Showing 60001 words to 63000 words out of 135422 words

Chapter 21 - Gidan Uncle Complete Hausa Novel

Fauzah   

06 Oct 2024

49711

mugun jiri ya debeshi yayi baya kansa ya hadu da glass din qofar ya fadi tim tare da ballewar jini a kansa.


Nufarsa tayi da gudu tana sakin wata qarar tashin hankali tana cewa  shikenan kin kasheshi Hajiya mun shiga ukun mu... riqo hanunta Hajiyan tayi cikin tashin hankali tace  kada ki tabashi babu aure tsakaninku" zubewa tayi a gurin tayi zaman tan bori kanta da kwakwalwar ta na juyawa jin abin take kamar a mafarki  Hameed ya sakeni" ta fada a fili tare da miqewa tana dafa bango ta nufi dakinta tana shiga ta zube a qasa sai yanzu kukanta ya dawo sabo zuciyarta nayi mata suya kanta na juyawa  Innanillahi wa innah ilaihir raji'un Allahummah ajjirni fi musibati wa'akalifni khairin minha



Su taketa maimaitawa batare da tunanin mafita tafi awa daya a zaune a gurin batasan lkc ya tafi ba saida wayarta tayi qara sannan ta iya rarrafawa ta daukota sunan Sa'ud tagani ta daga ta kara a kunnenta tare da fashewa da kuka tace  Sa'ud Hajiya ta rabani da farin cikina na shiga ukuna Sa'ud zuciyata zata fashe Ina tunanin mutawa tace ta iskeni a wannan lkcn salati Sa'ud ta dauka tace  ta rabaku Umaimah yanzu Ina Hameed din? bata iya bata amsa ba saboda wata hardewa da numfashinta yakeyi saurin kashe wayar tayi inda Sa'ud ta miqe cikin fitar hayyaci ta dauki motarta ta nufi gdan Umaiman amma tana zuwa get man din ya sanar da ita kusan sati batanan da mugun gudu ta juya ta nufi Sokoto road tana zuwa ta fara doka horn megadin yazo ya bude parking tayi cikin tsananin firgici ta bude ko kashe motar batayi ba ta shiga cikin gdan.



A durqushe ta sameta riqe da cikinta tana ta murqususu tare da cije lebe tana hawaye shiga tayi da sauri ta ruqota tana cewa  Subhanallahi Umaimah kada ki mutu don Allah tashi maza tashi mubar musu gdansu Umaimah na yarda maraya bashi da gata a wannan zamanin wannan dalilin yasa na ware kaina saboda kunci da baqin cikin rayuwa ya isheni tana fadin haka tana hadawa Umaimah kayanta a cikin handbag dinta tare da jan akwatunan kayanta guda biyu dake jingine a jikin bango ta fita da gudu? sauri? ta zuba a motar ta dawo ta dauki wayar Umaiman tare da magungunan ta ta dagota da iyakar qarfinta tana juya kai tana kuka tana komai tasata a mota ta shiga taja tare da zuge baqin glass din saboda gudun kada get man din ya gansu suka fita unguwar Hotoro suka nufa cikin wata hadaddiyar Unguwa me suna Farawa layout suka shiga unguwar ganin yanda Sa'ud taga aminiyar tata tana riqe cikine yasata nufar wani babban asibiti da ake kiza Zeenat clernic and digonostic ta shiga tare da fita da sauri tayima likitocin bayani suka nufo motar aka kamata ranga? aka nufi cikin wani daki da ita suka duqufa aikinsu.



Bincike sukayi sosai akanta kafin su gano inda gizo yake saqar tashin hankalin da take cikine ya assasa mata hawan jini me tsanani wanda yayi tasiri wajan lalata cikin dake jikinta yakeson fita amma babu hali saboda haka suka fara qoqarin ceto rayuwarta ta hanya cire mata cikin sannan suka daura mata ruwa tare da neman jini kasancewar kafin zuwansu asibitin ta zubar da jini yafi leda biyu kallon likitan tayi tace  Dr indai akwai abamu mu siya sai nayi muku transfer bamu da kudi cash a hanun mu bai wani damu ba yaje ya bincika yayi sa'a aka samu laida daya irin blood dinta ya maqala mata tare da rubuta mata magungunan qarin jini Sa'ud tayi musu transfer ta account dinta kamar yanda ta fada masa naira na gugan naira har 140,00 saida aka mayar da Umaimah dakin hutu sannan Sa'ud ta samu ganinta lkcn har tayi sallah take gida ta dawo tana kwance a gadon idanunta a lumshe tayi wani fari ta dashe saboda rashin Isasshen jinin da take fama dashi.



