Showing 93001 words to 96000 words out of 135422 words

Chapter 32 - Gidan Uncle Complete Hausa Novel

Fauzah   

06 Oct 2024

59902

ya dage akan bazata fita ba daga qarshe cillata yayi saman gadon ya fice ya kulleta ta waje.



Kifa kanta tayi a saman pillow ta rinqa kuka kamar ranta zai fita tanajin dama mutuwa tayi ta huta indai mutuwar hutu ce a gareta Shurafah ce ta rarrafo ta kwanta a jikinta itama tasa kukan miqewa tayi ta dauki yarinyar tana kuka tasa mata kaya ta bata nono tasha ta sake komawa ta kwanta tanajin zuciyarta kamar tayi tsalle ta fito.



Abin na Hameed kamar wasa saida suka qara kwanaki goma a Saudi babu wata mgn dake shiga tsakaninsu saidai kawai idan zai fita da safe ya kulle qofar parlourn idan ya dawo ya bude ya shiga yayi abinda yaga dama duk yanda yaso yaga ya shawo kanta taqi shawuwa takai ta kawo ma basa hada daki indai yananan to ita kuma zata kulle kanta a daki ta yini bata fito ba yasha tashi cikin dare yana buqatarta yayita dukan qofar yanayi mata magiya amma kamar batama san yanayi ba.



Hakanan a daddafe sukayi kwanaki goman suka dauki hanyar 9ja taso batace masa qala ba har suka isa katafaran gdan daya gina a tudun yola me part biyu har ciki dan taxi din ya shiga dasu suka fita ya sallameshi ya nufi wata qofa ya bude suka shiga tabi parlourn da kallo yayi kyau sosai sai qafar benen ya nufa tana riqe a hannunsa Shurafah tana daya hannun ya bude wata qofa yajata suka shiga ya sauke Shurafah dake bacci a wani qaramin gado dake gefe ya mayar da qofar ya danna Mata key ya tako zuwa gabanta yakai hanu zai ruqota ta zille da sauri yayi murmushi ya fara balle bottle din rigarsa ya balle belt din wandonsa ya zare Shortnicker din jikinsa ya nufota jikinsa na rawa ta janye ya cafkota da qarfi yace.



 Saboda zanyi aure Umaimah sai akace idan mijinki zai qara aure ki qaurace masa ki daina kulawa dashi ki daina sauraron kukansa da buqatarsa hakan shine zaisa yasoki ya fasa abinda Allah ya hukunta masa kada ki mayar da kanki jahila bayan nasani bakin gwargwado iyayenmu sun bamu ilimi kada ki biyewa son zuciya ki cutar damu Umaimah inasonki kina sona kada mu zalumci kanmu qarin aure bashine yake rusa zaman lfy da farin cikin gda ba rashin fahimtar junane ki yarda dani inasonki yana fadin haka ya janyota jikinsa yaci gaba da famfata da kalamansa masu saurin canza mata tunani duk da haka kuka takeyi hakanan ya rinqa sarrafata tana kukanta tana komai ya rabata da komai na jikinta ya kwantar da ita ya rinqa aika mata da saqonsa yana tsotseta hakanan badon tanajin dadi ba yayi abinda zaiyi ya dagata yaje yayi wanka yana fitowa wayarsa tayi ring ya dauka da sauri jikinsa har rawa yakeyi ya kara a kunnensa yace  hello my love ganinan fitowa kalmar ba qaramin girgiza nutsuwa da lfyr jikin Umaimah tayi ba ta zuba masa ido yanda yake ta sauri yanasa kayansa baiko bi takanta ba yayi ficewarsa ta miqe daqyar ta leqa ta window taga yanda yake wani gudu? ya shiga motarsa ya fice tana tsaye jikin windown wani malolo ya taso mata a zuciyarta yanzu duk wannan saurin da yakeyi saboda wata mace yakeyi yana ganin halin da take amma ya tsallake ya barta saboda buqatarsa ta biya.



