Showing 81001 words to 84000 words out of 135422 words

Chapter 28 - Gidan Uncle Complete Hausa Novel

Fauzah   

06 Oct 2024

49819

wani bacci ya dauketa itama yarinyar numfashinta saida ya canza saboda jin dumin uwarta data yini tana kukan nema ko madara taqisha saidai zamzam da ake bata.



Alhmdllh jikin Umaimah yana sauqi sosai amma fah shi Hameed abun baa cewa komai saboda ko motsa hanunsa baya iyawa komai saidai ayi masa da na'ura ga wani qarin tashin hankali penis dinsa data miqe tun ranar da abin ya faru bata kwanta ba tun Daddy yana ganin kamar sauqi zaizo har ya sallamawa ubangiji komai saboda baya hangen wani sauqi a ciwon Hameed.
Kwanaki bakwai din a asibiti sukayita saboda dinkin Umaimah daya rikice sosai saida aka tsaya a kanta kana aka samu ya koma normal suka koma gda ranar da suka koma akayima yarinyar hakika raguna uku Daddy ya yanka mawa amaryarsa Shurafah da Sa yasa akayi sadaka duka a maqota ana fada musu haihuwar babu wanda yasan abinda ake ciki aikuwa a ranar akayita tururuwar zuwa tayasu murna saboda kowa sanin da yayi Umaimah matar Hameed ce saboda haka babu wanda yasan matsayin yarinya Shurafah sai su isu.



Kayan da Daddy yayima Umaimah da Shurafah ya bawa kowa mamaki saboda babu wanda yayi tunanin yanda ya dauki zafin nan zai siyawa maijego da jaririyar ko pant, sai dare da mutane suka lafa Daddy yasa aka kira masa Umaimah gata ga Hajiya ga Aunty Zarah ga Aunty Jameelah ga Kaka duk a gurin Shurafah tana tsakaninsu sai yawo take tsakanin dangin uwa da uba Allah Sarki shima shege me asali dan gata ne gadone kawai bashi dashi yanda ake lelen yarinyar har kuka yakesa Umaimah tana nadama da danasanin abinda suka aikata da Uncle din nata musamman idan ta tuna halin da yanzu haka Hameed din yake ciki na rayuwa ko mutuwa.



Daddy ne ya katse shirun ta hanyar bude taro da addu'a ya dubi Umaimah yace  Baby ba komai yasa na taraku ba sai akanki kinga dai abinda ya faru tsakaninki da dan'uwanki kuma kinga irin matsalolin da suka rinqa fullowa qarshe dai ga ribar abinda kuka aikata nan kun samarwa zuri'ar Alh Abdulhameed Yauri Shuwa babu yanda zamuyi daku a dan qaramin family dinnan namu tunda daga ke harshi babu wanda zamu kora amma dai kun sani bakuyiwa zuri'arku da yarku adalci ba musamman keda kike mace yakamata ki nuna kedin mace ce wacce take fatan samun zuri'ar da zatayi alfahari da ita amma qarshe sai kika bige kika lalace wajen biyewa namiji da son zuciyarki saboda rashin tunanin me gaba zata haifar todai yanzu ga abinda gari ya waya yanan Allah ya sani munyi iyakar qoqarinmu na ganin kun kasance iyaye ababan koyi ga yayanku amma hakan yaci tura Umaimah dagake har Hameed nawane babu wanda zanyiwa baki saboda haka nidai na yafe muku batamin din da kukayi bada haqqina ba"




Dakatawa yayi yaja fasali kana ya dora da cewa  inayi muku fatan alkhairi a rayuwarku ta gaba sai Abu na biyu kamar yanda al'adata take kuma nayima yan uwanki Zarah da Jameelah lkcn da sukayi haihuwar fari to kema ga mukullin motar ki sannan ki zabi duk qasar da kikeso a duniya zan biya miki keda yarki kuje ku huta"




Tunda ya fara mgnr take wani irin kuka me ban tausayi kukan nata ba qaramin tasiri yayi a zuciyar duk wani wanda yake zaune a gurin ba har saida Jameelah da Zarah suka tayata,
Tsawa ya daka musu yace  banason shirme tanayi kunayi memakon ku rarrasheta sai ku qara turata ke mgn nakeyi miki ki fadamin qasar da kikeson zuwa nayi miki visa da passport zuwanan da sati biyu saboda saura 5 weeks hutu ya qare ki fara attend lectures"



Cikin kuka da rawar murya tace  Saudia Daddy" dagowa dukkansu sukayi suka kalleta saboda basu taba tunanin wannan zabin ba sunyi tunanin zata zabi Turkey ne saboda duk wanda ya kwana ya tashi a zuri'ar yasan burin Umaimah bai wucce taje Istanbul ba amma sai gashi lkcn da damar tazo Mata ta zabi wata qasar daban.
Kafin kowa yayi mgn Daddy yace  meyasa kika zabi Saudi Arabia Umaimah?" Cikin kuka ta bude baki tace.



