Showing 114001 words to 117000 words out of 141466 words

Chapter 39 - ZUCIYA kowa da irin tasa Complete Hausa Novel

unknown   

13 Oct 2024

15927

tai sai kuka.



*#ASHRAFEEMAH TEAM*


💞
*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com


*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡



*73*



Kuka take sosai a cikin band'aki tana tuno irin soyayyar da Ashraf ya nuna mata a 'yan kwanakin nan, ko dai da gaske ne dan ya riga ya santa a mace shiyasa yake mata haka?

Jin yanda wayarta taketa kara ga Little sai kiranta takeyi yasa ta daure ta share hawayenta ta fito.

Wayar ta d'auka tace " Ferry ya akai?"

Ferry cikin zumudi tace " albishrinki?"

Nafi ta daure tace " goro."

Ferry tace " 8 credit gareki including math and English."

Wani sanyin dadi ne ya kamata tace " haba?dagaske?"

Ferry tace " wlh goegraphy ne kawai kike da pass."

Nafi tai hamdallah sannan tace " kefa?"

Ferry tace " 7 credit nima da maths da English."

Nafi ta kara hamdallah sukai sallama.

Little ta fadawa nan little ta taso da sauri ta rungumeta tana tayata farinciki.

Nafi kam murmushi kawai take yi aranta fadi take inama yaya na kusa da farincikin yafi min dadi.


**********

A b'angaren Ashraf kuwa tun bayan fitar Nafi ya zauna shiru yana tunanin ta anya kuwa ya dace abinda yake aikata mata? To amma ya zaiyi? Yasan sarai zata iya taimakamai wajen plan dinsa sai dai yana ganin in har tasan ba gaske bane yana ganinta a kusa dashi bayaji zai iya jure wulakantata, yafisan tai fishi dashi har ya cimma burinsa sannan ya nemi yafiyarta ya kuma amshi punishment din da zata bash na using dinta dayai.


Anisa ce ta shigo d'akun ba ko sallama ta zo ta zauna kusa dashi tana zubamai shagwaba wai tun safe bata ganshi ba sai yanzu.

Daurewa yai yace " nima nayi missing dink ai sosai."

Kwantowa tai kan jikinsa tace " Yaya kaje asibiti?"

Cikin mamak ya kalleta yace " Asibiti kuma?"

Kallansa tai cikin dan hade rai tace " ba kace bakada lafiya ba? Jiya da daddare."

Tunowa yai ya dan mike da sauri yace " eh naje anma ban magani."

Ta dan turo baki tace " ka warke?"

Ya juyo tare da dafata yace " daga shan magani sai warkewa?"

Ta zumburo baki tace " nifa....."

Waskewa yai ya jawota jikinsa.

Bayan sun kwanta tana jikinsa itakam tayi missing dinsa, Ashraf cikin dabara yace " nikam kina shiga d'akin Kawu?"

Kallansa tad'anyi tace " ba sosai ba dai."

Yadan yi shiru hakan yasa tace " menene? Wani abu kake so?"

Kai ya girgiza alamar a'a yace " bashi kawai banasan kowa yaji ne."

Mikewa tai ta zauna tace " me kakeso?"

Yace " dama akwai akwatin Abba na a kasan gadansa ne to kuma naga kamar Kawu bayasan in dauka, kinga in yaji na dauka ba da saninsa ba zai iya jin haushi."

Anisa cikin rashin damuwa tace " menene a ciki?"

Yace " kayan Abba ne na da can, su kadai ne ba'a bada ba na rasa me yasa kwanan nan nake san ganin su."

Tausayinsa ne ya kamata tace " karka damu zan daukoma amma sai dai kana gama gani mu maida yanda bazai ma san ka dauka ba."

Ashraf yai murmushin tausayi ya jawota jikinsa yace " Nisa nagode."

Wani dadi ya kamata tace " yaya in akwai wani abu da kakeso ka sanar dani."