Da wannan tunanin tayi wanka ta fito ta shiga kitchen ta dora tea ta dawo parlour ta zauna tana zama tajiyo kukan Shurafah ta miqe ta haura ta daukota ta dawo ta zauna har lkcn idonta bai daina zubar da ruwa ba daidai lkcn wayarta tayi Ring ta daga da sauri ganin number Aunty Jameelah tace  he... helo aunty yaushe zakizo? yanda taji muryar yar uwar tata tasan ba lafiya ba tace  yadai meye ya faru Umaimah naji Daddy yace mijinki aure zaiyi saura kwana uku daurin auren hakane?" Ajiyar zuciya tayi tace  hakane Aunty Salman gdan Alh Musa zai aura.... katseta tayi da sauri tace  kutumar ubancan wannan tsinanniyar gantalalliyar yarinyar zai auro miki Umaimah kayyy Innanillahi wa innah ilaihir raji'un wannan wacce irin masifa ce ne Umaimah me kikayi masa haka?"



Cikin kukan da batasan yaushe ta fara ba tace  bansani ba Aunty wlh iyakar sanina banyiwa Abdulhameed komai ba Aunty meyasa rayuwa na zama karfa ne wacce batada rabon farin ciki meyasa kowacce masifa take fadowa kaina ne? Aunty meyasa su mama da Abba suka mutu suka barni Allah da nasan wannan muguwar rayuwar zan riska bayan mutuwarsu dana bisu mun tafi tare ........







*UMMUH HAIRAN CE...
' [1/26, 8:07 PM] UMMUH HAIRAN CE...
'

Ki biya kafin ki karanta idan kinaso ki kira number nan; 09031307566:














Daqyar Jameelah ta iya rarrashin Umaimah saboda yanda take kukan bilhaqqi da gsky tace  babu komai Umaimah ki kwantar da hankalinki kici gaba dayi masa biyayya kima kiyi hqr da duk abinda zakiji ko ki gani Umaimah da hqr da rashinsa taqinsu kadanne idan kuma kikayi hqr zaayi dake kuma shi zalinci baya tabbata indai Hameed yayi aurene ne saboda ya zalinceki da sannu zakiga sakayya batare da kinje ko inaba yauwa kuma nasan kinsan komai game da gdansu kishiyarki basu zama da kishiya balle ke da duk inda Hameed ya zauna bashi da zance sai naki bashida hira sai taki sannan ko badon wannan ba saboda kyawunki da quruciyarki Salma zata zafafa kishinta akanki to ke kiyi qasa da naki duk da kowa ma ya sani namu na gadone bama iya control dinsa idan ya motsa amma ki rinqa daurewa kina dagewa kina basarwa kada ki yarda mijinki da kishiyarki su gane raunin ki ta wajen kishi musamman kishiya Umaimah kada kiyi kuskuren nuna Mata ke raguwa ce sannan ki riqe Allah ki cire kasala ki rinqa tashin tsakar dare kina fadawa Allah damuwarki lkcn da kowa yake bacci da sannu Allah zai kawo miki mafita Umaimah wlh daga Daddy har Hajiya babu wanda yayi ammanna da auren nan kawai dai don babu yanda zasuyi dashi ne kinsan mijinki da murdadden hali akan raayinsa saboda haka ko kadan kada kiga laifinsu kuma kada kiga laifinsa shima ina zargin bayin kansa bane saboda nasan tarihin soyayyarsu da Salma tun zamanin quruciya ma baisota ba balle yanzu data zama abinda ta zama"




Kukanta take qoqarin tsayarwa tace  amma Aunty haka zanci gaba da zama dashi banida wani amfani a gurinsa sai lkcn biyan buqatarsa idan naqi ya gwadamin qarfi babu ruwansa da halin da zan shiga kawai shidai buqatarsa ta biya anya Hameed yana sona kuwa Aunty kamar yanda kike tunani?" Ajiyar numfashi Jameelah tayi tace  karki damu da wannan Umaimah nidai alfarma daya zan nema a gurinki duk rintsi kada ki yarda karatunki ya salwanta ki tsaya kaida fata wajen ganin kin gama karatunki ki fitar dashi daga zuciyarki Umaimah inada tabbacin duk ma inda yaje zai dawo gareki saboda kedin is naturally kinada qualities din da baduk mace ba




