Showing 141001 words to 144000 words out of 152911 words
buya, jikinsa ya Nuna yanzu bashi da damuwa,Itama Umma haka,Liman ya bude taro da Addua Wanda Umma ita bata ganewa sabo da Halin da take ciki,Liman ne ya ja Aya ya jawo hadisi,Umma bata hayyacinta sai dai aji tana ta faman furta Allahu Akbar irin tana jin waazin nan,liman yayi nasiha sosai sannan yace dan Allah kiyi hakuri haka ki koma dakin Mijinki,Sauran Yan uwan Umma suka ce to Dan Ubanta ma ita bata laifin ne shike nan ayi ta bin mutum sai kace me zuciyar dutse ai itama tana da manya ba da kanta take ba,sabo da haka mu mun Yanke yau zamu Maida aure,Umma ce tayi magana tace Kawu ai na hakura to mene ma rayuwar duniya,duniyar kanta nawa take Kuma dai zan koma sabo da Yaya na badan shi ba,Ko ke fa mu baza mu koma gida ba Aure zamu Maida a masallacin unguwar nan,Umma tayi musu shuru suka fita suka Tara mutane a masallaci aka Maida aure suka dawo,Su Rahma ne suka dawo suka ji ana zancen yaushe zata tare,Umma tace sai dai Yazo ya sameni a gidana ni bazan koma gidansa ba,Aka yi aka yi tace wlh baza ta koma wani gida ba tana gidanta,Uwa duk sun San taurin kan Umma,Uwa tace to ai da Kai da kaya duk mallakar wuyane ni ku barni a can ku zauna a nan,Abba yace a'a ni bazan iya barin Uwata ita kadai a gida ba waye zai kular min dake Abba Allah ya yishi da biyayyar Uwarsa sai abinda take so dalilin Hakan ya fada halaka sabo da sai abinda take so Shima shi yake so.
Umma ce tace ai nan gidan part biyu ne Uwa ta zauna a wancen bangaren mu Kuma a wannan ba shike nan ba,Abba yace Uwa Hakan yayi Miki? Idan bai Miki ba kawai mu koma gidanmu haka na dinga zuwa,Uwa tace Hakan ma yayi ba komai,sai da suka gama saita komai sannan suka bar gidan har Abba,yana fitowa ya kirani na daga ya fada min yace amma abinda Bai min ba wai sai dai mu zauna a gidanta shike nan Ina Namiji Kuma Ina zaune a gidan mace ai bazan ji Dadi ba,Nace tunda an daura Abba Karka damu ka dinga zuwa haka zuwa Dan lokaci kadan zamu maka wani Karka damu Karka fada mata kayi shuru kawai,yace Allah ya muku Albarka oh duniya Ina ganin Ishara matan da na guda Abba ya fashe da kuka,dariya nayi nace Abba ai ya wuce kaddarar mu ce ta jawo haka,Abba yace kaddara ce ta jawo Uba yaki yayansa,nace ba abinda bazai faru ba,Amma Abba yau kaje can ka kwana Karka bata space zata sake rainaka,Abba yayi dariya yace to shike nan Me local government,ance ke har local government ce dake,Abba bai San me ake cewa local government ba,Nace Abba wani birni ne a kusa damu fa nace Ina son garin shike nan akace Ina da local government,Abba yace to madalla ya kashe wayar,Cele ce ta Kira shi Abba ya fada mata yanda komai ya wakana,Cele tace ta kwana gidan Sauki Abba Karka damu za a San abinyi zanyiwa Rabi magana,yace na gode Yan Albarka.
Umma kuwa harda Yan hada magungunan na tsumi ta sha Abba kawai take Jira yau baza ta iya hanashi komai ba, amma da Babu magani da Abba yaji jiki a Hannun Umma kafin ta yarda da shi,yanzu kuwa jiransa take kawai.
