Showing 99001 words to 102000 words out of 141466 words

Chapter 34 - ZUCIYA kowa da irin tasa Complete Hausa Novel

unknown   

13 Oct 2024

15924

ba sai da suka shiga d'akinsa ya kalleta cikin tausayi ya runtse idanunsa, ransa na kara soyuwa, baya ya juya mata yana wani hucci da sauri da sauri.

Nafi da sauri ta matso ta rungumeshi ta baya, tasa kanta a bayansa tana kuka tace " Yaya please cool down, me yasa ranka zai baci akan abinda baikai ya kawo ba??"

Idanu ya runtse yanajin wani abu na tasomai a ransa yace " ina zaki gane bayan wani bangaren na sanar dani harda Mumy a salwantar da mahaifina, tunda nasan abu ya hadasu da danginta."

Nafi ta kara kankameshi ta baya tace " Yaya Mumy fa ba wai tsanar ka tai ba, ka taba ganin inda uwa taki danta? Ni inaji a jikina akwai dalilinta na yin haka."

Idanu ya sake runtsewa, Nafi ta zagayo ta gabansa ta rungumeshi tace "please yaya kadaina fadamata magana mai zafi haka tun balle in akainane."

Hannu yasa ya zareta daga jikinsa yace " Nafisa, kinsan ya nakeji a raina? A duk lokacin da matar nan tamin haka? Tun da nake da ita bata taba san abinda nakeso ba, bata taba yarda da abinda nace ba, bare in nemi kulawarta ko shawararta."


Hawaye ne ya zubo mai, Nafi kam hawayenta sai tsananta gudu suke yi, da sauri Ashraf ya juya dan bayasan taga hawayensa.

Kara rungumeshi tai tace " Yaya fitar da duk abinda ke ranka, inaji kamar abubuwan da kake hadiyewa sunyi yawa, shi hawaye rahama ne in kayishi yanasa bakin cikin mutum ya ragu, sannan maganar Mumy ni dai inaganin da wani abu."

Ashraf ya hadiye hawayensa yabar idanunsa a runtse, Nafi ta dago a hankali ta danyi dage ta sumbaci bakinsa kadan, tace " i am here with u, ka daukeni a matsayin mutum mara ji mara magana, ka fadi duk abinda kake boyewa a ranka ko ka samu sauki cikin ranka, Yaya na kula bacci ma bakayi yanda ya kamata, kuma ni nasan duk saboda abubuwan da kake hadiyewa ne kai kadai."

A hankali ya bud'e idanunsa ya jawota ya rungume tsam, yace " Nafisa I really Luv u."

Dagowa tai cikin mamaki, ya kara kankameta yace " kece mace ta farko ko ince mutum na farko da nake jin tabbas wannan itace, itace wacce takesona tsakani da Allah, itace wacce ta yarda dani, itace wacce zuciyata ta aminta da ita, itace nakeji in har tana tare dani i can endure everything."

Ya dan yi ajiyar zuciya yace " ban taba tunanin zan taba jin mutum haka a raina ba, ban tabaji na aminta da mutum haka ba, Nafisa please don't ever betray me"

Wani hawayen dadi ne ya zubo mata kai kawau take girgizawa tace " How can I! How can I......."

Sam ta kasa karasawa ya dago a hankali ya kai bakinsa cikin nata......




_Ni kaina idanuna yau sun ciciko, tabbas Ashraf yaga rayuwa ko ince yana gani, babu abu mafi soyuwar zuciya da kunci irin ka rasa wanda zaka aminta dashi, ka rasa wanda zakai shawara dashi, ka dinga ji kamar kowa na kusa dakai nemab ganin bayanka yakeyi_

Allah ya tsaremu daga sharrin mutum domin kuwa sharrinsa yafi na shedan.


Ameen


*#ASHRAFEENAH TEAM*
💞
*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com


*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡




*64*


Kwance suke tare a kan gado tana makale a jikinsa sun shiga bargo, fitilar d'akin a kashe take sai ta gefen gado da take a kunne, sunyi shiru sunajin dumin junansu.

