Showing 84001 words to 87000 words out of 135422 words

Chapter 29 - Gidan Uncle Complete Hausa Novel

Fauzah   

06 Oct 2024

49703

da zata roqi Allah tayi banda abu uku yafiya, samun lfyr yayanta da kuma shiriyar yarta Shurafah basu sukabar harami ba saida sukayi sallar asuba da yake tun kwanaki sha biyar da haihuwarta ta tsarkaka sai ciwon dinkin da tasha da har yanzu bai warkeba har zuwa wannan lkcn dingisa qafarta takeyi bata taketa sosai ba.



Haka sukaci gaba da gabatar da ibadarsu cikin rashin nutsuwar zuciya saboda itadai Umaimah hankalin ta yaqi kwantawa saboda rashin sanin halin da Hameed din yake ciki ranar da sukayi sati biyu a qasar Saudia ne ranar Daddy ya samu Umaimah a dakinsu shida Hajiya ya dubeta yace.



 Uwar masu gida Hajiya ta sameni da wata mgn a baya kinyi furucin bazaki sake rayuwar aure da Hameed ba kuma yanzu naji kince kin janye hakane?"



Jinjina masa kai tayi cikin kunya yayi murmushi yace  amma dai ina fatan ba wanine ya takuraki ya canza miki raayi ba?" Sake daga masa kai tayi yayi ajiyar zuciya yace  naji dadin hakan kuma nayi farin ciki da faruwar hakan Umaimah Allah yayi muku albarka ya shiga cikin lamarinku a gobe idan Allah ya kaimu zanje harami a mayar muku da auranku jibi saiku wucce Istanbul zuwa lkcn da zaku dawo komai yayi Normal da izinin Allah"



Dagowa tayi da sauri tace  aa Daddy nikam na fasa zuwa Istanbul dinnan ba" kallonta yayi da sauri yace  meyasa?" Qasa tayi da kanta tace  Daddy hankalina bazai kwanta ba ana zuwa yawon shaqatawa ne saboda nishadi toni nawa farin cikin yana asibiti baisan wake akansa ba wlh Daddy koda na tafi hankalina bazai taba kwanciya ba kayimin hqr bazan iya tafiya bansan halin da Abdulhameed yake ciki ba"........







*UMMUH HAIRAN CE...
' [1/23, 4:34 PM] UMMUH HAIRAN CE...
'

Ki biya kafin ki karanta idan kinaso ki kira number nan; 09031307566:










Ajiyar numfashi Daddy yayi cike da jin dadi ya miqe yace  shikenan ki zauna Baby bazan miki dole ba amma kinsan bazaku zauna anan ba tunda kun gama umararku zaku koma gda duk halin da ake ciki ma rinqa waya saboda makarantar ki kuma ma jikin Hameed da sauqi tunda yanzu numfashin sa yana fita sosai kuma wasu bangarori na jikinsa suna motsawa ba kamar baya ba"



Ficewa yayi ita kuma ta miqe ta haye gado ta kwanta inda Hajiya ta dauki Shurafah suka fice.
A washe garin ranar aka sake daura auranta da Hameed itadai a ranar yini tayi zuciyarta babu dadi hakanan bata farin ciki da auran nasu duk da ita kanta tasani yaudarar kanta ta rinqayi a baya da takejin kamar zata iya cireshi a ranta, kwana hudu suka qara a qasar Saudia suka dauko hanyar 9ja badan tanaso ba saidon batason yin musu da iyayen nasu musamman Daddy daya matsa akan sai sun tafi kwana uku ta huta Aunty Jameelah ta kama hanyar gdanta ita kuma ta shirya domin fara halattar makaranta micro biology take karanta kuma tanajin dadin course din sosai da yake Umaimah bamai hayaniya bace yasa ko qawa batayi a skul din ba daga ita sai Shurafah dinta suke harkokinsu yarinyar tayi qiba sosai tayi wayo cikin wata biyun idan ka ganta zaka dauka tayi wata hudu yarinya kyakkyawa abarso ga kowa ga Umaimah da sanin darajar kwalliya wa yaro kullum cikin ado Shurafah take hakan yaja Mata farin jini gurin yammatan department din nasu kowa Shurafah hakan yanasa Umaimah taji dadi aranta Saudat Alfah itama sabuwar daluba ce matashiya meji da gayu da tsayuwar naira a jikinta tunda ta shigo makarantar Allah ya hada jininta da Umaimah itama sanadin Shurafah Saudat Alfah itama matar aure ce da yaranta biyu tana auran wani custom tun Umaimah na janyewa abotar tasu harta saki jiki suka zama abokai sosai ita Saudat namiji take goyo Sudais kusan saanni ne da Shurafah.




