Showing 12001 words to 15000 words out of 141466 words

Chapter 5 - ZUCIYA kowa da irin tasa Complete Hausa Novel

unknown   

13 Oct 2024

15901

zan shiga ciki so nake ki shiga da wannan tai wanka taci abinci ki bata kayankk tasa. "

Kallan Nafi tai sannan tace " waccece? "
Yace "Zan fada miki, Mumy fa? "

Tace " duk fa muna bangaren Umma muna zazzaune, mumy jiya cir ruwa kawai tasha. "

Ya dan juya kai, little tace " Yaya ya kamata kaje ka ganta kafin ka shiga ciki dan da alama nan kafara zuwa. "

Kai ya juya baice komai ba, Kallansa tai cikin rashin jin dadin yanda sam baya kula mahaifiyarsu sosai bayan kowa yasan yanda take tsananin sanshi, zatai magana kawai ta hango Aneesa ta taho da gudu, ganin tana kallan wani gun yasa Ashraf ya juya hakan yaba Nafi damar juyawa ta kalli gun itama.

Da gudu ta taho sai data kusa zuwa inda suke sai kuma ta tsaya daga nesa ta kafe Ashraf da ido idanunta na zubar da hawaye, Nafi ta bi Ashraf da kallo, yanda taga yana kallan ta yasa tasan akwai wani abun tsakaninsu.

A hankali Ashraf ya fara takawa zuwa inda take tana tsaye tana mai wani kallo mai tattare da ma'a noni sanda hawaye nabin kuncinta.

Nafi tai tsaye jiki a sanyaye tana kallansu, sai da Ashraf yazo kusa da ita kawai ta gifta ta gefensa tasa gudu, ta kusa da Nafi ta wuce, ta nufi inda little ta nufa d'azu.

Turus yai agun, jikinsa duk yai sanyi, little ta kama hannun Nafi tace " wuce mu tafi xasu fara abin nasu. "

Sun je zasu shiga sai ga mutane kowa ya taho harda Mumy da Umma sun taho gun Ashraf, sudai suka karasa ciki.

Kallan fallon Nafi tai, aranta tace " lalai rayuwa tana wani gun. "

Sunje shiga d'aki Nafi ta kalli Little jin sheshekar kuka, Little tai murmushi tace" Neesan yaya kenan yau sai yayi lalashi mai karfi kafin abarmu musamu bacci. "

Nafi ta kalli kofar d'akin jikinta ya kara sanyi, Little tace" karki damu inda sabo sun saba, ita shagwab'a shikuma saurin b'ata mata rai shiyasa wannan kukan harya fara daina damuna. "

Nafi ta jinjina kai sannan tace " Amma kuna kama da ita. "

Little tai murmushi tare da tura kofar d'akin tace " Yaya tace ta gurin uba, shi kuma ya Ashraf yaya nane na gun uwa. "

Kallan mamaki Nafi ta mata tace " Ban gane ba. "

Dariya Little tai tace"Maman Mu ce ta auri baban Ya Neesah bayan Baban Ashraf wato yayan babanmu ya rasu. "


Nafi ta zaro ido cikin mamaki zatai magana sai idanunta yakai kan tangamemen d'akin, kallo tabi d'akin dashi cikin tsananin mamaki lalai dukiya tana wani gun, yanzu nan d'akine? Jitai Little tace " Yes. "

Nafi ta hadiye wani yawu cikin mamaki, take kallan d'akin.


Ashraf kam yana tsaye gurin 'yan uwansa manyan 'ya'ya maza na kanin babansa da kuma kannensa, yake kawai yakeyi dan shikansa yasan ba kowa bane yake farin cikin dawowarsa sannan shi ya kosa subarshi yaje ya lallab'a Neesarsa.

Mumy ta kalleshi tace " Ashraf kai wanka sai kazo kaci abinci ko??"
Ta sani sarai bazai amsa mata ba sai dai tasan zaiyi abinda tace, kallan yayen sa yai yace " Zan shiga ciki."

Yana kai nan ya wuce, nan suka juya, dadi da farin ciki ya kama Mumy da sauri ta nufi hanyar kitchen dan shiryamai abinci, duk wannan kin kulatan da Ashraf yake sam bata ganin laifinsa tasan dole ya ji haushi daga mutuwar mahaifinsa ba dadewa ta sake aure kuma gidan datake da anan take sannan ta auri kanin mahaifinsa.


Ashraf har ya nufi bangarensu ya zagaye ya koma bangaren su Aneesa.

