Showing 27001 words to 30000 words out of 141466 words
ma na baka? "
Ashraf ya juya kai tare da shafar kasan kansa da hannun da baya mai ciwo yace " Uba? Sai kuma ka manta wannan Uban nawa ne ko? Sannan banaji a wasiyyarsa yace inba matar da ban aura ba ko? "
Aneesa ta matso kusa dashi tace " Yaya?"
Matsawa yai daga kusa da ita baice musu komai ba ya juya ya fara tafiya, sai dai abin mamaki kasa cemai komai sukai sai Aneesa data bishi da sauri, tana kiranshi.
Ko Kallanta baiyi ba, ransu Umma ya sake b'aci, yana shiga falonsa ta bishi itama tace "Hubby? "
Matsowa ya farayi inda take harta isa jikin bango yasa hannunsa ya matseta har sai datai dan kara, sannan yace " wlh ki shiga hankalinki, inkikai wasa Wlh kinji na rantse duk sanda nake miki sai in ajiye maganar auranki, kinfi kowa sannin ni Ashraf nafi karfin mace ta wulakantani ko ta juyani. " saketa yai sannan yai d'akinsa.
Da kallo ta bishi dashi, wani mugun tsoro ne ya shigeta,A tsorace tai waje.
Ashraf kam yana shiga d'aki ya durkushe agun, kafad'arsa har kasan hannunsa banda azabar zafi ba abinda yake ji, d'ayan hannun yasa da niyyar sa magani, sai dai ina jin gun yai ya kara kumbura, ya tuna abinda likita yace mai.
"Ashraf a ina ka bugu haka? "
Da mamaki yace" ni ban bugu ba kawai da daddare ciwo ya tashi min."
Likitan yai shiru can yace " A 'yan kwanakin nan baka bugu ba? "
Ashraf ya kalleshi yace " na dai d'an sanu karamin accident to daga nan ina d'anjin gun ba dadi to amma bawai ciwi ya kemin ba. "
Likitan yai d'an ajiyar zuciya yace " Ashraf ya akai haka? Me yasa bakazo checkup ba bayan abin? "
Ganin bashida niyyar magana yasa ya mik'e ya bashi magunguna, sannan yace " a sa tsuma a ruwan zafi a dinga matsewa ana gasa ma gun, sai a shafa wannan. "
Asharf ya amsa, yacigaba "wannan kuma na had'iya ne. "
Nan ya bashi kud'inshi Ashraf ya mike, har ya fara tafiya likitan yace " Ashraf ka tabbatar an gasa ma sannan karkai amfani da jikinka sosai. "
Nan yai gaba, ta ina zai iya gasa gun da kansa? Gashi sunyi fada da waccan yarinyar, shikuma kaf mazan gidan bayaji akwai wanda zai iya kira.
Wayarsa ya d'aga ya dannan number Little yana fatan Allah yasa ta dawo.
Daga can b'angaren Little wacce ke kwance batajin dadi ta daga, bayan tagaisheshi bai amsa ba kawai yace "little kizo yanzu. "
Abinda ya fada kenan ya kashe, little wacce da alama ciwon mara take ganin yanda take a durkushe sai dai ita batasan meke damunta ba, ta kalli Nafi wacce ke xaune kusa da ita duk ta rikice kamar ita take ciwo.
Tace "Nafi dan Allah jeki yayane ke kirana nikuma kinga cikina murd'amin yake. "
Nafi ta kalleta daa idanunta da sukai raurau tace " taya zan tafi in barki? "
Little tace " naji muryar yayan ma kamar......"
Ai Nafi da sauri ta mike batama jira karashen zancen ba tai waje da sauri, ganin saurin bai mata ba ga ba mutane agun yasa tadan sa gudu, tabbas ciwonsa ne ya motsa abinda kawai tasa a ranta kenan.
Sam bata kula da Asim ba wanda ke kokarin shawo kwana ita kuma zata mike, dayake gudu takeyi iya karfinta kuwa ta bangaje shi, Asim ya juyo cikin tsananin mamaki ganin wani kwararen ne?
Nafi kam jikinta ya fara tsuma ta kalleshi a tsorace tace " Yahkuri yaya dan Allah. "
Asim ya d'ago da niyyar masifa, sai dai me? Can ya ganta ta mai nisa sai sauri take, ta sani bazai kyaleta ba sai dai yanzu abu d'aya ne a gabanta ba kuma taji akwai abinda zai tsayar da ita.
Tana murd'a kofar tajishi a bud'e nan ta shiga ta fara sallama, jin shiru cikin tsoro kawai ta dannu ciki, baya falo hakan yasa ta wuce d'akin shi.