Semester ta fara nisa sosai su Umaimah yan makaranta itadai karatun kawai tasa a gabanta amma rabin hankalinta yana wajen su Daddy da kullum sukayi waya saidai yace musu jiki yana kyau sosai a haka har suka cinye semester sukayi hutu a cikin hutun ta takurawa Daddy kan cewa tanaso taje ta gano jikin Hameed Daddy yaso hanata zuwan amma yanda yaga ta damune yashi dole ya qyaleta dake ya dawo dazai tafi suka tafi tare.



Kai tsaye asibitin da yake suka nufa suka shiga dakin tana rungume da Shurafah tunda suka shigo ya Hameed dake zaune jingine da matashin kai ya ya zubawa Umaimah ido ya kasa ko qiftawa sai yawo yake da idanunshi akanta kamar wanda ya warke daga ciwon makanta ajiyar zuciya ya sauke ta dago kanta da tayi qasa dashi tun kallon farko da sukayima juna idonsu ya qara sarqewa da juna a hankali ya daga hanunsa ya miqa mata alamun yana buqatar tabashi wani abu.



Cikin sassarfa ta qarasa gabansa ta dora masa Shurafah a jikinsa ya qurawa yarinyar da itama shidin take kallo ta qura masa ido sai bangale masa baki takeyi shima murmushin shima yayi mata tare da dagowa ya dubi Umaimah da taketa kallonsa ya rame sosai hancine kawai da ido sai dan qaramin bakinsa da yake motsawa a hankali alamun magana yakeson yi mata amma muryarsa bata fita sosai.
Shigowar Daddy da likitocin ne yasata neman guri kusa dashi ta zauna a sanyaye taji ya ruqo hanunta ta dago da sauri suka hada ido ya lumshe nasa a hankali ya bude tare da cewa  Kina kulamin da Shurafah yanda ya kamata kuwa?"



Yayi mgnr da murya me rauni a salube ta jinjina masa kai ya janye hanunsa daga nata tare da cigaba da kallon yarinyar yanajin qaunar da baitabaji akan sauran yayansa ba game da yarinyar dagata yayi a hankali ya dorata a qirjinsa.













*UMMUH HAIRAN CE...
' [1/23, 8:05 PM] UMMUH HAIRAN CE...
'

Ki biya kafin ki karanta idan kinaso ki kira number nan; 09031307566:















Likitan ne ya dubi Daddy sukayi larabcinsu ya miqawa Hameed hanu sukayi musabiha suka juya suka fita Daddy ya dubesu yace  zuwa sati idan ka qara warwarewa saimu tafi gda ko babana?" Lumshe idonsa yayi ya bude Daddy yayi murmushi yace  gadai Umaimah tazo ta kawo maka Shurafah nima hankalina ya kwanta yanzu zamu iya tafiya"



Daddy ne ya taimaka masa ya miqe kasancewar komai a asibitin ake masa babu abinda suka dauka sai kayansa yana rungume da Shurafah Daddy yana riqe dashi haka suka fita motar asibitin ta daukesu zuwa masaukinsu dakin da Daddy ya kamawa Umaimah nan yakaiwa Hameed kayansa ya juya ya fita ya barsu su biyu zama yayi a gefen gadon yana binta da shu'umin kallonsa me kashe mata jiki bata iya ce masa komai ba sai neman guri da tayi ta zauna a saman resting chair din dake gefen gadon ajiyar zuciya ya sauke tare da kawar da kansa daga kanta yace.



 Ina buqatar zan kwanta na huta da sauri ta dubeshi ya sake kawar dakai yace  ina nufin Ina buqatar privacy zaki iya fita kice da Daddy ya kama maki wani dakin" dagowa tayi zatayi mgn yayi saurin daga mata hanu yace  banason surutu kuma banason takura kitashi kije ki kwanta dare yayi"



Jikinta a mugun sanyaye ta miqe ta nufi gadon idanunta ya ciko da hawaye ta sunkuya zata dauki Shurafah ya daka mata wata tsawa data sata saurin yin baya yace  get out for my room" da sauri ta juya ta nufi qofar dakin ta bude a tsorace ta fice daga dakin.