Nafi dake zaune akan gado sai dan tsalle take kadan taji ana kwankwasa kofa sannan taji muryar Ashraf ya na cewa "Neesah?? "

Nafi tadaina wasa da gadon, tai shiru tana jin Ashraf, ya dan dade yana knocking kafin yace " shikenan Neesa na dauka kece ta farko da zaki fara farincikin ganina shine zaki shige d'aki kina jina ina magana? Shikenan na tafi. "

Nafi tanaji daga ciki cikin wata murya mai salo da jan hankali tace " Amma yaya kasan halin dakasani kuwa? Jiya ko bacci kasa yi nai ina tsoron kar in fara ace min ga gawarka can. ......."


Kasa karasawa tai, Ashraf ya murmusa yace " Neesah ki bud'e inganki please...."


Nafi ta sauka daga kan gadon ta zauna a kasa, murmushi ta kakaro da kyar tace " dama ai baice yana sona ba, kuma ya sanar dani hakan, shikenan."


Tanajin motsin bude kofar.


Ashraf na shiga ya karasa inda take akan gado, tana ganinsa tasa pillow ta rufe fuskarta, Ashraf ya matso sosai saitin kanta ya kwantar da kansa yace " Ko kallo na bazakiyi ba? Na d'auka yau in kika fara kallona sai na kwace kaina? "

Ta dago a hankali ta dan harareshi sannan ta dau pillow din ta makamai ta kara makamai, ta daga zata sake na uku yai saurin rikewa, yace " ya isa to dear ai kin huce ko? "

Ya fada yana mata wani kallo.......





*THE INNOCENT TEAM*
*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com

*For you my dear Friend Asiya Musa (Koxali) luv u soooo much😍*

9⃣



Little ce ta fito daga toilet ta kalli inda Nafi take tace " zo ki shiga kiyi wankan. "
Nafi ta mike jiki a sanyaye ta karbi dan towel din da little ta mika mata, kallo tabi towel din dashi tace" dan wannan abun zan daura? "

Little tai murmushi tace " to dame zaki daura? Ni shi kadai garen. "
Kallan zanin jikinta tai tace " na d'aura wannan. "

Little ta saki murmushi tace " ya sunan ki? "

Nafi a kasan zuciyarta so take tace Nafisa sai dai ta rasa me yasa batasan akirata da haka tafisan tadinga jin wannan sunan daga bakin Ashraf, "Nafi. "ta fada tana Kallan little.

Tad'anyi murmushi tare da mika mata hannu alamar gaisuwa tace "ni kuma Maryam amma little ake cemin ko kice little Maryam, mu biyu ne masu suna maryam babbar riketa akai agidan har tayi aurenta. "

Nafi ba tare data mika mata hannu ba tace" li?? Hmm nidai Maryam kawai zan dinga ce miki. "

Little tai murmushi sannan ta kara mika mata hannu tace " mu gaisa to. "

Nafi ta noke tare da girgiza kai tace " ba maza bane ke gaisawa?"

Little ta fizgo hannun Nafi tace "Mata ma nayi ai musabaha ce. "

Kai Nafi ta jinjina, little tace "shekararki fa? "
"16."
Little tad'anyi tsalle kadan tace "nima haka. "
Sukai murmushi a tare, Nafi ta daura zani ta nufi inda little ta kira da bayan gida, Da gudu Nafi ta dawo ta kalli Little tace " kina nufin anan zanyi wanka? Ta ina? Ta yaya kuma? "

Little ta kalleta tace "muje in nuna miki."

Nafi ta ja ta tsaya, Little tace "Nafi muje mana. "

Dum Nafi ta mata itadai tsoro take ta ina zatai wanka a wannan gun?
Little tadan had'e rai tace "Shikenan bari in je in fadama Ya Ashraf. "
Da sauri Nafi ta rike rigar Little jin an anbaci Ashraf tace "Zanje Maryam. "

Little tadanyi dariya tace "muje to. "

Sunje toilet nan Little ta nunama Nafi yanda zatai wanka, ganin hankalin Nafi yaki kwanciya da shaya yasa little ta tararmata ruwa a baho tace hakan fa?

Nafi tai murmushi alamar gwara hakan.
Nan little ta fita ta barta.


**********

Ashraf kam suna shiryawa da Neesah ya wuce bangarensa, ko ince bangaren mahaifinsa shikadai ne a bangaren saboda duk yanda akaso asashi cikin 'yan uwansa maza kin yarda yai yace " lalai shidai a bangaren Mahaifinsa yake san zama. "

Yana shiga ya wuce toilet yai wanka ya zura doguwar riga sannan ya fara rama salolinsa.