Kama hanunta Sa'ud tayi cikin hawaye tace  Sannu bloody kiyi hqr ki daina kukan nan kowanne bawa baya wucce qaddararsa kinji bude idonta ta rinqayi a hankali harta saukesu tar a fuskar Sa'ud idanunta naci gaba da malalar da hawaye tace  ina Uncle Hameed Sa'ud wanne hali yake ciki ya mutu ko? kada mata kai tayi tace  yananan Umaimah bazai mutu ba insha Allahu" lumshe idonta ta kumayi daidai shigowar likitan ya fara dubata yace  alhmdllh jiki yayi kyau sai fatan Allah ya mayar dana aika bude idonta tayi da sauri da tsananin mamaki tace  kamar yafa ban gane ba? shafa gashin goshinta Sa'ud tayi tace  damuwar da Hajiya ta jefaki a ciki ce tayi sanadin zubewar cikin jikinki Umaimah..." Miqewa tayi a tsorace tace  da gaske ya zube shima Innanillahi wa innah ilaihir raji'un shikenan farin cikin Uncle ya zube meyasa ya zube Dr inason cikina yanzu shikenan nayi biyu babu ba ubansa babushi


Tausayinta ne ya cika zuciyar Sa'ud ta kamota ta miqe tace  insha Allahu komai zaizo qarshe Bloody nasan akwai ciwo a rabaka da mijinka batare da neman shawararka ba amma babu komai akwai Allah kuma Ina tabbatar miki Hameed bazai iya rabuwa dake ba saboda kece kadai zaki iya zama dashi ki biya masa buqata yanda yakeso kuma ya samu gamsuwa dake =د? saboda haka karma ki wani damu tunda kinji qwari tashi mu qarasa gda kiyi wanka mu nemi abinda zamuci kinji shidai likitan binsu kawai yakeyi da kallon mamaki  dama matan aurene ku?" Yakasa jurewa ya tambaya kallonsa sukayi a tare Sa'ud ce tayi qarfin halin cewa  eh Hussaina tace am don Allah Dr mace da aka saketa da ciki kuma cikin ya zube matsayin iddarta yake a musulumci?"



Shafa kansa yayi sannan ya zauna yace  ma'anar iddah tana nufin tsarkin mahaifa tsarkin mahaifa kuwa shine yin jini bayan rabuwar aure to wacce aka saketa da ciki kinga bazatayi jini ba harsai ta haihu shiyasa iddarta take da wahala bayan ta haihun da zarar ta haihu to iddarta ta cika ko ranar zaa iya daura mata aure kinga kenan a shari'ance matar da aka saketa da ciki tayi bari koda a ranar da aka saketa ne to ita ta tsarkaka wannan shine amsarki a taqaice wallahu wa rasulihi aalam" yana fadin haka ya miqe ya fita tare da basu sallama Sa'ud ta kama hanunta suka fita a sanyaye jikin Umaimah yake ji takeyi dama zata iya mayar da cikinta jikinta jikinta yanzu shikenan ta fita daga sahun matar auren Abdulhameed?


Wasu hawaye masu zafin gaske suka gangaro mata da haka suka shiga motar suka nufi cikin unguwar sunyi tafiya me dan tsayi sannan sukayi parking jikin wani dan matsakaicin flat house me kyau saida Sa'ud ta tabata sannan ta dawo hayyacinta ta bude mata qofar ta fito tana daga qafarta daqyar ta nufi qofar da taji Sa'ud din na budewa ta bude mata ta shiga tanabin gdan da kallo wata qofar taga tasa key ta bude nanma Umaimah tasa qafarta ciki wani sanyi da qamshi me dadi ya daki hancinta ta lumshe idonta duk da zuciyarta babu dadi amma taji dadin qamshin ta bude idonta tanabin parlourn da kalloh yayi kyau sosai sai qofofi guda uku da suke a kulle, zubewa tayi a saman kujera tana sauke ajiyar zuciya tanabin parlourn da kallo amma gaba daya hankalinta na wajen Uncle dinta  ko wanne hali yake a ciki?" Abinda ta tambayi kanta kenan.