Cikin sanyin murya Ashraf yace " Nafisa."

Tana kan kafadarsa tace " Naam."

Yacigaba " Abba hatsarin dayai a kwai hadin baki a ciki."

Da sauri tai nufin mikewa yasa hannu ya maidata yanda take, shiru tai sai dai gabanta sai faduwa yakeyi, yacigaba " bansan takamaimai dalilin dayasa Abba ya tsole musu ido ba ko ince suka tsaneshi ba sai dai gobe nake sa ran tambayar Uncle Salim in har shima bai sani ba sai inyi bincike da kaina."

Nafi tai shiru, Ashraf ya cigaba " tun dana mallaki hankalin kaina nakejin komai ba daidai ba a gidan nan, sam na kasa yarda da yanda al'amuran gidan nan ke tafiya."

Nafi ta makalo hannunta ta kwibinsa a hankali itama tace " Yaya ni kaina bayan Little taban tarihin gidan nan na rasa dalilin dayasa na kasa fahimtar abubuwa guda uku."

Ashraf yace " me da me kenan?"

Ta gyara kwanciyarta tace " Mumy inaji a jikina akwai dalilinta na auren kawu cikin gaggawa."

Ashraf yai dan karamin tsaki yace "ba wani dalili dama kila can shi takeso ta yaudari Abba."

Nafi ta girgiza kai tace " karka bari zuciyarka ta nemi boyema gaskiya."

Kai ya dan kawar gefe sannan yace " next."
Tace " Meyasa kafin Abba ya rasu yafi zama dakai, naji hatta aiki ba fita yake ba kullum kuna tare dashi, nasan zai iya yiwuwa jikinsa ne yake bashi hakan sai dai yanda baya zama da kowa sai kai yasa nake tunanin da wani abu, ko yasan akwai manakisar da akemai ko kuma akwai wani dalili da mu bamu sani ba."

Shiru Ashraf yai yana tunani, Nafi tacigaba " nakarshe karkace kishi ne ko wani abun sai dai inaganin tayaya Abba dayakesan ka auri yaya nisa zai bada wasiyya akan aba matarka ta farko? Indai har yaya nisa yake so ta zama matarka banaji sai yace matarka ta farko sai dai kawai ya bada yace abawa Yaya nisa in aurenku ya tashi."


Shiru Ashraf yai yana tunani lalai wannan abun tambaya ne, Nafi tace " nayi mamaki danaji wasiyyar ta kudi ce ganin ba kudi kuka rasa ba,banaji akwai dalilin dazai sa Abba ya bada wasiyyar kudi."


Ashraf yai shiru yana tunani, Nafi ta matso da kanta tace " yaya karka damu da abubuwan danace, zargi nane kawai ba wani abu serious ba." tafada tare da kara shiga jikinsa.

Ashraf yai shiru yana tunani, ganin haka yasa Nafi tai bacci, sai daya tabbatar tayi bacci sannan ya jawo littafinsa ya zare jikinsa a hankali ya nufi falo.

Can tsakiya ya bud'e inda yaga Abba yasa " Baban burina bai wuce naga na hada zuri'a da Muktar ba."

Shiru Ashraf yai ya dade kafin ya dawo ya kwanta.

Da sassafe kuwa bayan sunyi sallah sun kwanta sai daya jira tai bacci sannan ya zare jikinsa yai waje.

Mota ya fada yai waje.


Gidan Uncle ya nufa kafin ya karasa ya kirashi a waya yace " dan Allah ya fito waje zasuyi magana ne."


Yana zuwa kofar gidan kuwa yaga Uncle a tsaye.

Ashraf ya karasa suka gaisa sannan yace " Uncle zaka iya tuna me ya faru tsakanin Abba da dangin Mumy kafin ya rasu."

Uncle ya kalleshi yace " Ashraf a ina....."

Hannu ya hade gu daya alamar toko yace " dan Allah kafadamin Uncle, nasan ba yanda za'ai case ya hada su da Abba ace lawyer dinsa baisan komai ba."

Uncle yai ajiyar zuciya yace " mu shiga motarka."