Raheemah suka gyara gidan na musamman suna cewa Umma Amarya sai su Kalli Umma suce Amarya Umma,bata kulasu ba har su Nazifa suka zo gidan suna Murna sunji labari,sai wajen Magriba suka bar gidan,Bilkisu ta tattara Rahma da Raheemah tace kuzo mu tafi kuyi min Dan kwana uku suka bita aka bar Umma ita kadai,Uwa kuwa ana daura aure ta tafi gidan Yar uwarta wai zata yi sati kawai Dan ta bar Danta ya Shana.
Abba yana Sallar Isha aka siyi su nama da kayan makulashe aka tafi gidan Umma,Yana zuwa yaji ko Ina ya dau kamshi yace af af na fada yanzu zan samu nutsuwa irin wannan kamshi haka, Sallama yayi ya shiga a Palo ya sameta tana zaune tana kallo a zahiri amma a badini zallar sha'awa ce ke cinta,Abba zama yayi a gefenta yace Hajjaju makkatu, murmushi tayi tace ai sai ka bari naje tukun,Abba sai wani kallon Umma yake yace uhm halina dake yanga tun da fa na sanki duk yaranki Basu yo ki ba a yanga,Umma dariya tayi tana dauke Kai,Abba yayi murmushi yana kallonta yace bana hayyacina sai kallonki nake yi irin wannan kyau haka wa zai ce kece kika haifi su Bilkisu ai sai ace Bilkisu kanwarki ce ma,Kullum wata Yar budurwa kike dawowa,Umma ana mamular labba hadi da murmushi tace hmm uhum uhum, ga hanci Malam kamar Karas cewar Abba harda dafa kafadar Umma Yace wannan Dinkin fa wanne tela ne ya tsara min Matata cikinsa haka kinyi kyau,Umma dai ledar ta Bude tace me ka siyo ne sai kace wata budurwa,ai kinfi budurwa a wajena,kyauta aka bani budurwa me zanyi da ita yana magana yana karkada kafa daya irin yana hutawa din nan,kayan makulashen su suka ci,sannan suka wuce bedroom,Abba harda yin wanka Umma ta fito da wasu kaya a akwati tace ga kayanka Rabi ce ta kawo tun farkon zuwanta tsarabar Makkah nice na hana a baka gasu nan jallabiyoyi ne guda hudu sai turarukanka,itama siyensu tayi bata San zata ga iyayenta ba shine dai ta taho maka da su Nima ta bani kala uku dogayen riguna,Abba yace yaran nan tsakanina dasu sai Addua,Umma tayi Shirin baccinta itama ta Saka rigar bacci,Abba jallabiyar ya Saka tare da hayewa saman bed din gefen Umma,Yace gashin nan dai yana nan gashi baki wuluk dashi ya fara shafa shi daga nan suka tsunduma cikin duniyar Dadi yau an tuna baya,suka rakarkashe abinsu kamar ba gobe.
Sabreen kuwa sai da bikinta yazo gaf taji wai me yasa ma tace ya kawo kudi gashi bazawara ce ba Jira kawai Papa ya Yanke sati biyu gashi bikin ma saura sati ba dama tace ta fasa.
Bikin Gaji ma Jira suke Rabi tayi arba'in sannan ayi bikin,abinka da me kudi maganarsa ake ji har matsayi ne da ni Rabi sai sanda nace ayi auren za ayi, har gadara nayi nace a bari sai nayi arba'in akace ba damuwa .