Tana zaune Sa'ud din ta shigo ta cire hijjab dinta tana murmushi tace  tashina kenan daga bacci kika kirani kinga ko rigar baccin ban cire ba na zari hijjab na fita" kawar da kanta tayi gefe saboda batason hayani ko surutu itama bata qara yimata mgnba ta bude daya cikin qofofin ta shiga bata jima ba ta fito ta bude dayan dakin tace  bloody ki shiga ki kwanta kafin na sama mana abinda zamuci nasan zuciyarki tana cike da zargi na da tarin tambayoyi akaina da kuma tunanin meyene yasa na daukoki na kawoki nan to kiyi hqr zan baki amsa nan da yan mintuna"



Tana gama fada mata haka ta riqo hanunta suka shiga dakin data bude mata mamaki ne ya cika zuciyar Umaimah ganin dakin a shirye tsaf kamar na matar aure gado wadroop madubi da bedsat komai dai akwai sai wata qofa da take nuna alamun bathroom ne qarewa dakin kallo tayi kafin ta zauna a gefen gadon ita kuma Sa'ud ta fita ta shiga daya qofar ta fara hada musu abinci.


*************************



Kusan awansu hudu da zuwa asibitin amma har yanzu bai farfado ba ko numfashi baya iyaye saida taimakon na'ura daga Hajiya har Aunty Zarah ba qaramin tashi hankalinsu yayi ba sun ma manta da baiwar Allah Umaimah da halin da zata iya shiga sai kaiwa da komowa sukeyi tare da likitocin a haka har dare yayi sai goma saura Zarah ta dubi Hajiya tace  Hajiya wai meye yayi coorsing din matsalar nan ne Ina matansa da banga kowacce a gurinnan ba?
Gaban Hajiya ne ya fadi ta miqe da sauri tace  na shiga uku na Zarah amanar Allah wlh na manta da ita" tana fadin haka ta fita da sauri ta tari dan sahu ta nufi gdan tun daga parlourn ta fara ganin gdan a hargitse dakinta ta nufa tana qwala mata kira amma shiru tura kanta tayi a dakin ta fara dube? amma babu alamar mutum a gurin kunna light din dakin tayi idanunta ya sauka akan inda Umaiman ta zauna dazun taga yanda jini ya bushe a gurin da sauri ta shiga ta banka qofar bandakin amma babu wata alama ta an shiga toilet din sake fita tayi tana kalle? a parlourn sai yanzu idanunta ya kai kan Nihal da Maliha da suke kwance a qasa kan tiles suna bacci matsawa tayi da sauri gurinsu tana haskasu fuskarsu duk tayi jirwaye da alamun kuka sukaci har sukayi bacci hankalinta ya dada tashi ta nufi wajen gdan ta fara qwalawa me gadi kira ya iso da gudu ya rusuna tace  ina Umaimah?"



Da sauri ya kalleta yace  banganta ba nidai bayan ansa yallabai a mota kun tafi naga wata motar tazo amma banga wanda ya ke ciki ba kuma bata dade ba ta fita... bata tsaya bata lkcn sauraron shirme ba ta juya gdan tana safa da marwa itakam taga ta kanta da yaran daga nema musu sauqi ta jangwalo fitina yanzu ina Umaimah ta tafi wata sani a garin wa take dashi a garin bayan su da zata wajenshi ta zauna? Tambaya ce mara amsa Hajiya take yiwa kanta har tana runtuma tuntube saboda tashin hankali.
Debe yaran tayi ta kaisu dakinsu ta kwantar dasu ta kuma shiga dakin Umaiman itace leqe har qarqashin gado miqewa ta kumayi tana rarraba idanu ya shege a rabon gado sai yanzu ta lura ma duk wani abu da yake mallakin Umaimah babushi a dakin zubewa tayi a qasa tana karanto Innanillahi wa innah ilaihir raji'un kanta yana wata muguwar sarawa a fili tace.



