Showing 126001 words to 129000 words out of 135422 words

Chapter 43 - Gidan Uncle Complete Hausa Novel

Fauzah   

06 Oct 2024

59883

fito ya zauna a dinning ya fara break yana raba idon ganinta amma shiru can yaji murda handle dinta ya zubawa qofar ido ta fito cikin shigarta ta alfarma data qara fito da asalin kyawunta sanye take da wata yaluwar atamfa dinkin doguwar riga data baje sosai a ciki ta yafa blue din mayafi takalmi da jakarta duk blue sai wata siririyar sarqa data sanya a wuyanta ta gold wadda kyautar Sulaiman ta haihuwar twins kudin sarqar ya haura million biyu amma Idan ka ganta a ido zaka dauka batafi dari biyar ba saboda sirantarta ta zauna dass a wuyan Umaimah da zobunan sarqar suma sirara guda biyu sai agogonta shima gold kai iya haduwa ta hadu Hameed kusan qwarewa yayi saboda kallonta ta zuba masa ido ta cikin siririn glass din dake idonta shima ita yake kallo ta rungume Daddy tace  morning lovely" yayi kissing dinta yace  morning lovely daughter" ta sakeshi ta sake rungume Hajiya tace  ina fatan uwata abar faharina ta tashi lfy" dariya Hajiya tayi tace  qlau yar albarka yau sai skull kenan?"




Ta gyada kai ta dagawa Hameed hanun tace  Hi brother" tana fadin haka ta juya ta fara tafiya da sauri tace  nayi let Hajiya bazan samu karyawa a gdannan ba Allah yasa ma Hassan ya wankemin motar ji tayi yace  jirani nazo na kaiki tayi kamar batajishi ba Daddy ne yace  bakiji ba yayanki yana miki mgn uwata" tsayawa tayi cike da takaici ya miqe ya nufi dakinsa ya dauko mukullin da wayoyinsa ya fito suka jera suka fito abin gwanin sha'awa ya bude mata ta shiga shima ya shiga yaja suka fita daga gdan suka dauki hanya a hankali yake tafiya cike da nishadi ya sanya waqar R-kelly yana sauraro zuciyarsa na raya masa yayi mata mgn amma girman kai da izzah irin tasa ya hanashi waishi jira yake tayi masa mgn haka har suka isa harabar mkrntar yayi parking a wani guri me yalwar bishiyoyi da furanni ya kalleta sosai yace  qarfe nawa zaku fito?" Batare da tunanin komai ba tace masa  hudu" tana bude qofar ya ruqo hanunta yace  ki kula da kanki zan dawo na daukeki" bata bashi amsa ba sai fita da tayi ta nufi Hall din nasu yabi bayanta da kallo tun kafin ta ida shiga suka hadu da Prof Khair wani balaraban Qatar ne da yazo Reasech a skul din kusan tare tasanshi da D.S yana ganinta ya tsaya yanayi mata murmushi itama murmushin tayi ta qarasa suka gaisa sosai ya tambayeta yara tace suna qlau yaci gaba da janta da hira har suka isa Hall din ta shiga shikuma ya wucce apartment din da yake duk wannan abun akan idon Hameed ya hadiya sosai  wato har larabawa take kulawa" ya fada yana bawa motar tasa wuta ya juya ya fice ya nufi sabon gdan da yake ginawa a Ribadu road Hameed kwai dan wawuya duk gdajansa hudu ya siyar idan baku manta ba yana da gda a Nassarawa G.R.A inda Sadiya ta zauna sannan yanada wanda ya ginawa Umaimah a Zingeru road sannan wanda ya siya Mata a Farawa layout sukayi zaman daduro still wanda ya gina na qarshe me part biyu da suka zauna ita da Salma amma duka ya tattara ya siyar ya zuba kudin a gidan gonarsa sai yanzu da akace masa mijinta ya rasu yazo yasai wani katafaran floot a Ribadu road ya wawaki gini na uban ubansun ya fara batare da iyayensa ma sun sani ba saidai ya turowa Yusuf kudin shikuma ya bawa yan kwangila aikuwa aikin yana tafiya sosai duk da bashi da burin idan sunyi aure su zauna anan California zai tafi da ita tayi master da PhD dinta acan in yaso idan wani Abu ya tashi sunzo sake sauka anan.



