Showing 126001 words to 129000 words out of 141466 words
zasu tashi jibi nan, dan dama yafisan su tafi da wuri to sai yai sa'a ya samu International saboda ya tabbata daga Asim ya sanar da kawu a inda ya dauko takardun nan to fa babu makawa yasan shikenan Kawu zai san shine ya shirya komai...
Hmmmmmm😷
*#ASHRAFEENAH TEAM*
💞*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_
© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*80*
Mikewa yai daga zaman da yake tare da furzar da wata iska sannan ya d'au wayarsa yama Nafi da mumy sako akan su shirya saboda tafiyarsu.
Nafi kam kallan sakon take tayi, duk da tana masifar san zuwa kasa mai tsarki sai dai abin ya zo mata a ba zata, na farko ga bikin Jibiya wanda ya matso daf sannan ita a iya saninta Hajj ake fara yi tunda shine farilla.
Sai dai taci alwashin yima Ashraf magana in ya dawo.
*********
Sai Yamma ya fito daga office station ya wuce inda acan ya samu Umma, kana ganinta kasan tana cikin wani halin kusa da ita ya karasa yace " Umma lafiya?"
Hawaye ne ke zubowa a idanta tace " Ashraf banga alama Mansir nada niyyar taimakama Asim ba, na sanshi sarai akan dukiyarsa zai iya hakura da Asim a matsayin d'ansa ni kuma na tattare dukiyata naba Asim ya sa a kudin company din da ya siya."
Ashraf yai shiru tabbas ganin halin da take ciki ya sa ya tausaya mata sai dai bazai taba yin bailing Asim ba dan kuwa shine key dinsa na kama Ubansa.
Umma yaji ta kamo hannunsa tace " Ashraf na sani tun kana karami ba sanka nake ba, ban damu da harkarka ba sai dukiyarka, har rayuwarka na nemi salwantarwa ni da Asim, sai dai a yanzu ina dana sanin hakan, banida wanda zan iya roka akan ya taimaki Asim sama da kai, ka sani iyayena ba masu karfi bane ga girma ta zo musu, ni kuma banida uban kudin da ake bukata, Ashraf ka dubi girman Allah ka taimaki Asim."
Ashraf ya kalleta cikin kulawa zuciyarshi ta farayin sanyi, sai dai tunowa dayai ita kadaice taga Auwal Max a yayin da yake lalata birkin mahaifinsa yasa ya dake.
Yace " Umma karki damu muna tattaunawa da 'yan sandan insha Allah komai zai yi daidai."
Idanu ta runtse tace " Nagode Ashraf ban taba tunanin zan nemi taimako a gunka ba."
Ashraf yai murmushi sannan ya mike.
Gun Kb ya nufa, Kb yace " ya za'ai da kudin nan?"
Ashraf yace " ka kai banki a jiya bayan komai ya kammala zamu maidamai kudinsa."
Kb ya jinjina kai alamar gamsuwa sannan yace " what are u planning to do next?"
Ashraf yace " D'an Siyasan nan fa? Har yanzu shiru?"
Kb yace " yau muke sa ran dawowar yaron daya tafi binciken."
Ashraf yace " Allah yasa a sameshi wannan karan."
Kb ya amsa da Amin.
Gun Asim ya shiga, Asim har yayi baki ya rame, dan tunda yazo gun nan ya kasa cin abincinsu.
Ashraf ya kalleshi yace " Asim ance baka cin abinci, kasan dai dole ne kaci abinci ko ma samu mu gama wannan fadan da ya tunkaromu lafiya ko?"
Asim wanda kansa ke kwance kan tabir din ya dago ya kalli Ashraf yace " Nasani ni kuma tawa ta riga ta kare."
Ashraf yace " Haba Asim da hankalinka kuwa?"
Asim yai wata dariya ta tsantsar takaici, yace " rayuwa kenan, mahaifina da na dauka duk duniya yafi damuwa dani sai gashi lokacin da nake bukatar kulawarsa ya nunamin karema ya fini matsayi a gunsa, sannan kai da nake ganin kaine babban makiyina a duniya yau gashi kaine kake kula dani."
