Showing 78001 words to 81000 words out of 135422 words

Chapter 27 - Gidan Uncle Complete Hausa Novel

Fauzah   

06 Oct 2024

49735

tayi yawa.



Hakanan suka yini a asibitin Hameed yana liqe dasu suna zuwa Hajiya dakinta takai Umaimah tana mata sannu har yanzu tana maqale da jikarta saida ta bawa Umaimah abinci da tea tasha sannan ta dora mata babyn a cinyarta tayi murmushi tace  yarinya kyakkyawa amma kun bata mata nasaba saboda son zuciyarku"



Hameed ne ya dago ya kalleta ya kalli Umaimah da kanta yake qasa yace  muma ba muso hakan ba Hajiya komai yana faruwa ne bisa buwaya da ikon ubangiji ku daina zargina wlh ba haka nakeba rabon wannan yarinyar zatazo a hakane yasa kika takura saina saki matata a halin inasonta tanasona kuma mun riga mun zama abu daya bazata iya rayuwa babu niba nima bazan iya rayuwa babu ita ba Hajiya ku taimaka ku dawomin da matata tunda ta haifemin abinda ke cikinta"








*UMMUH HAIRAN CE...
' [1/20, 7:57 PM] UMMUH HAIRAN CE...
'


Ki biya kafin ki karanta idan kinaso ki kira number nan; 09031307566:




*PAGE THIRTY-EIGHT*




Miqewa Hajiya tayi ta zugewa Umaimah rigar jikinta ta sanya hanunta ta ciro nononta ta dago yarinyar ta sanya mata a bakinta yarinyar ta kama tana tsotsa ya zubawa nonon nata ido yanajin wani shauqi da feeling na bijiro masa da sauri ya miqe ya fita daga dakin don ya fahimci zamansa zai iya haifae da matsala ko wanne lkc zai iya kai hanunsa ya cafki nonon ya taya yartasa sha.



Gidansa ya nufa yayi wanka sannan ya fara sanar da abokan arzikin sa anyi masa haihuwa matarsa ta haihu harda hotunan da yayi da bebyn ya dora a status dinsa na WhatsApp da Facebook aikuwa ya samu addu'a sosai zama yayi dirshen yana kallon bebyn da yayima huduba da sunan Hajiyansa Zulaiha yana kallon hoton yana hawaye yana Istigifari nadama yake da zuciya me tsarki tabbas ya aminta so masifa ne saboda sone umul aba'isin faruwar komai tsakaninsa da qanwar tasa amma meye ya sabbaba hakan?  Hajiya ya fada a fili tare da cewa  itace taja mana komai amma yanzu laifina suke gani saboda nine mara gata



Wayarsa ya dauka a karo na ba adadi ya kira layin Umaimah amma a kashe yasani koda a kunne take ba dagawa zatayi ba saboda ta dade da ajiyeshi da rayuwarsa a gefe gashi shikuma sai yanzune ma yake qara gasqata cewa soyayyarta itace take sarrafa rayuwarsa komawa yayi ya kwanta a kujera ya zubawa hotonsu ido lkcn farin cikinsu nanan bai gusheba shi abin ar mamaki yake bashi yanda yake hangen tsantsar qiyayyarsa a idon Umaimah Umaimah da a baya yake sarrafata da zuciyarta yanda yake so.



Da wadannan tunane? ya kwana da safe ya tashi ya shirya domin tafiya aiki saida ya fara zuwa yaga lfyr Umaimah da bebynsa daya laqabawa Shurafah sannan ya haura sama gurin Daddy daya dawo daga tafiya jiya da dare suka gaisa yayi masa barka kamar abin arziqi sannan yace.



 Alhmdllh babana Ina tayaka murnar samun qaruwar da kayi taya mace naji karar da kayiwa mahaifiyarku ka kyauta daka sanya sunanta wa baiwar Allan nan Shurafah so kamar yanda na fada maka lissafin da mukayi a baya zai canza ne bayan haihuwar Umaimah to alhmdllh ta sauka lfy saboda haka yanzu zabi biyu gareka kodai ka karbi yarka ka nemi wacce zata shayar maka da ita ko kuma ka rinqa biyan uwarta take shayar maka da ita"




Mamaki ne ya kusan kashe Hameed wannan fah shine tsugunu bata qareba ansai da biri ansai mage.
A sanyaye ya dago yace  amma Daddy na dauka cewa Umaimah koba itace ta haifi Shurafah ba ita me riqemin itace ta shayarmin da ita batare data nemi ko qwandala daga gurina ba...."