Miqewa yayi ya kwantar da Shurafah dake bacci yasha magungunansa ya kwanta tare da janyo yartasa a jikinsa da haka bacci ya daukesa.
Umaimah kam a tsayawa tayi jikin qofar dakin zuciyarta nayi mata wani zafi da ciwon irin korar da yayi mata takeji wai ta fice masa daga dakin wasu hawaye ne masu zafi suka ziraro mata ta zauna a parlourn saman carpet zuciyarta nayi mata suya wannan ko wanne sabon wulaqancin rashin lfyr tasa tazo masa da ita oho.



Da wannan tunanin ta kwanta saman carpet din bacci ya dauketa da asuba ya farka yayi alwala yayi sallah yana zaune saman sallaya ta bude qofar ta shigo ta saida gabanta ya fadi data ganshi zaune yana lazumi kamar wacce qwai ya fashewa a ciki ta nufi bathroom din ta dauro alwala ta juya ta fita zuwa parlourn ta tayar da sallah tana idarwa yana fitowa yana cilla Shurafah sama yana cafewa ya zauna saman kujerar yana yima yarinyar wasa cikin faduwar gaba tace masa.



 Ina kwana" kallonta yayi kallo irin na rainin wayo yaci gaba da yima yarsa wasa shiru tayi masa taci gaba da azkar dinta kamar daga sama taji muryarsa yana cewa  wato da nace kije ki fadawa Daddy bana buqatarki a kusa dani ya nema miki dakin da zaki zauna kafin mu koma gda shine saboda ban isa ba kika kwana anan ko? To bazan hanaki kwana anan ba tunda haka kika zaba amma kisani kada ki kuskura ki shigomin daki da dare ranki baci zaiyi"



Harya gama mgnr batace masa qala ba sai hawayen da take zubarwa a rayuwarta babu abinda yake mata ciwo irin jizgi da wulaqanci bata jurewa hakan ko kadan.
Bai sake bi ta kanta ba ya tashi ya miqa mata Shurafah yace  yarinyata me hqr ya kamata a bata abincinta taci" yana fadin haka yasa hanunsa ya zare hijjab din jikinta ya zuge zif din ya sanya hanunsa ya dago qosasshen breast din nata yayi ajiyar zuciya tare da hadiye wani yawu ya saita bakin Shurafah yasa mata ta kuwa kama da sauri harda sanya hanunta ta dafe.



Miqewa yayi ya shige dakin saboda wani yar da yakeji a jikinsa ya fada bathroom da sauri ya sakarwa kansa ruwa ya fito ya dauki wani magani da Dr Maheelr ya bashi wanda yake taimaka masa wajan control din feelings dinsa sosai yasha ya koma ya kwanta tare da jan blanket sanyi Umaimah takeji sosai saboda weather din sanyin Saudi akwai shiga jiki amma tsoron ta tashi ta shiga dakin take ta dauko rigar sanyinta saboda ta lura ya qaro rashin mutunci sosai hakanan ta zauna data gaji ta dauki pillows din kujerar ta kwantar da Shurafah itama ta kwanta.



Ta jima tana baccin kafin ta tashi yana zaune a parlourn yana kallo miqewa tayi ta nufi dakin ta shiga bathroom tayi wanka ta fito ta tsaya jikin mirrow tana gyara jikinta daidai lkcn ya shigo dakin da Shurafah a hanunsa ya cire mata kayanta saurin dauke idonsa yayi daga kan Umaimah ya nufi bathroom ya fara yima yarinyar wanka lkcn daya fito itama ta gama har tasa kayanta ta koma parlourn ta soma hada tea bai fitoba saida ya shafama yarsa mai ya bude jakar kayansu ya dauki kayanta yasa mata ya shafa mata powder tare da taje mata sumarta baqa sidik mai yawa da tsayi yayi kissing lips dinta ya dauketa yace  ehhhh beautiful daughter kinfi kowacce ya kyau a duniya"




Suna fitowa Daddy yana nocking door din qarasawa yayi ya bude Daddy ya shigo ya dubi Shurafah da taketa hanqoron zuwa gurinsa yayi murmushi tare da daukanta ya cillata sama ya cafe yace  kin tashi lfy ayar Allah" kallonshi dukkansu sukayi yayi murmushi irin nasu na manya yace  sunanta kenan iznah ce Zulaiha" share zancen yayi da cewa.