Ashraf ya hade rai yace " kai dai ka daina wannan tunanin na shirme ka kula da kanka har Allah ya kawo mana mafita."
Asim yai murmushin takaici baice komai ba.
Ashraf tare suka taho da Umma a motarsa tana sauka shima ya sauka yai bangarensa.
Ya sani Anisa na gun Umma hakan yasa ya fito falo bayan yayi sallar magrib sanyi da singlet da kuma gajeran wando.
Tv ya kunna yana kallan labarai, sai dai ya rasa ke yasa yau yakejin tsananin kewar Nafisansa, gyara kwanciyarsa yai ya koma rufda ciki, duk da yasan ba'asan kwanciyar sai dai yana ganin ita kadaice mafita.
Ganin hakan ma ya kasa kwantar mai da hankali kawau ya mike ya hau exercise, kwankwasa kofa yaji, sam ya manta shigar dake jikinsa ya karasa ya bud'e.
Nafi ya gani a tsaye fuskarta a maze.
Bari kofar yai a bud'e shikuma yai ciki, ta shigo tare da maida kofar ta rufe.
Sai da sukaje tsakiyar falo sannan ya tsaya tare da juyowa ya kalleta, Nafi itama kallansa tai, Ashraf kam wani abu ya dingaji yana taso mai, Nafi ta daure ganin kamar zuciyarta na neman yin rauni da kallan da yake mata, wanda shi kansa bai san yanayi ba.
Ta daure tace " Yaya mai kake nufi da zancen tafiya jibi?"
Ashraf kallanta kawau yake baice komai ba, ta dan motsa baki sannan tace " Yaya ke ka daukeni? Kaza? Tattabara? Ko me? Ba ka damu da ni ba, ka daina shiga harkata sannan kawai sai ka min sako akan inshirya wai jibi zanyi tafiya? In har a matsayin mutum kadaukeni banaji zaka dinga min abu haka, na rasa ya kakeso inyi da raina, ka daina kulani, na dauka na huri zuciyata nima na jure da kulaka, ka daina ko amsa wayata wannan ma na huri zuciyata na jure sai dai inma sako yanda kake min, sai dai banaji duk wannan abun da..........."
Yanda bakinta yake motsi tana magana gashi tasa jambaki light pink kawai yake kallo, kasa jurewa yai ya kai bakinsa cikin nata, wanda ya hanata karasa maganar da takeyi.
Wani irin salo yake mata wanda duk yanda taso taki biyemai ta kasa, kiss suke sosai wanda kana gani kasan lalai masoyan sunyi rashin juna da yawa.
Bakinsa na cikin nata suna mikama junansu sakon ni mai cike da kewa Ashraf kam duk ya rikice, ya saka controlling din kansa kan kace me? Ita kanta ya rabata da kayan jikinta, nan suka fada kan kujera........Hmmmm babban al'amari nikam ina ganin haka nai gaba.
Ashraf ya dade yana kwasar garar da ya dade bai ji ba, sai dai ya rasa dalili yau jinta yake daban ita kanta yau tasan Ashraf yayi missing dinta.
Suna gamawa ya rungumeta tsam a jikinsa, yana fitar da wani numfashi na farinciki, Nafi ma idanunta ta lumshe tanajin kaunarsa na kara ratsata, cikin wata irin murya mai cike da ma'anoni da yawa yace " Baby i really miss u."
Hannu ta runkule ta dan naushi kirjinsa tace " then y?"
Ya kara jawota jikinsa yace " dole ce ta sani hakan, saboda inasan amfani da Anisa."
D'agowa tai ta kalleshi idanunta suka ciciko tace " rashin yarda dani ne yasa baka sanar dani ba?"
Kai ya girgiza mata alamar a'a yace " Duk duniya kece mace ta farko dana yarda da ita 100% banaji dar a kanki, sai dai ina tsoron abinda ke zuciya."