Nan suka shiga, Uncle ya kalleshi yace " Ashraf mai nene dalilinka nasan jin abinda ya riga ya wuce?"

Ashraf ya kalli Salim cikin zakuwa yaji yace " ba komai kawai so nake naji ne."

Salim ya jinjina kai sannan yace " Mahaifin Ruma ya fara kasuwanci bayan yayi retire, ko da yake ba wai fara wa yai ba dan dama Hashim(mahaifin Habib) dan kasuwa ne, kasuwancinsu ya bunkasa alokacin da Abbas arzikinsa da matsayinsa yai fice a garin nan.


Bazan manta ba bayan ka gama nursery ka shiga primary 1 wannan mumunan al'amari ya faru.

Hisham da mahaifinsa sukayo dealer din kaya mai uban yawa wanda ya kunshi kusan duk arzikinsu, sai dai kaya aka hanasu shigowa, Customs suka rike musu kaya gaba daya container's dinsu.

Ba karamin tashin hankalu suka shiga ba duk yanda sukai a barmusu kayansu su wuce amma ina... Sam abu yaki yiwuwa."

Ashraf ya kalli Salim cikin mamaki yace " sunyo order din abu mara kyau ne?"

Ajiyar zuciya Salim yai yace " Kwarai kuwa sai dai sun b'oye hakan, ganin ba yanda za'ai kayan su ya fito ga dukiyarsu duk tana ciki yasa mahaifin Ruma ya yanke jiki ya fad'i, tashin hankali ya kara tsananta.

A wannan lokacin nan Hashim ya samu Abbas yace ya taimaka suyi cuwa cuwa a sakar musu kayansu, Abbas mutum ne mai tsaurin gaske jin Hashim ya zo mai da wannan uzuri yasa ya mai duban kurila yace " Hashim mai kuka sako a cikin kayanku?"

Ran Hashim ya baci yace " ko ma me muka sako ai ya zamarma dole ka taimakemu ganin mune muka samar ma aiki har kakai matsayin da kake yanzu."

Abbas yace " bai zamar min dole ba dan kuwa in har abinda kuka d'auko akwai abin cutarwa to wlh ko d'ana Ashraf ne bazan taimaka mai ba."

Nan dai suka rabu zuciya ba dadi, bayan Abbas yayi bincike nan ne ya gano mugayen abubuwan dake kasan kayayyakinsu, ciki kuwa har da hodar iblis da 'yan kanananan makamai."

Ba karamin tsorata Abbas yai ba ya samu Hashim cikin tsananin fushi yace " Hashim da hankalinka zaka saro wannan mugayen abubuwan?"

Hashin cikin zafin rai yace " ce maka akai nawa ne? Na wani abokin Abba ne dan majalisa ne yace mu taho mai da sakonsa."

Ran Abbas ya sake b'aci yace " to meyasa shi baiyi magana an sakar muku kayan ba?"

Hashim ya dan shafi kansa yace " tun bayan faruwar abin nan yabar kasar ma gaba daya, ba yanda zamuyi mu sameshi."

Abbas yace " kanaso kacemin kaf mugayen abubuwan nan ba naka ko na Abba ko daya a ciki?"

Hashim cikin hasala yace " akwai mana, bayan yace mu taho mai dashi nima nai tunanin sawa a dan samomin jin yanda suke da tsada sosai."

Abbas ya bud'e baki cikin mamaki yace "Hashim kanka daya kuwa??"

Hashim ya mike rai a b'ace yace " me? Yanzu dan ka zama babban mutum kana tunanin zaka wulakantamu? To wlh kayi kadan dolene kaje kasan yanda zakai su sakar mana kaya."
Yana kai nan ya nufi hanyar waje, daidai nan Ruma na kawo kai, Abbas ya mike yace " ba dole a ciki, sannan tunda dai bakuji kunyar cutar da mutane ba banaji nima ya zamarmin dole na bi bayanku, kasan inka sai da hodar da makaman wadanda za'a cuta dasu? Kasan bayin Allahn daza'a halakar dasu?mai makon ma ka dauki laifinka akan kuskuren dakai sai ma gani kake baka aikata komai ba?"

