Showing 33001 words to 36000 words out of 152911 words

Chapter 12 - Yar Aikin Karuwai 2

22 Oct 2024

4688

Cele tana kashe Larabci, hannunsa ta jawo harda cewa ta'al ta'Ali na'am shuwayya tana rikeshi suna tafiya tana cewa shuwayya Shuwayya a kujera ta zaunar da shi tace Ijilis,Yace Jalasna Wai ya zauna,Cele tace ya gane ya Gane na Fara iyawa a tafa min tana tafawa kanta Yana ta dariya Idonsa sanye da glass baya gani Wai, Maheerah Tsaki taja da larabci tace bata iya komai ba Babu abinda ta iya sai lalata Mana yare,tasowa tayi zata ta dawo kusa da mijinta Ahsan,Cele da sauri ta kankane shi tace karki zo Mana mu,Maheerah Takaici yasa ta tafkawa Cele mari Ahsan da larabci yace plate ne ya fashe haka? Maheerah tace Marinta nayi na gaji da abinda take min idan ciki ne nace bana so na hakura a sallameta Ni wallahi Zan iya zubar da cikin ma kowa ya huta,Ahsan yace mari haka wanne irin zalunci ne wannan ki mareta,ciki baza a zubar ba Ina son abina,Cele tace bashi Kika ci wallahi Kuma bazan tashi ba mijina ne ta kwanta a jikin Ahsan Yana kokarin janyeta yace Haram ya Subhannallah ya Subhannallah, Cele tace kaji da shi ta sake narkewa a kirjinsa tace Ina nan ta Sosa kumatunta tace fata gata Fara ashe karfi ne da ita kamar bayan kada,Ido suka hada da Maheerah ta Mata gwalo tace ke dai ta ko Ina baki hadu ba fata kamar bayan kada, Ahsan Yana so ya janye jikinsa Cele tace Kai dai baka San Dadi ba kafi son waccen me duwawu Kamar shape din Albasa, tashi tayi taje kitchen zata kawo Masa shayinsu da Suka Saba Sha,Maheerah ta koma jikinsa ta kanmake mijinta Cele ta fito ta ajiye shayin tasa hannaye ta fisgo Maheerah,ita Kuma ta manne a jikinsa,Ahsan yace shayi zai Sha Cele tayi sauri ta ebo shayin a spoon ta Kai bakinsa Maheerah tace wlh bazan yarda ta kwace min miji ba sai dai muyi ta yi ta Shige kitchen itama ta hado shayinta da snacks ta kawo Suka tsaya su biyu akan Ahsan Cele tana bashi Shayi Maheerah ma ta ebo nata ta Mika Masa shi kadai yake dariya a ransa dukkansu ya dinga karba ko wacce ta bashi ya karbe Yana Sha,Maheera ta dauki Snacks Ana shafa Masa gashi noorul Qalbi ta Mika Masa ya gutsira Yana ci,Cele ma ta shafa gashinsa tace ni harda gemun Zan taba duk da ni Haram ce to nace Haram nima ta shafe gemu da gashin Kansa shi kuma Alhaji Salmau Yana zaune kurum abinsa,Maheerah ta duka zata Masa kiss a lips,Cele ta durma mata duka a gadon baya ta bangajeta ta kwace Snacks din itama Wai ita zata bashi Ahsan Yana ji Yana ta ci shi kam Mata biyu akansa suna ta masifa,Maheerah tana zuwa ta fisge shayin ta Kai kitchen ta zubar duka ta dawo ta kwace Snacks din ta maida kitchen tace ya koshi da larabci,Ahsan yace shi bai koshi ba Yana masifa,Cele ta fahimci me yake nufi ta Shige kitchen ta Dora indomie tana Mata hadin Nigeria Amma bata sa yaji ba,Maheerah ma kitchen da shigo ta dasa tukunya tana girkinta na larabawa itama Cele tana nata duk a cikin Ahsan za a bashi, Cele ta riga Maheerah gamawa.