 Na shiga uku ni Zulaiha yau naga bala'i me hakan yake nufi Baby ta gudu saboda na rabata da abinda zai cutar da ita? Allah ka sani bada wata muguwar manufa nayi hakan ba Allah naji tsoron kada yaron nan ya hallaka ta ne Allah ka fitar dani kunyar duniya ka jefa marainiyar ka hanu na qwarai tana maganar tana kuka me ban tausayi wayewar garin yau tayi danasani tafi dari tilon danta yana kwance baisan inda kansa yake ba ga marainiyar Allah ta gudu  wallahi saboda ni bazaka rayu cikin tsinuwar mahaifiyar kaba Hameed ka sakeni saika sakeni Hameed ba wannan dalilin ne kadai yasa takeson ta rabamu ba akwai wani qulli a zuciyarta... kalaman Umaiman ne suka rinqa dawo mata tare dana Hameed din lkcn da yake kuka yana cewa  ki barni na rayu da farin cikina Hajiya nayi miki alqawarin bazan qara kusantar Umaimah ba har abada Hajiya ita kadai ta ragemin wadda takejin tausayina Hajiya kada ki rabamu tana sona kuma kema shaida ce inasonta babu wanda ya isa ya raba tsakanin hanta da jini& ..



A matuqar sanyaye ta miqe ta fita zuwa dakinta ta dauki wayarta ta fara kiran wayar Umaiman tun kiran farko aka fada Mata a kashe wayar take amma bata daina Kiran ba har saita charging wayar tata ya dauke ta koma ta kwanta zuciyarta tayi mata wani mugun nauyi daidai lkcn kiran Daddy ya shigo a tsorace Hajiya ta daga cikin rawar murya tace  hel...lo Daddy" bai iya amsawa ba yace  nakira wayar babana najita a kashe na kira ta Umaimatu itama a kashe nayi miki Miss call yafi ashirin baki daga ba Zarah ta kirani tacemin babana yana asibiti cikin mayuwacin halin da baisan wake a kansa ba meye yake faruwa ne".......









*UMMUH HAIRAN CE...
'



[1/15, 8:46 PM] UMMUH HAIRAN CE...
'

* ( _Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers)_



*GIDAN UNCLE*
( _Love and romantic story_)


*SHORT AND TRUE LIFE STORY*



*MALLAKAR*
=?G? *FAUZIYYA TASI'U UMAR*
*?FAUZAH*




www.fauzahtasiu41@gmail.com



Ki biya kafin ki karanta ta GTbank akan wannan account number: 0255526235; sai kiyi screenshot ki tura wannan number: 09013718241;
Ko katin waya MTN or Airtel ta wannan number:09031307566:




*PAGE TWENTY-SIX*



Cikin in..Ina Hajiya tace  ba...babu komai Alh kawai dai dama bashi da lfy ne kawai ita kuma Umaimah batajin dadi don harma tayi bacci haka kawai yaji bai gamsu da abinda take fada ba amma bayason musu da ita saboda haka ya ajiye wayar da qudurin gobe zaiyi asubanci ya diro Kano tunda dama ba nisa yayi ba South Africa yaje.



*************************



Kwance take saman kujerar parlourn washegarin ranar da abin ya faru zuciyarta tana mata wani irin suya tanajin takaici da tsanar Hajiya data rabata da farin cikinta taji shigowar Sa'ud miqewa tayi da sauri tana kallon Sa'ud din dake sanye cikin rigar bacci ta zauna a kusa da ita tana miqa tace  jiya bamu samu zama ba na shiga naga kinyi bacci da wuri yanzun dai me zakici?"