Daga masa hanu Daddy yayi yace  ai wai da take uwar tata shiyasa muka fada maka haka dama da ace ba ita ta haifaba ma aida mu da kanmu zamu bata ta shayar maka da ita saboda haka zabi ya rage naka idan ka yarda zaka rinqa biyane to wajibine duk wata ka kawo min 5 million na ciyarwa"



A matuqar mamakance ya dago yace  5 million fah Daddy me Shurafah zataci da har zata cinye 5 million a duk wata Daddy duk mutanen dake gdannan ma bazasuci 2 millions a wata ba balle jaririyar da aka haifa jiya?"



Shiru Daddy yayi ya dauki wayarsa ya fara latse? bayan yan sakanni aka daga yace  kuzo dukkanku inason ganinku a parlourn sama" yana fadin haka ya kashe wayar yaci gaba da duba wayarsa yana murmushi irin nasu na manya,
Shigowa sukayi suka hada ido ita dashi gabanta ya fadi sosai saboda wani kyau da taga yayi mata duk da ramar da yayi.



Daqyar ta iya samun guri ta zauna saman tumtum saida Daddy ya gama danne?nsa yace  Hajiya bashi yarsa" dagowa sukayi da sauri musamman Umaimah da taji mgnr kamar dirar kwarankwatsa a kanta.
Miqawa Hameed yarinyar Hajiya tayi jikinta a sanyaye hanunsa na rawa ya karba yana cije lebe wasu hawaye masu zafi suka zubo masa ya kwantar da yarinyar da taketa sharar baccinta a cinyarsa ya dago ya kalli Daddy yace.



 Na yarda zan rinqa badawa Daddy ka taimakeni kabar yarinyar nan a gurin mahaifiyarta idan na tafi da ita bansan ya zanyi da ita ba ko kuma ka mayar mana da aurenmu mu raini yarinyar nan cikin kulawar da duk wani da me gata yake samu a gurin iyayensa.... daukeshi da mari Daddy yayi yace  zaka tashi ka barmin gurin nan da shegiyar yarka kosai naci mutuncinka"



Miqewa yayi a matuqar sanyaye ya matsa gaban Umaimah da take kallon Daddyn tana mamakin furucinsa kalmar shegiyar daya Kira Shurafah da ita tafi komai dukanta ya dora mata babyn a cinyarta cikin kuka me ban tausayi yace  Koda kowa na duniya zaiqi Shurafah bai kamata ta rasa gata biyu ba nawa da naki Umaimah ni namiji ne banida nonon dazan bawa Shurafah ta rayu dashi kada kibada qofar rabaki da yarki da qaddara ta qadarta mata zamowa me rangwamen gata duk da nasani a gurin gama garin mutane take me rangwamen gata amma a gurina me cikakken gatace saboda na yarda itadin qaddara tace Umaimah babu wanda ya isa yayi maka wannan kyautar bayan Allah kuma bakida tabbacin sake samun wani bayan ita ta yuwu ita kadaice rabon dake tsakanina dake karki manta Umaimah kinsani komai yana faruwa ne bisa buwayar buwayi gagara misali badon hakaba dasai kice ya zaayi muna matsayin ma'aurata mu samu yarda bata sunnah ba to wannan kadai ya isheki misali ganin damarsa ne hakan ta faru Umaimah na roqeki kada kibada qofar banzatar da rayuwar yarinyar da bataji ba bata gani ba laifi nawane naji ayimin hukunci a kankin kaina amma kada ya shafi Shurafah dan Allah Umaimah....."



Wata tsawa Daddy ya sake doka masa yace  wlh tallahi Hameed idan baka bacemin da yarinyar nan a gurin nan ba sainayi maka abinda baka taba tunani ba jikinsa har bari yake ya miqe ya dauki yarinyar ya rungume a qirjinsa yana wani kuka mecin zuciya ya juya ya kalli Daddy yace  hakan ma na gde daka bari aka raini cikinta a gidanka amma kasani Daddy wannan zata zama rana ta qarshe da zaka rasani nima zanbar maka gdanka kuma Shurafah zatabar maka gdanka bari na har abada"



Yana fadin haka ya juya zai fice Umaimah tayi saurin riqo qafarsa cikin kukan tashin hankalin abu biyu rabuwa da yarta qwaya daya tak a duniya tace   Ina neman alfarma daya Daddy baa matsayina na mahaifiyar Shurafah ba a matsayina na yar'uwar mahaifinta ta jini wacce zan iya fansar rayuwata da tasa ina neman izinin shayar masa da yarsa batare dako sisin sa ba Daddy na roqeka kayimin wannan alfarm....."