Da wadannan kalaman ta rinqa rarrashin qanwar tata harta tursasa ta akan taje tayi masa girki batayi musu ba tana ajiye wayar ta tashi ta shiga kitchen ta fara shirya masa dinner tare da kunna karatun qur'ani saboda ragewa kanta quncin zuciyar da take ciki bayan ta gama ta shiga wani daki a qasan abin yaso bata dariya dakin guda kayan wasan Shurafah ne ajiyeta tayi a ciki ta nufi sama tayi wankanta tayi kwalliyarta me kyau tsari ta dawo parlourn ta???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? zauna tare da daukowa Shurafah motar wasanta taci gaba da zagayawa a parlourn tanata debewa uwarta kewa sunata dariyarsu saidai idan lkcn sallah yayi ta tashi tayi ta dawo ta zauna haka har lkc yaja ta tashi ta shiga dakinta ta sake shiryawa cikin kayan baccinta tana tsaka da fesa turare ya shigo gdan yaga yanda ta gyara ko ina sai abin ya burgeshi Umaimah akwai tsafta komai nata kaf-kaf cikin tsari yunwa yakeji sosai saboda shi iya wuya bai yarda yaci abinci a waje ba indai ba qasar ya bari ba.




Dinning table ya nufa ya zauna yana bude abincin qamshi ya dakeshi ya lumshe idonsa ya bude tare da fara zuba abincin daidai lkcn ita kuma ta gama lallaba Shurafah ta sauko da gudu?n ta domin daukar wayarta tun tana saman ya qura mata ido yanajin wata muguwar faduwar gaba yarinyar komai nata daukar hankalinsa yake towai shi mene ma yaja raayinsa ga Salma har yake sha'awar aurenta ita ba kyau na azo a gani ba ita ba diri ba nagarta ba ita ba komai ba amma yanajin kamar zai zauce akanta amma dai ya sani koma me yakeji akan Salma baikai wanda yakeji akan Umaimah ba saboda duk inda yake a fadin duniya indai a cikin hayyacinsa yake to ita kadai yake tunawa.



Baiji qarasowarta ba saida yaji sautin sassanyar muryarta tace  sannu da zuwa" firgigit ya dawo hayyacinsa ya sakar mata murmushin sa me tsada ya lumshe idonsa tare da budewa daidai lkcn data bar gurin ta matsa kusada center table din ta dauki wayarta ta juya zata wucce ta tsinkayo muryarsa yana fadin  Hearty tsayawa tayi cak ya taso a hankali ya sanya hanunsa ya tallafo faffadan hips dinta daya baje cikin blue din rigar baccin jikinta iya gwiwa yaja numfashi me qarfi yace  bazaki tambayeni meyasa naje nakai dare ban dawo ba wani mugun yawu me zafi ta hadiye tare da kada kai tayi gaba zata tafi saboda batajin zata iya furta masa kalma daya me dadi a yanda takejin zuciyarta na tafasa idan ta ganshi sake ruqota yayi yace  naje gurin Salma ne akan tsare?n yanda bikin zai kasance so abin yazo unexpected babu wani shiri bazan samu damar yimata lefe ba shine tace na bata million daya da rabi tasai kayan fitar biki so naje na cira na bata shine nakeson kema ki fadamin abinda kikeso nayi miki?



Yamutsa fuska tayi ta hadiye wani yawu me daci tace  na gde" daga haka bata kuma cemasa komai ba ta juya zata tafi ya sake ruqo hanunta yace  kamar kina sauri Babyn Uncle wai bakyason gani nane kome? da sauri ta daga masa kai tace  eh hakane Abu Shurafah wlh banason ganinka jinake kamar na kashek.... da sauri ya hade bakinsu ya matseta a jikinsa sosai qirjinsa yana bugawa da sauri?.
Sosai take kiciniyar qwacewa amma yawi qyaleta yaqi sakin mata baki saida yasha iya shansa sannan ya saki wasu hawaye masu zafi suka zubo masa yace  wannan kalmar ita Hajiya ta fadamin yanzun nan kema kuma kika sake maimaita min Umaimah nima wlh bansan meyasa nakeson auran nan ba nasani babu wata mace da nakeso da sha'awar kasancewa da ita a duk fadin duniya data wucceki ki yarda dani Umaimah aure na qaddara ce kuma kece kika jayo nasani badan kin gujeni ba da qila bazan hadu da Salma ba balle naji inason aurent....."