Ahsan ne yace da Cele kiyi sauri ki gama abinda kike mu tafi tace to,a Kaduna GRA ya siya mata katafaren gida tace ta barwa Abba gidan su tare da Umma kawai,Abba sai murna yayi gidansa me kyau na gani na fada,haka Umma ta hakura suka koma ciki har Uwa gidan Umma Kuma ta zuba Yan haya wani Ango ne manager bank ya shiga ciki da Amaryarsa,gidan Abba ma dai wani ne Shima sabon Aure ya karbe shi haya gida me kyau an kashe masa kudi,Cele tace da su Bilkisu zata Bawa mazajensu jari Bikiisu tace a'a karki sake ki bawa mazan mu wlh suje suyi mana kishiya maza ba Yan goyo bane duk suna da aikin yi da rufin asirinsu Kuma dukkan mu muna muhalli me kyau kawai mu ki bamu jarin mu kama business ki bude mana katon shago mu uku ni Nazifa da Nazira mu dinga juyawa shike nan ma ya ishe mu,Cele tace to kin San Miji ba daga aure zai ta baka kudi ba Amma ki bari abinda ke hannuna da ni da Rabi sai mu hada a bude muku a hankali,Bilkisu tace dama duk kudin Namiji zai ta daukan kudi yana baka ne sai dai da dabara har ka samu rabonka,Cele tace shi yasa fa na nace masa sai ya siya min gida shine na barwa Abba shi kawai dama sabo da Hakan nayi,yanzu yace nashi gidan zai siya a nan garin su Miracle nace ya siya wannan nashi ne ba nawa ba,Bilkisu tace Dan ubanki ya siya Miki ba wani zama zakuyi a nan ba gida ai kamar naki ne da yaranki,Cele tace tun yaushe ma zan karbe takardun Jira nake ai ya siya din wata sabuwar gra ce ake ta gina gidaje a nan zai gina gidan Nawwar ne zai wuce gaba ayi komai,Bilkisu tace Masha Allah yar nan kunyi dace sai dai a dage ayi biyayya.
Suna gama wayar Ahsan ya shugo da zanen gidan da yake so ya nunawa Cele yace yayi mata? Cele tace ae yayi,yace Idan munje Saudi fa dole na bar aiki a asibiti sabo su tsarin saudiyya indai ka auri ba Yar kasarsu ba to zasu koreka daga aiki Kuma ko me ka tara baza a bawa yaranka gado da ka Haifa da ba Yar kasar ba,shi yasa in kasan haka to ka bar aikin gomnati kawai sannan duk abinda Yayanka zasu gada ka kaisu garin uwar yaran haka suke yi wannan ba karya haifaffen dan Saudiyya baya auren yar wata kasa taci gadonsa yanzu ne ma suka dan sassauta abin nasu amma aiki dai baza ka musu a karkashin gomnati ba indai sun San ka auri wata ba Yar kasa ba,shi yasa suke aura a boye ba tare da an sani ba ko Kuma suyi ta Zina kawai suna son su aura amma da matsala,Cele tace to ai kana Business wannan Kuma ba a karkashin gomnati kake ba,yace ae ai shi yasa ma tun kafin na aureki na ajiye musu aikinsu dama na gaji da aikin,Cele tace to duk wata kadara ka siya mana a nan yanzu gaskiya yace Inshallah,tace a Arewa Kuma yace ba damuwa ai komai ma na dukiyata Basu da hadi da gomnati duk Yan uwana sun sani komai da yardar su nayi.
Washe gari Omar Baso shi ya fara tashi a bacci yayi Alwala ya wuce masallaci Omaira taji sanda ya tashi Yana fita ta tashi itama tayi brush tare da Alwala ta fito ta gabatar da Sallah tana zaune tana Azkhar ya dawo ya zauna a gefen bed yana jiranta ta gama ta juyo tace Ina kwana ka tashi lafiya,Baso yace ragas ke fa? tace Yar lafiya dai,murmushi yayi tare da shafa sumarsa Omaira ta Kalli gashinsa tace askin ya maka kyau,yace ke kin auri fine boy kamata ai mu komai sai me kyau muke yi,Murmushi tayi ta koma ta kwanta bargon ya ja musu suka koma bacci,8am suka ji ana bubbuga gidan tsaki ya ja ya fita ya Bude yaga abokansa su Only Yan kwaya akan yace su dawo gobe shine suka yi uban sammako suka zo,ba yanda ya iya yace ku shigo Yan iska sai kace dole ko da ku aka daura mana aurenta ai sai haka,suna dariya suka shigo Palo sai ihu suke sun San gidan amma cewa suke yau she aka gina wannan gida,gaskiya gidan yayi shege mutumina irin wannan gida haka Kuma har furniture din da su aka shirya su amma kwaya ta sa sun manta,Baso yace ai baza ku