Tana zuwa ta kawo Masa ta dawo dashi kasan carpet ya zauna tasa fork tana bashi a baki yana ci sai ga Maheerah ma da nata a plate ta zauna suke jere ita da Cele,Cele ta matsa jikinsa Kamar zata shige cikinsa Maheerah Kuma ta biyo da abincinta ta saman Kan Cele ta shallake zuwa bakin Ahsan,Ahsan ya gaji ya shiga surfa bala'i da masifa yace baya cin na kowa a cikin su sun dame shi ya mike Yana lalube da kyar ya koma bedroom shi Dadi ya isheshi Mata sai fada suke a kansa.
Maheerah ce ta bi bayansa harda sawa kofa key Kar Cele ta biyo ta,Cele tace zaki fito ma.

Kannen Wise su Uku Mata ne Suka zo wajen Wise sun kawo Mata Ziyara,Tunda Auta yayiwa Iyamami fata fata bata sake Shiga Harkar Wise ba sannan Iklima ma tsorata tayi ta gudu garinsu Amma har Yanzu Iyamami da sauranta,Kannen Wise Suka ce Aunty yau kwanan mu hudu ko kofar gida bamu je kisa a kaimu yawo,tace Zan kaiku da kaina amma Bari nasa Nawaf ya kaiku gidan su Rabi ku gaishe su,Wise a waya ta Kira Auta tace Autan mu,yace Ina jinki dan Allah su walida zaka Kai gidajen kawayena su Star,yace karfe nawa? tace 11am dai tunda yawon nasu da yawa,yace to su shirya Amma Kar a barni da jira, sun ma shirya su Kai suke jira kaga yanzu 10am yace to gani Nan.
Auta wanka ya dauka cikin kana nan Kaya kamar zai bar kasar 11:30am yazo yace ku fito Suka fito suna ta kallon Iyayin Auta,Walida tace gashi kyakyawa haka shi dai Auta bai San suna Yi ba har Suka je jikin mota yace Babbar ta shigo gaba,Suna kunshe dariya Walida ta shiga gaba,Yana shiga ya kunna uban kida,Walida tace wow haka nake son mota da kida amma sululu motar wasu ba dadi,Auta yace wannan motar manyan Yara ce ai,Suka ce munga alama,Iyamami ce ta wuce tana musu kallon banza a cikin mota tace ai fa mun shiga Uku an auri jinin kudi kullum dangi suna Nan Kai Kuma bawan Mata da kaga Mata shike nan sai ka kasa zaune ka kasa tsaye,Auta yace ya ranki ya rufe mota yaja yayi gaba,Walida ta zake da yawa ita a Dole sai ta nuna ita wayayyiya ce a wajen Auta,Bata San maza Indai mutum na kirki bane me zakewa da nuna ta waye bata birge su,Yan matan yanzu da yawa haka suke burinsu su nuna su fa sun waye suna wani fitsara Wanda wannan baya birge mazan.

Gidan Star ya Fara kaisu tana kitchen tana girki Malam Abhulkhair Yana ta yanka Mata salat ya zauna dirshan a kujera,ana Sallama Suka amsa Auta yace baki ne mu shigo,Malam yace Muna zuwa yace da namiji Nawaf ya balaga saka Hijab,Star tace to ta saka hijab har kasa ya bude kofa yace ku shigo Nawaf Kaine ka kawo kannen namu kenan? Yace ae suka zauna,Star yace Dan duniya shine baza a dinga zuwa gaishe bi ko ya Jin Dadi? Auta yace Jin dadi ai sai me aure Abhulkhair ya dinga dariya,Star ta kawo musu kayan ci da sha, Abhulkhair ya koma kitchen Yana kula da girki su kuma suna ta hirarsu,Auta yace Malam guda a kitchen ko ni da ba Malam ba ai baza a min wannan rainin ba,Star tace wlh karka cika baki yaro,sun dade a gidan Star sannan Suka tafi gidan Yar Zabil,Nan ma sun dade,sai gidan Mandula da Sera daga Nan Suka yada zango a gidan Nawwar daga nan sai dare ya maida su gida harda siya musu kayan makulashe.