Yace " abinda yasa ma ban fada miki da wuri ba banaso ne kowa ya sani, na kuma sanki komai sai kin fadama umma."

Kai ta girgiza da sauri tace " wlh wannan bazan fada mata ba ko da kuwa kamani Kawu yai bazan taba fadan kaine kakesan gani ba."

Cikin sanyin murya yace " Nagode Nisata."

Nan sukai murmushi dukansu.


************


Washe gari kuwa kafin kawu ya fita gun aiki Anisa ta shiga d'akinsa, bayan sun gaisa ya kalleta cikin kulawa dan yanasan Anisa sosai yace " Anisa ta yau kuma ganina aka zo yi?"

Kusa dashi ta zauna tace " Abba ba kai bane ka daina nemana?"

Yai dariya yace " ina na isa in daina neman 'yata Anisa?"

Itama dariya tai tace " Yaya na koma fa."

Ya kalleta yace " Ummanki ta fadamin amma ni hankalina bai kwanta da Ashraf ba kina ganin fa abinda yamana akan yarinyar can."

Dariya ta sakeyi tace " Abba kenan bakasan yanda Yaya ke kula dani ba yanzu komai nakeso shi yake min."

Kawu ya kalleta yace " shiyasa ai banyarda dashi dinba."

Anisa tadan tabe baki tace " Abba kenan."

Kallan agogo yai yace " mu tafi ko?"

Ta kwanta akan gadonsa tace " ni bacci ma zanyi anan."

Cikin mamaki yace " anan din?"

Kai ta daga tace " ina missing din kanshin Abba nane."

Dariya yai yace " ni inada meeting bari naje inkin tashi kya kullemin kofar ki ajiye makullin agunki, karkuma ki bari kowa ya shigo, ki rufe kofar kafin ki kwanta."

Tai dariya tace waye ma agidan dazai shigo.

Yace " tashi muje ki kulle kafin ki kwanta."

Ta tashi yana fita ta kulle sannan ta kira Ashraf tace "Yaya kana ina?"

Yace " ina d'aki."

Tace " in kawo ma."

Da sauri yace " A'a Nisa in kika fito dashi wani ya gani fa?"

Tace " ah haka ne, to ya za ai?"

Shiru yai kafin yace, bari nazo nan din in yaso sai kije gun Umma in na gama gani sai in kiraki."

Tace "bazan iya tsayawa mu gani tare ba?"

Yace " banaso ne ki ga yanayin da zan shiga."
Tai murmushin sannan tace " shikenan sai kazo."

Yana fita ta leka karkashin gadon, karamin akwati ta gani dab kit, tai dariya tace " wannan ai karamin akwati ne nasan baifi kala daya bane a ciki "


Ashraf na zuwa sukai canje ita tai bangaren Umma shi kuma ya shiga.

Akan gado yaga akwatin jikinsa ne ya fara rawa a hankali ya karasa gun akwatin cikin shakku da tsoron abinda zai gani.

Bayan ya zauna ya dade kafin ya daure ya bud'e akwatin.

Idanunsa ya bud'e a hankali ya kalli cikin akwatin.

Waya ya gani, da kuma envelope guda biyu.

Wayar ya d'aga waya ce irin ta da jiki a sanyaye ya kunna wayar, hotonsa yana karami ne ya bayyana akan wayar idanunsa ne suka fifito, wayar mahaifinsa ce kenan?


Envelope daya ya d'auko hotuna ne a ciki nan ya fito dasu, kana ganinsu kaga hoton da dan farare ne irin black and white din nan.

Na farko hoton Kawu ne shida wani mutum suna tsaye jikin wata mota suna gaisawa da alama ma basusan an d'aukesu ba.

Na biyu kawu ne da Dady da kuma wannan mutumin sun fito daga wani gida nan ma kana gani kasan basu san an daukesu ba.

Na uku kuwa hoton Abbansa ne da Kawu ga Mumy a tsakiya.


