Showing 24001 words to 27000 words out of 135422 words

Chapter 9 - Gidan Uncle Complete Hausa Novel

Fauzah   

06 Oct 2024

49726

cikin gdan a guje kamar mahaukaciya.



Hakanne yabashi damar figar motar a guje ya nufi Abdullahi Wase specialist hospital yana zuwa aka karbeta aka shiga da ita emergency duk inda sukayi binsu yake kamar wani zautacce daqyar Dr Saleem ya lallasheshi ya zauna a reception din ya hadakai da gwiwa cike da tashin hankali ji yayi an tabashi ya miqe da sauri yace  na shiga uku ta kasheta ko Dr?" Murmushi Dr Saleem yayi yace  ka kwantar da hankalinka bata mutuba munsamu nasarar tsayar da jini amma akwai buqatar wani jinin da gaggawa saboda ta zubar da jini sosai ajiyar zuciya yace  alhmdllh cikin jikinta fah?" Girgiza kai Dr Saleem yayi yace  saidai muyi hqr wannan ya lalace muyi addu'ar Allah ya kawo wani me albarka wasu hawayene suka zubo masa yace  shikenan tayimin sanadinsa ya zube dafa kafadarsa yayi yace  karka damu zaa samu wani da wuri bamuda lkcn wannan yanzu jini muke buqata hanunsa ya miqa masa yace  ka diba wanda zai isheku janshi yayi suka nufi Lab din cikin saa jinin nasu iri dayane zama yayi aka dabe leda biyu sannan suka nemi daya aka siya suka fita har dakin yabisu har yanzu tana kwance kamar gawa Dr Saleem ya daura mata jinin nurse din dake kula da ita ce ta kalli Umaimah ta kalli Hameed tace  yallabai qanwarka ce ko matarka?" Dr Saleem yace  nima abinda ke raina kenan wannan aikin mijine yallabai samada shekara ashirin nake aikin kula da lfyr iyalan Alh Adamu Hameed Shuwa a tsayin shekarun nan Umaimah autar Hajiya ce qanwa a gurinka amma kuma naga wani baqon lamari tsakanin jiya da yau"



Lumshe idonsa yayi ya kwanta a gadon dake facing din na Umaiman ya zuba mata ido yace  qanwata ce kuma matatace iyakar abinda zan iya fada muku kenan" murmushi nurse din tayi tace  kamar ku kadai ta Isa ta bayyana hakan..." banko qofar da akayi ne yasasu miqewa da sauri a tsorace ya nufi gadon da Umaimah ke kwance ya nuna Sadiya dake shigowa da hanu yace  kada ki qaraso nan ki tsaya anan wlh idan kika bari na waiwayoki zakisha mamaki idanma baki sani ba ina qara sanar dake Umaimah matata ce ta sunnah wacce take iya dauke lalurata Sadiya kiyi a hankali kada ki dauki haqqin marainiyar Allah batajiba bata gani ba wlh batada laifi saboda itama batasan da aurena akanta ba....



 Ina ruwana Hameed kai wannan ta shafa cin amana ba ni zakuci amana saboda kai tsinanne ne mayaudari maci amana azzalumi ni zakaci amana ka fakemin da wata qaryarka wai matarka ce to na rantse da Allah ba matarka ba ko uwarka ce saina kasheta saidai Khadijah ta dawo duniya ta haifi wata kuma kaima saika tafi inda ta tafi..." Zabura tayi a guje ta nufi gadon Umaiman yayi wani tsalle ya tareta tare da riqeta ga dukkannin qarfinsa ya hankata baya ta fadi Tim a qasa kafin yayi wani yunquri ta kuma tasowa ta fakaceshi ta haye ruwan cikin Umaimah shima kanta yayi a guje ya tunkudata qasa ya zare belt din wandon jeans dinsa yace  wlh kika qara tabata sainayi miki abinda bantaba yimiki ba kashe yar mutane kikeson kiyi Sadiya me tayi miki wanne irin haukane wannan kawai don takasance matata to ki sani aurena da Umaimah hadin Allah ne haukanki bai isa ya rusheshi ba abinda yasa na boye aurannan kenan saboda nasan ke mahaukaciya ci shigowar Hajiyansa ne yasashi yin shiru da bakinsa gadan? tayo kansa kafin ya ankara yaji ta daukeshi da wani gigitaccen mari ya dafe gurin da sauri ya dago kansa yace  Hajiya... sake zabga masa mari tayi tana kuka tace.