Kallan mamaki tamai tace " kamar ya?"
Yace " in har kikasan ba da gaske nake ba, bazaki taba nuna jin haushin ki da kishinki ba yanda zasu aminta ba."
Ta dan maka mai harara tace " shine nima kai using da feelings dina?"
Sumbatar lebenta yai fuskarsa da daf da tata yace " do u think it's easy?"
Murmushi tai, tace " amma duk da haka ka wahalar dani."
Sumbatar idanunta yai yace "am sry Baby, na wahalar dake ni kaina na sani, shi yasa nace zan amshi punishment dina."
Ta sake murmushi tace " maganar tafiya fa?"
Yace " Yanzu it's eye for eye, thooth for thooth, we are in a war ni da kawu i am afraid kar wani abu ya samarmin ke ta dalilin revenge dina."
Baki ta turo tace " Amma......"
Hannu yasa ya toshe mata bakinta yace " Baby please."
Idanunta ta rufe sannan a hankalu ta bude jiki a sayaye ta daga kai alamar to."
Mikewa yai ya dauketa yai toilet da ita.
Sai daya cika musu bahon wankan sannan ya sa kayan kamshi na ruwa sannan ya sata a ciki shima ya shiga.
Ta kalleshi tace " Allah baiyi zan tsaya bikin Jibiya, thanks to someone."
Idanu ya kankance yace "someone? Do u mean me?"
Ta dan murguda baki tace " nidai ban fadi suna ba."
Kallanta ya tsaya yi, ta debi ruwa a hannunra ta watsa mai tace " yallabai kallan fa?"
Dariya yai yace " fada kikeso?"
Ta tsuke baki, shima hannu yasa duka biyu ya riga watsa mata ruwa, nan itama ta dage tana watsa mai, dariya sosai suke yi wanda kana ganinsu kasan suna cikin tsananin kaunar juna.
Bayan sun gama wanka, ta jawo towel d'aya ta rufa sannan tace " na fita."
Kallanta yai yace " nifa?"
Tamai gwallo tace " ka dauka da kanka."
Tai d'akinsa tare da zama kan gado tana dariya.
Ashraf ya fito yana zuwa ya sa hannu a gugunta ya matse da karfi, wanda ya sa ta saku kara yace " ni kika ki daukoma towel?"
Tana ihu da dariya tace " sry Yayana na tuba na daina."
Yace " inaa baki dainaba sai na hukuntaki tukun na."
Ganin yaki saketa yasa tace " Yaya Nisa?"
D'agowa yai da sauri ta mike da gudu tana dariya.
Murmushi yai sannan ya mike sambal akan gado tare da rufe idansa.
Ahhh na kosa in gama wannan case din in ganni tare da matata kullum.
Abinda yake fada kenan a ransa.
*#ASHRAFEENAH TEAM*
*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_
© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*Gareku yan gro din World of Hausa Novel, Mumbari M.Jabo, Maryam mai dala grp na gode kwarai da yanda kuke san littafin nan. ILYSM😍*
*81*
Washegari da safe bayan Kawu ya fita, Dan Litti yazo ya dauki Mumy da Nafi yai abuja dasu dan tacan zasu tashi gobe.
Little kam taji takaici sai dai Nafi tace mata ai ita saboda makaranta, tunda su sai nan da 1mnt akace list dinsu ma zai fito.
Ashraf sai dayaga tafiyarsu sannan ya kira Kb yace " a ina kace an samu Dan Siyasan?"
Kb yace " yana nan asibitin Murtala ashe bashida lafiya ne shiyasa akaita nemansa aka rasa."
Ashraf yai murmushi sannan yace " ganinan zuwa ka turon ward din da yake da number d'akinsa."
Nan take Kb yamai Text Ashraf yaja mota yai gaba.
Bayan ya isa asibitin ne ya tafi ward din masu cancer sannan ya duba number d'akin.