Sabreen yau tana gidan Santana tana kallon soyayya Kawai burgeta sukeyi sai taji wani haushin kanta da Dana sani da yanda ta samu Miji na kirki ta tsaya shirme gashi yanzu Kamar Santana ma ta rasa, Bayan Santana ya fita Jamcy ta rakashi ta dawo tace sai rayuwarku take birgeni Jamcy idan na tuna abinda nayi Ina nadama gashi na rasa kowa ko me matar ma ban samu ba Kuma auren nake so,a shirye nake idan na samu Miji Zan daina Shan komai cuta dai na Riga na cuci kaina,Jamcy tace Ni kaina da ban zaci Zan so Santana ba sai gashi zabin Alkhairi kullum cikin nishadi nake sai Naga shaye shayen da Muka dinga Yi rayuwa ce Kamar ta dabbobin da Basu San me suke ba,a da har mijinki na so Sabreen na so na Miki kwace sabo da kin kasa fahimtar gaskiya shaye shayenki yayi yawa Amma hakan Bai faru ba Nima ban cimma burina ba Allah yasa aka hadani da Santana wannan rayuwar ta fimin daraja da mutunci akan shaye shayen da ya Zama ruwan dare ga Mata da maza Ni Kam na daina Ina Miki Addua kema Allah yasa ki daina, Sabreen tayi mamaki tace yanzu da Nawwar yace Yana sonki sai ki yarda? Da gudu wallahi ke dai Allah ya kiyaye Kawai,Sabreen ta Sha mamaki tace rayuwa kenan gashi na rasa kin rasa shike nan,gobe Zan tafi garin su Mama zanje nayi sati daya,Jamcy tace Allah ya kaimu Dan Allah ki gaishe min ita,zata ji Inshaallah.

Mami yau taji Baffa zaizo Auta ya fada Mata tun sassafe take gyara part dinta tana kalkale kalkale sai kamshi da sheki ko ina,ta shirya girki lafiyayye taci kwalliya cikin hadadden leshi sai kace wata budurwa harda sa Riga da skert sai kace wata matashiya haka Mami ta koma ta kafe dauri,Nawwar bai sani ba ya dawo daga Office part dinta ya wuce direct tun daga Shiga yake karewa ko Ina kallo dan gyaran na daban ne,Mami ya samu a bedroom ta tsaya jikin mudubi tana ta kallon kanta tana zancen zuci ita kadai,shiga yayi da Sallama ta juyo da sauri,ya bita da kallo yace amma party Zaki je ko? Party Kuma bana son Iskanci yau ka taba gani Ina saka Riga da skert,Uhmm Nawwar yace ko dai bako zakiyi,ban sani ba karka dameni da tambayar masifa bana son irin wannan Auta ma Nema yake ma ya fiku hankali, Nawwar yayi dariya yace Baffa yace Auta ya fini kema kince Auta ya fimu ai shike nan,Duk yarana babu me sanin yakamata irin Auta Kai ai girman banza ne dakai,Nawwar yace yau Kuma Mami,Allah ya baki hakuri ga Auta nan Indai shine,Kudin da Kika ce na tura Miki tace na gani na gode Allah ya Kara budi yace Ameen ya juya ya fice, Yana shugowa bangarena na buya a bayan kofa na tsorata shi

Dariya yayi yace Dan cikinki Zaki tsorata ba ni ba Muka haura sama,nace yau akwai show a gidan nan yau Baffa zaizo inji Auta,Nawwar yace no wonder ai naji a jikina bako Mami zata yi irin wannan kyau haka yau,ba a dade ba Driver ya kawo Baffa sai kace wani Ango ya Sha fararen Kaya harda babbar Riga sababbi gal,tare da Auta aka zo shine dan Kira shine me iso,Palo Suka shiga da sallama Auta yaga gyaran Mami sai dariya yake boyewa ya haura sama yace Mami yazo fa ki fito,Mami harda bata rai Wai aji tace gani nan,Auta ya dawo yace Baffa gata nan,Baffa yace to jeka abinka,Auta ya fice ya dawo part din Nawwar ya barsu.