 dama abinda yasa ka dage sai anbaka ita kenan Hameed irin taka amanar kenan me yaja hankalinka harka lalata tarbiyya marainiyar Allah na tabbata Umaimah bazata taba banzatar da tarbiyyar da kayi mata ba saidai kai ka banzatar da taka itama ka lalata mata tata meye ribarka Hameed qanwarka ka lalata harda ciki Innanillahi wa innah ilaihir raji'un wannan wacce irin baqar rayuwace wacce irin qaddara ce Hameed da kanka da kanka ka ketama Umaimah haddi ka cucemu Hameed kaci amanar maraici bazanyi maka baki ba amma da sannu zaka girbi abinda ka shika tunda ta fara mgnr kansa na qasa harta gama ta juya ta nufi gadon da Umaiman takekai ta ruqo hanunta cikin tausayawa tace  Allah ya isanki Umaimah Allah ya isar miki miqewa Sadiya tayi ta kalleshi tace  zaka dawo ka iskeni har gda wlh saidai koni ko kai azzalumi


Yanajinta amma bai iya tanka mataba harta fice zuciyarsa mugun tafasa takeyi yasan duk bayanin da zaiyiwa Hajiya bazata saurareshi ba saboda haka yaja jikinsa ya fita ya zauna a kujerar dake qofar dakin, daidai lkcn da Umaimah ta bude idonta ta saukeshi akan Hajiya ajiyar zuciya Hajiyan tayi tace  sannu kinji Umaimah daga Mata kai tayi cikin sarqewar murya tace  Hajiya ki tafi dani gdanki Aunty Sadiya da Uncle zasu kasheni wlh Hajiya kasheni zasuyi kama hanunta tayi tace  wa ai dama kin gama zaman tsinannen gdannan ni dama tun farko banso zamanki ba dandai wannan azzalumin ya nace ne kuma Daddyn ku ya goya masa baya yanzu ga abinda gari ya waya kwallar dake zubo mata Hajiya ta share mata tace  kiyi hqr wlh saiya gane kuransa wannan ai zalumci ne shekaran jiya yaje yake fadamin wata shashashar mgn saboda Daddyn ku yace yabarki ki fitar da miji bayan Daddyn ku ya tashi yake cemin wai yayi miki miji ashe abinda yake nufi kenan Allah ma ya rufa mana asiri da cikin ya zube da munga ta kanmu don wannan me raayin riqau din ba bari zaiyi a zubar dashi ba macuci kawai



Abinka da zuciyar mace duk saitaji babu dadi aibata Uncle din da Hajiya takeyi lumshe idonta tayi daidai lkcn daya dawo dakin yace  Hajiya ta farka ne?" Tsawa ta buga masa wadda tasa Umaima bude idonta tace  ban sani ba dan iska mara imani ubanka zakayi mata idan ta tashin kaga Abdulhameed idan baka fita daga rayuwar Umaimah ba wlh saina sallama ka... kallonta Umaimah tayi taga yanda yake zubar da hawaye tace  Kayy Hajiya kibari don Allah kinga fah kuka yake don... bige bakinta Hajiya tayi tace  eh lallai gskyr hausawa da sukace baa dan iska daya wato ke har tausayin wannan annamimin bawan kikeyi ko to zan qyaleki dashi idan ya gama daibe albarkar jikin naki a banza kya nemi tudun dafawa kuma wlh kaji na rantse saikayi dana sanin abinda ka aikata tunda kaci amana ka rubuta ka ajiye amana sai tacika"


