Showing 18001 words to 21000 words out of 141466 words

Chapter 7 - ZUCIYA kowa da irin tasa Complete Hausa Novel

unknown   

13 Oct 2024

15911

ta kalli wayar, cikin tsananin mamaki ta daga tace "Ashraf? "

Gyaran murya yai sannan yace " Mumy dazu me Nafi ta ce miki? "


Mumy da mamaki tace " me ya faru? "

Yace " ba komai, sai da safe. "

Da sauri ganin zai kashe wayar tace " Ashraf!"
Naam kawai yace.
Nan ta sanar dashi duk yanda sukai, ajiyar zuciya yai sannan yai saurin kashe wayar, mumy tabi wayar da kallo cikin mamaki da rashin fahimta sai dai hakan a tabbatar mata akwai wani abu.


Ashraf yabi wayar da kallo tare da furzar da wata iska yace " Da alama tanada wayau."


Murmushi yai sannan ya zauna a bakin gadonsa.






*THE INNOCENT TEAM*
Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel, makeup and kitchen1⃣
AND
Cool novel, makeup and kitchen2⃣)

WHATSAPP NO:
+2349030159301
*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com

1⃣2⃣


Karfe hud'u Nafi ta bud'e idanunta kamar yanda ta saba, shiru tai daga kwance tana tuno mahaifinta ta kalli little wacce take ta baccinta hakan yasa itama ta koma bacci.

Har asuba tai Little ta tashi tai Sallah Nafi bata farka ba, ganin ta idar yasa tadan tab'a Nafi, da karfi Nafi tace " Baffah kayi hakuri na tashi wallahi. "

Ta fada tare da mikewa zaune da sauri, little tad'anyi dariya tace " Nafi nice! Da alama Baffan nan bulala yake miki. "

Ajiyar zuciya Nafi tai ta kalli Little tai murmushi kawai batace komai ba.

Little tace " Tashi kiyi sallah. "
Nafi ta amsa da to tare da mikewa tsaye tace "kin tarar mi..... "
Katseta Little tai tace "Na tarar miki ke da bakya mantawa. "

Nafi tai toilet tana murmushi.
Bayan tayi Sallah ne ta kalli Little wacce ke kwance kan gado da alama bacci zatai tace " Maryam naga kin kwanta?"

"Me zanyi to? Bayan sai karfe sha d'aya zan fita?"
Nafi tace" nima me zakiyi a kwancen nake tambaya. "
Little ta zauna tare da kallan Nafi tace " Bacci mana. "

Idanu Nafi ta zaro tace" Bacci kuma? Mu kwana muna kwanciya yanzu ma ki kwanta? Tab di. "

Little tai dariya tace " Uhm hm i kam dai bacci zanyi. "tai maganar tare da kwanciya.

Nafi ta kalleta tana mamakin wannan al'amari, mutum ya kwana yana bacci sannan ya kara kwanciya da safe? Shi ba ciwo yake ba?

Ganin tana ta zaune ga zaman ya fara isarta yasa ta mike sanye da hijabin datai Sallah tai waje.

Ba kowa a wajen garin ya yi hasken gabanin asuba ta kalli katun gida a ranta tace" Masu gini sun sha aiki. "
Kitchen ta nufa tana tafe tana kara kallan gidan mai cike da sha'awa, sukam 'yan kitchen sunata hada hadar aiki, ta gaishesu suka amsa cikin sakin fuska, Matar jiyar nan ta kalleta tace " yanaga kinzo da wuri? "

Nafi ta dan murmusa tace " in ma na zauna ba abinda zanyi shi yasa naga gwara na taho. "

Kai ta jinjina, Nafi ta kallesu tace " me zan fara? "
Wata daga ciki ta kalli matar tace " Goggo me zatayi? "

Goggo tai shiru can tace " ke wani bangare kika fiso? Akwai masu wanke wanke? Akwai masu bangaren dake dake da yanke yanke akwai masu bangaren girki. "


Ba tare da dogon nazari ba Nafi tace "Nafisan b'angaren masu abinci saboda inaso in iya irin abincin jiya. "

Dariya suka sa mata, Goggo tace " Bangaren Abinci fa sunfi kowa wahala saboda da safe kowa da abinda yakeso a dafa mai, wani sa'in da rana ko dare ma haka."

Nafi tace " Bakomai."

Nan ta zauna gun Goggo, takarda Goggo ta dauko ta shiga karanto abinda za'ama kowa yau, sunyi sa'a wasu suna zuwa iri d'aya, nan suka shiga aiki.