Yaje ya yini sur a gurin aikin ginin qarshe uku da rabi ya koma makarantarsu yana zuwa ya kirata tana ganin kiran taqi dagawa Saudat Alfah ta kalleta tace  ba wayarki ake kiraba" tabe baki tayi tace  itace mana niyyar dagawa ne banyi ba" daukar wayar Saudat tayi har yanzu sunan sa haka yake  Bloody" tayi murmushi tace  Allah sarki masoyan asali Umaimah jinki kawai nakeyi wlh bazaki taba iya rabuwa da Hameed ba kada ki wahalar da shari'a ki bada kai kawai bori ya hau dama rabon twins ne ya rabaku kuma rabon wasu da bamusan adadinsu ba ya kashe D.S saboda haka kiyi hqr kawai ki rungumi qaddara wlh a duk duniya baki da masoyi saman Hameed"




Daga mata hanu tayi ta miqe tace  inma kwangila ya baki to kice masa nafi qarfinsa yanzu idona yayi budewar da bazan iya hqr da mulkin kama karyarsa da son kansa ba nariga na shaqi iskar yanci D.S ya nunamin yancina ya bayyana min cewa zaman aure ba zaman bauta bane zamane na yanci kuma rayuwace me dadi a cikinsa inason Hameed nasani shidin wani bangare ne na rayuwata amma bazan iya sake rayuwar aure dashi ba keni auren ma gaba daya ya ficemin a kaina bana sha'awar sake aure a rayuwata wlh" miqewa Saudat tayi suka jero suka fito tana tafe tana rangaji kamar bishiyar gamji harta qaraso inda ta hangi motarsa sukayi sallama da Saudat ya bude mata ta shiga yaja suka tafi yanajin kishinta a ransa baisan sanda yace.




 Waye wanda kuka jera dashi dazu kuka shiga ciki dashi" batare da damuwar komai ba tace  abokin mijina ne" ya kalleta da sauri yace  abokin mijinki ince dai ba mijin naki bane?" Tabe baki tayi tace  ba abin mamaki bane idan kaji cewa ya zama mijin nawa ma..." wani uban birki daya taka shine yasata saurin dagowa tayi baya tayi gaba kawai saita fada jikinsa ya sauke wata ajiyar zuciya me qarfi yasa hanunsa ya maqaleta daga ita har shi sunajin wani irin yanayi a jikinsu janyewa tayi da sauri ta koma ta zauna ya sauke numfashi ya bude idanunsa akanta yace.




 Don Allah kiyi hqr da wasannan da kikeso muyi wahala zansha ki bani dama ta qarshe bloody idan har nayi wasa da ita kiyimin duk hukuncin da kikaga ya dace kada ki tausayamin amma yanzu ni abin tausayi ne a gurinki saboda zuciyata takasa hqr dake nayi iyakar qoqarina naga na cireki a raina amma na kasa nayiwa Daddy mgnr aurena dake tun jiya yace bazai miki dole ba sai abinda kikeso zaiyi miki har yana gargadina kada na takura miki"



Kallonsa tayi da wani irin salo na baka da wayo tace  aure kuma" dagowa yayi yace  Eh haka nace" dariya tayi sosai tace  tab kana ruwa iya wuya kuwa" daga haka bata kuma cewa komai ba shima baice ba yaja motar suka tafi gdan gonarsa yakaita yayi horn megadin ya bude ya shiga gurin ya girma sosai ya qawatu bangaren kaji daban na kifaye daban na gigs daban na shanun madara daban da bangaren tsuntsaye irinsu talo? dawisu da jimina abun dai baa cewa komai.
Wata qofa ya bude ya shiga ya tsaya yana jiranta amma sai yaga ta cake a waje ta tsuke fuska sosai ta yanda saida yaji gabansa ya fadi ta motsa dan qaramin bakinta tace  bance da Hajiya zan biyoka muzo nan ba saboda haka kazo ka mayar dani gda ko na fita na nemi abin hawa




