Showing 111001 words to 114000 words out of 135422 words

Chapter 38 - Gidan Uncle Complete Hausa Novel

Fauzah   

06 Oct 2024

49834

basan ya akai naje dakin ba kai anya ma kuwa nine?" Tsayawa yayi cak bayan ya gama karade gdan lungu da saqo bai ganta ba yana kiranta yana kiran sunan Shurafah yana cewa  na shiga ukuna Umaimah bake kadai bace kada kisawa kanki damuwa wlh yau zan saketa na tsaneta Umaimah kada ki wahalar da kanki da cikin jikinki"





Waje ya sake fita ya nufi gurin megadi yana fadin  Mal Ibrahim Ibrahim Ina Ummuh Shurafah take Ina kaga ta tafi?" Cikin in...Ina yace  ranka ya dade jiya misalin 12:30am Hajiya da Daddy sukazo suka dauketa da alamun batada lfy...."  What? Sukazo suka dauketa ina ina ni meyasa bata fadamin batada lfy ba Mal Ibrahim meye yake faruwa ne?" Juyawa yayi da sauri ya koma part din Umaiman ya fada wanka ya tsarkake jikinsa a gurguje yayi sallah ya dauki key din motarsa lkcn bakwai na safe ya fita a guje zuciyarsa tana bugawa da qarfi yama rasa tunanin da zaiyi yana zuwa gdan megadi yace masa yanzu suka shigo gda ya shiga yayi parking ko kashe motar baiyi ba ya shiga gdan a guje sukayi karo Daddy yana qoqarin fitowa daga dakin Hajiya da jariri a hanunsa matsawa yayi da sauri yace.




 Yawwa Daddy ina take ta haihu ne?" Kallonsa yayi batare da ya nuna masa wata damuwa ba yace  Eh Allah ya sauketa lfy Hameed bata mutu ba Allah bai cika maka burinka na kasheta da kayi niyyar yi ba banda abinka Hameed ai ko baka batta cikin halin ciwo ba takardar sakin daka batama shaida ce ta baka buqatar zama da ita to yau dai qurunqus dan kan barya Hameed aure babu tsakaninka da Umaimah kuma aure indai irin nakane to Umaimah ta barshi har abada wlh indai irin zaman da tayi a gdanka ne gara nasata a gaba nayita kallonta" duk cikin kalaman na Daddy babu abinda ya fahimta ya dago zaiyi mgn Hajiya dake fitowa ta daki bakinsa har saida ya fashe tace  sannu da zuwa tatacce dan'uwan koko ubanme kazo fada mana kazo ka jaddada mana ka saki Umaimah saki biyu ne ka cike mata ya zama uku?" Murmushi tayi me ciwo tace.




 Ai dama kayi zamanka gurin matarka abar qaunarka basai kazo ba saboda zuwan naka bashida wani amfani" dagowa yayi cikin tashin hankali da kidima yace  na roqeku badon halina ba ku taimakeni ku warwaremin qullin nan wlh fahimci me kukeso kuce ba" kallonsa Daddy yayi kallon tsaf yace  waye Abdulhameed Adam Hameed Shuwa ne?" Dagowa yayi yace  nine Daddy" ya kuma cewa  wace Umaimah ne?" Sake dagowa yayi yace  qanwata ce kuma matata ce Umaimah" murmushi Daddy yayi me ciwo yace  to tunda hakane karanta wannan takardar rubutun waye a jiki?" Miqa hanunsa yayi jikinsa na rawa ya karbi takardar daya rubuta da manyan kalmomi _ NI ABDULHAMEED ADAM HAMEED SHUWA NA SAKI MATATA UMAIMAH SAKI BIYU BATARE DA WANI DALILI BA_



Tashin hankali wanda baasa masa rana wata uwar zabura da yayi yayi cilli da takardar yana ja da baya yana girgiza kai yanason bude bakinsa amma ya kasa wani mugun jiri yakejin yana fuzgarsa kuma ya kasa tsayawa da tafiyar da yakeyi da baya da baya Daddy ne ya miqawa Hajiya Shuraif dake hanunsa ya tafi da gudu ya ruqoshi yana dafe da kansa dake sara masa yace  rur.. rubuta nane Daddy amma yaushe na saki matata ni da kaina na saketa Daddy aa wlh bani bane"........