Daga masa hanu tayi tace  ya isa haka Abu Shurafah nasani kuma naji auranka qaddara ce kona yarda ko kar na yarda ba fasawa zakayi ba saboda haka yardata batada wani amfani amma nidai nidai nasan auranka ba qaddara bace son zuciyarka ne duk da haka inayi maka fatan alkhairi ka matsamin na wucce inada abinda yafi wannan surutun muhimmanci" tana gamawa ta fincike hanunta ta haura saman da gudu?nta bin bayanta yayi da kallo yana hadiyar yawu mace iyakar mace.




Daga murya yayi ya kira sunanta amma Ina ta shige dakinta ta datse yaja wani gwauron numfashi ya sauke ya koma gurin abincin ya rinqa turawa daqyar danma yanajin yunwa ne kawai Umaimah ta riga ta rikita masa lissafi ba dafaffan abinci yakeso ba danye yakeso kuma na jikinta, da wannan tunanin ya gama ya tashi ya shige dakinsa yayi wanka ya dauki remote control din qofar dakin nata ya fita ya nufi dakin ya bude ya shiga a saman sallaya ya sameta tayi sujjada tana kuka tana roqon Allah cikin larabcinsu na shuwa kuka takeyi sosai tana roqon Allah ya kawo mata dauki ya rabata da qaddararren auransa.
Miqewa yayi da sauri ya dagota zuciyarsa na tafasa baisan meyasa kowa ya juya masa baya akan auran Salma ne koda yake dama yasan haka zata faru amma baitaba tunanin zafin kishin Umaimah yakai haka ba baitaba tunanin zata nemi rabuwa dashi akan wannan qaramin dalilin ba..........










*UMMUH HAIRAN CE...
' [1/27, 9:02 AM] UMMUH HAIRAN CE...
'

Ki biya kafin ki karanta idan kinaso ki kira number nan;09031307566:























Hadata ya fara qoqarin yi da jikinsa amma taqi yarda ta rinqa tureshi tana dukansa ta ko Ina tana mgn cikin yarensu tana fadin  ka sakeni Hameed ka sakeni na gaji da zalincinka Hameed nagaji dayi maka biyayya kana cutar dani Hameed ka sawwaqemin wannan masifaffen auren naka na tsaneka Hameed bazan iya cigaba da rayuwa dakai ba cikin wannan rayuwar da komai nayi maka ban iyaba baka yabawa bare na burgeka wlh Hameed nagaji da zama dakai ko ka sakeni ko kada ka sakeni sai nabar maka gdanka bazan yarda hqrna da kawaicina da kuma rashin gatana yasa ka debomin masifa ka kawomin ba Ina baka isa ba Hameed koda kuwa kai kadai ka saura namiji a duniya wlh yau saika sakeni idan ba hakaba zan baka mamaki mamakin da bazaka samu damar yinsa a duniya ba




Sassauta murya tayi tayi qasa ta zame ta zauna tare da riqe qafafun sa ta dago ta kalli cikin idonsa daya kada yayi jajur saboda zafi da radadin kalamanta tace  Abdulhameed pls daivoce me qwace qafarsa yayi ya juya zai fita zuciyarsa tana tafasa ta miqe a mugun guje ta datse qofar tare da zare mukullin tayi saurin danna mata sabon password juyo kamar zautacciya tayi jifa da hijjabin jikinta tayo kansa ta shaqeshi ta jijjigashi da qarfin dabai taba sanin tanada shi ba tace.




 Billahil lazi La'ilaha illah huwa fitar daga dakin nan baka bani cikakkiyar amsar da nake so daga gareka ba daidai yake da yankewar numfashi a jikinka dan wlh saina zama ajalinka a gdannan Abdulhameed da hanuna zan kasheka na kashe banza jahili mara amfani a duniya ta kuma butulu da baya taba hangen tarin alkhairaina a gareshi kullum burinsa ya cutar dani Hameed baka isa ka kasheni da baqin cikin kaba wlh qarya kake azzalu....




