Showing 21001 words to 24000 words out of 152911 words
da ruwa ta zauna a gabansa gwiwoyinta a kasa ta goge Masa bakin da Maheera ta shafa Masa a gira ta goge Masa jambakin tas ta zauna ta gyara Masa cola din rigarsa,ta mike ta koma dakinta ta dakko cumb tare da gyara Masa gashinsa Yana jinta Yana ta Murmushi Yana ta mata godiya Shukran
Maheerah ce ta fito Fuska a kumbure ta iske Cele tana kula da Ahsan zuwa tayi ta ture Cele,Cele ma tace Kai Kai Kika tureni ta sa kugunta ta bangaje Maheerah, Maheera ta fusata Suka hade kugu kowanne gefe daya suna tura juna Kamar zasu fada Kan Ahsan suna kokawa kowacce tana Nishi,Maheera tasa Hannu zata gyarawa Ahsan gashi Cele ta bige hannunta tace karki ta min shi na kwace shi ta fada jikin Ahsan ta kakkare shi da hannayensa biyu Maheerah baza ta taba Mata ba,Maheerah tana mamakin karfin hali da shishigi irin na Cele,Celeta kankane Ahsan,shi Kuma yasan itace a jikinsa yace Celei Haram...Haram yana kiran matarsa Wai itace muharammarsa,Cele tace Sannu Alhaji Saluhu kaikam Kayi asara Sam baka da basira ka gama Zama Sallamamme duk abinda ta maka baka ji har wani kiranta kake Zauji zauji Kai dalla rufe min baki dan ma ana Jin kamshinka Naga shegiyar da zata sake tabaka yau taki tashi ta kankane a jikinsa,Maheerah ta dage iya karfinta sai ta banbare Cele a jikin Mijinta Amma ta kasa ta Kira Ayusha tace taimaka Mata,Ayusha tana tsoron Cele tace ba ruwanta,Maheerah hakan ya Kona Mata rai Nan take tace ta kori Ayusha daga aiki ta San inda dare ya mata,Ayusha tana bata hakuri ta dauki takalmi ta bita ba shiri Ayusha ta bar gida an koreta daga aiki,Ahsan Yana jinsu bai ce komai ba ga Cele ta makale shi,Maheerah kwafa tayi ta koma bedroom.
Ko Sallah Zaiyi Cele ce take kaishi ta zuba Masa ruwa yayi Alwala ta sashi a Sallaya yayi Sallah,da dare ma zai kwanta ita ta kaishi dakinsa,Maheerah tana ganinsa ta jashi har da kwace hannunsa a hannun Cele ta kaishi toilet ta Masa wanka Suka fito ta shirya shi Suka kwanta,Cele tace Maheerah sai kinci ubanki wanka tayi ta shirya cikin kayan bacci ta nufi dakin su Maheera ta Bude kofa tana zuwa ba ko magana sum sum ta wuce tare da haurawa saman bed din Kamar yarsu ta Shige tsakiya ta kwanta,Maheerah zaune ta mike tasa hannaye ta jawo kafafun Cele kiiii zuwa kasa ita ta koma ta kwanta,Cele ta mike itama tace karya kike Dan ubanki Zikri sunan Baban Maheerah Zikri dama Cele taji ana ce Mata Maheerah bint zikri ta sake jawo Maheerah itama kasa ta koma ta hau saman bed din,Maheerah ta gaji ta fashe da kuka ta zauna a kasa tana rusa kuka,Oga Ahsan shi baccinsa ma yake yi Yana jinsu suna ta fama ya musu magana sunki ji,Cele tace daga yau wlh sai dai mu kwana tare Zaki ga tsiya,Maheerah tana masifa da larabci tace bata son dan dake jikin Cele ta bar musu gidansu Kawai yafi,Cele bata San me take cewa ba ta Mata Gwalo tare da Jan bargo ta kwanta nesa da Ahsan,Maheerah haushi yasa ta mike ta hau Kan Cele tana dukanta,Ahsan ko kulasu baiyi ba suna ta kokawa,karshe da ya gaji yayi magana wai Maheerah ta maida shi Palo ya kwana a kujera,ta Masa jagora ta maida shi Palo ya kwanta a saman kujera ta kawo Masa bargo,Cele tace wlh sai dai muyi asara ni da ke Babu me kwana da shi ta baje akan gadon tayi kwanciyarta,Maheera harda zuwa tace da Ahsan su koma daya dakin su kwana yace ta kyale shi a kujera zai kwana a palo.