Hashim ya kalli Ruma yace " ke Ruma!"
Mumy ta kalli Yayanta cikin tsoro, yace " wuce mu tafi gida, da alama Abbas ba sanki yake ba inhar bazai taimaki mahaifinki dake kwance a gadan asibiti ba saboda wani shirme can da zuciyarsa ke sanar dashi ba."

Nan yai waje Ruma tabi bayanshi.

Abbas yai shiru yana mamakin wannan al'amari, sai dai tabbas in har zai taimaki Hashim to lalai sai ya yi nadamar abinda ya aikata."

Ashraf ya kalli Salim jin yayi shiru, yace " Uncle sai akai yaya?"

Salim ya goge gomin daya keto mai yace " anyi haka da kwana d'aya Allah ya dauki ran mahaifin Ruma, wanda kuma shock din mutuwarta ya kwantar da mahaifiyarta ta samu ciwon paralyze."

Idanu Ashraf ya zaro tsananin tsoro ya kamashi, Salim yai ajiyar zuciya yace " Abbas yayi dana sani sosai nakin taimaka musu da wuri, shi kuma yana ganin dolene Hashim yayi nadama saboda gaba.

Sai dai faruwar wannan mumunan al'amari ya tada hankalin kowa, yayi nadama takin karawa gani yake daya taimaka da wuri Abban Ruma bazai rasu ba, haka ma Mahaifiyarta bazata kwanta rashin lafiya ba.

Sanda Abbas yaje gaisuwa Hashim ya sanar dashi kada ya kuskura yasa a saki kayan basa so sun kuma fahimci abinda yake nufi."

Yai dan hucci sannan yace kaji abinda ya faro.

Ashraf banda Inalilahi wa Ina ilaihi Raji'un ba abinda yakeyi.

Can ya daure yace " Nagode Uncle."

Salim har ya bud'e kofa zai fita Ashraf yace " Maganae wasiyae Abba ta matata ta farko fa? Kasan dalilin sa nayin hakan?"

Salim ya girgiza kai yace " bansani ba gaskiya sai dai nasan ana gobe zaiyi hatsari kunyi tafiya dakai dashi da malam kunje kauyuka bada taimako, yana dawowa a daren ya bani wannan takardar."

Ashraf yai ajiyar zuciya sannan ya kara cewa Nagode.

Salim har ya fita ya dawo yace " karfa ka kawo komai a ranka, kasan Hashim na sanka."

Ashraf ya daga kai alamar to, Uncle na tafiya ya kwantar da kansa a jikin kujera yana fitar da numfashi sama sama.......





*#ASHRAFEENAH TEAM*
💞*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com


*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡




*65*

A hankali yaja mota ya nufi office ji yake numfashinsa na fita da sauri da sauri dole yai parking a gefen titi tare da kwantar da kansa kan kujera, waya ya dauka yama Dan Litti text din inda yake sannan ya maida kansa jikin kujerar.


Nafi kam karfe 7 ta tashi saboda tanasan Ashraf yai break kafin ya fita, sai dai me? Bataga kowa a kusa da ita ba hakan yasa ta fito falo da sauri, nan ma ba Ashraf, ta zauna akan kujera tare da kiran numbersa, sai data kusa katsewa sannan taji ya daga cikin wata irin murya mai tsoratar da mai sauraro yace " Hello!"
Mikewa tai a tsorace tace " Yaya menene? Me ya sameka?"

Sama sama takejin numfashinsa ganin yanda ta rikice yasa yai saurin katse wayar.

Zubewa tai a kasa tanajin zuciyarta tana kuna, hawaye ne ya zubo mata ta dafa kanta tace " wannan wani irin masifa ce? Ya Allah ka dubi wannan bawan naka ka sassautamai ka agazamai."

Kara kiran wayar sa tai saima tajita a kashe.

Mikewa tai da sauri ta nufi bangaren Mumy ba tare da tunanin komai ba.