gane ba tunda bakwa ganewa,Only yace Allah waccen gidan ne? Wanda dai muka sani? Karya ne magina ka kawo suka canja komai,wai Ina Amaryar tazo tayi mana girki,Rabona da abinci tun jiya da dare cewar wani Jaga,Omaira wanka tayi a gurguje ta shirya cikin leshinta na lefe tayi kyau Riga da skert taci dauri ta fito Palon taga su Only suna ta hauka,Only harda mikewa ya Sara mata kamar Soja,suka ce Aunty ya aka yi ne wai,Suka daki kafadar Baso matsiyaci wannan ta gaban mota ce Ina ka samo ta,Omaira tace Ina kwananku suka ce ba yawaa ba yawaa karki damu ba sai kin gaishe mu ba yawa ne kije ki shirya mana jullof din tafiya,Jaga yace ki hadata da wake,wani da ake Kira da Hayaki yace ki Kara da Alayyahu,wani Shima yace da shayin wiwi Aunty a kawo ki dafa mana,Baso ya dura musu ashar yace zaku bar gidan nan wlh mahaukata,Only yace ya naga Kwan Palon guda Daya ne ya kawo haske? Baso yace ka hau ka gyara shi ga tv nan ka hada ta sune dama jiya baku karasa ba,Only akwai shi da basirar gyara Abu indai zai taba maka Kaya sai ya iya gyarawa,kujera ya taka yace miko min star din nan,ya bashi karamar star ta kwance abu Nan take ya gyara kwayayen Palon duk suka dauka,ya dawo ya hada musu tv din da komai har settelite shine ya hada musu yace Umarun Farooq ga channel din shegun a bar muku su,yace wlh zaka bar gidan nan channel din Bf din zaka bari,ai irin taku ce masu aure,Baso ya dada masa duka a kafada yace Dalla cire su,suna dariya yayi hiding nasu,Omaira dai tana ganin ikon Allah ta wuce kitchen ta dafa shayi tayi soye soyenta tayi warming naman jiya ta kawo musu komai ta jera a gabansu,suka ce Ina taliyar? Baso mikewa yayi ya jata kitchen yace kwaya ta cinye musu ciki Queen wannan soye soyen ba abinda zai musu ki dafa musu taliyar, Omaira tace wai kaima da haka kake? Yace ai na fisu hauka ma nine ogansu fa tunda Oga ya tuba inshallah yaran ma zasu tuba ne komai sai a hankali,Omaira tace to bari ayi musu yace yanda suka ce haka Zaki dafa fa,Omaira tace kana shagwaba su,yace baza ki gane ba mu fa sanda Ina talaka dukkansu sun fini samun kudi ba Wanda bai taimakeni ba a cikinsu tare da su muka rike Salma bata yi kukan yunwa ba ko baki gane bane? Omaira tace to ba Alayyahu ba kifi tunda ba a kawo ba,yace dafa musu haka zasu ci watarana ayi musu yanda suke so,Omaira ta dora musu girki kafin ta gama har Omar din sun cinye soye soyenta sun sha tea dinsu,Only yace Aunty muna jiran taliyar mu,sai da ta gama ta kawo musu a flask suna ta murna ko a plate Basu zuba ba a katon flask din kowa yasa cokali suka cinye tas Banda Omar Baso ya koshi shi, suna cinyewa suka tashi suka ce sai watarana Kuma Aunty a kula da Oga sosai,Omaira tace to ku gaida gida suka Kara gaba,suna tafiya Omar ya jawo Omaira ta fado jikinsa a kunne ya rada mata kin ci abinci? tace ae a kitchen naci,yace to duk Wanda Yazo a cikinsu indai yace zai ci abinci ko babu sai iya nawa ne kawai ki bashi ya cinye,kawai dai Idan Zaki fito ki Saka hijab kar a kalle min Matata,Omaira tace to shike nan lallai kana son su,yace gudun kar su min hauka a wajen daurin Aure yasa ban fada musu ba sai da aka daura,Baso ne ya mike yace bari na tayaki aikin tare suka gyara gidan ko Ina da ko Ina, fita yayi ya yo mata cefane 11:30am ta shiga kitchen zata yi girki,Yajin Albasa ya shiga idonta Baso yana kitchen din yana dariya ya mike tare da rungume ta ta baya ta cikinta ya zuro hannayensa yana yanka mata Albasar a haka yana tsokanarta da Yar gatan Mubaraq tana dariya Kasa kasa,yace yau zamu fita yawo ko? Omaira tace daga kawo Amarya jiya,to mene a ciki ni bana son wannan abin na mutanen mu fita zamuyi a machine ko a mota? Kana da machine? Baso yace sabo ma siyensa nayi Ina son machine yace irin kirar lifan ce da shi,Omaira tace to Allah ya kaimu.