 Saboda na kusanci ubangiji na na ziyarci kabarin annabi na roqeshi ya roqamin gafarar ubangiji ya yafemin wannan kayan dana daukarwa kaina nasani Daddy na take sani na aikata zunubi mafi girma wanda laifi biyune a duniya yafishi nauyi a mizani shirka da giba Daddy hukuncin kisane akaina ta hanyar jefewa meyasa bazaka kaini a yankemin hukuncin ba nasan zanfi samun sauqi idan na mutu ta wannan hanyar Daddy wanne jin dadi ne ya ragewa rayuwata Daddy da nasan wannan qaddarar tana cikin abinda zai faru dani ta haihuwa ba aure wlh dana roqi Allah na mutu na huta Daddy meyasa Mama batayi barin cikina ba? Daddy me zancewa Shurafah ranar data girma ta tsinci wannan mugun tabon da rudin zuciya yasamu mukayiwa rayuwarta....."




Rufe mata baki Jameelah tayi ta rungume yar uwar tata a jikinta tana kuka tana cewa  kidaina fadar haka Umaimah ki daina roqon ki mutu ke bamu da yawa a zuri'ar mu kuma tun ran gini tun ran zane Umaimah waman qaddarallahu haqqan qadarihi haka wannan mgnr take babu wanda ya isa ya canzata naku dakyau ma tunda kinsan uban yarki kuma ya karbi abarsa kuma yanasonta kuma yar dangi ce qarshen dai abin ace idan mgnr aure ta taso tunda mace ce to koda mutane a duniya ko babu indai muna raye kuma muna haihuwa Shurafah zata auru ko a tsakanin yayanmu....



Sake rungume Aunty Jameelah tayi tana wani kuka mecin zuciyar me imani itama Zarah kwantowa tayi a jikinta itama kukan takeyi tace  mu rufe mgnr nan tsakanin mu kada ta fita waje Umaimah don Allah koba Hameed ne uban Shurafah ba a qaramin family dinmu zamu karbeta mu riqeta saboda bamu da yawa muna buqatar yawaita a duniya abu daya ya rage Daddy kayi ka mayarwa da Umaimah da Hameed aurensu su riqe yarsu cikin aminci da kulawa"




Saurin dagowa tayi ta kalli Aunty Zarah ta girgiza kai tace  na roqeku kubar mgnr nan koda son Uncle Hameed zai kasheni na hqr da aurensa har abada kada kayimin dole Daddy hakan zaisa na rinqa kallon kaina a matsayin marainiya mara gata kuma bazan taba farin ciki a rayuwata ba Daddy bazan boye maka ba na tsani Uncle Hameed...." Ba qaramin girgiza kowa kalmarta ta qarshe tayi ba amma babu wanda yayi qoqarin sake maimata mgnr saboda suna ganin kamar ciwon abinda ya farune yasata furta haka.



Murmushi Daddy yayi yace  Shikenan Uwar masu gda tunda bakya raayin zama dashi babu meyi miki dole amma kinsan aure dolene akanki bada jimawa ba saboda haka zan baki shekara guda ki shayar da amaryarta ki fitar da miji kiyi aure sannan kamar yanda kika zaba zamu tafi Saudi dani dake da Hajiya sai Hameed da zamukai a dubashi acan saboda ciwonsa yafi qarfin asibitocinmu na nan sai kuma Yayarki Jameelah da idan kun gama umararku zaku wucce Turkey ki cika burinki na zuwa Istanbul kafin ki mutu"



Dariya tayi me hade da kuka ta miqe cikin tafiyarta da bata koma Normal ba ta matsa kusa da Daddy tayi kissing hanunsa ta rungumeshi ta kuma fashewa da kuka tana jera masa dubun gdy murmushi yayi yace komai nayima uwata ba faduwa bane fatana dai karta qara irin kuskuren da tayi a baya" jinjina masa kai tayi ya rungumeta yace Allah yayi miki albarka yabaki miji na gari wanda zai riqemin ke amana"



Amsawa kowa yayi da amin Daddy ya sake rufe taron da addu'a tare da yima yarinya Shurafah addu'ar shiriya da kariyar ubangiji kowa ya tashi ya nemi gurin kwanciya inda Daddy ya fice ya koma asibiti gurin Hameed.