Kaka zaune yake a daki dawowarsa daga bara kenan Yana irga kudinsa,kudin ya rike a hannunsa Yana kallonsu Yana tunanin Cele kuka ya saki ba tare da shiri ba ya tashi a fusace ya fice sai inda yasan Askawaran kame sunfi tsayawa ya tafi can Yana uban sauri ya samesu Kuwa da yawa suna ta kame cikinsu ya fada ya Mika musu hannaye Wai a sa Masa ankwa yana cewa Nigeria wa Shan Koko da kosai wa dankalin Hausa ya fiye min dadi a rayuwata,suna kallonsa sun gane me yake nufi Suka kece da dariya Wai a maida shi Nigeria Suka ce la lah Suka ki Kama Kaka suna ta dariya sun San wuya yaji yayi rokon duniya Suka ce ya tafi gida ya huta ga Makkah akwai dadi haka Kaka ya dawo falau falau da jallabiyyarsa Kamar buhu Yana yawo a ciki.
Mami ce tayi bakuwa kawarta Hajiya Karimatu tazo suna ta hira Mami tana bata labarin Makkah,Hajiya Karimatu tace Wai ya akayi kika kashe aurenki Allah ya Miki zabi na gari balarabe ance me kudi kyakyawa? Murmushi Mami tayi tace Ina kyau ai kudin banza me zanyi da su da kyar Allah ya kwace ni bawan Allah zai kashe ni Dana dawo da sai da nayi jinya,yaron nan Nawwar ya fada min gaskiya naki ji naje mutumin nan Kamar Allah ya Aiko shi Kamar ya samu akuya Ina lallaba tsufana zai karasa ni ni ba yarinya ba,Abarsa takai tsayin hannuna kamu Uku ke Naga bala'i Dan nonon da Yaran da na haifa Suka rage kala sai da ya kusa karasa su, Hajiya Karimatu ta dinga dariya,Sai ga Nawaf Auta ya shigo cikin Jean crazy ko Ina a farfashe Wai shi gayu,Mami Shuru sukayi duf Kamar ruwa ya cinye su Kar yaro yaji,Mami tace Auta, yace Na'am ya gaida su sannan yace Mami baki kusa iddar bane? Hajiya Karimatu tace Kai ka ji min yaro Ina ruwanka,Baffa ne ya damu wlh duk ya rame bana son ganinsa haka har fa mu zancen yake Mana ya koma yaro,Mami Fuska ta bata tace Ina ruwanku da idda ta kowa ya isheni cikinku idan Kuna tunanin Zan koma wajen tsohon ku to ku daina ba inda zanje,Nawaf yace Allah ya baki hakuri ya mike ya fice ya dawo part Dina harda tagumi shi a Dole Yana cikin damuwa,Ni da Nawwar muka kalli Nawaf Muka yi dariya,Nace Auta ga abinci na gama, yace bana cin abincin me ciki daga yawu sai Amai bazan iya ba,ki fadawa kawarki ta daina kallona a gida tunda ta auri tsoho na Mene zata dinga kallona sabo da Ina birgeta,Nawwar yace Wise din ce take