Nafi dai sai dai juyawa dan ko sunan abubuwan bata sani ba bare ta dinga mikowa.
An fara da masu fita karfe takwas, sai da aka gama dasu sannan aka fara ma 'yan gida su kuma nasu aka fita dashi.


Nafi kam abin sai birgeta yake, sai wajen karfe tara suka gama, Nafi ta musu sallama ta tafi.


Har sanda ta dawo Little na ta uban bacci, Nafi tanasan tai wanka gashi bata iya bud'e famfo ba, dole kawai ta samu guri ta zauna a kasa.

Bacci ne yai gaba da ita, wajen 9 da rabi sukaji ana kwankwasa kofa, da sauri Nafi ta mike tare da bud'ewa, Wasu yarane su biyu d'auke da ledoji suka kalli Nafi sukace " Dama Yaya ne yace mu kawo ma Yaya Little. "

Little dake zaune akan gado tace "Amra ku shigo mana. "

Nan suka fara kokarin jan ledar, Nafi ta amsa ta shiga dashi, little ta kalli kayan tace " me yace?"

Wacce ta kira da Amra tace " cewa yai mukawo miki zai kiraki. "
Amra na rufe baki kuwa sai ga kiran Ashraf, da sauri tai gyaran murya dan ya hanata wannan baccin, tace "Yaya ina kwana? "

Yace " kinga dama kin tashi? "

Kallan Nafi tai sannan tace " Yaya ba bacci nai ba. "

"Hmm ai inaji gaba ni da kaina zan dinga zuwa ina dubaki."

Little ta d'an turo baki sannan tace " Yaya ga su Amra sun shigo da ledoji."

Yace " Yanzu za'a kawo manyan, naga su bazasu iya d'auka ba ko kuma turo Nafi ta dauka. "

Little tace " to kana ina? "
Ina gun motor park, Sai Amra ta rakota. "

Little tace " to amma yaya kayan meye? "
Kayan Nafi ne so nake da yamma inkin dawo ki d'au driver ya rakaki gun mai d'inkinki sai a gwadata a mata. "

Baki little ta bud'e to kawai tace tanaji ya kashe wayar.
Nafi ta kalla ta fadamata sakon sa tare da cewa kimai godiya daga nan duk ke ya siyowa kayan. "

Cikin mamaki Nafi tace ni kuma? Little tace " eh mana ya san baki da kaya ga nawa sun d'an miki yawa. "

Nafi tai shiru tana mamakin ledojin da aka kira da nata.
Little ta katseta "ki tashi dan Yaya baisan jira. "

Nan suka mike itada Amra.


Yana zaune cikin mota kafafuwansa na waje sannan hannunsa rike yake da waya yana dannawa.

Nafi ta karasa inda yake ta tsugunna ta gaidashi, kallanta yai kawai maimakon ya amsa sai yace " kema daga baccin kike? "

Kai ta girgiza alamar a'a, yace " ki d'au kayan suna bayan mota."

Nafi ta mike a hankali har ta je inda zata d'auka sai kuma ta dawo inda yake ta tsaya kyam tana wasa da 'yan yatsun hannunta, Ashraf ya kalleta yace " Nafeesa da wani abun ne? "

Yawo ta had'iya sai dai ta kasa magana, ganin haka yasa ya cigaba da danna wayarsa baice mata komai ba shima.

Nafi kam tayi tsuru ta kasa magana, Amra kam tafiyarta tai ya rage saura su biyu, ta dade agun kafin ta daure tace " Yaya. "

Dasauri ya d'ago ya kalleta, tai saurin yin kasa da kanta dama abinda ta kasa fada kenan.
Kallan mamaki ya mata sai kuma ya maida kansa kan waya.

Ta kara daurewa tace " Yaya Na gode. "

Tana fada ta juya zata d'au kaya, jitai yace " Nafisa!! "

Tsaya wa tai cak sannan ta juyo a hankali cikin tsoro, ya kalleta kad'an sannan yace " Jiya me yasa kika rufemin kofa ina miki magana?"