Koda suka koma daki Aunty Jameelah ce ta hauta da fada wai bata kyauta ba da tace ta tsani Hameed tanajinta tayi mata shiru taci gaba da feeding din yarta har saida taga ta qoshi ta canza mata Pampers ta kwantar da ita tare da kissing din jajayen lips dinta tace  sleep well my lovely daughter kiyi dreaming dina kinji abin dariya yabawa Jameelah sosai tace  oh ni Jameelatu Umaimah da ya hauka ya qaru wannan ya zakiga hauka gurin uwarki" dariya tayi tace  Allah Aunty bansan haka iyaye sukeji ba sai ranar da Hameed ya tafi da yarinyar nan wlh hankalina gushewa yayi ban iya sanin komai da nayi ba saida aka bani labari Aunty wai dama haka kukeji akan yayanku tab aini wlh babu mai dukar min Shurafah gara ka bugeni daka bugarmin ita dan zan iya rufe idona na ci mutuncin uban kowa"



Dariya sosai Aunty Jameelah da Aunty Zarah sukeyi Aunty Zarah tace  harda ubana ko?" Kunyace ta kamata don tama manta da Aunty Zarah a gurin ta kwanta tace  Allah aunty dan bakisan abinda nakeji bane" murmushi tayi tace  kafin kiji na rigaki ji Umaimah" da haka sukayi bacci.









*UMMUH HAIRAN CE...
'



[1/22, 4:45 PM] UMMUH HAIRAN CE...
'


Ki biya kafin ki karanta idan kinaso ki kira number nan; 09031307566:



*PAGE FOURTY ONE*



Kwanaki bakwai tsakani Umaimah tayi shar da ita baby Shurafah tayi wayonta tayi qiba kalar fatarta kalar fatar iyayenta kamarta da mahaifinta ta fito sosai Daddy ya gama musu komai na tafiya qasar Saudia duk tsayin lkcn nan Umaimah bata taba zuwa ta duba Hameed ba kuma ko a baki bata taba tambayar ya jikinsa ba.



Kwana biyu tsakani jirginsu ya daga qasar Saudi tun ranar da Daddy yace Hameed ya tafi da Shurafah rabon da t???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?a sanyashi a idonta sai yau data hangeshi a zaune saman welchair kansa yayi gefe sai gyara masa kan yakeyi gefe ta koma ta zauna har lkcn tashinsu yayi suka shiga jirgin suka daga zuwa qasa me tsarki itadai bata cewa kowa komai game da Hameed din ba kowa yana jajanta jikin nasa amma banda ita da tayi qasa da kanta ta zubawa yarinyar ido wasu hawaye masu zafi sunabin kuncinta.



Koda suka sauka a filin jirgin saman Saudi Arabia motar asibitin da akayima Hameed boorking ce tazo Daddy da Yusuf suka shiga Umaimah da Hajiya da Aunty Jameelah suka shiga ta masaukinsu suka tafi.



Wani babban hotel ne kusa da harami anan suka sauka Hajiya dakinta daban Umaimah da Aunty Jameelah suna shiga dakin ta kwantar da Shurafah ta shige bathroom ta fara kukan da taketa qoqarin hadiyewa tunda suka taho koda wasa bata taba tunanin jikin Hameed din yayi zafi haka ba tausayinsa ya kara darsuwa a zuciyarta mutum lafiyayye me tashe quruciya da qarfi da mazantaka wai yau shine a kwance haka kamar gawa saidai a kwantar dashi a tayar.



Lallai Allah ya cika me ikon yin komai a lkcn da yaso a hankali cikin kuka ta zube ta dora goshinta saman tiles din toilet din tace  Allah kaji qaina kabawa dan'uwana lfy Allah ka yafe masa zunubansa Allah kada ka kashe Uncle ka mayar min da Shurafah marainiya kamar ni Allah ka tausayawa bawanka me qoqarin tsayawa akan dokokin ka Allah na sani qaddara ce da sharrin shaidan tasa Hameed watsi da umarninka wannan jarabta tayi masa yawa da wanne zaiji"



Ta jima a bathroom din sannan ta fito ta zauna kusa da Shurafah ta daukota ta sanya mata nono ta kuma fashewa da kuka Aunty Jameelah ta dubeta da sauri tace  mene kuma na kuka Baby?"