A zaune yake a kasa ya kifa kansa akan gado, ba riga a jikinsa sai dogon wando hakan yasa Nafi ta juya baya da sauri, a hankali tace "Yaya ga...... "
Yanda yakeji yasa bai bari ta karasa ba ya katseta "Little yi sauri ki d'au roba a toilet ki taro ruwan zafi ki sa tsuma a ciki kizo ki dinga matsewa kina gasamin gun nan. "
Nafi ta juyo a hankali tana san cemai ba little bace tace " Ya.... "
"Little wuce mana"
Jiki a sanyaye Nafi ta wuce toilet yanzu ta iya kunna famfo ta kuma san inda ruwan sanyi dana zafi yake, nan ta tara a roba ta saka towel karami dake rataye a ban d'akin ta fito, ganin yanda ya kifa kansa ko d'agowa baiyi ba yasa tasan yanajin zafin gurin, kallan gun tai taga ya kara tashi ba kamar da safe ba, idanunta ne suka fara cicikowa, ta karasa a hankali tai kneel down ta bayansa ta fara matsewa tana gasa mai gun, dun sanda tasa sai taga ya d'an motsa kad'an.
Kamar a jikinta takejin ciwo nan, intaga ya motsa sai ta runtse ido.
Asim kam wanda ransa yakai kololuwar tashi ya tsaya ya d'auka yanzu zata dawo yaci mutuncinta, jin shiru yasa yabi bayanta a kufule.
Bud'e kofar yai a zuciye yai ciki, me zai gani????? Me kuma idanunsa suke gane mai???????
Tofah! Babbar magana........
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
A b'angaren su Datti kam haka sukai ta yawo suna neman taimako, kayan da maman hanne tazo dasu suma sai siyarwa tai.
Da kyar suka hada kudin mota suka koma Gwaram.....
¤¤¤¤¤¤¤
Shikam d'an litti ya musu bayani har ya gaji amma ina... Sunce dole sai ya fada musu wanda ya sani yazo yayi bailing shi.
D'an litti yace " ku nemo min Ashraf. "
Officer yace " Ashraf wa? A ina yake? Meye number wayarsa? "
To fa! Da masifa D'an litti yace " nidai ba na fada muku ba? Sunanshi Ashraf a kuma kano yake. "
Officer yace " me kake nufi to? So kake mu shiga kano mu fara neman masu suna Ashraf ko me? "
D'an litti takaici ya kamashi ya zauna a cell d'in kamar yasa ihu, gashi sunce inya sake musu turancin nan nasa sai sun fasamai kai........
*THE INNOCENT TEAM*
*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_
© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com
*I Sincerely Dedicated This Page To You Billy S. Fari and My Samrah.... ILYSM*
1⃣9⃣
Dakyar Ashraf ya iya watsa ruwa a jikinsa, wajen sa kaya kamar yai ihu, haka dai ya daurw yasa riga, makuli ya d'auka ya nufi hanyar waje da niyyar zuwa asibiti.
Yaje fita Umma ta kirashi hakan yasa ya karasa gunta, falo suka shiga bayan sun gaisa ya kalleta yace "Umma ya akai? "
Ta d'anyi murmushi tace"Dama tun jiya nakesan magana dakai. "
Kallanta yai kawai baice komai ba, ganin haka yasa tace " yanzu saura wata d'aya da sati biyu bikinku da Aneesa shiyasa nake tunanin kamar ya cancanta a bata sakon mahaifinka..... "
Wani kallo ya mata wanda ita kanta batasan ke yake nufi ba, sannan murmushi ne ya biyo bayan fuskarsa ya kalleta yace " Ashe har na bada sadaki an shaida kenan? "
Umma tace "mene? "
Yai wani murmushin rainin hankali yace "a iya sanina wanda ya bada wasiyyar nan cewa yai matata ta farko, banaji yace matar dana kusa aura. "
Ta kalleshi sannan ta motsa baki zatai magana, mik'ewa yai sannan yace " inada abinyi Umma sai anjima. "
Tabishi da kallo cikin maimaita kalamansa, asanda yai maganar sam kwakwalwarta kullewa tai amma yanzu kam datake maimaita kalaman ta fahimci banda tsananin rainin hankali ba abinda Ashraf ya fad'a mata.
Shikam cikin tsananin b'acin rai ya shiga mota, yayi tunanin zai iya tuki sai dai jin zafin da kafad'arsa take yasa ya na driver d'in mumy magana, ba'a dad'e ba ya karaso nan ya jashi suka fita.