Bai iya cewa da Hajiyan komai ba sai gaban Umaman daya matso ya kamo hanunta doke masa hanu Hajiya tayi tace  kul baka kiyayeni ba shashasha kawai babban kawai yanzu Hameed badon Allah ya duba maraicin yarinyar nan ya kawo shegen cikinnan daka kunsa mata ya zubeba daya zamuyi kenan to wlh ka fita daga idona na tsani halinka Hameed na tsani mutum maci amana baka moreba Hameed" bazai iya jure kalaman nata ba saboda haka ya juya har yakai bakin qofa ya tsaya yace  laifi nane dana boye muku gsky tun farko da ace na fada muku Umaimah mata tace da baku zargeni ba nasani Hajiya dole dama zan fuskanci wannan matsalar tunda nakasa hadiye qwalamata na sauketa akan Umaimah a lkcn da yake bai kamata ba kamata yayi ace na sanar daku matatace kafin wannan lkcn amma duk da haka inaso dake da Umaimah da Sadiya dama duk wanda yake zargina ya sani niba mazinaci bane Hajiya baki haifi fasiqi ba bantaba shuka a haramtacciyar gona ba kuma banacin itaciyar da Allah ya haramta min Hajiya koda ace ma zina nakeyi da Umaimah wannan ta faru yakama ace kuyimin uzuri nima dan Adam ne ba waliyyi bane ni inada buqatar inda zanke zuba ruwana idan na tara tun farkon aurena naso hana Sadiya aiki kukace ban isaba nasha kawo muku matsalata kuma kin kasa yimin maganinta sau nawa nazo nace muku inason qara aure amma saiku hanani kullum burinku na farantawa Sadiya wacce nine na daukota na kawota cikin family dinmu babu ruwanku da matsala babu ruwanku da damuwata Hajiya nayi hqr shekara bakwai Ina fama da matsala daya a halin inada wata matar bayan ita to me kikeso inyi idan ban nemi haqqina ba a gurin Umaimah shekara biyar tana matsayin matata ina rainonta Hajiya ko tari nake a asusun qasa yaci ace yayi cikar da idan na fasashi zai bani abinda nakeso Hajiya nasha fada miki Umaimah tanada miji kina daukan zancena wasa to ba wani bane mijinta nine matatace"



Yana fadin haka ya juya ya fice tare da jan qofar da qarfi a mugun fusace ya dauki motarsa ya nufi gdansa yana zuwa yayi parking ya nufi cikin gdan tun tsayawar motarsa tajishi saboda haka yana shigowa ta tareshi da bala'i tace  ai dama nasan dole ka dawo fasiqi la'anallahu wanda baisan Allah ba ka shammaceni Abdulhameed bantaba tunanin haka daga gareka ba saboda kaikam kwai dan akuya.... bata ida qarasawa ba ya dauketa da mari ta dafe gurin da sauri tace  kan ubancan ni ka mara Hameed tabdi wlh ka mari bala'i na rantse da Allah saika gwammace baka sa hanu ka mareni ba ihu kwarto jama'a kuzo ga kwarto Allah ya tsine maka Abdulhameed Allah ya isa tsakanina dakai azzalumi maci amana kisa tsaf saina kashe shegiyar yarinyar nan saidai idan bazata gdannan ba murmushin takaici yayi yace.


 To dama wanne tsautsayine zai dawo da ita ta zauna dake itama ta samu yanci bautar da tayi miki a bayama ta rainon yayanki da kula miki da gdanki kina gantalin yawon aikin banza ta isa yanzu lkcn kula da mijinta ne itama da ita ta shayar dashi farin ciki tayi masa maganin matsalarsa dake kika kasa ta bashi lkcn da kika kasa bashi kinga dama jinin dake yawo a jikinta shine a jikina ita zata iya dani tunda irinmu daya bazata gaza kamar yanda kika gaza ba tana da dadi sosai" yana gama fada Mata ya shige dakinsa ya datso qofar yanajinta tana dukan qofar kamar zata balleta tana kiran sunansa harda na iyayensa tana qare masa zagi tare da tsinuwar diban albarka a haka yaran suka shigo gdan driver yaje ya daukosu suna shigowa dakin Umaimah suka nufa suna kiran  Aunty mun dawo zo kiga assignment dinmu ki kawo mana dakin ta nufa kamar mahaukaciya ta finciki charge dake jikin surket ta rufesu da duka kamar Allah ya aikota tana zaginsu tana fadin  dagaku har uban naku kutumar ubanku zanci ita ta haifamin ku tsinanniyar yarinyar da take neman rabani da ubanku to wlh duk shegiyar yarinyar dana sakejin ta kiramin sunan yarinyar nan sainaci wancan kwarton mazinacin fasiqin uban naku" yanajin irin tujarar da takeyi yasan duk dan ya kulata ne don haka ya bawa banza ajiyarta.