Bayan sati Daya Maheerah ta shirya da dare zata fita Ahsan Yana Main palo Cele ma haka da littafinta tana bitar larabcinta a gabansa idan ta fada da yarensu sai ya gyara Mata yanda ake fada dai dai tana fassarawa da Hausa shima sai ya rike hausar yasan me ake nufi a haka suke karatun,Cele ta kalli Maheerah tace da tsohon Daren nan Zaki fita gidan uban wa zaki je wato kwartanci Zaki tafi kenan to baza ki fita ba,Maheerah ba Jin hausa take ba ta juya zata fita Cele ta riko rigarta tace wlh sai dai ki Kira kwarton gidan nan yazo na ganshi idan da rambon Zan masa bille kaciyarsa to yazo,Maheerah bata sani ba ai kuwa ta koma daki tace da Saurayinta yazo gidan tunda dai mijin Nan nata baya gani ita a bukace take yaga wancen karon yazo ya fita lafiya,wannan karon ma sai yazo a gaban Ahsan Suka wuce ciki,Cele dama labewa tayi a dakinta suna shiga ta fito ta dakko sabuwar reza data gani a dakin, Maheerah ta nemi key din dakin ta rasa haka ta kulle ba key sunyi tsirara a dakin suna Masha'arsu Cele ta Shige ciki,Balaraben nan yayi mugun tsorata,da larabci yace wannan wacece? Maheerah tace wacce aka yiwa dashen ciki ce ta dameni ta hanani sakewa Ina ganin Nan gaba gidan nan Zan bar mata shi Kuma Ahsan baya so a taba ta ko kadan na gaji,Saurayin yace Yana makahon ya Zama miskini Amma ya dinga takuraki,Cele taji ance miskini tace na miskinawa Uwarka zagi,tace yau sai na maka bille a kaciyarka shege me Kan fir'auna ta nufe su Suka tsorata sunga ta zaro reza tace wlh sai na Miki bille a Fuska irin na Nigeria Zaki ci ubanki yau,na taba ganin Yar iska irinki da mijinki sabo da baya gani ki koma kawo kwarto,rayuwa Kamar ta dabbobin dama haka kike yi ku ba kunya ba tsoron Allah,na taba ganin tashin hankali irin wannan wannan wanne irin masifa ce wallahi yau baza ku tafi free ba.



BAN YARDA A MAIDA MIN DA NOVEL AUDIO BA BABU IZINI NA,MASU AUDIO KAR KUCI HAKKINA

GA MASU SIYAR MIN DA LITTAFINA BAN SANI BA KU SANI KUN CI HARAMUN WLH KO NI KYAUTA NA BAYAR KUNA SIYAR MIN DA NOVEL







AsmaBaffa
08061929616
[8/9, 10:59 PM] +234 806 192 9616: 🌼'YAR AIKIN KARUWAI 2 🌼
MATAFIYA


BOOK 2


26-30


Official

By
AsmaBaffa


SADAUKARWA NE GA
ZAINAB USMAN


MASU AUDIO DUK WACCE TA MAIDA MIN NOVEL AUDIO BA IZININA TACI HAKKI NA TACI HAKKIN WACCE TA SIYA,KUJI TSORON ALLAH.


PAKE NAKU NE



Ina masu bukatar unique kitchen utensils . fabrics adult and children's wears shoe's and bag's.
Da masu bukatar ahada musu lefe ko masu bukatar iya luggage's din kawai duk inkazo
R&U EXCLUSIVE KITCHEN AND MORE.
Zaku samu duk abinda kuke bukata ko a awanne state kake zaa kawo

Masu bukata ga number. 0703 455 9202

https://chat.whatsapp.com/LAizQA6PofSLoFhQ7XeaQx



Kwashe kayan karton Cele tayi tare da na Maheerah sannan ta Kama kunnen kwarton tace wato Kai kunnen kashi ne dakai matar wani kake bi har gidan mijinta Kai ga tsohon bunsuru,kasa magana yayi ya hade hannaye biyu Alamar bada hakuri Cele ta Kama gashin gemun ta yanke rabi ta bar Masa rabi tace kana motsawa Dan ubanka wlh sai na tsaga ma jikinka,bai San me tace ba ya mike zai gudu ta zabga masa duka a dokin wuyansa tace zauna,So yake ya kwaci Kansa shi ba lusari bane gani yayi da gaske Cele zata wulakantashi ya tashi ya kwaci kayansa ta karfi Yana zage zage,ya duka Yana kokarin saka wandonsa Cele tasa kafa ta daki duwawunsa ya tintsira Saura kadan ya fadiya juyo a zuciye ya Mari Cele sabo da kwallon Dan Iska ne bashi da mutunci,Cele haushi yasa tasa Rezar ta tsaga Masa bille kato a barin duwawunsa daya, larabawa da kwailo ihu ya saki ya kwalla Kara ko wandon Bai karasa sawa ba ya fice da gudu,Ahsan Yana Palo yaga kwarton ya fito da wando a hannu da riga Yana Kare gabansa, Maheerah Cele ta kalla ta fada toilet da gudu ta kulle da key Cele tace Zaki fito ne wallahi ko ba yau ba kafin na bar gidan Nan sai na Miki billen Yan fulani.
Maheerah ta tsorata yanda taga Cele ta tsagawa Saurayinta duwawu cikin dare ta fice daga gidan gaba daya ta tafi gidansu Kai Kara gwara a dauki mataki akan cele gaskiya ta gaji.