Knocking yai nan akace ya shiga, a hankali ya tura kofar d'akin, wani ne a kwance jikin nan duk ya rame kamar me kanjamau sannan ga wani matashi a kusa dashi a zaune.
Jiki a sanyaye Ashraf ya shiga tare da karasawa bakin gadon.
Matashin wanda baifi shi ba yace " ban gane ba?"
Ashraf yai murmushi sannan ya dauko complimentary card dinsa ya mika mai yace " sunana Ashraf."
Kallansa yai, wanda hakan yasa Ashraf yace " ba Dan siyasan dayai House of rep bane da?"
Matashin yace " shine."
Ashraf ya kalli mara lafiyan yace " Alhaji Uba ka san Mansir?"
Kallan Ashraf yai fuskarsa dauke da alamar tambaya, Ashraf yace, " Mansir kanin Abbas marigayi mai A&A Food. Ltd?"
Haryanzu dai bai fahimta ba sai dai ya maimaita kalmar A&A?"
Ashraf yace " eh wanda yake auren kanwar Hisham."
Jin sunan Hisham yasa ya fara kokarin mekewa zaune, hakan yasa d'ansa ya taimakamai ya zauna, kallan Ashraf yai yace " ina Hisham? Ka taimaka ka kiramin shi."
Ashraf yace " baya kasar ne yanzu haka ma shiya turoni nadubaka, baisan baka da lafiya ba."
Hannun Ashraf ya kama guda d'aya wanda Ashraf ya dana start da d'ayan hannunsa a wayarsa dake aljihunsa.
Mutumin yace " Yaro ka ba Hisham hakuri, a zahirin gaskiya nayi laifuka da dama a rayuwata ta duniyar nan, wasu na nemi yafiya wasu kuma banma san inda mutanen dana cuta suke ba, na hau mulki, dadinta yasa na manta da Allah na kwashi dukiyar jama'a sannan na cuci jama'a Hisham na d'aya daga cikin mutanen da bazan taba mantawa ba saboda nine sanadin talaucewarsa."
Ashraf yai shiru tausayin mutumin ya kamashi, ita dama rayuwa haka ne, yau in kaine gove ba kai bane.
Mutumin ya cigaba, ka san kanin mijin kanwarsa?"
Ashraf ya ce "eh shine Mansir din ai.",
Mutumin yai ajiyar zuciya yace " kacema Hisham wlh wannan mutumin shine ya sani komai, shawara yazomin da ita ta neman kudi, nikuma alokacin idona ya rufe, zuciyata ta zarme ina ganin zan samu kudi mai yawa da xai sa inyi campaign ba tare da matsala ba, shi yasa na dauki shawararsa, sai dai dalilina yasa aka kama dukiyarsu mai yawa har hakan yakai ga ajalin mahaifinsa, wanda tsoro yasa nakasa fadar abinda ya faru a lokacin, ina tsoron kar nima azal ta fadamin."
Kuka ne yaci karfin mutumin ya shiga yin tari a hankali,yace " yanzu gashinan kowa ya gujeni, wannan yaron shi kadai ke taimaka ta, shi kuma ba jinina bane rikonsa nai, nawa 'yayan duk sun gudu sun barni."
Idanun Ashraf ne ya ciciko, yasa stop sannan yace "amma wace irin cancer ce ke damunka?"
Murmushin yake yai yace " blood, anyi maganin har an gaji shiyasa nace shima yaron nan ya barni kawai a gida in kwanana yazo in tafi."
Ashraf ya kalli matashin, hawaye yaga yana gogewa, tausayi ya kara kamashi, ya kalleshi yace " ya sunanka?"
"Abdulmalik."
Ya fada
Ashraf yace " wani aiki kake?"
Yace " kasuwanci nake a kwari, inada karamin shago."
Ashraf ya kara tausaya mai, yace " aure fa?"
Yace " shekarar Alhaji 5 kenan ba lafiya ina ni ina tunanin aure?"