_Kuyi hqr da wannan banida charge kuma inason muyi fira_







*UMMUH HAIRAN CE...
' [1/31, 8:55 AM] UMMUH HAIRAN CE...
'

































Yana fadin haka yayi baya luuuuuu cikin fitar hayyaci ya dafe saitin zuciyarsa data daukar masa wani mugun zafi yaci gaba da cewa  ya yama zaayi kuce na saki matata me tayimin dazan saketa bayan itace rayuwata Daddy koda Umaimah yankar jikina takeyi tanaci wlh bazan iya rabuwa da ita ba Daddy ku duba lamarin nan kuyimin rai wlh Allah Daddy bansan sanda na rubuta mata takardar nan ba bansan meye ya faru dani daran jiya ba a dakin Bloody na kwanta amma dana tashi da safe saina ganni a dakin Salma wlh Daddy bansan komai akan takardar nan ba ku dabeni kuji qaina ku tausayamin kada ku rabani da matata




Yana mgn muryarsa na kakkatsewa saboda tashin hankali kamashi Daddy yayi ya zaunar dashi a kujera ya dora masa Shuraif a cinyarsa yace  abinda ya faru ya riga ya faru ka saki Umaimah a daren jiya ta haihu a daren jiya ta tsarkaka daga iddarka ga danka nan kasa masa albarka dama rabonsa ne yasa ta koma gdanka nayi maka shisshigi nayi masa huduba da sunan marigayi babanku da fatan banyi laifi ba don kai yanzu hukuma ne sai lallashi




Shigewa Daddy yayi daki ita kuma Hajiya taja qofar dakin da Umaimah take ciki ta datse da mukulli ta nufi kitchen tafi awa daya a kitchen din ta fito ta tarar dashi a zaune tayi mamakin ganin yanda ya rungume Ahmad Shuraif a qirjinsa numfashin sa yana sarqewa bata kobi takansu ba ta shige dakin hakan ya bashi damar miqewa yana hada hanya ya nufi cikin dakin ya tsaya a bakin qofar ya zubawa Umaimah manyan idanunsa da suka kada sukayi jawur tana kwance nannade da blanket amma yana jiyo shassheqar kukanta daqyar ya iya jan qafarsa ya matsa ya zauna a gefen gadon yana jiyo sautin muryarta tana maimata kalmar innanillahi wa Innah ilaihir raji'un hanu yasa ya janye bargon data rufa dashi ta dago da sauri suka hada ido tayi saurin kawar da nata yakai hanunsa zai r????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
uqo nata tayi saurin make hanunsa tace  kada ka tabani Hameed na haramta gareka har abada insha Allahu sai Allah ya sakamin wannan baqin cikin daka qunsamin Hameed nayi danasanin saninka a rayuwata bantabajin tsanarka da tsanar zuri'ar dake tsakanina dakai ba sai dama ashe haka so yake meyasa ka cusamin sonka da tausayinka bayan kasan bazaka rayu dani ba Allah ya isa tsakanina dakai Hameed kuma wlh azeem idan baka daina bibiyar rayuwata ba zan gudu ku nemeni ku rasa kowa ma ya huta




Fitowar Hajiya ne yasata tayi shiru da kukan da takeyi ganin a zaune yayi mugun qonawa Hajiya rai ta nunashi da hannu tace  tashi ka fita daga dakinnan dagowa yayi yace  amma Hajiya ya kamata ku tsaya ku fahimceni waini meyasa kullum ni me laifine bakwa yimin uzuri Hajiya kada idonki ya rufe kema kamar yanda na bloody ya rufe take caccakamin maganganu masu ciwo son ranta kuyimin adalci kafin yanke hukunci naji ni me laifine amma ku tsaya kuyi tunani da hankalina zan saki Umaimah har saki biyu wlh Hajiya ko maqiyina yasan inayiwa bloody son da bazan taba yiwa wata mace ba a duniya bazan iya rabuwa da itaba itace rayuwata Hajiya itace farin cikina




Wani murmushi Hajiya tayi me ciwo itafa ta fara tantamar hankalin dan nata saboda kalaman gaba daya babu hankali a cikinsu dauke yaron tayi daga jikinsa ta kama hanunsa tace  miqe ka tafi gdanka safiya ce yanzu matarka tanacan tana jiranka ka cika mata burinta tayi nasara ta rabaka da matarka me qaunarka domin Allah ga gidannan ku zauna ku kadai" tana fadin haka ta turashi waje ta rufe qofar.