kallonka ta San da zamanka ma a duniya,yace wlh ta sani ai Ina kallonta tana kallona kullum a fada mata Ni bana son matar aure sannan ka fadawa Mami in ta Gama Idda ta koma wajen Baffa,Baffa har kuka yake fa,Nawwar yace Allah Auta? yace ae baka gani ba abin tausayi jiya kasa kallon ball nayi wlh Zan tafi kallon ball ya kirani yace Autan Mami ya Mamin taku nace tana lafiya,yace har yanzu tana can da mijinta? nace ae, baka gani ba yaya Baffa zai min kuka wlh, nace Masa ya dawo da tsohuwar matarsa yace har abada ya Gama aure Wai aikin ma kwana nan zai daina zuwa, Kai Yaya ka tsira kana da kudinka idan Baffa ya talauce ni ya zanyi ko University ban Gama ba bare a samu a aurar dani,Kuma ni babban aiki nake so da me Baffa zai bani jari tunda Kai ka Zama na Mata na mata sai abinda Aunty Rabi tace in tace ka daina kulani ma dainawa zaka yi gaskiya a San yanda za ayi mune a ruwa idan baya Neman kudi kadarorinsa zai Fara siyarwa mu yanzu idan ta Allah ta kasance fa ya cinye kadararsa gashi bamu da aikin yi ya mutu ya barmu ba harka a'a da sake mu Baffa ne gatanmu wallahi Indai Ina nan a duniya dole mami ta koma ba a tausayinmu Kawai an watsar damu wannan ai ba yi bane, Baffa ya koma abin tausayi yayi kuskure ai ya gane ba sai a yafe Masa ba,ni gaskiya tana Idda Zan fada Masa gaskiya ta fito tayi idda da Zan iya walicci ma nine waliyyin Mami a sake daurawa na aurar da ita, dariya Auta ya bamu yana ta masifa sai ya aurar da Mami ga Baffa,Nawwar Tsaki yaja yace mahaukaci ai sai ka Zama waliyyin mu gani ni tashi ka bar min gida,kina ji Aunty a Haka zai iya rike mu idan ba Baffa? to Baffa dai ya dauki hanyar talaucewa ba ruwana kullum Yana daki Yana tunani ya fice ya bar gidan, Nawwar yace wannan Autan namu bashi da Kai,kyale shi Bari ya Fara University Allah yasa ya kawo wata yace Yana sonta wlh sai na Masa aure Naga yanda zaiyi lalataccen yaro,Ni dai dariya Kawai nake Auta da abin dariya kullum aure ne a ransa.
MASU AUDIO BAN YARDA A JUYA MIN LITTAFI BA BABU IZININA,NA RIGADA NA SIYAR DA WANNAN LITTAFIN
Masu sharhi Ina godiya
AsmaBaffa
[8/9, 10:59 PM] +234 806 192 9616: 🌼'YAR AIKIN KARUWAI 2🌼
MATAFIYA
BOOK 2
16-20
MASU AUDIO DUK WACCE TA JUYA MIN NOVEL ZUWA AUDIO WLH TA CI HAKKINA NA BAR KO WAYE DA ALLAH
NA RIGADA NA SIYAR DA NOVEL DINA.