Idonta a lumshe yake amma hawaye take fitarwa tace  Abdulhameed kallonta Sa'ud tayi tana mamakin kalmar bakinta tace  kinsan kuwa me kike cewa bloody" bude idanunta tayi tar akan Sa'ud tace  nasani Sa'ud shi kadai nakeson ci shi nakeson gani kuma shi nakeso naji a jikina jiya ban iya bacci ba Sa'ud saboda tunanin halin da mijina yake ciki yanzu shikenan na tabbata sakakkiya na tabbata ba matsayin matarsa ba wannan wacce irin rayuwa ce meyasa banida saa a rayuwata Sa'ud son Hameed shine zai kasheni a jinina yake ya zanyi na rayu babu Hameed Sa'ud na saba dashi..... kukane yaci qarfinta Sa'ud ta kamota ta rungume ta tana sharar hawaye cikin kuka itama tace  yanzu Ina Uncle din yake" kuka takeyi sosai tace  yana asibiti bansan halin da yake ciki ba inajin tsoron kada na rasashi Sa'ud ruhi nane a jikinsa nasane a jikina Sa'ud farin cikin Hameed shine nawa bazan taba iya rayuwar da babushi a cikinta ba


Daqyar Sa'ud ta rarrasheta tayi shiru tare dayi mata alqawarin zasu tsayawa juna kaida fata wajan dawowar farin cikin rayuwarsu rungume juna sukayi suna kuka Sa'ud ce tace  Umaimah rayuwarmu tana fuskanta matsala sati uku kenan da su Hajiya suka koreni daga gdansu saboda nace bazan auri Yaya Auwal ba Umaimah banida da kowa a Kano bansan kowa ba saisu haka na dauki kayana na fito bansan inda zan dosa ba gashi babu waya a hanuna saboda tun kafin wannan lkcn aka karbe wayata aka iyakar layin ne a hanuna nayi tunanin zuwa gdanki sai naji tsoron kada naja miki matsala kema a wajan yan garuwar unguwar mu na ari waya nasa layina na Kira Anwar nake fada masa halin da nake ciki banyi tunanin samun taimako daga gurinsa ba saboda irin cin mutuncin da yan uwana sukayi masa shida mahaifinsa amma ga mamakina sai naji hankalinsa ya tashi yacemin na jirashi gashina baifi minti biyar ba ya iso ya daukeni ya mayar dani gda amma Hajiya da Abba suka rufe ido sukaci mutuncin mu qarshe suka koromu harda cemin ai dama karuwanci nakeyi abinda ya karbeni kenan saboda haka naje nayi abinda na zaba karna qara sanya kaina cikin zuri'ar su"



Dakatawa tayi saboda muryarta dake shaqewa saida tayi kuka me isarta sannan tace  muna fitowa Umaimah Anwar ya figi hanuna a fusace ya cillani motarsa yaja muka nufi wani hotel dake na'ibawa mai suna Rayhan ya kama mana daki suit anan muka kwana dagani harshi babu wanda yayi bacci kwana yayi yana rarrashina daqyar ya samu nayi shiru muka fara abinda muka saba.
Da safe ya fita yace zaije ya nemamin gdan da zan zauna kafin komai ya daidaita tunda ya fita sai yamma ya dawo yacemin ya samu gda anan Farawa layout harya siya ya biya kudin komai akwai a cikinsa ban wani bata lkc ba na taso muka taho tun daga ranar shima ya dawo nan da zama kasancewar dama aikine ya kawoshi nan asalinsa dan kaduna ne Umaimah kowa dake unguwar nan dauka yake zaman aure mukeyi da Anwar bayan ke babu wanda yasan zaman dadiro mukeyi dashi Umaimah banason rayuwar nan da mukeyi amma ya zanyi haka qaddara ta zabamin


A hankali Umaimah ta janye jikinta daga na Sa'ud tana girgiza Mata kai tace  meyasa Sa'ud meyasa kike da qaramar kwakwalwa meyasa baki tafi Niger gurin dangin mamanki ba wlh danice ke bazanyi wannan qazamar rayuwar ba" rufe Mata baki tayi tace  kinsan nasan komai Bloody laifin da kayishi tsakaninka da ubangijinka me sauqi ne da ace haqqin wani na dauka ko giba nayi shine zai zamemin matsala kiyi hqr bazan saurari uzurin da zaki bani ba Umaimah inada burin fansa akan abubuwa da yawa na farko korar karen da akayimin na biyu haqqin gadona da Abba da Hajiya suka cinyemin dole zanyi fito na fito

Join Our Groups
16, January 2025
Abdullahi

Mun bude sabon Whatsapp group na cin duri Mai suna Sirrin Dadi idan ki/ka na bukata kayimin magana ta Whatsapp number 07032700869

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login