Kansa ya kwantar akan kujera ya lumshe idanunsa, menene dalilin dayasa mutane suka damu da abinda mahaifinsa ya bari? _Fatiha an d'aura auren Ashraf da Nafisa yar gidan Datti_
Abinda ya fad'o mai a rai kenan, kallan driver yai yace " Adamu kaini wajen malam Yunus "
To abinda driver d'in ya fad'a kenan tare da murd'a kan sitiyari, sunyi tafiya sosai kafin su isa wata katuwar makarantar islamiya, nan yai parkin Ashraf ya fita, wani babban office ya nufa ya kwankwasa, daga ciki aka ce shigo, Ashraf ya murd'a kofa ya shiga.
Malamin na ganinsa ya mike cikin tsananin farinciki ya karaso kusa da Ashraf tare da mikamai hannu alamar musabaha, shi kanshi Ashraf d'in ya saki fuskarsa sosai, nan shima ya mikamai suka gaisa cikin girmamawa.
Nan ya nunama Ashraf guri ya zauna, sunyi gaisuwa tare da tambayan juna bayan rabuwa, dattijon Malami ya kara washe baki yace "Muhammad sam ka daina ziyartata. "
Ashraf yai murmushi yace " wlh malam uzuri ne ke hanani zuwa. "
Sunjima suna gaishe gaishen su kafin Ashraf yai gyaran murya yace "Malam ina cikin wata 'yar matsala ne wacce duk duniya ba wanda na sanar ma kuma ba wanda zan sanarwa sai kai. "
Malam yunus ya kalleshi cikin tsananin kulawa, yace" Inajinka."
Ashraf yai shiru, yana tunani.
Malam yace "Muhammad karka b'oyemin komai. "
Ashraf yai kasa da kai nan ya zayyane mai kaf abinda ya faru sannan ya d'oramai da wasiyyar mahaifinsa.
Malam Yunus hankalinsa ya tashi dajin wannan al'amari ya kalli Ashraf yace" Tausayi da Taimako ne yasa ka aureta sai dai Muhammad inasan tunasar dakai aure ko a wasa akayishi indai har anyi auran yanda musulunci yace to fa tabbas wannan auran ya d'auru sannan hakkin matarka na wuyanka. "
Kallan Malam yai cikin tsananin damuwa yace " da ina tunanin saki..... "
Da sauri Malam yace " kul Muhammad akan me? Ba taimako kakesan yi ba? Meye amfani taimakon kenan? "
Ashraf jiki a sanyaye ya kalli Malam yace " me zanyi da ita? A kauye fa take ko ince a riga, yarinyar da banaji sallah cikake ta iya, batasan komai na rayuwa ba, infact shekarunta ma inaji basufi 16 ba Malam me..... "
Malam yai murmushi yace " naji duk bata iya komai ba, kamin alkawari d'aya nikuma zan taimaka ma. "
Ashraf yace "Name kenan? "
Malam Yunus yai murmushi yace " Inaso kasa ta a makaranta inma taa kwana ko ta jeka ka dawo ka kula dacinta da shanta da suturarta har ta kai shekara 20 zuwa da d'aya, inhar aka kai lokacin Bakaji komai a tattare da ita ba inaso ka bata takardarta ita kuma sai ta nemi wani ta aura. "
Cikin rashin damuwa Ashraf yace "nama wannan alkawari. "
Malam yai murmushi sannan yace " game da wasiyar mahaifinka kuma kasan yanda zakai a rabu lafiya dan kuwa wannan wasiya ta matar daka aurace ba wacce zaka aura ba. "
Shiru Ashraf yai yana tunanin lalai akwai chakwakiya inhar yace bazai ba Aneesa wannan wasiyar ba, Malam yaji yace " zaka iya jinkirtawa zuwa sanda ka rabu da matarka."
Ashraf yai shiru, sai dai yasan wannan shawarar itace daidai,sunyi Sallama Ashraf ya ajiye mai kud'in talafi na makaranta sannan ya tafi.
Mota ya koma nan sukai hanyar Asibiti.
*Dan Allah kuyi Hakuri da wannan wallahi rasuwa aka mana shekaran jiya.*
Nagode![5/9, 09:58] Ayusher✍🏻: *ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_
© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com
*Dedicated This Page to World of Hausa Novel 1*
And *Taskar Lubie Mai Tafsir*
2⃣1⃣
A tsorace Nafi ta mike gabanta sai fad'uwa yake, shikam gogan ko mikewa baiyi ba sai cewa dayai "Little mikomin rigata a kan gado. "
Nafi ta mikomai sannan ta fito daga d'akin da sauri tare da ja mai kofar, dan ta kula kamar bayasan asan bashida lafiya.
Tana fita falo Asim ya karaso tare da jan hannunta da karfin tsiya, Nafi ta d'an turje sai hawaye da takeyi.
Asim ya haska mata wani wawan mari yace " banza karuwa, a ido kamar bakauyiya ashe kinfi karuwai iya iskanci. "
Nafi ta shiga girgiza kai hawaye na zubo mata.