Mumy kam tana zaune kan sallaya tana kallan su Afra sun gama shiryawa zasu tafi makaranta, ta musu sallama sukai waje suna fita ita kuma Nafi tana shiga, Mumy cikin mamaki ta kalleta.

Zubewa Nafi tai a gabanta idanunta na zubar da hawaye tace " Mumy dan Allah ki tausaya wa Yaya ki sanar dashi dalilinki nakin shiga harkarsa da kulashi da nunamai soyayya "

Mumy ta buga mata wani kallo zatai magana Nafi ta katseta da sauri tare da hade hannayenta cikin sigar roko tana kuka sosai tace " kin taba tunanin yanda yake bacci da yanda yake rayuwarsa? A da na dauka ina cikin bayin Allah wanda suke bukatar a tausaya musu sai dai yanzu na fahimci cewa nice ya kamata in tausayama wasu badai a tausayamin ba, duk wahalar danasha a kauye har yaya ya tausayamin banaji nakai kashe 10 acikin 100 wanda yaya yake fuskanta"

Tadan ja hanci sannan ta cigaba " He is so lonely, mutum ne wanda bai yarda da kowa ba sai kansa,Mumy nasan har kasan ranki kina tausayamai sai dai shi akullum kina daya daga cikin mutanen da suke bakin ciki ga rayuwarsa gani yake ba sanshi kike ba, kema kina daya daga kashe 20 bisa 100 na bakin cikin sa da damuwae dake ransa."

Nafi ta kara matsowa tana kuka tace " Na rokeki Mumy ki tausayama wannan marayan Dan naki ki sanar dashi dalilinki na mai haka ki kuma ja shi a jiki, mutum ne wanda bai san dadin uwa ba."

Idanun Mumy ne suka ciciko, Nafi tai kasa da kanta tare da share hawaye tace "indai nice bakyaso zan bar Yaya har abada zan koma kauyenmu sai dai dan Allah ki duba darajar Allah ki sassautama wannan dan naki, maraya ne shi kice gatansa in har kika nuna bakyasan jininki waye zai soshi? Na rokeki Mumy dan Allah........"

Kuka ne ya kufce mata kawai ta kifa kanta akasa tana kuka, da sauri Mumy ta mike tai cikin daki, a bakin gado ta zauna itama tana kuka.


Nafi kam ta dade agun kafin ta tashi a hankali tai waje, taje fita daga bangaren sai ga Anisa.

Sam bata kula da ita ba saboda hankalinta sam baya jikinta.

Ji tai an bangajeta da karfi har tai baya tala tala kamar zata fadi, ta dago idanunta da suka sha kuka ta kalli Anisa.

Anisa ta sa hannu ta daki kafadarta da karfi tace " me? Kuka kike dan ance dole ki rabu da mijina? Ko kuwa da kina tunanin banza ta shani ne?"

Ran Nafi yakai kololuwa gun b'aci, ta kafe ta da wani mugun kallo, Anisa ta matso tace " ke? Ni kike ma wannan kallon?" ta fada tana kallan Nafi.

Nafi ta ki dauke idanta, haushi ya kama Anisa ta daga hannu zata mari Nafi.

Nafi ta rike hannun da sauri sannan cikin dakakiyar zuciya tace " kada ki kuskura ki kara tunanin dukana, nice matar yaya ta farko, balle kiyi tunanin na miki kwace, sannan uban me kika tsinana ma Yaya? Bakin ciki? Ko me? Tun da kike dashi kin taba kula da halin da yake ciki? Kin damu da cinsa? Sannan sai anyi magana kice ke matarsa ce?"

Ta cillar da hannun Anisa tace " da rashin wayau ne yasa nabar Mijina a kulawar ki sai dai yanzu ni zan kula da abina, ni zan bashi hakkin da mace ke ba mijinta."

Tana kai nan tai waje a fusace.

Anisa kam kasa motsi tai mamaki da tsoron yanda yarinya karama ta kafeta da ido da kalamai takeyi.


Tana shiga d'akinsu ta fada kan gado, Little ce ta shigo rike

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login