Durqushewa yayi jikin qofar yana kiran sunan Umaimah sai yanzu yaji wasu zafafan hawaye sun zubo masa ya dade a gurin ganin babu wanda zai fito daga dakin yasashi miqewa jiri na dibansa ya fita ya fada motarsa yaci gaba da kukansa yana buga kansa da sitiyarin motar jin abin yake kamar almara wai shine ya saki Umaimah saki har biyu to me tayi masa meye ya hadasu yaushe ma yayi sakin kuma yaushe ya rubutashi kai ina bazai taba yarda ba wannan gonarsa akeson shiga ayi masa barna.




Daqyar ya iyajan motar ya nufi gdan abokinsa Yusuf dake asabar ce yana zuwa ya tarar dashi tsaye tare da megadi mamakine ya cika Yusuf saboda rabonsa da Hameed tun lkcn daya fada masa zai auri Salmah ya fito ya nuna masa bai amince ba so ko waya basayi kamar aikin asiri ya daina kulasa ko wayarsa ya daina dagawa.
Takawa Yusuf yayi har motar ya bude ya shiga yace  yadai mutumin yau amintakar ce ta motsa asirin ya sakeka kenan... hadiye mgnr yayi ganin yanda jikinsa yake bari haqoransa suna haduwa ya damqi hanun Yusuf yace  Yusuf wai su Daddy ne sukace wai nine na saki Umaimah da hanuna jiya da daddare har saki biyu yanzu shikanan bloodyna ta haramta gareni...."




A tsorace Yusuf ya dago yace  kamar ya wai akwai wanda ya isa yace ka saki matarka idan baka saketa bane?" Cikin fitar hayyaci yana qara dafe qahon zuciyarsa yace  ru...rubutu nane a jikin takardar amma wlh tallahi bansan yaushe na rubuta ba Yusuf nasani kai zaka gasqatani wlh inason matata bazan taba iya rubuta mata saki har biyu ba yama zaayi na saki Umaimah har saki biyu bayan nasan rabuwa ce ta qarsh...."




Bai iya qarasa mgnr ba saboda numfashinsa da ya fara sarqewa ya fara kokawa dashi tare da danna qirjinsa da sauri yace  kaini gda Yusuf maxa kaini gdana na mutu a dakin Umaimah Yusuf mutuwa zanyi...."



Yana fadin haka ya fara kakarin amai kafin kace meye wannan ya balle murfin motar ya fita ya durqushe a qasa ya fara sheqa aman jini tashin hankalin da Yusuf ya shiga ba kadan bane ya fito ya rirriqeshi yana jijjigashi yana cewa  dama saida na fada maka kada ka auri Salma bakai takeso ba farin cikinka takeson rabaka dashi kaqi ji yanzu ga irinta nan ta rabaka da matar da kakeso kuma Kai dama ba cikakkiyar lafiya ba idan ka mutu ai kowa ma ya huta saki kuma ya saku tunda harka ambata sunan Umaimah a takardar kuma ka dawo hayyacinka ka gani da idanunka Hameed da ace bayan kayi sakin baka dawo hayyacinka ba har kowa ya fahimci baa cikin hayyacinka kayi sakin ba da kana da damar dawo da matarka saboda babu alqalami akanka lkcn da baka cikin hayyacinka amma dawowarka cikin hayyacinka da wuri da kuma karbar takardar ka duba shine ya tabbatar da sakin Hameed Umaimah ta saku kuma ta haramta gareka harsai taje ta auri wani mijin yayi mu'amala ta aure da ita tukunna ta halatta gareka...."



Duk da azabar da yakeji a qirjinsa hakan bai hanashi daga masa hanu cikin azababban kishi ba yace  wlh aa ne babu namijin dazai shiga jikin Umaimah saidai dukkanmu mu mutu babu aure ka kaini gdana nace kada na mutu anan....." Yana mgnr yana qara qanqame qirjinsa kamashi yayi ya taimaka masa suka shiga motar yaja suka fita ya juyo yace  amma da asibiti muka fara zuwa" daga masa hanu yayi yace  bazani ba gda nakeson zuwa nafiso na mutu na huta meye amfanin rayuwata babu Umaimah" bai sake masa mgn ba saboda yasan tunda ya musa to bazaiyi ba horn yayi a qofar gdan suka shiga ya dauki biro da takarda ya rubuta rubutu kamar haka.