Official
By
AsmaBaffa
SADAUKARWA NE GA
ZAINAB USMAN
*👭GARKUWAR MATA👭*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*
*GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi💯
Nono💯
Sanyi💯
Karin kiba💯
girmar hips💯
Ni'ima💯
Sabulai💯
Humra💯
Turarukan wuta💯
Matsi💯
Miski💯
Dilka💯
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari
DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
*08089965176*
*07084653262*
PAGE NAKU NE
BINTA UMAR ABBALE
MRS ALEEYU
MOM SANI
SALMA
AMMEY LAYLAH
INDO
LA REINA
BELLOMARYAM
MARYAMBELLO
AMATULLAH KAMSHI
A'EESHA
AISHA S MAIBANKEEY
MAMA GEE
ZAINAB HASSAN
RUKAYYA ABDULKADIR
Sultana da Nasira gulma suke yi Sultana tace kinji wai me yasa aka saki Mami nima a wajen Kawayen Mami naji suna gulmar da naje gidan Hajiya Suwaiba wai mijin da Mamin mu ta aura Hariji ne shine tace sai ya saketa,Nasira ta rike baki tace shi yasa kwana kadan aka sako Mana Mami duk ta rame tayi wani iri,Auta ne ya shigo palon daga wajen Nawwar direct gida ya dawo yaji ma hirar su Sultana amma ya nuna ma bai ji ba,yace wai me aka dafa ne? baka ci a gidan Yaya ba? matarsa tana da cikin zanci abincinta taje garin girki ta zuba yawu a cikin abinci,dariya sukayi Wise ce ta shigo sanye cikin Less gown tayi Matukar kyau dinkin manyan Mata sai walwali take yi,Aunty Ina yini dukkansu Suka gaisheta Banda Auta shi ai tsohuwar budurwarsa ce sai Yace Wise dama kina gari,ban sani ba dan banzan yaro ni kake wa wannan Iskancin taso muje dama aikenka zanyi ,Fuska ya bata yace da girman nawa amma muje zanje ya zanyi nazo a karami,Wise tana gaba yana binta a baya,Auta yaga mazaunai yace Ki tsaya a bayana mana ya za ayi ki wuce gaba Babu hijab Ni ba muharraminki bane Yana Kunkuni ya wuce gaban Wise Yana cewa za a lalata mutum,Wise a ranta tace inama banyi aure ba da yaron nan ya raina Kansa a fili tace Auta Ina da kanwa in kana so,akai kasuwa Ni ba a min tallan mace sai dai na gani nace tayi min ko Ido Kika fini,Papa ya aureki ni na auri kanwarki a gidanku zamu kare dama Miracle tana da kanwa ne to dama dama,Wise tayi dariya Kawai Suka shiga har bangarenta ko Ina sai kamshi ke tashi Yana sheki,Nawaf ya zauna a kujera yace su Papa an samu sabon jini ko kunya ya aureta uhmm Papa anji kunya.
Wise ce ta fito tace yawwa kaga Nawaf Kai ka waye ba ruwanka magani Zan gwada idan na gaske ne please,Auta yace wanne irin maganin karfa kiyi tsafi dani,Wise tace a'a maganin ciwon Kai ne,Kuma sai a gwada a kaina,tace please babu yaron da Zan gwada da shi sai kai ni da Kai fa 5 and 6 ne karka fadawa kowa kaji,yace to ba Alheri bane duk abinda akace Kar a fada to ba abin kirki bane,Kash Auta Wai mene haka Kawai rikewa zakayi a hannunka abinda kaji ka fada min,Auta yace kawo ya Mika Mata Hannu,ta Mika Masa wani Abu Kamar tsohon nama bushashe maganin mata ne idan me kyau ne da maza ake gwadawa ta bawa Nawaf, Nawaf ya rike magani nan take Antena ta mike ya Fara hada zufa ya Mika Mata abinta da sauri yace Yana Yi na gaske ne Papa ya shiga Uku,Dariya Wise tayi tace ka San na mene wai? baki ya tabe yace ke Kika sani me magani dai taci kudinta Yana yi sosai ya furta Yana Sosa Kai,tace ai ba a gama ba ga wannan rike,ya karba yaji baiji komai ba yace baya Yi wannan na karya ne,Wise tace bana son karya yace ko a Bude Miki ne ki gani Zan Miki karya ne mufa duk mun san abin nan Kuna rainani , ya tashi ya fice ball dinsa ya tafi.
Wise Kuwa Su star ta Kira tace na gaske ne Yana yi Auta ya gwada min,Star tace gaskiya Baki da mutunci yaron mutane zaki bawa suna dariya Wise tace ai Auta Yana da hankali babu me Jin zancen.
