b'angaren Ashraf, a hanya suka had'u da Mumy baice mata komai ba sai dai yasan gunsa tazo, nan ya bud'e ya shiga tare da kunna kwan wuta.

A bud'e ya bar kofar hakan yasa Mumy ta shiga.

Shikam d'aki kawai ya wuce, ya d'au ruwan da Nafi ta gasa mai gun ciwon ya zubar a toilett, sannan ya matse towel d'in ya shanya sannan ya fito.

Mumy na zaune hakan yasa yaje d'an nesa kadan da ita ya zauna a kasa, Mumy ta kalleshi jiki a sanyaye tace " Ashraf abinda ya faru d'azu kayi hakuri....."

D'agowa yai ya kalleta idanunsa sunyi jaa jikinta ya kara yin sanyi, cikin wata irin murya wanda mai sauraro shi kad'ai zai fahimci abinda ke zuciyar me maganar Ashraf yace " Kin taba yadda dani Mumy? Ko me aka fada a kaina tun ina karami kin taba yin bincike kafin kimin fada? "

Mumy idanunta suka cicika da kwalla sai dai tsananin tausayin Ashraf dake yawo a ranta.

Hannu yasa a bugi inda zuciyarsa take da karfinsa wanda kana iya juyo karar dukan ya cigaba " Kinsan ya nakeji a raina? A duk sanda kika zargeni da abinda banyi ba?....."

Kasa karasa kalamansa yai saboda wani rad'ad'i da zuciyarsa take mai, Mumy wacce ganin yanayin d'anta da bata taba gani ba yasa hawayen datake b'oyewa suka zubo ta gefen idanta.

Kallansa tai cikin dauriya tace " ba haka bane Ashraf. "

Ya kalleta sannan yai wani murmushin takaici yace " Nafi zata tafi makarantar kwana a satin nan insha Allah. "

Mumy bata d'auke ido a kanshi ba tace " amma naga kamar ba tada karatu? "
Ya sake yin wani murmushin wanda itakam mumy sam batasan taga yayi saboda bata sani me yake nufi yace "eh hanya za'a mata ta shiga Js ko 3 ne inyaso sai a dinga mata lesson kuma a makarantar. "

Mumy ta jinjina kai tace " hakan yayi sai dai baka ganin karatun zai mata wahala? "

Ashraf ya d'an tab'e baki yace " wannan kuma ruwanta. "

Mumy tace " shikenan in makarantar ta fito sai ka fadamin sai muje a mata shopping Allah ya baka lada ya kuma yi albarka. "

A cikin ransa yace Ameen, ta mike tace " bari inje. "
Bai amsa ba ko ince tasan ma bazai amsa ba, tana fita yabi bayanta da kallo sannan ya koma d'aki ya d'auko diary d'in mahaifin sa wanda wasiya ce kawai ya barmai.

Shafin farko wanda a kullum sai ya karantashi yau ma shi ya karanta " _Ashraf kada ka kuskura kabar mutane susan abinda ke zuciyarka,_ _ka dinga kokarin b'oye bakin ciki ko farin cikin dake ranka, kar ka bari wani yasan sirrinka, wannan ita kadai ce hanyar da zaisa ka kare kanka...ko da kuwa 'yan uwanka ne na jini..._"


Ashraf ya share zufar data keto mai duk da sanyin AC d'in da ke d'akin, Murmushi yai wanda kana ganin kasan na bakin ciki ne a fili yace " Dad zan iya jure hakan kuwa? I am really lonely."


Ya kwantar da kansa kan gado, kafad'ar sa na masa zugi sai dai zugin dake zuciyarsa tafi karfin wannan.......




¤¤¤¤¤¤


Habib kam da kansa ya samu Abbansa ya mai bayani, Abban Habib na tsananin san Ashraf a lokacin ya kira wayar abokinsa ya sanar dashi, sunyi rashin sa'a matar tashi an mata transfer zuwa Rumfa Collage sai dai ya sanar dasu ai kanwarta ma principal ce ta FGC na kazaure, nan ya sanar musu in suna san can d'in to a yanzu zai kira kanwar matar tasa ya fada mata.

Nan Habib ya ma Abba alama da a yadda, sunyi sallama akan zai kira anjima.

Ba'a dade ba ya kira tare da sanar dasu ba matsala duk sanda suka shirya ko gobe ne su kaita.

Nan Habib ya kira Ashraf yamai bayani.

¤¤¤¤¤



A b'angaren D'an litti kuwa yan sanda sun gaji da ajiyarsa gashi abin haushi bashida alamar sanar dasu Inda Ashraf yake, duk kuwa da dukan da sukamai, hakan yasa haushi ya kamasu suka cilloshi waje tare da kwace wukar dake jikinsa.


D'an litti ya sha kuka wiwi gashi ko ficika bashida shi, ga wunya datake damunsa.