Murmushi yayi ya fito ya janyo qofar ya rufe ya qarasa kusa da ita yace  kina tsoron kada nayi miki fyade ko? Hmn itadai batace komai ba suka koma suka shiga motar suka tafi gda suna zuwa ta bude zata fita ya ruqo hanunta ta juyo idonsu ya hadu tayi saurin janye nata yace  ki daina jamin aji Umaimah ni ba wanda zaki jawa aji bane ko yau kika amince min gobe zaa daura aurenmu so nakema naje nayi miki VISA saboda nagaji da zaman kadaici wlh kuma duk saboda kene bloody bazan iya zama da wata mace ba bayan ke idan har na rasaki to na hqr da aure har abada balle ma bazan rasaki ba wannan karon wancan ma qaddara ce ta rabamu kalaman nasa mugun qonanta zuciya sukeyi saboda haka ta fizge hanunta ta shiga cikin gdan a fusace.........







*UMMUH HAIRAN CE...*
' [2/4, 9:05 AM] UMMUH HAIRAN CE...
'

























Yanda Hajiya taga ta shigo gdanne yasata zuba mata ido sannu kawai tace mata ta bude qofar ta shiga daidai lkcn dashi kuma ya shigo gdan shima baiyiwa Hajiyan mgn ba ya shige dakinsa ya kwanta ya lura wahala zaisha sosai da Umaimah tunda ya fahimci babu digon tausayinsa a qwayar idonta amma duk da haka zai jure zai gwada tasa baiwar har ya cimma gaci.



Wayarsa ya dauka yayi short write ya tura mata tana zaune a bakin gado tana feeling din yayanta tana kallonsu saqon nasa ya shigo ta dauka ta bude
_Tunda na rasaki Umaimah mace ta fita a raina ki daina jin tsorona wlh ba Hameed din da bane nasamu lfy ki bani dama bloody banason komawa California batare dake ba banajin dadin rayuwa ni kadai bloody inason mu rayu tare yaranmu su rayu a cikin kulawar mu inason twins dina amana tace babansu ya bani su tun kafin a dora masa ajalinsa yayimin kyautarsu tun kafin suzo duniya ki aminci su rayu qarqashin kulawata_




Jikinta ba qaramin sanyi yayi da kalamansa ba wata kalma daya da D.S yayi mata ranar data haifi twince ta fado mata _ nayi farin ciki da haihuwar nan Sweet duk da inaji a jikina bazan rayu dasu ba amma banajin komai saboda Hameed yana raye_


To dama kalamansa abinda suke nufi kenan ajiyar numfashi tayi cikin sanyin jiki da sallamawa rayuwa farin ciki wata kalmar da yake yawan maimata mata ta dawo mata.



_ Umaimatu ina kishinki bana fatan ko Nazir qanina ya riqe hanunki mutum daya tak nake burin bayan bana numfashi ya zama replacing dina Sweet Hameed nake nufi da ace zan iya dana halatta masa ke ina raye amma bazan iyaba course_ _inasonki sonda idan na rayu babuke zan galabaita sweet zansha wahala fiye da wadda Hameed yakeyi saboda ke dalili ni qaramar zuciya ce dani bantaba shiga tashin hankali makamancin wannan ba kiyi hqr kada ki qullaceshi wlh ba laifinsa bane sharrin qaddara ce yanzun wacce ta zama sanadin rabakun tana ina? Tana asibitin mahaukata idan ba saaba ita da hankali har abada itama ki yafe mata duk da nasani Hameed bazai yafe mata ba saboda ta cutar dashi ita duniya qaramin gurine da zaka zo ka taka rawarka ka kauce wani ya taka Umaimah ki yarda da hakan_ _watarana _muma zamu kauce mu rabu rabuwa ta har abada rabuwar da bazaki sake ganina ba _




Wannan kalamai suna dukan zuciyarta dole tayi biyayya ga kalamansa wannan kamar wasiyya ce adali aqili managarcin mijinta ya bata miqewa tayi a sanyaye ta zaunar da yaran ta nufi bathroom taci kukanta me zuciya ta jima kafin ta daure ta miqe ta fito a zaune ta tarar dashi yana yiwa twince wasa ya dauki madara yana basu yana mitar anbar masa yara da yunwa bata kulashi ba ta fice daga dakin ta shiga kitchen ta zubo abinci ta zauna a dinning din tana juya cokalin Hajiya tana ankare dasu amma batace musu qalaba tanajin lkcn da Hameed din ya shiga dakin taso yi masa mgn amma ta lura duk a zauce yake wani abun ma baisan yanayi ba tarasa wanne irin so yakewa Umaimah kamar wanda tabawa ruwan nono yasha indai yana ganinta baya iya control mind dinsa har tausayinsa takeyi musamman wannan karon data lura kwata? baya gaban Umaimah.