Ahsan ne ya shigo dakin Cele da lalube Yana so zata bashi shayi ta fito da wanka zata Yi Shirin bacci ta ganshi zaune a gefen bed dinsa tace gaskiya makafi da basira suke ji yanda ya gane Yana iya zuwa da Kansa,ganin baya gani Cele tace su Saluhu ba a gani me Zan zauna Ina wahala ta cire towel din ta jefar sintir da ita,Ahsan dariya ta kamashi ya boye ta a ransa ya sake zooming idanuwansa Yana ta Shan kallo a hankali yanda baza ta ji ba ya furta Astagafurillah,Cele taje jikin mudubi harda karewa kanta kallo tayi girgiza tace Kai cika fa nake duk na bude sai kiba nake kalli jikina ga cikina tumbini ko cuta ce oho, Abubuwa haka Kai Cele kinfa hadu sai babban Alhaji, Ahsan ko kyafta Ido bayayi ya manta shi makaho ne,Jin zaiyi loosing control ya rufe idonsa har Cele ta shirya ta gama komai ta saka kayanta Riga da skert sannan tazo gabansa tare da rike Masa hannu tace Allah sarki Dan makahon Maheerah,Idonsa ya Bude a hankali yayi wani ja,Cele tace Kai Kuma lafiya uhm ta ja shi ya mike tsaye,Mutumin ba hakuri hannunta ya fisgo ta fado kirjinsa ya rungumeta sosai abinda bai taba ba,Cele tayi lakwas tana shakar kamshinsa,kanta ta dago a hankali tana kallonsa tace Haram,Kamar ta tsikara Masa Allura ya matsa da sauri daga jikinta yana istingifari,dariya ya bata yace uhm ta rike hannunsa Suka fice
Washe gari Ahsan ganin Maheerah bata gidan komai Cele sai taga Yana yi da Kansa normal ya dawo Yana gani,Ido Cele ta zaro Murmushi ya saki ya nunawa Cele da hannu Wai Yana gani dama amma tayi Shuru da bakinta,Cele tunawa tayi jiya ta gama tsirara a gabansa Takaici ya kamata da kunya ta tashi ta gudu daki ta buya tana cewa wayyo ya ga komai nawa shike nan,dariya Ahsan yayi yasan me ta tuna.
Tunda ta buya bata fito ba sai da me karatu tazo Hajiya Hauwa tazo ta koya Mata ta rubuta sosai ta tafi ta bar Cele da hadda.

Baffa Yana zaune ya hakimce,takun mutum yaji ana taga steps a hankali,wani kamshi na musamman ya daki hancinsa,a hankali ya juya Suka Yi Ido biyu da Mami,Ido ya zuba Mata ta wani tsare gida wai aji ita,Sallama tayi Masa ya amsa da fara'a ta zaune ta wani kame, ko gaisuwa babu ne Baffa ya tambaya,Mami Fuska ta yatsina ta dauke kai, Haba ranki ya dade tuba nake yi har yanzu baza ki yafe min ba ne, haba my Uniform ko Ina Zan Shiga sai dake,me farar aniya, idan ba ke a rayuwa ta bazan taba rayuwa ba cikin Jin dadi,shifa tuwo duk darajarsa sai an Sanya miya,bazan sake rikon ki da Wasa ba har abada,kece me sharen min hawayena bazan sake saka ki kuka ba,Dan Allah kiyi hakuri ki yafe tunda

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login