Bayan ya idar ne yaga sakon meeting a babban falo, in kuwa za'ai wannan taron to acan ake cin abinci.



An sanar da kowa akan akwai meeting a babban falo saboda dawowar Ashraf.
**********

Nafi ta fito daga wanka ta shafa mai kawai littleta bata doguwar rigar atamfa tasa, saboda little ta fita kiba hakan yasa rigar bata mata kyau ba ga wuyan rigar sai fad'owa yake, ga ta kima daurin dan kwalinta ta matse kanta tamau.

Itadai little taso mata magana sai dai tasan daga zuwan mutum gari bazai wuyo ace ya canza abinda ya saba ba, gashi tana tsoron karsuyi latti wajen meeting.


Nafi na gamawa little ta kama hannunta tace "muje ko? "
Nafi wanda gabanta ke faduwa tace " Maryam gani nake ni bai kamata inje ba. "

Dariya Little tai tace"to yaya na kira na tambaya yace muje tare yanasan introducing d'inki. "

Nafi ta kalleta da mamaki tace "me? Inkiro me? "

Dariya little tai tace "ke dai muje kawai. "

Nan suka fito sunyi sa'a Neesah ta riga ta fita, nan suka taho har zuwa babban falo.


Katon falo ne sosai wanda gefe aka kawatashi da wani round din dinning table manya guda biyu, d'aya maza ne a zazzaune d'ayan kuma mata ne, sai dai duk a kusa da juna suke.

Tunda suka shigo kowa ya zubama Nafi ido yana mata kallan mamaki sai dai banda Ashraf wanda ke zaune fuskar nan tasa kamar yanda ya saba a murtuke, Haka little ta jata har zuwa inda zasu zauna.

Zuciyar Nafi kam kamar zata fado saboda tsananin tsoro da ganin mutane dayawa maza da mata, kanta na kasa, sunje zama kawai tai tuntube ta fad'i, kwashewa akai mata da dariya sai ta samu kanta cikin tsananin tsoro ta kasa mikewa, Ashraf ne ya kallesu ran nan a had'e ya kalli Nafi wanda itama shi take kallo ya mata alama data tashi.

Jiki a sanyaye ta mike little ta taimaka mata ta zauna.

Kanta ta sunkuyar, kawu yai gyaran murya hakan yasa kowa ya nutsu yace "Bismillah."

Nan kowa ya fara zubama kansa a binci, Umma kuwa mahaifiyar Aneesa da ita Aneesan sun kafe Nafi da ido.


Kowa ya fara zuba abinci, itadai Nafi a zaune take sai gabanta dake ta faduwa, ganin batada niyyar zuba abinci yasa Little ta zuba mata shinkafa da miyar carras sannan ta matso mata da papper chiken da salad, Nafi ta kalle ta sannan ta d'au chokali, ganin yanda kowa yakecin abinci yasa ta fara cin shinkafar a hankali, sai dai lomarta biyu taji inaa bazata iya cigaba da ci ba, gani tai kamar kowa kallanta yake, ta zaune tare da matse kafafuwanta dake rawa, little ta kalleta tace "Nafi tafiya fa kikai kici abinci mana? "

Nafi ta kakaro yake tace " a koshe nake ai naci abinci a mota Yayanki yaban doya da kwai.

A hankali sukai maganar, Ashraf yadan kalli inda take ganin bataci abinci baiyi mamaki ba, ta ina zata iya cin abinci a cikin mutane?

Bayan kowa ya gama ne Kawu yai Hamdalla sannan ya fara magana "Alhamdulila Allah ya taimakemu d'an mu ya dawo da ransa da kuma lafiyarsa wannan ba karamin abin farinciki da alfahari bane, lalai Muna godiya ga Allah wanda yasa muke zaune yau da Ashraf kamar yanda muka saba. "

Kowa ya jinjina kai alamar jin dad'i, akace Ashraf yai magana.

Shiru yadanyi nawasu dakika kafin yace " Nagode da kulawarku, Sai dai inaso in nuna muku Nafeesa wacce itace sanadiyar zamana anan gurin haka, Itace wacce ta taimakeni a lokacin da nake tunanin yanke alaka da duniya, Allah ya kawomin ita ta taimakeni ta ceci rayuwata. "

Jin haka yasa kowa ya kara kallan Nafi wacce kanta ke kasa, sai gabanta daya tsananta fad'uwa.