Kanta na kasa sai gabanta dayake fad'uwa, Ashraf yace " meye dalili? Ko raini ya fara shiga tsa...... "

Katseshi tai da sauri da cewa " Wlh ba haka bane, matsowar dakai kusa danine yasa gabana yaketa fad'uwa shiyasa na rufe. "

Da mamaki yake kallanta yace " Nafisa yaushe kika koyi karya? "

Idanu ta zaro cikin mamaki tace "Wlh ba karya nakeba Yaya. "

Ya d'an kura mata ido hakan yasa tai kasa da kanta, a ransa yace " dole dan da alama namiji bai taba tsayawa kusa da ita haka ba. "
Wani abu ya tuno ya d'auke kansa daga kanta a hankali yace " da alama sanda kika ciren riga gaban naki bai fad'i ba "

Idanu ta zaro da sauri ta juya ta fara tafiya, ya kalli yanda take sauri yace " kayan fa? "

Idanu ta rufe, cikin tsananin kunya ta shiga neman tahowa gun idanunta a rufe, batasan har tazo inda yake ba, jin tayi dan tun tube da kafa yasa ta bud'e ido da sauri, Ashraf ya kalleta yace " Toh da alama gaban naki baya fad'uwa ko? "

Tsugunnawa tai da sauri cikin tsoro tasa kanta a cikin cinyoyinta, idanunta suka ciciko, Ashraf ya mike tare da d'anyin murmushi, ya matso saitin kunnenta yace " in kin gama kunyar sai ki rufemin mota. "

Tanaji ya tafi, ta dade kafin ta mik'e ta shiga bubuga kanta a hankali a jikin motar, jin goshinta ya fara zafi yasa ta d'au kayan tare da rufemai mota tai gaba.


Tana isa d'aki ta taradda Umma da Aneesa a zaune, gefe kuma Little ce tsaye da towel da alama wanka zatai.

A hankali cikin tsoro ta shiga d'akin, tare da ajiye kayan, Umma tace " Yauwa Ke muga ledar nan. "

Nafi ta mika ma Ummaa taja gefe ta tsaya, Umma ta kalli Aneesa tace " wanene lace d'in? "

Aneesa ta ciro wani dankararen lace wanda kana ganinsa zakasan lalai mai tsada ne na gaske.

Little ta kalli Umma tace " Umma nikam yaya fa bai fadamin ba?"

Umma tai murmushi tace " Little kenan bakiji me nace ba? Nice na aiki Aneesa ta fara siyomin kayan biki ita kuma ta manta ta bashi a cikin kayan wannan. "ta fada tana nuna Nafi.

D'aukan lace din sukai suka tafi, little ta shiga toilet ranta duk a b'ace.

Nafi kam ko ajikinta dan batasan darajarsu ba, itadai kunyar Ashraf ce ta kara kamata ya zatai inta ganshi?






*THE INNOCENT TEAM**ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com


*I Sincerely Dedicated This Page To All Masoyan Xuciya, Nagode Kwarai da san da kuke mai.... *😍 *ILYSM*😍


1⃣3⃣

Nafi tanannan zaund har Little ta fito ta kalli Nafi cikin takaici ganin tana murmushi ita kad'ai tace " Nafi bakiji haushin abinda su Umma sukai ba? "

Cikin rashin kulawa da abin tace " name fa? "

Little ta zauna a gaban madubi tace " kina gani sunzo sun dauki lace mai tsada da sunan wai aike akai? "

Nafi ta kalleta tace " lalai Maryam meye abin jin haushi? Kika sani ko da gaske suke? Sannan ko d'auka ma sukai ai sun isa ne naga ita zai aura? "

Little tai d'an karamin tsaki tace "Wlh ba wani kayansu, sannan dan ita zai aura sai akace tazo ta d'au abinda ba nata ba? "

Nafi ta mike tace " kafin ki shirya bari na anso miki abinci. "

Bata jira amsarta ba tai waje da sauri, Little ta bita da kallo a fili tace " lalai wato dan indaina maganar shine zaki gudu? "

Nafi kam tana fita tai murmushi tace " ni da naga kaya daga sama? Dan an d'au d'aya menene? "

Kitchen ta wuce, ta amso abincinsu kenan zata shiga bangarensu taji ance "Ke!"
Juyawa tai dan tasan Umma ce, Umma tace " zo nan. "

Ajiye tiren tai sannan ta karasa gunta, Aneesa ta maka mata hararra tare da juya kai gefe.

Nafi ta karasa tare da rusunawa tace "gani. "

Umma ta mata wani kallo tace " munafuka kinje gun aikin ko kuwa? "
Da sauri Nafi tace "Naje wlh. "
Duk da dama Umman ta riga ta tambaya ankuma shaida mata taje amma sai cewa tai "in kika min karya na tambaya wlh kinji na fad'a miki jikinki sai ya fad'a miki. "

Nafi tai kasa dakai ba tare da ta sake magana ba, Umma ta kara kallanta sannan ta ce " me Little tace bayan mun fita? " dama wannan shine dalilin kiran wancan burga ne so take taji me akace bayan sun fita.