Bai iya barinta ta qarasa tsauraran kalamanta gareshi ba ya sauke mata wasu kyawawan maruka guda uku a fuskarta tayi baya a gigice tare da dafe kumatun ta tace  kutmar uba nika mara Hameed?" Kafin ya ankara yaji saukar wani abu qwal ga goshinsa ya dafe gurin da sauri ta kuma jefoshi da kwalbar turare itama ta sameshi a goshin nasa ta qara jefoshi da wata ya goce da sauri tare da dafe gurin da jinin yake zuba yama rasa meya ya kamata yayi mata saboda ya lura da gaske take kasheshi zatayi a yau din shikuma yayiwa zuciyarsa alqawarin duk rintsi bazai saketa ba sake nufoshi tayi cikin bushewar zuciya dauki wani dan qaramin table din glass zata buga masa ya riqe da sauri tare da hada hannuwanta a cikin nasa yace.



 Kee Umaimah baki da hankali ne meye yake damunki...." ta katseshi da sauri da cewa  duk ma me zakace ka fada a yau dai baka isa ka rintsaba idan bakayimin abinda nakeso ba na tsaneka! na tsaneka!! na tsaneka Hameed ka sakeni kawai ka huta nima na huta aure ne na gamashi dakai dama ka fadamin nayi gangancin dawowa rayuwarka Hameed... daqyar ya samu nasarar hadata da jikinsa zuciyarsa tana bugawa da qarfi ko lkcn da ya auri Umaimah haukan Sadiya baikai na Umaimah Umaimah ba a lura da gaske Umaimah takeyi kasheshi zatayi.



Qanqameta yayi a jikinsa yanajin sabon sonta da tausayinta na kwarara a zuciyarsa ya rasa meyasa ya dage akan auran Salma har yana fito na fito da iyayensa akanta ya rasa meye yake damunsa shidai Allah ya sani ma baitabajin son Salma a ransa ba amma yanajin I bai rayu da itaba zai iya hallaka yana masifar son yaga ya aureta.
Wasu hawayen tausayin kansa ne suka zubo masa shidai kullum cikin laifi yake da zunubi bashida wata hanya da zaibi ya samu sauqi a gurin parents dinsa da matarsa daya tilo da yakewa so na mutuwa da rayuwa tabbas dada yanda zaiyi ya dojewa auran Salma da yayi badan farin cikin kowa ba saidon farin cikin Umaimah tunda ta yarda taji ta gani zata iya dauke lalurar rayuwarsa ita daya yasan yanzun ma duk shine yaja take gudunsa tunda a baya batayi masa hakaba amma tabbas da aiki ba qanqani ba a gabansa saboda itama Salman ya fahimci ta tsani yayi mata mgnr Umaimah wanda shi a duniyarsa hira idan bata shafi Umaimah ba bayajin dadinta ko kadan"




Cikin sarqewar harshe yace  ya isa haka kiyi cooling mind dinki pure heart wlh ki rubuta ki ajiye Hameed nakine ke kadai zuciyarsa tsarkakakken so take miki baso irin na sha'awa ba Umaimah kece cikon farin cikina kece rayuwata ruhina yana qirjinki idan kika kumayin nisa dani wlh azeem rayuwata ta qare don na tabbata koda ban mutu ba to zanyi rayuwa mara yanci kuma mara amfani Umaimah ki daina daukata me son kai nafi sonki fiye da kaina zan iya hqr da komai saboda ke wlh da zan iya da tuni na hqr da auren Salma amma na kasa idan ta kirani jikina har rawa yake wajen amsa kiranta idan na ganta sai naji zuciyata tana muradinta amma idan muka rabu sai naji ta fita a raina banason komai ya sake hadamu to yazanyi Umaimah ke kika ja kinsanni fiye da kowacce mace a duniya babu macen da zatayimin sanin da kikayi min wlh Umaimah Sadiya matatace ta sunnah a baya amma bantaba wanka tare da ita ba bantaba yin sex da ita da rana ba kuma bantaba saduwa da ita a cikin haske ba amma ke wanne ne bana miki har yanzu da kika canjamin kike azabtar da zuciyata ban fasa nemanki ba bana iya zuciya da duk abinda ya shafeki Umaimah danke kadai aka halicceni kamar yanda aka halicceki saboda ni kadai nasani kuma

Join Our Groups
16, January 2025
Abdullahi

Mun bude sabon Whatsapp group na cin duri Mai suna Sirrin Dadi idan ki/ka na bukata kayimin magana ta Whatsapp number 07032700869

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login