Showing 3001 words to 6000 words out of 141466 words

Chapter 2 - ZUCIYA kowa da irin tasa Complete Hausa Novel

unknown   

13 Oct 2024

15894

tabirma ba, ta tsaya a waje tare da rik'e inda zuciyarta take, a tsaye take kamar gunki, jitai ance " Wato Nafi kin fara zarewa ko?"

Dasauri ta kalli inda maganar ta fito, Baffa ta gani a zaune, hannunta ta zare cikin tsoro ta kalleshi tsoru tsuru tace " Baffa.."
" Inajiyoki daga d'aki kina magana ke kadai wato zama ke kadai a gida yasa kin fara zarewa ko? "

Tai kasa dakai cikin tsoro batace komai ba, baffa yai tsaki sannan ya juya kansa yace " damomin fura insha dare nayi."

Cikin rawar murya tace " to Baffa yauma bazamuci abinci ba......"
Katseta yai cikin masifa yace " Inkin gaji dashan fura da nono kiyi zuciya kiyi aure, nifa banga dalilin dazaisa yarinya kin kai aure incigaba da ciyar dake ba, sannan haka kawai inada shanaye dayawa bazanje insai abinci ba ah to."

Nafi bata amsa ba ta juya dan shiga d'akin dasuke ajiye fura, nan ta debo, ta d'ebo nono a kwarya ta zauna ta dama, itakam yanzu warin nono ma yafara damunta, tunda uwarta tabar kasar nan kullum abincin da suke ci kenan, sam Baffa ya rufe ido ita kuma tasan inya fita shago yana siyan shinkafa yaci amma ita kullum abinda takesha kenan.

Tana gamawa ta zubomai a langa ta rufe ta daura ludayi ta kawomai, sannan ta dauki nata tai d'aki, kallan mutumin dake kwance tai, tace " Nasan kaima yunwa kake ji ko?"
Matsawa tai ta kara tab'a goshinsa, da zafi har yanzu, nan ta matsa kusa dashi ta dan dagoshi kadan tasa kafarta ta tareshi, ta dinga deban furar data dama tana bashi a hankali da cokali, wani yasha wani ya zube, ganin yadan sha dayawa yasa ta mik'e jiki a sanyaye ta zare zanen data shimfida na saman ta goge mai jikinsa sannan ta dauke numfashinta itama tasha, dan sam batasan sha.


Waje ta fito da kwaryar sannan ta koma ciki tare da tura kofarta ta rufe, kusa da mara lafiyar ta koma ta zauna, ta hard'e cinyoyinta kallansa kawai takeyi, sai dai tunaninta nakan mahaifiyarta, a haka har bacci yai awun gaba da ita.


Wajen gabanin asuba ya bud'e idanunsa a hankali, yarinya ya gani kwance kusa dashi ta dan dukunkune jiki tana baccinta, kallanta yai sannan ya shiga kallan dakin, mamaki yashiga yi a ina yake hakan? Yadauka ya mutu shikam, Nan ya shiga juye juye, tare da kallan d'akin dakyau "wannan kuma inane hakan?"
Gashidai kamar d'aki sai dai gaba daya baisan dame akai rufin dakin ba, sannan ba komai a dakin banda ta birmar dayake kai sai gefe kuma bakko da 'yan samiru, kokarin mik'ewa ya fara sai kuma yaga kamar yarinyar tana neman tashi, dasauri ya maida idanunsa ya rufe.

Nafi ta mik'e zaune tare da sa hannu akan goshinsa, murmushi ne ya bayyana a fuskarta jin zazzabin yaragu sosai, ta kalleshi fuskarta dauke da murmushi tace " Zazzabin ya ragu aradu, dan binni ya kamata ka farfado ko na samu in baka hakurin abinda nai maka."
Tai kasa dakai tana murmushi tace " kaga sanda na sa bakina a naka a bakin ruwa wannan taimakon ka nai. "

Shikam dake kwance jiyai kamar yasa ihu, bakinki? Yamaimaita a ransa, wayyo ni.
Tacigaba " sanda kuma na cire maka kaya har tsautsayi yasa na kalleka wannan shine zan baka hakuri, bansan me yasa na kafeka da ido ba.


" wayyo na shiga uku, kallon jikina? Ciremin kaya? Inalilahi, hannu wa na fada haka? Ba dai har wando tacire............?

Jiyai ya kasa tunanin komai saboda tsoron abinda yake tunani.
Nafi ta mike jin mostin baffa tasan yanzu zaice ta tashi tayi tatsar madara, ta mike hartaje kusa da kofa ta juyo tace " kema kina shan madara? "
Sai ta juya tana murmushi.