Dakyar ya mike ya dingisa ya shiga gari, yayi sa'a ya sami wani mutum ya bashi naira d'ari.

Nan ya gangara yasai wainar gero kan kace me ya cinye, ta gumi ya baza yace " Oh Ni D'an litti haka rayuwata ta koma? Daga boko sai a nemi halakani? Yanzu ni ina zan nufa in nemo Ashaf d'in? "

Ya jingins kansa da bango zafin rana na damunsa.



Nace wayyo🤦🏻‍♀



*THE INNOCENT TEAM**ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com

*Fatie Shafi'u ina tayaki murnar kammala Jarabawarki. May Almighty Allah help and protect u.... ILYSM*


Washe gari da safe Habib yaje makarantar mahaifinsa yama Nafi takardun karya na primary da kuma Js 1 and 2, sai dai takardun sun nuna sam batada kokari.


Nan ya taho da shi gidansu Ashraf.

Yau gidan an tashi kowa zuciyarsa ba dadi musamman ma Umma da Aneesa, Little kam ta fita makaranta.

Itakam Nafi tana kitchen ta zake sai aikin girki take, sunayi suna 'yar hirarsu da Goggo.
Suna gamawa ta fito duk jikinta ya d'an baci Amra ce ta karaso gunta da gudu tace " Wai kizo inji yaya. "

Nafi ta kalleta cikin zak'uwa tace " Ya Ashraf? " kai Amra ta d'aga mata ai kam Nafi da sauri ta nufi b'angarensa tana tafe tana gogee fuskarta da hannu, tun jiya takesan ganinshi sai dai ba yanda zatai.

Fuskarta a sake ta kwankwasa kofar, ta saba in yana ciki sai dai yace ta shigo in dai har ba makulli yasa ba, sai dai yau gani tai anzo an bud'e da fara'arta ta kalli mai bud'ewa tace " Yaya ina kwa...... "kalamanta ne suka tsaya ganin Habib a tsaye yana mata murmushi.

Jin ta tsaya da magana yad'an kanne ido cikin salonsa yace " Haba Nafi ba ni kika so gani bane? "

Da sauri ta girgiza kai alamar a'a sannan ta d'ora da cewa " ba haka bane Ya Habib. "

Habib ya d'an matso kad'an hakan yasa ta d'an kara matsawa, kara matsowa yai itama ta kara matsawa, sam bata kula tazo karshe ba tayi baya zata matsa kawai taji zata fad'i, da sauri yasa hannu a kugunta ya tarota.

Nafi kam har ta runtse idanta kam, jin an riketa yasa ta bud'e ido a hankali, Habib ya sakar mata wani lalausan murmushi, sannan ya matso da fuskarsa yace " Me yasa kika tsaya da maganar ki to? "

Yawu ta had'iya da karfi sannan ta d'an motsa baki tace " Ya Habib d'an sakeni. "

Jin ta waske bata bashi amsa ba yasa ya d'agota tare da sake cewa " Shikenan na hakura da gaisu.... "
Bata jira ya karasa ba tace ina kwana? "

Dariya ya d'anyi sannan yace " Nafi kina burgeni na rasa me yasa. "

Kasa tai da kai dan itakam tasan wasa ne ace tana burge wani.

Ashraf dake zaune a kujera duk yana kallan me sukeyi kasancewar kofar a bud'e Habib ya bata yaja wani karamin tsaki tare da girgiza kai yace " in kun gama sai ku shigo, dan ni inada abinyi. "


Nafi ta kalli inda Ashraf yake haka kawai taji gabanta ya fad'i tare da tsananin takaicin ganin ta dayai.

Habib ya matso da niyyar rike mata hannu da sauri ta b'oye hannun a baya kallanta yai fuska a sake sannan ya d'anyi gaba yace " Ki shigo. "

Da sauri ta shige jikinta duk yai sanyi.

Ashraf na zaune yana kallo ta karasa tare da zama a kasa, Habib ya kalleta yace " zauna a kan kujera mana? "

Ashraf ya bugamai wani mugun kallo yace " Mu sa'aninta ne? Kai meyasa kake kokarin zubar mana da mutunci agurin yara kanana? "

Nafi wacce ko alamar tashi dama batai ba ta d'ago ta kalleshi sai dai zuciyarta ta d'anji ba dadi.

Ashraf ya d'auke idansa, Habib ma kasa magana yai, Shiru ne ya d'an biyo baya kafin Ashraf yace " Nafisa! "

Gaba d'aya tun daga kan yatsar kafarta har zuwa kanta sai dataji wani abu ya wuce mata, d'agowa tai a hankali ta kalleshi.

Ashraf kam ko a jikinsa yace " yau zuwa gobe zakuje da Little da kuma mumy xakuje siyayyar kayan makarantarki. "

Kallonsa tai cikin mamaki batasan sanda tace " naam? "

Ya had'e fuska sosai yace " bakiji me nace ba? "

Tace "

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login