Sai yamma liqis ya fito daga dakin yana daura agogo bata parlourn sai yaran suna zaune sai matsar hawaye sukeyi Nihal ce ta taso ta rungumeshi ta sake fashewa da kuka tace  Uncle me Aunty tayiwa Mom take zaginta kuma yau da safe bata bamu abinci ba da zamu tafi islamiyyah sai bobbo da biscuit Uncle yunwa mukeji Maliha har kuka ta rinqayi a makaranta saida Mu'allimah ta siya mata cheese sannan tayi shiru" ransa ne yayi mugun baci wai kamarshi ace yayansa suna fita basu karya ba kawai saboda sakacin uwarsu kama hanun yaran yayi yace  kuyi hqr Auntynku batada lfy tana asibiti kuzo muje kuganta sai kuci abinci acan" murna suka hauyi da tsalle da kansa ya cire musu kayansu yasa musu wasu ya jasu suka fice daga gdan suna zuwa asibitin ya nuna musu dakin suka shiga da gudu lkcn an cirewa Umaimah roba ta biyu ta jinin tana zaune ta jingina da pillow da gudu suka nufeta suna murna suna tsalle itama taji dadin ganin yaran saboda ta saba dasu koya ta yini bata gansu ba sai taji babu dadi haurawa sukayi saman gadon suka rungumeta Maliha tasa kuka tace  Aunty shine jiya Uncle ya daukeki kika tafi kika barmu kikaqi dawowa kiyi mana break yau sai haka muka tafi bamu karya ba nayita kuka a makaranta inajin yunwa Nihal ce me wayo tace  Aunty kin rame kinyi fark meye yake damunki aka kawoki asibiti? murmushi tayi vta shafa kansu tace  banida lfy ne amma naji sauqi da ganinku kunajin yunwa ko?" Daga Mata kai sukayi tace  no wonder indai yarana sunajin yunwa Ina ganewa Hajiya dake zaune tana kallonsu tana murmushi tace  kaji yan jakar uba ina iyayen naku da suka barku da yunwa kawar dakai Umaimah tayi tace  mudai ki bamu abinci yarana suci Hajiya idan sunci sayi miki bayani Nihal ce tace  mu Mom dinmu bata sonmu yau ma duka tayi mana saboda mun tambayi ina Aunty


Daidai lkcn ya turo qofar ya shigo tare da sallama dago kanta tayi da sauri idonsu ya sarqe guri guda yanayi mata kallonsa me narkar da zuciya murmushi yayi mata tare da ajiye kayan daya dauko mata da shopping din da yayo yace  Hajiya sannu da qoqari yame jikin?" Ko kallonsa batayi ba bare yasa ran zata amsa masa abincin ta zubo jallop din shinkafa ce data wadatu da alayyahu da kifi banda sai qamshi takeyi ta miqawa Umaimah ta karba tare da zaunar da Maliha ta fara basu abincin a baki sunata zuba mata santi itadai batace musu komai ba saboda yanda takejin qwayar idonsa na yawo a jikinta muryar Hajiya ce ta katseta tace  idan kaga dama kaje Daddyn ku yana nemanka yanzun nan ya fita zashi gdanka amsawa yayi da  to ya miqe yace bari naje na biyasu kudinsu na dawo dakatar dashi Hajiya tayi tace  aa aikai ka gama aikinka saura namu ubanka ya biya komai" dagowa yayi da sauri ya kalleta yace  amma Hajiya..." Dakatar dashi tayi da cewa  karkace min komai Hameed wlh da zaka yarda ma daka daina zuwa inda nake saboda idan na ganka jinake kamar na kasheka






*UMMUH HAIRAN CE...
'



* ( _Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers)_



*GIDAN UNCLE*
( _Love and romantic story_)


*SHORT AND TRUE LIFE STORY*



*MALLAKAR*
=?G? *FAUZIYYA TASI'U UMAR*
*?FAUZAH*



Wattpad=?I?


www.fauzahtasiu41@gmail.com


Alhmdllh a madadina da iyalaina munayiwa daukacin al'ummar duniya barka da shiga sabuwar shekarar gogerioun calendar duk da dai mu munci wata hudu a tamu ta musulumci Allah ya hadamu da alkhairan cikinta sharrikan dake tattare da ita Allah ya kade manasu yanda muka shigeta lfy Allah yasa muga qarshenta lfy idan kuma bamu da rabon gani to Allah ya karbi ranmu muna cikin musulumci muna masu aikata ayyukan alkhairi sannan yasamu a ceton Muhammadur rasulullahi (S.A.W).