Dagowa tayi tace  Aunty kinga Hameed fah yanda ya koma aunty anya Hameed zai koma normal kamar da?" Harara ta zabga mata tace  to meye damuwarki da komawarsa kamar da Umaimah na dauka ko babu komai tsakaninki da Hameed yafi qarfin wannan wulaqancin daga gareki Umaimah me Hameed yayi miki da zafi haka da zaki kwana ki tashi ki kasa tambayar iyayensa jikinsa kina ganin hakan daidaine a gurinki Umaimah kina tunanin Daddy da Hajiya basajin zafi da ciwon ko in kula din da kike nunawa dansu gudan jininsu akan laifin daba tursasa ki yayi ba kece kikaba da qofar da hakan ta faru Umaimah ko kina tunanin Daddy da Hajiya zasu soki fiye da son da sukewa dansu na cikinsu? Amsar itace aa Umaimah qaramin misali yanzu ki duba ki gani shekara nawa kikayi kina wahala da Nihal da Maliha kwana nawa kikayi da haihuwar Shurafah amma soyayyar Shurafah ta disashe hasken soyayyar da kika dauki shekaru kina nunawa Nihal da Maliha saboda itadin jininki ce da wani bangare na jikinki aka halicceta balle su da suka dauki shekara sama da talatin da biyar da dansu wacce soyayya zasu nuna miki data dara ta dansu? Ki fadamin ita Umaimah"



Ta qarashe mgnr tana matsawa kusa da yar uwar tata ta kamo hanunta tace  amma saboda tsabar rashin kunya da tsageranci da cin fuska kika iya duban tsabar idonsu kika iya furta musu bazaki qara zaman aure da dansu ba kuma kin tsaneshi hmn yarinya kiyi gaggawar sake tunaninki wlh mutanen nan basu cancanci wannan sakayyar daga gareki ba Umaimah kinsani Hameed yana sonki bazai iya rayuwa babu keba kamar yanda yasha fadamin, ko kinsan yasha zuwa ya fadamin irin wulaqancin da kikeyi masa da tsanar da kike nuna masa Umaimah Hameed yasha zuwa har Damaturu yasani a gaba ya rinqa yimin kuka yana fadamin zuciyarsa zafi take masa a duk lkcn da yaso ganinki ko yaso jin muryarki yazo gdan kikaqi yarda ku hadu ko ya kiraki a waya kikaqi amsawa Umaimah ko kinsan Hameed yasha fadamin sonki shine zai kasheshi ko kinsan a ranar da abin ya faru yana fitowa daga gdan Daddy ya daga waya ya kirani yake fadamin zuciyarsa fashewa zatayi Ina bashi hqr naji ya saki wata qara tare da kiran sunanki shikenan har yau tsayin sati biyu da kwanaki uku baisan kansa ba"....



Ajiyar zuciya ta kumayi kana ta dora da cewa  bakiyi kuka ba Umaimah sai ranar da kika daura aure da wani ba Hameed ba aka kaiki gdansa dare yayi ya shigo yayi mu'amalar aure dake minti biyu ya sauka ya bingire ya fara bacci bai farka ya sake nemanki ba saida safe ki nemeshi yace kin cika karuwanci da takura shi ya gaji to a sannan ne zaki fara kukan nadamar gujewa namiji daya tamkar da dubu namijin da mace da yawa take burin mallakar irinsa kuma namijin da bazaki qara samun irinsa ba a duniya ke bari nayi miki kalmar qarshe Umaimah wallahi tallahi billahillazi La'ilaha illah huwa bazaki iya zama da kowanne namiji ba sai Hameed shine ya fara saninki dashi kika saba kuma shine daidai dake saboda danshi kadai aka halicceki kamar yanda yasha fadamin"......



_Kuyi manege da wannan_ =?H?