Zama Hajiya tayi a parlourn tana zaune yazo ya wucceta hankalinsa nakan Umaimah yaje ya zauna a kujerar kusa da ita ya ajiye twince suka tafi harkarsu yasa hannunsa ya dago fuskarta yaga yanda hawaye kebin kuncinta gabansa ya fadi sosai ya sanya hanunsa ya fara share mata hawayen yana girgiza mata kai idanunsa nakanta yace  don Allah kiyi hqr wlh ban turo miki text din da nufin bata ranki ba bloody bani na dorawa kaina sonki ba Allah ne ya jarabceni da qaunarki tun bakisan kanki ba wlh bazan iya rayuwa da wata mace ba da zan iya kema shaida ce a yanda nake da tuni nayi aure amma na hqr na zabi na rinqa azumi akan na hadaki da wata Umaimah ke dayace matata bazan qara hadaki da wata mace ba....




Daga masa hanu tayi tace  ya isheni haka Hameed ka matsamin wlh banason ganinka banason tuna baya shiyasa bana fatan sake rayuwa dakai Hameed me zaka fadamin na qara yarda dakai wacce kalma ta rage maka da zaka fadamin tayi tasiri a zuciyata ina cikin halin mutuwa ko rayuwa ina tsananin buqatarka da buqatar taimakonka lkcn da kowacce mace take samun soyayyar mijinta da tausayinsa lkcn da ya kamata kaji qaina ka tausaya min lkcn ne ka yanke shawarar rabuwa dani rabuwa ta qasqanci da wulaqanci Hameed saki biyu a lkcn da nake naquda ba lallai ne na tashi naci gaba da rayuwa ba ma nayi maka Hameed me kake tunanin zakayimin na manta da wannan abun a rayuwata Hameed wannan abun bazan taba mantawa dashi ba a rayuwata Hameed banyi rayuwar farin ciki ta shekara guda dakai ba tunda na fara rayuwa dakai cikin damuwa nake daga wannan matsalar sai wannan amma qoqarin dannewa nakeyi saboda so da tausayinka daka cusawa zuciyata Hameed bansan dadin aure a gdanka ba sai a gdan D.S wlh Hameed abubuwa da yawa idan na tuna badan arzikin zumunci ba dako gaisawa bazamu keyi dakai ba Hameed na tsani zaman aure dakai bana fatan sake shi idan ma kuma qaddara tasa na amince da sake rayuwa dakai to kasa a ranka Umaimatun daka sani da me sadaukar da farin cikinta akan na wani me qoqarin tursasa zucciyarta tayi biyayya ko bataso Umaimah shashasha da batasan ciwon kanta ba bata da choice a rayuwa sai naka Hmn Hameed wlh babu kaffara a kaina yanzu bada ita kake zaune ba na shaqi iskar yanci wata qaddarar gata ce rabuwata da qaddarren aurenka ta sanya idona budewar da bazan taba zabar farin cikin wani fiye da nawa ba




Tana gama fadin haka ta miqe ta kwasa da gudu ta fada dakinta a guje ya bita yana qwala mata kira amma Ina ta datse qofar ya durqushe a gaban qofar cikin rawar murya idonsa na zubar da hawaye yace  wal...wlh duk yanda kike tunanina ba haka nakeba bloody ki bude kiji abinda zan fada miki ni kaina shaidane kin canza daga yanda na sanki bakya tausayina amma koma ya kika zama inasonki sonki ya rufemin idona banaji bana ganin kowa sai ke zan rayu dake a haka Umaimah so dangin mutuwane baya duba rarrashi so gubane kamarsu daya da madara wlh ko zaki rinqa tsinkar gashin jikina ina mutuwa Ina dawowa kece zabina sonki yariga ya illatani bana iyayin komai sai Ina tare da tunaninki Umaimah baki taba soba shiyasa baki gane so ya yakeba wlh Hameed nakine ki yarda dani bloody....