Daka mata tsawa Daddy yayi yace  wlh baki isaba Umaimah saidai ki tashi kibishi tunda kin zabi farin cikinsa akan nawa kin fifita darajarsa da matsayinsa akan nawa to kitashi maza ki hada kayanki kibisa bana buqatar ganin shegiyar yarinyar nan a gdannan" bata iyajin kalmarsa ta qarsheba ta toshe kunnenta tare da sakinsa ta fashe da wani gigitaccen kuka me firgita zuciyar me imani tanaji tana gani ya juyo ya kalleta shima yana kuka daidai lkcn yarinyar itama tasa kuka da alamun nono take buqata amma ya juya ya fice da sauri ta miqe tana hada hanya zata bishi Daddy ya ruqo hanunta ta kuma rushewa da kuka tace.



 Tun safe Daddy Shurafah batasha nono ba ka taimakeni kabarni nabata koda shine na qarshe da zatasha daga jikina......" Dauketa yayi da wani gigitaccen mari tayi qasa ta zube yaraf ta qara dora hanunta a kanta ta rushe da kuka tace  shikenan Daddy ka rabani da yata qwaya daya tak a duniya...." Miqewa ta sakeyi da gudu ta nufi window daidai lkcn da Hameed ya kwantar da yarinyar a kujerar me zaman banza ya shiga ya tashi motar a guje yabar gdan har lkcn kuka yakeyi.



Zamewa tayi ta zauna a qasa tama manta da dinki akayi Mata soyayyar da da mahaifi ta mantar da ita ciwon komai sai ciwon rabuwa da yarta, saboda tsabar kuka har muryarta ta dashe Daddy ya tsallake ta ya shige dakinsa inda ta miqe tana hada hanya ta fita daga dakin ta fara taka matattakalar benen amma bata iya sauka ba jiri ya debeta tayo qasa luuuuuu daga saman ji kake tim ta fado tsakiyar parlourn qasan kamar matacciya Hajiya dake zaune take gursheqen kuka ta taso da gudu hakan yayi daidai da fitowar Kaka dake baccin asara a daki......







*UMMUH HAIRAN CE...
' [1/21, 9:52 AM] UMMUH HAIRAN CE...
'


Ki biya kafin ki karanta idan kinaso ki kira number nan; 09031307566:



*PAGE THIRTY-NINE*



Da gudu sukayo kanta cikin tashin hankali Hajiya taja da baya tace  mun shiga uku Kaka jini ta bakinta da hancinta kinga wani yana fita ta qasanta zata mutu Kaka anya Adamu bashida mental problem kuwa yaraba uwa da yarta a daidai wannan lkcn da kowacce uwa tafi buqata da tausayin danta Kaka ina Hameed zaikai Shurafah yanzu idan Umaimah ta mutu akan wannan dalilin me Adamu zaice da ubangiji?"



Riqeta Kaka tayi tace  me..mekike cewa Zulaiha maza ku tafi Asibiti ina zuwa nima" tana fadin haka tayi sama da gudu gurin Daddy ta fara buga qofar kamar zata balleta fitowa yayi ya bude ta cukuikuiyeshi tace  ina ka bari Hameed ya tafi da yarinyar nan to wlh ka fita da gaggawa ka nemoshi ka karbowa Umaimah yarta kafin fushina ya hau kanka ku baku da hankali da tunani kullum baku da aiki sai yanke hukunci cikin fushi"



Tana fadin haka ta sake juyowa ko mayafi babu a jikinta ta fito waje ta tsari taxi ta sanar dashi inda zai sauketa suna tafiya tana cewa dashi ya qara gudu cikin saa tana zuwa qofar gdan nashi dake FRW Layout ta hangi motarsa da wata motar a qofar gdan ta cillawa driven 1k tayi ta fada cikin gdan a guje amma me sai ta rinqa jiyo wani kakari yana fitowa daga parlourn da sauri tasakai ciki idonta kan Shurafah ya fara sauka dake dauke hanun Sarah tanata kukan neman uwa shikuma yana kwance a qasa sai fitar da dafara yakeyi mijin Sarah yanata bashi taimakon gaggawa tare da danna masa.