 _Qaddarar ki rabani da farin cikina ya hadani da baqar ashana irinki wlh baki isa kici gaba da zama dani ba ni Hameed na saki matsiyaciyar mace irinki Salma saki uku _



Yana gamawa ya bude motar ya fita da sauri a duqe yake tafiyar har ya shiga cikin bangaren Salma ya danna kai ya shiga qanwarta ya gani a parlourn baiko kula gaisuwar da takeyi masa ba ya shige dakinsa ya zare wata qatuwar belt a jikin wandonsa ya bude qofar ya nufi dakinta ya tarar da ita kwance ta baje gindi tanashan iska ya kawar dakansa tare da sanyawa dakin key ya fusgota daga gadon ya fara nada mata na jaki kamar mahaukaci tun tana ihu da dasasshiyar muryarta da kukan neman daukin daran jiya ya qarar da ita harta daina motsi bai daina jibgarta ba yayi mata fata? da jiki sannan ya cilla mata takardar yana haqi yace aje aci gaba da zawarci Hameed yafi qarfin ki la'anallahu




Bude qofar yayi yana budewa yaga uwarta a parlourn ko kulata baiyi ba ya fice jiri na dibansa ya nufi inda Yusuf yake jiransa a mota amma kafin ya qarasa ya yanke jiki ya fadi da sauri Yusuf da megadi suka nufoshi suka rufar masa Yusuf na danna masa qirjinsa yana kiran sunansa wayarsa ya zaro a kidime ya kira layin Daddy bugu daya aka daga yace  Daddy Hameed ne bashi da lfy muna gdanshi ka Kira likita akwai matsala"
Yusuf yana aje wayar suka kinkimeshi suka nufi bangaren Umaimah dashi suka kwantar dashi a parlour sai gumi yake hadawa zuciyarsa na bugawa da qarfi baafi minti ashirin ba Daddy ya shigo shida Dr Saleem wata Allah ya fara yimasa sannan suka fita dashi zuwa asibiti suna zuwa aka shiga dashi aka fara bashi taimakon gaggawa wannan karon bai shiga commer ba amma baisan inda kansa yakeba.......











*UMMUH HAIRAN CE...
' [1/31, 2:24 PM] UMMUH HAIRAN CE...
'


























Gumu tayi gumu hankalin wannan family ya tashi wannan karon lamarin yafi qarfin fushi saidai addu'a saboda Hameed yana asibiti Umaimah ma tana asibiti har satin suna ya zagayo duk inda taso cirewa kanta damuwa da soyayya gami da tausayin halin da Abdulhameed yake ciki ta kasa saboda a jininta yake ji takeyi kamar ta cire ciwon ta mayar jikinta duk da a cikin qahon zuciyarta tanajin ciwon cin mutuncin da yayi Mata a daren da tafi buqatar taimakonsa da kusancinsa a daren ya yanke shawarar datse igiyoyin aurensu saida tayi sati biyu tana jinyar rabuwa da masoyinta a asibiti kadan ya rage itama zuciyar tata ta harbu amma jininta in yana kaiwa dubu ma to ya kai ga kuka babu dare babu rana tazama kamar zautacciya duk wata kalmar bakinta bloody ko ya jiki kace mata to amsarta bloody.




Hakan ba qaramin daga mawa su Hajiya hankali yayi ba kakace taga abin na Umaimah ya zama kamar tabuwar qwalwa hakan yasa tasa aka sauke mata qur'ani sannan akayo mata rubutun dangana aka rinqa bata tanasha satinta uku da haihuwa suka koma makaranta sabuwar motar da Hameed ya siya mata wacce yace itace gift dinta ta haihuwar Shuraif ita Daddy ya bata take zuwa makaranta da ita kamar yanda ya kafa mata doka har yanzu haka take bata fasa ba niqaf ne kawai bata sawa saboda dama a dole take sanya shi saboda farin cikinsa.