Shassheqar kukan Hajiya ne yasashi waiwayawa ya miqe da sauri yana dafe da qirjinsa ya fadi a gabanta yace  haj... Hajiya ki tayani bata hqr kinsani baa cikin hankalina na saki Umaimah ba wlh duk duniya bata da masoyin da yafini Hajiya ku auramin Umaimah idan ba haka ba komai zai iya faruwa dani wlh duk ma abinda take tunanin nayi mata a baya don zalinci nasani banyi don cutar da itaba Hajiya bayin kaina bane ciwone da ubangiji ya jarabceni dashi kuma na samu lfy wlh duk yanda takeso haka zamu rayu idanma tace batason na riqe ko yatsanta ne na amince nidai naji a raina itadin tawace matata ce yafimin komai dadi Hajiya kice wani abu mana"..........




*UMMUH HAIRAN CE...
' [2/4, 6:58 PM] UMMUH HAIRAN CE...
'





















Kawar dakai Hajiya tayi tace  toni meye nawa a lamarin nan Hameed tsakaninku ne babu wanda zaiyi ma Umaimatu dole kaje kaci gaba da jarraba sa'ar ka idan rabonka ce zata sauko ku daidaita amma abin da ciwo kuma Umaimah bazata fahimceka ba sai kayi da gaske saboda haka Allah yabada saa" tana fada masa haka ta shige dakinta ya buga kansa da kujerar kusa dashi yanajin wani ciwo a zuciyarsa baisan meyasa son Umaimah yaqi qyale rayuwarsa ta hutaba tabbas so masifa ne yanzu badon ta fahimci yana sonta ba da bazata fada masa mgnr nan ba amma babu komai a juri zuwa rafi.




Miqewa yayi daqyar ya shige dakinsa ya fada gado yaci gaba da rera kukansa ya kasa control tear dinsa akan lamarin daya shafi Umaimah kuka yafi masa komai sauqi akan lamarinta baitaba zubarwa da mace hawaye ba sai akan Umaimah miqewa yayi yayi sujjada yace  Allah ka mallakamin Umaimatu a karo na biyu Allah banyi zato ba ka bani ita a karon farko Allah kada kabata ikon wahalar dani yana addu'ar yana kuka me shiga jiki.



Haka kwanaki sukayita shudewa duk ta inda Hameed ya biyo Umaimah gocewa takeyi duk wani wanda yasan zai hadata dashi ta saurareshi ya hadata dashi amma taqi sauraron kowa kalmarta daya ce tagama zaman aure da Hameed.
Wannan kalma tana caccakar zuciyarsa da haka har lkcn da aka bashi a gurin aiki ya qare ya juya California zuciyarsa taf da damuwa Umaimah tana neman fin qarfinsa qarfi da yaji ana ya gobe zai taho ne yayi mugun ganin da ya daki zucciyarsa ya rabonsa da sanyata a idonsa kwanaki uku kenan daya bita makaranta ta zage ta cire girmansa da nasabarsu ta debe masa albarka tsaf har tana fada masa ta tsaneshi ya fita daga rayuwarsa ranar yayi nadamar zuwanshi duniya da kasancewarsa namiji haka ya koma gda jiki babu qwari.




Sai yau a karin banza ya ganta tsaye da wani qato Alh Jabir a shopping suka hadu ya gigice ya rinqa binta tana yagashi hardai ya samu ta saurareshi ya biya mata kudin siyayyar da tayi naira dubu tamanin sannan ya karbi compliment card dinta sukayi sallama ta shiga motarta shima ya shiga tasa suka tafi ranar

Join Our Groups
16, January 2025
Abdullahi

Mun bude sabon Whatsapp group na cin duri Mai suna Sirrin Dadi idan ki/ka na bukata kayimin magana ta Whatsapp number 07032700869

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login