Nafi da mamaki ta kalleta tace " Bangane ba. "
Da kuwa Umma ta mata ta kara da kinci gidanku, ni zaki kalla kicewa baki gane ba?

Nafi tai kasa da kanta a hankali tace "kiyi hakuri. "

Cikin takaici Aneesa tace "Dalla malama kara gaba. "
Nafi wacce bata fahimci me ake nufi da kara gaba ba tace "Naam? "

Cikin kuluwa Umma takaimata wani wawan mari wanda sai da Nafi tai baya tare da rike kuncinta.

Umma ta nunata da yatsa tace " kin bar nan ko sai na karya ki? Shigeya wacce asalinta bashida tabbas. "

Nafi ta juya ta fara tafiya sai dai tana tafe hawaye nabin kuncinta, haka ta d'au tiren tare da goge hawayenta ta shiga.

Little har tana shirin fita sai ga Nafi ta kalleta tace " lalai Nafi sannu da zaman hira. "

Nafi tai murmushi kawai batace komai ba sai hanyar toilet data nufa.

Tana shiga ta tsugunna sai kuka, itakam Little abincinta taci ganin Nafi bata fito ba yasa taje bakin kofar toilet d'in tace " Nafi na tafi. "
Da kyar ta daure tace "To. "

Sai dataji alamun fitarta sannan ta dawo ciki, ta dade kafin hawayen su tsagaita taci abinci sannan ta fara gyara d'akin.




_A Company_

Kawu zaune a kan kujerar dake tsakiyar dogon tabirin, gefe da gefe mutane ne kowa zaune akan kujerar sa, Wanda ke daga b'angaren hagu na kusa da kawu ya kalleshi yace " A gaskiya Chairman mun gaji da abinda Chief Director(Asim) yake mana, a duk sanda muka bukaci sa hannunsa akan wani aiki ko meeting a b'angaren mu ya dinga mana wala wala kenan, sam baya yin aikinsa na Chief Director."

Kawu ya kalli Asim wanda yaketa juyi a kujera cikin rashin damuwar abinda ake kararsa dashi, ran kawu ya kai koluluwar b'aci ya kallu wanda yai maganar yace " kar ka damu Director idan har Asim bai canza halayensa ba nan da one month ni a matsayina na shugaban wannan company d'in zan saukeshi daga matsayinsa. "

A zabure Asim ya kalli mahaifinsa wanda yana gama magana ya mike yai waje, Asim cikin tsagali da raini ya kalli mutanen gun yace " ni kuka had'a da mahaifina? Lalai ran kowa in yayi dubu sai ya b'aci. " shima yabi bayan mahaifinsa.

Office d'in kawu ya shiga, yana shiga yaganshi a tsaye kusa dashi ya karasa yace "Abba.... "

Littafin dake hannun kawu ya makamai iya karfinsa, Asim ya fad'a kan kujera cikin tsoro yace " Yahkuri Abba amma sharri suke...... "


Yatsa kawu ya nunamai idanunsa sunyi jaa yace "kai dakikin ina ne? Meyasa sam kwakwalwarka bata aiki? "

Yai wani hucci sannan ya cigaba "Company d'in nan na Waye? Kana tunanin dan na rike shi na shekara ashirin yana nufin ya zama nawa? "

Kai ya jijiga sannan ya cigaba " A'a, da zarar Ashraf yaso zai zo ya amshi matsayinsa ne babu kuma yanda zamuyi. "

Asim cikin b'acin rai yace " ta ina zamu barshi? "
Tsaki kawu yai yace " 50% d'in yaya(mahaifin Ashraf) gaba d'aya a gunsa yake, kai kasan duk karshen wata kud'in dake shiga account d'insa ya ninka nawa mai 20%?"

Asim wanda ya fara huccin takaici ya kalli Mahaifinsa, kawu yacigaba "In baka rike matsayin ka ba ka nuna ma mutane zaka iya kana tunanin Ashraf mai taurin kai zai bakka ka cigaba da abinda kaga dama in har ya fara aiki anan? "

Asim ya mike cikin takaici yace " shiyasa duk duniya ba wanda na tsana irin yaron nan, mahaifinsa kaf arzikinshi sunan sa yasa, kai daka wahala gurin taimakama uban sanda yana da rai bai ma kara ya barma ko da wannan companyn ba. "

Kawu ya zauna kan kujera cikin b'acin rai shima ya kalli Asim yace " Ka kula sannan ka dinga kokarin b'oye tsanar da kakema Ashraf dan naga kamar kanka

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login