Naso na bari sai nan da kwanaki shidda mu tafi so amma wani uzuri ya tasomin na gaggawa saboda haka yau da yamma nakesa ran zan tafi..." da sauri Umaimah ta tari numfashin sa da cewa  yawwa Daddy dama inason ce maka nima zan bika mu tafi saboda saura kwanaki uku hutunmu ya qare wani malolon kishine ya tasowa Hameed yayi saurin kallon Daddy yace  hutun me Daddy?" Murmushi Daddy yayi yace  hutun makaranta ta fara degree dinta a Skyline University har sunyi semester guda



Daure fuska yayi ya zabga mata wata uwar harara ya juyo ya kalli Daddy yace  kayi tafiyarka kawai Daddy idan na qarajin qwarin jikina zamu taho" dagowa tayi cikin tsoro saboda ita tunda taganshi jiya yayi Mata wani kwarjini sannan tsawar daya daka mata jiyan tasata jin wani mugun tsoronsa ya darsu a zuciyarta tace  amma don Allah Uncl...." hanunsa ya dora a lips dinsa alamun tayi masa shiru yace  ba dake nake mgn ba malama banason rashin kunya"




Kallonsa Daddy yayi da mamaki yaga yanda ya wani tsare gda shi a dole me iko yasan tabbas idan ya barta bazaa shuka abin arziqi ba ya miqe yace  debo kayanki kizo mu tafi Jidda mu jira lkc mu tafi" miqewa tayi zuciyarta fari tas ta shiga dakin ta fara hada shirginta saboda Allah ma ya sani bazata iya zama inuwa daya da wannan sabon Hameed din mara mutunci ba.
Baiyi mata mgn ba har saida ta gama hada kan kayanta ta goya yarta tabi bayan Daddy har Daddy yakai bakin qofa ya zai fita suka tsinkayo muryar Hameed yana cewa  nine mijinki ba Daddy ba idan kika taka qafar wajen dakin nan a bakin igiyoyin aurenki"........







*UMMUH HAIRAN CE...
' [1/24, 9:32 AM] UMMUH HAIRAN CE...
'

Ki biya kafin ki karanta idan kinaso ki kira number nan; 09031307566:


















Tsayawa sukayi cak daga ita har Daddy saboda girma da mamakin da furucin nasa ya basu amma shi ko a jikinsa miqewa ma yayi ya shige bedroom ya rufo qofar.
Hawayene suka fara bin kuncinta tace  muje Daddy girgiza mata kai yayi da sauri yace  bazaayi haka ba Umaimah ya kamata mu daina yanke hukunci cikin fushi saboda munyi a baya bamuga ribarsa ba qarshe ma sai tarin nadama da fargar jaji da ya sanyamu kiyi hqr kibi umarnin mijinki yafi komai muhimmanci kinsan har yanzu ba daidai yake ba sai kinyi hqr da yanayinsa kafin ya koma normal



Sanya hununsa yayi a aljihunsa ya dauko kudi Riyadh da batasan adadinsu ba ya miqa mata yace  ki kasance me hqr aduk inda kika samu kanki Umaimah komai yayi farko yanada qarshe" komawa tayi ta zauna saman kujera tayi watsi da kayan hanunta tare da kwance Shurafah ta rungumeta a qirjinta tasaki kuka me ciwo tana jinjina yanda zaman nasu zai kasance miqewa tayi ta shiga dakin yana kwance saman bed din yana sauraron qira'ar Shaikh Sulaiman yanabi a hankali ta zauna gefen gadon tare sanya hanunta ta dan daki cinyarsa kadan.