Tana fita ya mike zaune da sauri ya duba wandansa, ajiyar zuciya yai a sanda yaga wandansa nannan ya koma ya kwanta yana hakki kamar wanda yai gudu ba shakka ya tsorata kwarai, tunani ya shiga yi ya zaiyi yai alwala yai sallah?

Muryar namiji ne ya katseshi yaji yana cewa " ke nafi? Ke Nafi. "

Saurin amsawa tai daga garke tace "Baffa ganinan. "
Ya kalli inda take yace " Dan gidan ku jiya bance ki karo wa dabobbi ruwa ba?? "

Ta dan matso inda yake jiki a sanyaye tace " Baffa naga jiyan dare yayi nasan kuma bazakaso inje rafi dadaddare ba. "

" to yar gidan manyan mutane, kin rika sosai wato ina miki magana shine bakiji kunyar maidamin ba ko??"
Duk maganar da sukeyi da yarensu sukeyi hakan yasa baisan me suke cewa ba amma tabbas ya fahimci abu daya masifa akema yarinyar, har kasan ransa yaji tausayinta masifa da sanyin safiyar nan?

Nafi tai kasa dakai cikin hausarsa mara fita yace " Kin wuce ko kuwa? "

Nan ta shigo ta dau kallabinta tai waje, yana kallan yanda take share kwalla dazata fita.

Bokiti ta dauka cikin tsoro t nufi rafi, tayi sa'a gari ya fara haske, nan ta shiga debo ruwa sai datai sawu hud'u ta debo na karshen ne taje shiga gida taga maza carko carko a kofar gidan rike da sanda sunata masifa, cikin mamaki ta kallesu sai dai ganin yanda ransu yake a b'ace yasa ta shige gidan sukuku....

Tana juye ruwan ta shige daki dan da alama wad'annnan mutanen ba alheri ne ya kawo su ba, zama tai a kusa dashi tace " kasan me?"

"Bansan me wasu maza sukazo yi ba amma da alama masifa sukazo yi, hmmm basusan halin Baffa bane. "
Tad'an tab'e baki tace " ni kaina tsoronsa nake gani nake kamar ba shi ya haifen ba, mahaifiyata ma saboda masifarshi tsoronshi take, hmmm bansan ko su basa tsoron Baffan ba. "

Dariya yake a cikin ransa lalai wannan akwai surutu.


Jitai an fasa abu yasa ta mik'e da sauri tai waje, yabi bayanta dakallo tareda yin dariya lalai wannan yarinyar ga hausartata mai abin dariya.

Tana fita taga mutanen nan ne suka fasa musu randa, ga mamakinta Baffa na zaune a gefe yana kallansu, wani daga cikinsu yace " wallahi kaji na fad'ama Datti ka bani kud'ina tun kafin rai ya b'aci. "


Baffa ya juya kai yana murmushi yace " Nina rantar muku kud'i? "

Mutumin yace " bakai bane amma ai matarka ce tace injika. "
Yasa dariya yace " Matata? Wa kenan? "

Haushi ya kara kamasu, Nafi dake tsaye jikin kofa ta matso kadan, ai kuwa Mutumin na ganinta ya matso tare da rike hannunta yace " Uwar wannan yarinyar."

Baffa yai dariya yace "Ali kasan Allah ficikata bazatai ciwo ba dan ba ninace ka bata uban kudi ba, banda sacemin saniya datai har kake tunanin zan kara kashe mata wani kud? "

Wanda ya kira da Ali shine ya matso a shekaru ya girmi baffa sai dai bai tsufa ba, yace " Datti wlh in har ka cigaba da batan rai to kuwa zan dauki wannan 'yar taka amaimakon kud'ina ne.?

Baffa ya bugamai wani kallo, Nafi wanda tsananin tsoro ya kamata ta kalli Baffa hawaye suka fara zubo mata.

Baffa ya juyar da kai.
Ali yace " Aradun Allah ko ka biyani kud'ina ko kuma a yau d'innan insa a auramin 'yarka sai ka zab'a.


Dan binni dake tsaye yana jinsu ya mike cikin tsananin mamaki kasancewar da hausa suke maganar yasa ya fahimta, ya kula su masu masifar kamar hausawa ne, meke faruwa?
Muryar Nafi ce ta katseshi tana kuka tana cewa " Baffa dan Allah ka taimakeni kaji? "

Baffa ya kallesu kallan wulakanci yace " kuna tunanin saboda 'yata sai in sadaukar da dukiyata? "
Ya sa dariya yace " Dama na gaji da ita, in kanaso yanzu ma sai in aurama ita menene a ciki? "


Ba Nafi ba ba kuma Dan binni ba hatta 'yan ansan bashi sai da tsananin mamaki ya kamasu, Nafi ta kalli Mahaifinta cikin tsananin mamaki sam tama kasa magana banda rawa da jikinta ya shigayi.