Saida yayi sati biyar a asibitin yana jinya sannan ya fara samun kansa shima da sunanta ya tashi a bakinsa Hajiya tana tausayawa dan nata tasan kafiyarsa shima da rubutun zatasa ayi masa saboda tasan akwai badaqala a gaba.
Haka suka koma gda dashi duk yawan gdajensa amma yaqi komawa ko daya daga ciki shima dakinsa tunna samartaka yasa Daddy dole saida ya gyara masa ya koma cikinsa sai lkcn ne Hajiya ta samu damar zuwa ta debowa Umaimah kayanta tsaf shikuma yasa gdan a kasuwa saboda ko gdan bazai qara zuwa ba balle ya tuna da baqar rayuwa da baqar ranar data riskesa a gdan ranar dabai taba tunanin zuwanta ba a rayuwar aurensa da Bloody dinsa.




Bincike yakeyi sosai akan sakin da ake iqirarin yayiwa Umaimah malamai sun bashi fatawa sosai inda kaso mafi rinjaye suka tafi akan ta saku saboda mgnrsu ta cewa lkcn da aka saukar da suratul dalaq manzon Allah ya sauqaqa sosai a cikin lamarina na saki harma yace idan mutum ya saki iyalinsa saki uku a kalma daya to zaa iya barinsa a saki daya idan yayi mata saki daya a baya kuma yazo yayi mata biyu to zaa iya barin biyun nan a daya a hada da wancan na farko ya zama biyu sannan idan mutum ya saki matarsa a cikin maye ko gushewar tunani to wannan sakin babushi.




So inda aka samu matsalar bayan wafatin ma'aiki (s a.w) sai abubuwa sukayi tsamari mutane suka rinqa wasa da aure sai mutum ya saki matarsa saki uku kuma yaje ya dawo da ita ko mutum yaje yasha giya ko wani abu me gusar da hankali yazo ya nadawa matarsa duka ya saketa idan ya dawo hayyacinsa ya koma ya dawo da ita wannan abu ya batawa Sayyadina Umar (R.A) rai zamanin khalifancinsa ya kira majalissar sahabbai aka sakewa dokar qwasqwarima saboda sauyawar zamani aka buga mata guduma akan cewa idan har mutum ya saki matarsa saki uku a kalma daya to ta saku sannan ko cikin gushewar tunani mutum yayi saki to matarsa ta saku sannan idan kayiwa mace saki daya sannan kazo zaka sake sakinta bayan kasan da daya a baya kuma ka furta mata biyu to ya zama uku saboda haka ta haramta gareka harsai tayi aure da tsarkakkakiyar niyyah ba niyar kisan wutaba kuma harsai mijin yayi mu'amalar aure da ita sannan tasu ta hadosu suka rabo to a lkcn ne ta halatta gareka sai ku sake daura aure fresh me igiya uku.




Wannan kalma ta sai Umaimah ta auri wani har ya kwanta da ita sannan zata halatta gareshi tana mugun dukan zuciyarsa yakanji dama ya mutu ya huta da ganin wannan baqar rana dalilin yasashi dawowa gdan dalilin ya qudurce a ransa bazaiyi aure ba itama bazatayi ba saidai su qare rayuwarsu a haka.
Abu daya da yake cin zuciyarsa yanda Umaiman tayi watsi da duk wani abu daya shafeshi so tari idan bashine yayi mata mgn a gdan ba itadai bai isa ta daga kai ta kalleshi ba yana yawan kiran wayarta amma bata dagawa har layi ya canza musamman saboda ita amma daya kirata tana dagawa taji muryarsa tace  hello bloody ya akayi Allah yasa dai lfy?"




Ajiyar zuciya yaja yace  ki taimaka ki fito come pound din gdannan inason ganinki don Allah" murmushi kawai tayi ta kashe wayarta bata fito ba kuma bata sake daga wayar tasa ba ransa yayi matuqar baci amma bashi da yanda zaiyi saboda baya iya fushi da lamarinta wani azabbaben so yakeyi mata wanda yake neman turashi lahira bai shirya ba haka lkc yayita tafiya tafi? har watanni takwas suka shude kullum cikin dagewa a karatunta take inda shi kuma

Join Our Groups
16, January 2025
Abdullahi

Mun bude sabon Whatsapp group na cin duri Mai suna Sirrin Dadi idan ki/ka na bukata kayimin magana ta Whatsapp number 07032700869

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login