*UMMUH HAIRAN CE...
' [1/22, 8:35 PM] UMMUH HAIRAN CE...
'


Ki biya kafin ki karanta idan kinaso ki kira number nan; 09031307566:



*PAGE FOURTY TWO*




Kuka ta sake saki me ciwo tana girgizawa Aunty Jameelah kai, sake Mata hanu tayi tace  bazanyi miki dole ba kamar yanda Daddy yayi alqawarin bazaiyi miki dole ki yarda ki auri Hameed ba amma ina tausayawa rayuwarki a gdan wani ba Hameed ba domin shine mahadinki shine abokin rayuwarki kuma shine qaddararki ko ki yarda ko kada ki yarda Hameed nakine kema tasace kamar yanda yasha fadamin danshi kadai aka halicceki saboda haka kiyi gaggawar dawowa hayyacinki kafin kiyi abinda zai zame miki ciwo har qarshen rayuwarki



Tana fadin haka ta dauke Shurafah a jikin Umaimah ta cire mata Pampers tayi mata tsarki karbarta Umaimah tayi ta fita zuwa dakin Hajiya ta bude ta shiga da sallamarta tasa kai ta shiga turus taja ta tsaya ganin Hajiya zaune gefen gado ta hada kai da gwiwa tanata gursheqen kuka.
Jiki a matuqar sanyaye ta qarasa ta tsugunna a gabanta ta kwantar da kanta a cinyar Hajiya kawai itama ta saki kukan da sauri Hajiya dago tace.



 Ke meye hakan Umaimah?" Cikin kuka tace  kiyi hqr don Allah Hajiya insha Allahu Uncle zai samu lfy zai warke kuma zaici gaba da rayuwa cikin farin ciki kamar baya don Allah Hajiya ki daina kukannan banaso ya kikeso muyi keda zaki rarrashemu" shafa bayanta Hajiya tayi tace  na fidda rai da rayuwar yaronnan Umaimah koda ya farfado idan yaji hukuncin da kika yanke na bazaki qara rayuwa dashi ba zaiyi mutuwar dungurungum saboda nasani kece zuciyarsa Umaimah bazai iya rayuwa babu keba..."



Zamowa Hajiya tayi tayi knilling a gaban Umaimah ta ruqo hanunta tace  Don Allah badon niba Umaimah ki taimakeni ki yarda ki rayu da dana kece cikon farin cikinsa Umaimah zan rasashi idan kikaqishi don....." Saurin rufewa Hajiya baki tayi cikin kuka tace.



 Kada ki qara hadani da Allah Hajiya ko baki hadani da Allah ba nasani kuma na amince Yayana Abdulhameed mahadin rayuwata ne bazan iya rayuwa babu shiba bansan inason Uncle ba kuma bansan ciwonsa nawa ne ba sai yau dana ganshi Hajiya na shirya sake komawa qarqashin inuwar auran Uncle Hameed indai wannan shine zaisa yaci gaba da wanzuwa cikin farin ciki...."



Wata runguma Hajiya tayi mata tana kukan dariya tace  na gde miki yata Allah yayi muku albarka Allah yabawa dan'uwanki lfy kuci gaba da qawatamu da salon qaunarku mai ban sha'awa" murmushi tayi tace  ina Daddy Hajiya?" Ajiyar zuciya tayi tace  yana Riyadh gurin Hameed shida Yusuf"



Sunkuyar da kanta tayi tare da qurawa Shurafah idon har yanzu idan ta kalli Shurafah sai taji tsanar Hameed a ranta amma tayi alqawarin kankareta a zuciyarta saboda cikar farin cikin iyayensu miqewa tayi a salube ta kwantar da Shurafah tace  na kawo miki ita ta tayaki hira inason zuwa harami ne Hajiya" murmushi tayi ta matsa kusa da Shurafah tace  ja'ira mekan qwanqwalati bata da aiki sai bacci kamar kasa nidai bansan ina kika debo ragwanta ba iyayenki duk ba ragwaye bane" murmushi Umaimah tayi tace  kun daifi kusa ta kwana tana maki waqa itama dariya Hajiya tayi tace  to ya zanyi hausawa sunce abin cikin qwai yafi qwai dadi ai Allah ya taimaka saikun dawo



Amsawa tayi da amin sannan ta fice taje ta tarar da Aunty Jameelah har ta shirya suka fito da qafa suka tattaka har masallacin harami suka fara gabatar da ibadarsu kamar kowanne musulmi itadai Umaimah rasa abin

Join Our Groups
16, January 2025
Abdullahi

Mun bude sabon Whatsapp group na cin duri Mai suna Sirrin Dadi idan ki/ka na bukata kayimin magana ta Whatsapp number 07032700869

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login