Baffa yai tsaki yace " Zancen banza kenan. "

Ali ya kalli mutanen gun yace " kowa yaji abinda Datti yace ko? "
Duk suka amsa da eh, Ali yace dan haka anjima da azahar zamu dawo a bakin nan za'a daura aure lalai zanga karyar iskaninka Datti. "

Suna kainan suka saki Nafi suka juya.

Nafi kam haf yanzu jikinta rawa yake, baffa ya kalleta yace " ke menene damuwarki? Ali fa nada kudi da dabobbi sannan matansa uku sai 'ya'ya guda sha shida kinga gwara ki aureshi can ki xauna cikin mutane ko kyafiyin hankali. "

Yana kainan ya juya yai waje.


Dan binni yai tsuru yana kallan ikon Allah wace irin zuciya ce da wannan mutumin? Bakomai a ransa sai dukiyarsa?





*THE INNOCENT TEAM*
*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com

4⃣


D'akinta ta shiga tana tafe tana layi, shikam yana jin motsinta yai saurin kwanciya dan ya tabbata bazataso wani yaji wannan mumunan abun ba, Nafi na shiga ta karasa kusa dashi ta zauna hawaye ne kawai ke malala a idanunta, can tasa hannu ta goge sannan ta kalleshi cikin wani yanayi mai wuyar fassarawa tace "Dan binni yazanyi da ke? Gashi baki farfad'o ba bare ki bar wannan gidan mai cike da abin takaici dasan zuciya. "

Zuciyarshi ce ta karye da mamakin tana cikin wannan halin amma tausayinsa take? Wannan wace irin yarinya ce wacce zuciyarta take da tsananin kyau?

Nafi ta kara sa hannunta ta goge hawayenta sannan ta cigaba " Dan Binni ina cikin wani yanayi mai wuyar fassarawa, Mahaifina baisan komai ba sai dukiyarsa baya ganin mutunci ko darajar kowa banda ta dukiyarsa, mahaifiyata kuma san kanta ya mata yawa haka na taso a cikin irin iyayen nan, ba wanda ya damu da halin da nake ciki ko wanda zan shiga, a dazu nafijin haushin Baffa akan kin biyan bashin dayai sannan bai damu da in auri sa'ansa ba wanda a cikin 'ya'yansa akwai wad'anda suka girmeni ba. "

Tai ajiyar zuciya sannan ta cigaba " yanzu kuwa nafijin haushin Inna ta, tafi kowa sannin halin Baffa amma duk da haka taje ta ranci kud'i da sunansa, ni kuma da ko naira biyar bangani ba bashi na neman............ "

Kuka ne yaci karfinta ta kasa karasawa, mikewa tai tsaye tace "bari in samoma madara kasha nasan yunwa kake ji."

Tana fita ya bud'e idanunsa ga mamakinsa jiyai gaba daya jikinsa yayi wani mugun sanyi, meyasa mutane basuda imani?
Yanzu me wannan yarinyar tayi da hakan ke faruwa da ita?

Shiru yai yana tunanin meya kamata yai dan cetan rayuwarta? Bata dade ba ta shigo dauke da kwarya karami da chokali, nan ta dagoshi kadan ta shiga bashi, mamaki tayi dan kuwa yau madarar bata zubewa sai dai batai tunanin komai ba.

Shikam sha kawai yake gardin madarar ce kesashi sha sai dai rashin sigari yasa madarar batamai armashi sosai ba.

Ganin yadansha dayawa yasa ta gyaramai kwanciya sannan ta mike tai waje.


A can bangaren Datti kuwa yatafi rigar Mahaifinsa nan ya shiga suka gaisa da iyayensa da 'yan uwansa ya kuma sanar dasu auren Nafi wanda za'a daura anjima, tsananin mamaki ne ya kama Iyayensa da yayensa, mahaifinsa wanda ya tsufa sosai ya kalleshi yace " yanzu Datti za'ai auren Nahi shine sai ranar auren zaka sanar damu? "

Datti cikin halin ko in kula yace " to Kawo menene aciki nima sai yau naji zancen auren. "

Gaba daya suka kalleshi cikin tsananin mamakin kalamansa, Aji mahaifiyarsa tace " Datti me kake san kace? "

Ya kalleta yace " Aji to menene ban fada ba? Nima aradun Allah sai dazu nan na sani."

Tsannnanin akaici ne ya kama Aji ta mike cikin zafi tai gaba hartaje wajen dakinta ta dawo ta kallesu tace " in har na isa da ku babu wanda zaije daurin auren Nahi ta gurin datti sannan ba wanda zai aika mata ko da kwayar samira ce, na sani ba laihinta bane sai dai Datti ya ja mata komai. "
Tana kai nan tai gaba a fusace Tanaji Datti nacewa " Karki damu Aji nima ba kai mata samirun zan ba mijinta inya damu ya sai mata. "

Yayansa Sambo yace " Datti me kake san fad'a? Bazaka mata kayan daki ba ko me?"