Kofa aka bud'e, mamaki ne ya kama Ashraf ganin Nafi, sai dai bai bari mamakin ya fito fili ba cikin isa ya karaso ya sa hannu ya rike hannun da Asim ya rike.
Asim ne ya kalleshi cikin masifa yace " Me kenan? Kazo karema karuwarka ne? "
Nafi kam kanta na kasa, kunyar Ashraf duk ta gama rufeta ta sani sarai bai san ita bace sai yanzu.
Ashraf ya kalli Asim yace " Saketa ko? "
Nafi kam hannunta sai zugi yake yi, Asim yace " bazan saketa ba sai munje gaban kawu ta sanar mai abinda kai da ita kuke aikatawa. "
Ashraf yai wani murmushi ya kalli agogo karfe 6 na yamma, sannan ya kalli Asim yace " ai banaji sai ta bika wajen isar da sakon kai kad'ai ma ya wadatar kaje ka sanar. "
Asim ya kara cika baki da takaici yace " Me kake nufi? "
Ashraf ya kalli Asim ya mai alama da ya sakar mata hannu, cikin takaici Asim ya saketa, Ashraf ya kalleta yace " wuce ko? "
Nafi ta kalleshi idanunta sun cika da kwalla tanasan bashi hakuri sai dai bataga fuska ba, da kai ya mata alama ta wuce mana, jiki a sanyaye tai gaba tana yi tana waigensa.
Tana fita Ashraf ya kalli Asim yace " D'an sako mai kake jira? "
"d'an sako? Nine d'an sakon? "
Ashraf yai wani murmushi yace " Au na d'auka danace kaje ka sanar ai zaka wuce da sauri ka gurfana agaban kawu ka sanar mai. "
A zuciye Asim ya kama wuyan Ashraf cikin masifa yace " Ni kake fada ma haka? "
Ashraf yad'an juya ido kad'an yace " inmu uku ne to dana ukun nake."
Ya ja jikinsa ya koma d'aki dan yin alwala.
Asim ya naushi iska cikin tsananin takaici yai waje jiyake kamar ya lumama Ashraf wuka hankalinsa ya kwanta.
Ashraf kam alwala yai sannan ya fito waje.
Nafi kam d'aki tai tana kuka, Little ta gani ta fito daga wanka, da sauri Little ta karaso tace " Nafi menene? Wani abin ya miki? Laifi kikama yayan? "
Kai kawai Nafi take girgizawa, Little tace " to menene?"
Nafi ta kalleta tace" me karuwa yake nufi dan Allah? "
Little da mamaki ta kalleta tace " Yayan ne ya fada miki hakan? "
Kai ta girgiza alamar a'a sannan tai hanyar ban d'aki da sauri, da alama kalmar bata da dad'i ganin yanda fuskar Little ta canza.
Little ta bita da kallo, sannan ta d'au always d'in da Mumy ta kawo mata ta sa, zama tai jiki a sanyaye, waye yacema Nafi karuwa?
Asim kam ana idar da sallah ya tari kawu acikin masallacin ma ya fad'amai, ran kawu yayi dubu gurin b'aci, ganin haka yasa Asim ya saki wani murmushin mugunta.
Kawu ya fito cikin tsananin masifa nan yace Ashraf ya biyoshi, duk da kasan zuciyarsa yaji ba dadi sai dai bai nuna ba, nan Asim yabi bayan kawu.
A falo Mumy, Umma, Asim da Ashraf ne a zaune sai kawu.
Cikin fada kawu ya kalli Ashraf yace " Ashraf meke faruwa? Wani banzan labari nake ji haka? "
Ashraf ya kallesu kaf sai dai kafin yai magana Aneesa ta shigo cikin tsananin kishi ta karaso kusa da Ashraf tace " Yaya me kenan? Ni zakaci amana? "
Mumy wacce jikinta duk ya mutu dan ta taba ganinta ta fito daga d'akin, tai shiru yau kam batada halin kare Ashraf.
Kawu ya daka mata tsawa yace " Aneesa bakida hankali ne? "
Ta kalli kawu cikin tsananin takaici tace " Amma Abba..... "
Hannu ya d'aga mata hakan yasa Umma ta zaunar da ita a kusa da ita.
Ashraf wanda ke zaune sai dai duk masifar mutum bazai tab'a gane meke yawo a ransa ba, sam babu b'acin rai ko farin ciki a tattare dashi.
Kawu yace " Asim fad'i me ka gani. "
Hankalin Asim a kwance ya sanar da abinda ya gani har da karin cewa wai suna ganinshi suka tura kofar d'akin suka rufe, sai daya dade kafin su fito.
Mumy ta runtse ido zuciyarta na wani irin zafi, Umma ta shiga tafa hannu tana salati, itakam