Wata zabura yayi ya miqe zaune tare da watsa mata wani mugun kallo yace  meye kuma na zuwa ki dameni wato bakiji abinda na fada miki ba ko?" Share hawayenta tayi tace  Don Allah kayi hqr kabarni nabi Daddy banajin dadin rayuwar qasar nan ni kadai" murmushi yayi na isa yace  bakyajin dadin rayuwar qasar nan ke kadai ko? Hmn tashi ki bani guri"


Kallonsa tayi da manyan sexy eyes dinta da suke cike da qwallah ta bude baki zatayi mgn yayi saurin daga mata hanu yace  silent pls nayi waya da reception kije ki karbi key din dakin kusa da wannan banason takura" miqewa tayi ta koma parlourn ta hade kanta da gwiwa taci gaba da rera kukanta cikin tausayin kanta wai yau ita Hameed yake kora daga sashin sa ta fada tare da miqewa ta nufi reception din suka bata key din tare dayi mata jagora har dakin shima suit ne kamar wanda Hameed din yake ciki larabawa akwai tsafta dakin sai zuba qamshi yakeyi tayi ajiyar zuciya ta haye gadon ta kwanta.



Yinin ranar gaba daya bataga Shurafah ba itama bata nemeta ba tunda tasan idan taje ma rashin mutunci zata jawowa kanta haka tayita harkokinta ita daya saidai tayi waya a kawo mata abinci idan taci ta sake waya azo a dauka haka har dare yayi ta miqe ta shiga bathroom tayi wanka ta dauro alwala tayi sallar isha sannan ta tashi ta murzawa jikinta mai ta fesa turarenta ta zura rigar baccinta ta haye gadon taja blanket tayi kwanciyarta.



Cikin bacci taji ana danna Bel din qofar ta miqe tare da tambayar  waye?" Cikin muryarsa mai kama data wanda yakejin bacci yace  waye kike tunanin zaizo gurinki a daren nan?" Ajiyar zuciya tayi ta bude dakin ya shigo tare da qarewa dakin kallo har ya sauke idanunsa akanta qirjinsa ya buga da qarfi ganin yar yaloluwar rigar baccin dake jikinta itamma kallonsa takeyi ganin yanda ta kafeshi da idone yasashi saurin dauke nasa idon cikin son nuna baiji komai ba a yanayin daya ganta yace.




 Na lura baki damu da yarinyar nan ba tun safe rabon daki sanyata a idonki amma tunanin qaramar qwalwarki bai baki cewa kije ki duba lfyrta ba" kawar dakai tayi ta fara takawa cikin takunta na isa da ko in kula komai na jikinta yana girgiza ta haye gadon taja bargonta ta rufa batare da tace masa komai ba saboda ta lura da take?nsa idan ta gaba da nuna masa damuwarta akan abinda yakeyi mata to ya samu qofar wulaqantata kenan ita kuma ko kadan bata dauki wulaqanci ba toma banda tsabar rainin wayo irin nasa meye yake sabo a gurinta game dashi da har zaiyi tunanin zata jure wulaqancinsa saboda shi.



Matsawa yayi jikin gadon ya janye bargon data rufa dashi ya kwantar da Shurafah a gefenta yace  ki tashi ki bata tasha banason ake barmin yarinya da yunwa" kuda bakwa gurin idan kun samu arziqin motsawa to itama ta motsa wani takaici ne ya tokare masa maqoshi ya haye gadon a fusace ta miqe da sauri zata sauka ya cafkota da sauri ya hadata da jikinsa suka kama kokawa ta tureshi ta miqe da sauri ta nufi parlourn da sauri ya sake cafkota yace  wlh idan kika fusatani zakiji a jikinki buge hanunsa tayi tace  ka ficemin daga daki banason ganinka dacan kaine kake sani nake bata nonon ko kuwa biyana kake da zaka titsiyeni saina bata




Sakinta yayi da mamakin irin rainin dake tsakaninsa da Umaimah juyawa yayi ya fice saboda yanda zuciya ke fuzgarsa ya afka mata amma bayaso so yake ya nuna mata ko babu ita zai iya rayuwa so yake ta gane kuskurenta na banzatar da rayuwarsa ta watsar da lamarinsa har tabada qofar faruwar komai.



Dakinsa ya koma ya zauna tare da dafe kansa so yake ya saba da rayuwa

Join Our Groups
16, January 2025
Abdullahi

Mun bude sabon Whatsapp group na cin duri Mai suna Sirrin Dadi idan ki/ka na bukata kayimin magana ta Whatsapp number 07032700869

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login