Cikin tashin hankali Kaka tace  mun shiga uku mukam wannan wacce irin masifa ce ta nufomu ne" daidai lkcn Daddy ya shigo don cika umarninta.



Dafe bango yayi da sauri tare da furta  Innanillahi wa innah ilaihir raji'un" mantuwa daya Daddy yakeyi a rayuwarsa shine matsalar zuciyar da aka haifi dannasa Hameed da ita.
Da sauri ya qarasa inda yake kwance yana fitar da wani wahalallan numfashi ya rungumoshi yana jijjigashi yana cewa  Abdulhameed! Abdulhameed!! Abdulhameed!!! Babana ka tashi kada ka fada a bakin mala'iku kada muyi irin wannan rabuwar dakai kada ka mutu kabarni babana ba qinka nakeyi ba wlh inasonka"



Kuka yakeyi sosai kamar qaramin yaro yana girgiza dannasa Kaka itama tana kuka tace  Shikenan ai kun kashesu kun huta saura yar itama gatanan Adamu kasa wuqa ka yankata sai ayi jana'izarsu gabadaya su ukun kukuma ku rayuwa a duniyar ku dawwama babu jarabawar ubangiji amma inaso ka sani nidai bazan yafe maka haqqi yarannan ba kuma Allah bazai yafe maka ba saboda shugabanci ba hauka bane Allah ma daya haliccemu munayi masa laifi ya yafe mana balle kai abin halitta Mai tarin dauda da zunubi"



Tana gama fadin hakan Hameed yaja wani dogon numfashi komai na jikinsa ya daina motsawa, wani ihu Daddy ya saki yace.



 Shikenan na kasheshi da kaina Innanillahi wa innah ilaihir raji'un Hameed...." Abubakar ne ya matso ya daga hanun Hameed din ya matse wata jijiya ya zubawa yatsun qafarsa ido babban yatsansa yada ya motsa yayi ajiyar zuciya yace  bai mutu ba akwai sauran numfashi a jikinsa ayi saurin kaishi asibiti


Ai kafin Abubakar ya ida rufe bakinsa Daddy ya hada qarfinsa ya dago Hameed din Abubakar ya taimaka masa suka sashi a mota tun a hanya ya kira likitansa ya sanar dasu abinda ke faruwa.
Suna zuwa aka rufar masa aka fara jorner masa na'urori.



*************************



Ita kuwa Umaimah tunda aka kaita asibitin batasan waye a kanta ba daqyar likitocin sukayi nasarar tsayar da jinin dake zuba ta qasanta na hancinta da bakinta kam basusha wahalar tsayar dashi ba saboda kawai buguwa ce, saida aka farke dinkin da akayi mata aka kankare aka sakeyi mata sabo sannan aka daura mata drip Hajiya tana zaune a kusa da ita ta zuba mata ido tausayinta yana qara narkar Mata da zuciya Kaka ta shigo dauke da Shurafah a hanunta.



Da sauri Hajiya ta tareta ta karbi yarinyar da tayi kukanta harta gaji ta koma bacci tanajan zuciya tayi hamdala tace.
 Hankalina yana gurin yarinyar nan Kaka ina Hameed din? zama Kaka tayi tace  yana emergency section kunsan matsalar danku kunma fini sani tunda kune kuka haifeshi saboda haka idan kun kasheshi hankalinku zaifi kwanciya"



Da sauri Hajiya ta tare Kaka da cewa  wai kina nufin ciwonsa ne ya tashi?" girgiza kai Kaka tayi tace  abubuwa da yawa daya dade yana binnewa a zuciyarsa sune suka hadu da wannan abun da kukeyi masa akan qaddarar da baku isa ku canzata da bacin ranku ba na tabbata da ace ana dawowa da mutum book din predestinations dinsa da Hameed yana cikin mutane na gaba? da zasuyi gaggawar sauya tasu qaddarar amma kun kasa fahimtarsa kun kasa yi masa adalci da uzuri a cikin rayuwarsa komai fa da kuka gani yana faruwa ne cikin sahalewa da buwayar ubangiji wlh na tabbata idan yaron nan ya rasa rayuwarsa ta wannan hanyar kema kina da kamasho kuma kece umul aba'isin faruwar komai Zulaiha kinada kaso me tsoka cikin abinda ya faru tsakanin Baby da Hameed saboda haka kiyi gaggawar tuba kema don basu kadaine suke cikin fushin ubangiji ba harda ku da kuka kasa sama musu mafita me kyau"