*PAGE ELEVEN*



A salube yake kallon Hajiya lallai ta dauki lamarin nan da zafi saboda tunda yake da ita ko baqar mgn bazai iya tuna ranar data fada masa ba amma yau gashi tana neman tsine masa, cikin rashin qarfin gwiwa ya matsa jikin gadon na Umaimah yace  sannu Babyn Uncle ya jikin yanzu inane yake miki ciwo? ya fada yana dora hanunsa a saman kanta ajiyar zuciya sukayi a tare cikin sanyi muryarta tace  da sauqi murmushi yayi yace  ok kuzo mu tafi kada ku dame Aunty kunga batada lfy ko? Nihal ce tace  Mudai anan zamu zauna gurin Aunty da safe ta dafa mana tea tayi mana wanka" Maliha kam kuka tasa wai a dole bazata koma gurin uwarta ba.



Daqyar ya shawo kan yaran suna kuka suna komai yajasu suka fice daga dakin itama Umaimah gawayen ta share batason ko kadan taji yaran suna kuka jinshi take har cikin lakarta, Hajiya kam haushine yakusa kasheta ita a tunaninta mgnr data fadawa Hameed dince tasa Umaimah kuka.



Kwanansu daya a asibitin yazo da safe dazai tafi aiki ya dubata ya jima sannan ya tafi office a CBN Kano yake aiki, bayan tafiyarsa babu jimawa Dr Saleem ya basu sallama suka tafi gda yayar Hameed Aunty Zarah tazo gdan saboda Hajiya ta kirata ta zayyane mata komai suka hadu a parlour sukayita Allah wadarai da abinda Hameed yayima Umaimah abin takaicin harda Daddy shima ya biye musu yace  wlh badon Hameed dana bane babu yanda zanyi dashi dasai nayi qararsa an fiddawa marainiyar Allah haqqinta jiya fah tsabar ya rainamin hankali na kirashi inayi masa fadan kuskuren da yayi sai cemin yayi shifa baiyi wani laifi ba Umaimah matarsa ce laifinsa daya daya boye mana gsky danaji rainin hankalin nasa yayi yawa sai nace ya tashi ya bani guri kawai saiya fashemin da kuka waishi ba mazinaci bane idan bamu yarda da abinda ya fada mana ba mubashi dama ya gabatar da wasu daga cikin shaidun da suka shaida daurin auransa da Umaimah fada na haushi dashi kamar zan cinyeshi amma bai fasa fadamin ba shifa matarsa yayi mu'amala da ita ba wata ba har yana neman yimin rashin kunya wai gobema idan yana buqatarta zai nemeta yayi duk abinda yaga dama da ita tunda shi yasan ba zina yakeyi ba saboda haka Hajiya sai kinsa tsaro sosai akan yaronnan saboda idan kikayi sake zaa samu matsala tabbas shima mgnrsa abar dubawa ce saboda haka zanyi binkice sosai kuma nace ya gabatar min da shaidunsa nanda kwanaki uku idan ba hakaba zan sauki matakin shari'a akansa



Yana fadin haka ya tashi ya nufi samansa itama Umaimah miqewa tayi daga jikin Hajiya ta shige dakin da idan tazo take zama a ciki ta kwanta itadai zuciyarta babu dadi kwata? batajin dadin yanda suke aibata Uncle din nata saboda koba komai yayi mata abubuwa da yawa da bazata iya mantawa dashi ba, tana wannan tunanin

Join Our Groups
16, January 2025
Abdullahi

Mun bude sabon Whatsapp group na cin duri Mai suna Sirrin Dadi idan ki/ka na bukata kayimin magana ta Whatsapp number 07032700869

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login