Washe gari dukkan su Cele makara sukayi,Ahsan ya Dade da tashi Yana ta Kiran Maheerah zaiyi Sallah amma Shuru lokacin Cele tana saman Sallaya tana Azkhar ta mike tare da Fitowa tazo Palo inda yake,hannunsa ta rike ya mike Yana duru duru tana jansa har toilet sannan taje Daya bedroom din ta samu Maheerah tana bacci,Tsaki Cele ta ja tare da tashinta tana bubbuga bayanta da kyar ta tashi,hannunta ta fisgo tace kizo ki kula da mijinki Yar iska idan kwana da namijj ne kin iya burinki a sa Miki itace a fadama ta jawo Maheera ta kaita toilet tare da nuna Mata Ahsan ta kula da shi, Maheerah a gabansa ta tsaya tana yatsina Masa Fuska tana galla Masa harara tana masa kallon banza,Hannu takai Wai zata mare shi sai ta fa ta Kai Masa naushi nan ma ta fasa wata uwar harara ta Masa tare da jansa tana Jin haushinsa har yayi wanka da brush tare da abubuwan bukata,Alwala yayi Suka fito ta shimfida Masa Sallaya tana zabga masa uwar harara sannan ta jawo shi saman Sallayar tana kukan karya Noorul Qalb kayi hakuri mutumin kirki da kai an jarabceka da wannan Lalaura gwalo ta Masa ta yatsina fuska ta sake Kai Masa Mari sai ta janye hannunta ta zazzage shi kasa kasa, Sallah ya tayar bayan ya Mata godiya, itama wanka tayi ta fito tare da gabatar da Sallah,bayan ya idar har azkhar cikin larabcinsa yace na gode matata Allah ya bani mace me kaunata me kula dani, Maheerah ta wani yatsina Masa Fuska tace idan ban maka ba wa Zan yiwa amma fa Ina bukatarka sex nake so ni bani da hakuri ka sani,Ahsan yace kina kallo bani da lafiya,oh nufinka sabo da ka makance baza muyi rayuwar aure ba yau kwana biyar fa rabon da ka min wani abu kasan kuma ya nake tunda baka gani ai wannan waje ba sai me Ido ba ma zai gane Hanya,Banda ni bazan gane ba cewar Ahsan,ba sai na saka a Hanya ba,bakinsa ya dan tamke yace bana mood yanzu baki da hakuri ki bari na samu nutsuwa a zuciyata bakya ganin halin da nake ciki.
Maheerah kwafa ta ja ta manta ta kori Ayusha ta kwanta baccinta ta barshi a kasa saman Sallaya, sai 11am ya tasheta yana fada Mata yunwa nake ji ya kamata ki sama min wani Abu naci tunda kin kori mai aikin naki,ko kulashi bata Yi ba Wai bacci take yi bayan tana jinsa, a hankali da lalube ya samu ya fito Palo tare da Zama a kujera,lokacin Cele ta gama girkinta tsaf ta fito ta ganshi yana hamma,tace karka cinye ni da hamma haka yunwa yake ji ne,tarkacenta ta kawo gabansa ta rike hannunsa tace Cele Rufaida,Murmushi yayi tace Sabahul khair,Kai ya jinjina Mata kawai, tea dinta data hada tasa spoon ta rike hannunsa tare da dawo da shi kasa ya zauna saman carpet yanda Suka saba cin abincinsu, Shayin ta ebo a Spoon sai da ya huce ta Kai bakinsa yaji spoon a saman lips dinsa bakinsa ya bude ta zuba Masa ya shanye,Ahsan a ransa yace Anya Kuwa bazan Yi Mata biyu ba,ai Mata biyu sunyi a rayuwa idan wannan ta Bata maka sai wannan ta faranta maka Allah yayi gaskiya mu larabawa da kudin ma Sai dai mutum ya Kara