Sosai kalaman kaka suka daki zuciyar Hajiya kuma sukayi mugun sanyaya mata jiki qafafunta taji suna neman gaza daukarta ta sulale ta zauna a qasa kan tiles tana kuka me tsima zuciya tana qara shigar Shurafah jikinta tace  Allah na tuba astangafurullah ya Rabbil samawati wal ardi kaicona dana kasance me yanke hukunci cikin fushi kaicona dana zamo me gyara barna da barna kaicona dana zamo silar zuwanki duniya bata hanyar aureba Zulaihat me zan fada miki ranar da kikaji labarin nice silar zuwanki duniya ta wannan qazamar hanyar wayyoh Allah dama ka karbi rayuwata kafin wannan lkcn na zamo uwa mara amfani uwa me qoqarin rusa farin cikin yayanta da furucinta na tabbata da banyi furucin tsinuwa ga Hameed ba da babu abinda zaisa ya saki matarsa....."



Ta qarasa mgnr cikin wani irin kuka me ban tausayi sun jima a haka kafin ta samu qwarin gwiwar miqewa ta fita ta nufi pharmacy din asibitin ta siyo madarar da zaa iya bama yarinyar ta dawo ta jorner kettle ta dafa ruwan zafi ta hadama yarinyar ta sanya a cikin feeder ta sanya cikin ruwan sanyi kafin Shurafah din ta tashi.



Sunanan zaune zaman jiran tsammani Daddy ya budo qofar ya shigo dukkansu suka zuba masa ido guri ya samu ya zauna ya hada uban tagumi yana share hawaye, Hajiya ce ta sake fashewa da kuka tace  Nikam naga ta kaina ni Zulaihatu ya mutu ko Alh shikenan Hameed ya mutu...." Dakatar da ita yayi ta hanyar girgiza mata kai yace  bai mutu ba amma yana tsakanin mutuwa da rayuwa Zulaiha Hameed yana fama da heart attack wanda zai iya zamowa sanadin salwantar rayuwarsa yanzu haka ya shiga commar wanda ko babu heart attack zaiyi wahala mutum ya shiga commer ya tashi yaci gaba da rayuwa...."



Ya qarashe mgnr cikin kuka tare da tashi ya bude fuskar Umaimah da taketa baccin wahala yayi ajiyar zuciya sannan ya koma ya dauki Shurafah da tunda aka haifeta sai yanzu ya dauketa ya zuba mata ido yanajin son yarinyar na ratsa jinin jikinsa ya rungumeta a jikinsa yana ajiyar zuciya.






*UMMUH HAIRAN CE...
' [1/21, 7:02 PM] UMMUH HAIRAN CE...
'


Ki biya kafin ki karanta idan kinaso ki kira number nan; 09031307566:



*PAGE FOURTY*



Sun dade a zaune jugum? kafin Daddy ya tashi ya miqawa Hajiya Shurafah ya fita daga dakin sai dare Umaimah ta farka shassheqar kukanta ne yasa Hajiya fahimtar ta farka ta tashi da sauri ta qarasa gabanta ta ruqo hanunta tayi ta bude idanunta ta zubasu a kan Hajiya qwallar naci gaba da kwarara a idonta mgn takeson yi amma ta kasa sai jujjuya ido takeyi yarta kawai takeson gani ganin babu alamar yarinyar yasata qara sautin kukanta da sauri Hajiya ta juya gadon da aka kwantar da yarinyar tanata bacci ta daukota ta kwantar Mata da ita a gabanta.



Dagowa tayi ta kalleta kawai batasan sanda wani smiling ya qwace mata ba itama Hajiyan murmushin yaqe tayi mata ta koma ta zauna tana kallonta yanda idonta yake juyawa akan yarinyar duk da babu bakin mgn amma da ganin kallon da takewa yarinyar kasan nasone da farin ciki hadi kuma da tarin tausayi na da da mahaifi lumshe idonta tayi tare da daukan hanunta ta tallafo bayan yarinyar ta hadata da qirjinta

Join Our Groups
16, January 2025
Abdullahi

Mun bude sabon Whatsapp group na cin duri Mai suna Sirrin Dadi idan ki/ka na bukata kayimin magana ta Whatsapp number 07032700869

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login