Wani daga cikin mazan gun yace "Lalai Ashraf to dan ta taimakeka shine ka taho da ita nan ko me? Iyayene batadaso ko me? "

Ashraf ya bugamai wani kallo baice komai ba, Umma mahaifiyar Aneesa tace "Ashraf ina ganin gaskiya Nuhu ya fada in ta taimakeka sai a bata kud'i ban gane dalilin tahowarka da ita ba. "

Ashraf ya dan kalleta kadan nan ma bai tanka ba, Mumy tai murmushi tace " tunda ya taho da ita akwai dalilinsa nayin hakan nasan halin Ashraf sarai. "

Kansa ya juya sai dai fuskarnan a had'e take tamau, nan aka dan fara musu wasu suce ya kamata wasu suce bai dace ba, Anisa kam kallan kyana kawai takema Nafi.


Cikin wata kakkausar murya mai zafi Ashraf ya mike yace " Me? Dan na taho da yarinya shine ake cece kuce? A kan wani na ajiye ta ko me? Ko kuwa anaso ace ni Ashraf ban isa in kawo wanda na ga dama cikin gidan nan bane? "

Wannan kalamai dayai ya gigita kowa itakam Nafi idanunta ne suka ciciko tsoro ya kara kamata, Kawu ya kalli Ashraf yace " Kada ka manta Ashrac akwai iyayenka anan, taya dan ranka ya baci zaka hada da kowa ka fara fad'a? "


Ashraf ya kalli Asim sannan ya kalli inda Nafi take yace "Duk wanda yake ganin hukunci na bai mai ba sai ya tareni muyi magana. "
Yana kai nan yai waje, Umma tabishi da kallo, Mumy kam da sauri ta mike ta bishi.

Nan aka cigaba da 'yan maganganu, little ta kama hannun Nafi tace "Nafi mu bar nan ko? "

Suna kokarin mikewa sai ga Ashraf ya dawo daga bakin kofa kawai ya kalli Nafi sannan ya kalli Aneesa yace " Neesah inasan ganinki. "

To fa gani nai Nafi ta mike itama Aneesa ta mike, Umna ta kalli Nafi tace " ke yake kira? "
Nafi wanda itakam jitai kamar yace "Nafeesa"tai tsuru tana kallan Umma.

Aneesa wani haushi ya kamata, a zuciye ta bangaje Nafi tai gaba.

Nafi ta tsaya cak kamar gunki sai hawaye, Kawu ya mike shima da zuwanta bai wani burgeshi ba yai waje.

Little ta taso ta kama hannunta Asim yasa dariya yace "ko dai akwai wata manufa ne a tahowa da wannan kwailar? "

Yai maganar yana kallan Nafi aka kwashe da dariya, sudai sukai waje.


Suna fita Nafi tasa kuka.

Aneesa kam a gefe taga Ashraf ta karasa inda yake fuska a had'e tace " menene? "
Shima fuskarnan a had'e yace " ki fadama ummanki tadaina min abinda takemin menene nata dan na taho da Nafisa? Akan wani zata zauna? Ko kuwa yarinya ce ita daza'ace wanka ma yi mata za'ai? "

Aneesa ta kalleshi cikin bacin rai tace " Yaya dama saboda kamin fada ka kirani? Sannan yanzu kace Neesah amma dayake yarinyarcan yar rainin hankali ce ta d'auka wai ita kake kira. "

Ashraf ya kalli su Nafi dake tahowa ganin tana kuka ya kalli Aneesa yace " ki fadama Umma tadaina min haka sannan kema na dauka ko me na kawo gidan nan zakibi bayana in har kina sona, na gode da nunamin din dakikai abinda nake tunani ba haka bane. "yana kainan yai gaba.

Nafi tabi bayansa da kallo sannan ta kalli Aneesa ta maida kanta kasa.





*THE INNOCENT TEAM*
*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com

*Kuyi hakuri jina shiru da kukai jiya, na shiga tarone wlh kuma dana dawo na gaji.....na gode kwarai da kulawarku da kuma san da kukema littafin nan*😍😍



1⃣0⃣


Little ce rike da hannunta kawai tana tafiya amma idanunta nakan Ashraf dake tafiya, Aneesa kam har wuya tazo ganin yanda Ashraf ya hauta da fada akan wata banza kucaka, da saninta ta taho ta mangaje Nafi wanda har sai da ta kusa kai kasa, Little ta kalleta tace "Haba Yaya Neesa? "

Aneesa ta kalli Nafi tace "Sorry ban kula ba."tai gaba.

Little ta kalli Nafi wanda ta kakaro murmushi tace "Maryam karki damu ai bata kula bane, kuma taban hakuri. "

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login