Kallan hotunan ya tsaya yi sai kuma ya d'auko wayarsa dake cikin jaka ya d'auki hutunan hoto.

Sannan ya bud'e d'ayan envelope din, wasika ce.

Mamaki ya kamashi ya kalli kasan wasikar an rubuta daga D'an uwanka Abbas.

Idanu ya zaro da sauri ya zari takardar sannan ya nemo wata takardar a cikin jakarsa plain ya sa a ciki.

Sannan ya sa waccan a aljihunsa.

Wayar ya sake dauka, ya jujuyata sannan ya maidata, ya rufe sannan ya fito.

Anisa yama waya ta dawo sannan yai office.


Wanene wannan mutumin?abinda yake ta mai yawo kenan.

Da sauri ya kira wayar D'an litti bayan sun gaisa yace " Dan Litti kana ina?"

Yace " ka manta kace inje gidan Lawyer din nan inji ko mutumin ya dawo?"

Ashraf ya dan shafi kansa yace " bar wannan kazo company yanzu akwai abinda nakeso kai da wannan dan sandan ku nemo min."

Dan Litti yace " Yes sir."


Nan ya juyar da kan mota yai gun Ashraf.

Bayan ya shiga office dib Ashraf ya turamai hotob Kawu da wannan mutumin yace " wannan mutumin nakeso a nemomin inda yake, ni kuma zanje gub Uncle inji wanene shi."

Dan Litti ya mai salute sannan ya fita.



Ashraf ya zaro wasikar nan daga aljihunsa ya kura ma wasikar ido, a zahiri tsoron karantawa yake dan baisan mai zai jiyo wa kunnensa ba.



Sai dai ko dan ya dawo da Nafisan sa kusa dashi dole yai saurin yib solving din wannan case din.



************


Nafi kam ita kadai tana kwance a d'aki yau ma ruwan zafi kawai tasha sam ta kasa cin komai taji an banko mata kofa.

D'agowa tai a hankali dan ganin wanene.

Anisa ce da Umma hakab yasa tadanyi tsaki kadan tare da maida kanta.


Umma da Anisa suka shigo, Umma tace " ha'a su bora ashe ananan? Ko da yake anci jan miyan anci nama anci shinkafa inafa za'a yarda a koma riga a sha fura da kunu?"

Nafi ba tanka musu ba, Anisa tai dariya tace " Umma ina tunanin ince yaya ya d'aukeni muje honeymoon ko paris ne muyi ko 1week ne."

Nafi barasan sanda ta dago ba ta kalleta wani irin kalli wanda ita kanra batasan ta yi ba."


Umma ta sa hannu ta hankadata kan gadon tace " me? Kishi kike? Ji kike kamar ki daketa?"

Nafi kam shiru kawai tai, Anisa tai dariya tace " karki damu zan kawo miki takardar sakinki."

Nafi ta mike tsaye ta musu wani kallo tace " in kun gama please kuyi waje."

Anisa tace " mene?"

Nafi tace " inda saura kuma ku gama kafin ku fita."

Tana kainan ta kwanta akan gado tare da rufe idanta.

Haushi ya turnukesu, Umma tace " Kyale ta zamugani ko bakin nanan in har aka bata takardarta."


Dariya suka sa sannan sukai waje.