Su Baso an Saba da tashanci wajen magriba Omaira ta shirya cikin kana nan kaya ta dora Abaya tare yin da rolling,Baso kuwa shadda ya Saka fara Kal ita Kuma cikin bakar a baya,a gaba ya sa Omaira maimakon a bayansa tana gabansa suka fita Ya bawa machine wuta,ga Baso popular duk inda suka wuce sai an samu Wanda ya Sanshi ana ta daga masa hannu ko yayiwa mutane horn,Baso yace dole ki koyi machine Omaira tace bazan iya ba sai kace Cele,Ko ayi Miki tukin tsaye Omaira tace ni dai a'a Dan Allah kar muyi hatsari,yace to da kafa daya fa?,ni dai a'a cewar Omaira.
Wajen shakatawa ya kaita wuri ne me kyau Omaira tana kallo tana nishadi harda riketa yace taka a hankali kar a fama ciwon jiya,dariya tayi tace yi mana pics ya dakko wayarsa ya dinga daukanta pics ya shiga suka dinga Selfie,sai bayan sati daya sannan Nazifa ta Kira Omaira ta fada mata an Maida auren Umma da Abba ta bata labari,Omaira tayi murna itama,lokacin Kuma ana gobe daurin auren Sabreen Baffa yace a daura Dana Hamra tunda shi Mijin Bai gama gidansa ba daga baya ta tare ai yace sai saura sati biyu ya gama,ba Shiri ba komai duk har lefe sai daga baya za a kawowa Hamra,Angon Hamra sai murna yake da danginsa duk sun yarda a hada daga baya a Kai Amarya,washe gari Friday ana idar da Sallar juma'a aka daura auren Sabreen da Hamra da angwayensu,
Ranar su Santana sune akan gaba kawar matarsa tayi aure,har gida Yazo ya yiwa Sabreen murna yace oh Allah yayi aure da marar kwabo to kinga dai da yanda kika lallaba kika samu shiga sai ayi hubbasa a tallafi Antena a bata muhimmanci,kina da kishiya ki zage ayi biyayyar aure ato karki bamu kunya,Sabreen tayi dariya a ranta tace wannan wahalar da Nasha kafin na samu Miji ai dole nayi biyayya,ba wani biki aka yi ba su Wise Iyayen Amarya anci gayu ana ta Kai kawo,Mama tazo zuwa yamma aka Kai Sabreen gidanta Masha Allah
Bayan kwana uku Cele ta dauki Kaka suka tafi zance wajen Maman Sabreen.
Kaka yace tunda tayi Miki kina sonta Cele Nima Ina sonta Cele tace ta hadu Kaka itace dai dai kai kana aurenta za a ga kana wani ja kana kiba,Mama tasan zasu zo harda yin girki taci kwalliya cikin Atamfa Riga da skert tayi kyau,suna zuwa gidane karami ba wani me kyau ba can,wani daki ta sa aka kaisu Wanda ba komai a ciki sai carpet,suka zauna a kasa aka cika musu gabansu da girki,Kaka yace juma'ar da zata yi kyau tun daga laraba ake ganeta Cele tace ai wannan ma tun daga talata aka ganeta,Mama ce ta shugo tana