Ashraf yai shiru kafin daga baya yace " ka zo ka sameni a address din dake jikin katin, inada sha'awar kasuwanci inyaso sai in bude ma babban shago sai ka dinga mana."
Kallan mamaki Abdulmalik yama Ashraf, shikam Uba kuka kawai ya saka yana godiya kamar me, Ashraf yace ba komai, sannan ya ajiye musu kudi dubu 30 ya fita.
Yana fita ya runtse ido cikin tsananin tausayi yace " Rayuwa kenan."
**********
Kawu ne zaune kusa da Asim ya kalleshi yace " wlh kaji na rantsema yau itace rana ta karshe da zaka ganni anan, in har baka fadamin inda ka samu takardun nan ba."
Asim jiki a sanyaye cikin tsoro yake kallan Mahaifinsa.
Kawu yace " to shikenan, ka karashi rayuwarka anan ni dakai kuma......"
Da sauri Asim yace " Sata nai a d'akin Ashraf."
Idanu kawu ya zare cikin tsananin mamaki yace "mene?"
Nan Asim ya bashi labarin abinda ya faru.
Hannu kawu yasa cikin takaici ya wankama Asim wani wawan mari yace " bakada hankali ne? Me yasa ne nikam kwakwalwar kifi Allah ya d'orama? Kana tunanin Ashraf Shine zai ajiye takardunsa a fili? Yaron da nafi shekara 10 ina sawa a min bincike akan ma yawan dukiyar Abbas daya barmai amma sam hakab ya faskar saboda tsananin wayau da takatsantsan irin na yaron, shine kakeso kacemin ya ajiye takardu a d'akinsa?"
Asim yai shiru, Kawu ya naushi iska cikin takaici yace " kana xaune sokon banza ya kamaka cikin ruwan sanyi, kai wannan yaro nikam bansan jakantarka ba."
Waje yai da sauri cikin takaici, yana fitowa Anisa ta kirashi tace "Abba nikam Mumy tayi tafiya ne?"
Cikin fada yace " kamar ya?"
Tace " a'a naga bangarenta ansa kwado ne sannan su Afra sun koma bangaren Little shine dazu da Afra tazo tacemin ai Mumy tayi tafiya."
Cikin tashin hankali yace " ina Ruma zataje ba da sanina ba? Sannan d'azun nan fa na barta a gida."
Kashe wayae yai a zuciye ya kira wayar Mumy a kashe ya jeta, nan fa idanunsa suka kada.
Ya na kokarin saukowa daga steps din gun sai ga Ashraf.
Kallansa ya dingayi harya iso, Kawu ya kalleshi yace " ina Uwarka?"
Ashraf yai dariya yace " haba kawu wannan ai wayan zagine, kace ina matarka dai?"
Kawu ya fara huccin takaici, Ashraf yai murmushi tare da girgizamai dan yatsa yace " no no no ai bai kamata ka nuna tashin hankalinka tun yanzu ba, inkai haka u will spoil the game, it won't be fun."
Ya sake murmushi sannan yai ciki.
Wani irin ihu kawu yasa na takaici, Ashraf ya wani murmushi sannan yai ciki😏
*#ASHRAFEENAH TEAM*
💞*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_
© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*82*
Kawu cikin tashin hankali yai gida, b'angaren Mumy ya nufa ko mota ma bai rufe ba, yana zuwa kuwa yaga kwado a kofar da zata sada ka da b'angaren, Ruma! Ruma! Ruma! Abinda kawai yake fada kenan cikin tsananin tashin hankali, kofar ya taba tare da rike kwadan.
Ya dade a haka kafin ya koma na sa bangaren cikin takaici, ba shakka dolene ya nemo Ruma dan kuwa in har bai ganta na kwana biyu ba bayaji hankalinsa zai kwanta, a iya saninsa mutane kan ce in har ka auri mutum ka zauna dashi na shekaru to fa soyayya na gushewa sai dai zaman hakuri da na 'ya'ya, shikam a yanda yakejin