Nace uhmmmmm



*#ASHRAFEENAH TEAM*

💞
*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com


*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡



*74*



_Zuwa ga Muktar_

_Ba sai munja duguwar magana ba, na sani bazan tashi daga kwanciyar nan ba._
_Da farko dai ina mai baka hakuri abisa rashin sanina na san Ruma da kakeyi wanda kai baka aureta ba ta kuma zama matar yayanka, Allah shine shaidata ban taba sanin kana santa ba ko da kuwa da wasa ne._
_Abu na biyu shine kayu hakuri abisa rashin kula dakai da banyi ba, ganin yanda ka canza hali ka rikid'e zuwa mutum mai tsananin buri da kuma neman sai ya samu abinda yakeso ko ta halin ka ka ne yasa na shiga tunanin laifinane da ban kula dakai da kyau ba, Muktar ita rayuwa da kake ganinta ba'a mata buri mai yawa, ba kuma a cewa komai sai an samu, na sani sarai kaine kai manakisa ka sanar da abokinka da yake aikin custom akan su Hisham sun saro miyagun abubuwa, bayan rasuwar mahaifin Ruma nai bincike akai anan na gano kaine kasanar da abokinka, na fahimci so kake ka hadani fada da Hisham da iyayen Ruma wanda harzai sa su rabani da Ruma._
_kai ka zuga dan siyasa wato Chirman Santa akan ya ba Hisham makudan kudi ya kuma nemi ya taimakamai da saro miyagun abubuwa, sannan ka karkata ka sanar da abokinka, duk daga baya na gane trap ne ka shirya dan rabani da Hisham da iyayensa._
_Muktar na dade ina mamaki akan wannan al'amari, na d'auka ka hakura da Ruma ganin akwai zuri'a a tsakaninmu, sai dai daga a yayin da nai hatsari na gane lalai ba hakura kai da ita ba shiri kakeyi ta yanda zaka sameta ko ta halin kaka ne._
_Muktar na sani sarai da kai da Hisham kune sanadin wannan hatsarin nawa, domin kuwa na san komai, kun samu Auwal Max akan ya lalata birkin motata sai dai a lokacin da na sani lokaci ya riga ya kuremin domin kuwa ina cikin mota nayi nisa da fara tafiya, Isma'il ya turomin da hotunan ku gidana wanda Ruma ta kirani cikin gaggawa sai dai lokaci ya riga ya kuremin, ko ince dama can kwanana ya kare._
_Ban taba tunanin tsanar da kakemin zatakai ga hallakani ba, na maka komai na rayuwa, na kuma nemi 'yarka da ta zama matar d'ana, sai dai a wannan lokacin na janye zancen auren Anisa da Ashraf, banaso d'ana ya fiskanci kiyayya da wahalar danasha a gunku, ya rayuwarsa zata kasance inhar yaji Mahaifin matarsa shine yai sanadiyar nasa mahaifin?_
_Muktar nayi iya bakin kokarina wajen farantamaka da janka a jiki duk da nasan tsananin kiyayyar da kakemin akan Ruma da dukiyata sai dai ina rokonka kar wannan kiyayar ta koma kan d'ana, na yafe maka duk abinda kamin, amma bazan taba yafemaka ba in har ka cutar da Ashraf._

*Daga D'an uwanka Abbas*


Da sauri Ashraf ya saki takardar yana girgiza kai cikin tsananin firgice, lalai Kawu mutum ne wanda dole aji tsoronsa, kasa ya sauka jikinsa sai rawa yake ya jingina da bango tare da hade kafafunsa yana girgiza kai kenan Kawu shine yasa aka kama kayan su Dady dan yasan halin Abbansa bazai taba taimakon su ba akan harkar miyagun aiyuka ba.


Kansa ya cusa cikin cinyoyinsa a hankali hawaye ya fara zubo mai, wayarsa ce take ta kara sai dai sam ya kasa ko da mikewa, yanaji wayar har ta gaji ta katse.

Ya dade a wannan yanayi kafin ya daure ya d'au wayarsa da taketa faman kara, Dan litti ne da kyar ya daga batare da yace komai ba.

Dan litti yace " Oga Auwal Max ne a hoton nan."

Kai ya daga kawai dama jikinsa ya gama bashi nan ya katse wayar tare da yin shiru, ya akai hotunan da aka ba mumy suka kare a hannun kawu?

Da sauri ya mike ya zari makulli yai waje cikin tsananin rudani.