Datti ya mike yace " nifa nazo sanar daku ne bawai cewa nai kuzo ba, yar nan tawace ra'ayinane in mata kayan daki ko inki. "

Kallan mamaki suka bishi dashi inda sabo sun saba da halin Datti sai dai mamaki suke tunda yanzu abun ya shafi zancen 'yarsa.



***********


Sukam su Ali da ragowar abokansa murna suka shiga tayashi akan yasamu abu a bagas, lalai sun yadda Datti baya cikin hayyacinsa, waye zai saida 'yarsa saboda dubu ashirin?

Sukam sunje sun sanar da liman nan suka shiga shirye shiryen, Ali yasa aka share mata daki daya acikin gidansa, matansa kansu basuyi kishi ba jin yarinya ce suna ganin baifisu kara samun mai musu girki ba.



**************



Nafi ta gama aikin gida tsaf ta gyara dabobbi, shikam zaune yake yana addu'a fatansa d'ayane Allah ya bashi ikon taimakon wannan baiwar Allah, kamar yanda ta taimakeshi, yanaji a kasan ransa kamar Allah ya kawoshi garin nan ne dan ya ceci wannan baiwar Allah.

Tunani guda d'aya ne ya tsayamai dole ne shi ha dauki nauyin biyan wannan bashin kila itace mafita.


Mikewa yai ya fito daga dakin, ba kowa a wajen hakan yasa ya fita daga gidan.

Toh fah!!!! Ganinsa yai a tsurar daji baya ganin komai sai daji mamaki ne ya kamashi, yanzu ace mutum ne yake rayuwa anan? Sai kace mara gaskiya?

Jiyai ance kai waye nan? Da fillo akai maganar, Juyawa yai dan jin yasan kamar mai muryar nan.

Ya kalleshi tare da da dan yin kasa dakai sannan ya mikamai hannu alamar gaisuwa, Datti ya bugamai harara sannan yace " me kake anan? "
Yaa fada tare da kallan kayan jikinsa kamar yasan kayan nan, shikam dan binni ya daure ya sauke hannunsa sannan yace " Dan Allah cikin gari nake tambaya.

Jin yamai hausa yasa Datti yace " Ka mike nan hanyar inkai tafiya mai tsaye zakaga gari. "

Bai jira komai ba yace " Na gode yai gaba. "

Datti ya bishi da kallo kamar kayansa, sai dai ta ina kayansa zaije gun wannann kad'on?

Yayi tafiya mai nisa dan har ya gaji sannan yaga gari, a ransa yace nan ne garin?

Kauye ne sai dai yanada girma sosai ga mutane sunata hada hadarsu, wajen wani mai tabir din rake ya tsaya ya mikamai hannu suka gaisa sannan yace " Dan Allah akwai ATM anan kusa? "

Kallan mamaki mai raken ya masa yace " A me? "

Yadan dafa kansa sannan yace " Banki fa? "

Me raki ya kalleshi sosai kana ganinshi duk da rigar dake jikinsa zaka gane ba daga nan yake ba, ya girgiza mai kai alamar bai sani ba sannan yace " amma kaje can gurin masu mashina akwai Dan liti wanda yai karatun boko sai ka tambaye shi. "

Yamai godiya sannan ya karasa gun masu mashina, sallama ya musu sannan ya tambayesu waye D'an liti, wanda ke zaune ya sha riga da wando ya wani tsuke shi a dole dan boko ya kalleshi yace " Yes ganinan. "

Kallansa yai ya wani daura kafa d'aya kan d'aya akan mashin, dariya tadan so kamashi ya daure yace " Dan Allah tambaya nake san ma. "

Dan litti ya dan wani rangwad'a kai sannan yace " what is your ansa? . " wai so yake yace "what is your question?" lol

Dariya ce ta kama Dan binni yai kasa da kansa tareda murmusawa jiyai abokansa sunce " Kai Dan litti ka kure gayu fa. "

Dan litti ya wani sosa keya irin jin dadin nan, Dan binni ya dago sannan yace " So nake in tambayeka ko akwai ATM anan kusa."
Fuska dan litti ya canza yadan gyara zama sannan yace " AT me? "

Dan binni yai murmushi yace " ka gane mana inda ake cirar kudi ba tare da anshiga banki ba. "
Tafi Dan litti yai yace " Ohhhhhh ATN? Ha ha ha kai ne bakamin bayani ba, akwai amma gaskiya sai dai muje can gwaram. "


Dan binni yace

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login