Bangaren Mumy ya nufa zuciyarsa na masa wani irin radadi, banko kofa yai da karfin tsiya wanda ita kuma tana zaune rike da karamin hoto, tana jin yanda aka banko kofar ta mike da sauri hoton ya fadi kasa, kallan hoton yai ganin Abbansa ne a jiki.

Wata irin dariyar takaici ya saki ya matso kusa da ita ya tsugunna ya dau hoton ya kalleta cikin tsananin takaici yace " me kikeyi da wannan?"

Kallansa take cikin wani yanayi, ganin yanda ya rikid'e gaba daya, tace " Ashraf."

Kallanta yai idanunsa sunyi jaa sosai yace " me kikeyi da hoton mahaifina? Bayan da ke aka hada baki akai komai?"

Kallansa tai tace " Ashraf wai meke damunka ne kwanan nan da baka iya boye emotion din ka?"

Ha ha ha ha! Yai tafi da hannunsa yace " Emotion? Kamar yanda kikeyi? Ku halaka min uba sannan ki wani dauki hotonsa kina kallo?"

Idanu ta runtse cikin wani yanayi, wayarsa ya bud'e ya shiga nuna mata hotunan nan, yace " hoton nan ke Isma'il yaba shaidar shirin da Dady da kawu sukeyi na halaka mahaifina, tambaya ta anan shine tayaya akai hotunan nan suka isa gun Kawu?"

Kallansa tai sai dai ta kasa magana sai hawaye kawai takeyi, Ashraf yace " Good! Dama nasan bakida amsa, sai dai Mumy dukanku sai kun amshi laifinku a gaban hukuma an muku hukunci."

Yana kai nan ya juya zai fita, haryaje bakin kofa yaji tace " Kana tunanin duk a san raina nake komai?"

Tsayawa yai cak ba tare da ya juyo ba, tana kallan bayansa ga hawaye na zuba sosai a idanunta tace " me kake tunani? Banasan Mahaifinka? Ashraf na auri mahaifinka ne saboda soyayya ba dan komai ba."

Juyowa yai yace " a'a kin aureshi ne saboda kudin sa."

Cikin zafi tace"lokacin dana auri Abbas kana tunanin yanada kudi? Mahaifina shine ya neman masa aiki har ya zama abinda ya zama."

Ashraf ya kalleta baice komai ba.

Mumy ta zauna jabbas akan kujera ta share hawayenta tace " Zauna."

Jikinsa a sanyaye ya zauna yana kallanta.

Mumy ta kara share kwallarta sannan tace " Muktar bakasan wanene shi ba haryanzu, mutum ne wanda inyace yanasan kaza to fa sai ya sameshi ko da kuwa ta wani hali ne, bayan aurena da mahaifinka har Allah ya azirtashi ya gina wannan gidan baisan Muktar na sona ba, ni kaina sai bayan mun zauna tare sannan nai dana sani sosai dana amince da wannan hadin gidan.

Muktar haka zai zo bangarena ya dade duk yanda naso ya tafi bazai tafi ba, anan zaici abinci ni kuma sai dai in shige d'aki.
Danama Abbas magana sai yace kar in damu ba komai.
Tsoro na ya fara yawa ne daga sanda Muktar ya shigomin d'aki ina bacci ya zauna kusa dani, idona a rufe na dauka Abbas ne inaji yana ta shafamin kai ina murmushi, sai dai daga sanda na bude ido na ganshi na mike da sauri na sa hijab na fara mai masifa.

Abinda ya tsoratani shima cikin masifa ya matso ya turani jikin bango gaba daya idanunsa sun canza kamar bashi ba yace " Ruma kinsan tun yaushe nake dakon kaunarki? Banaji duk duniya akwai wanda ya isa ya rabani dake, wlh kinji na rantse miki sai na mallakeki ko ta wani hali ne."

Ya sakeni yai waje a fusace.
Tun daga wannan rana na fara rufe bangarena sai kuma awannan lokacin Abbas yasan komai sai dai bai taba kawowa Muktar zaiyi

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login