Showing 39001 words to 42000 words out of 152911 words

Chapter 14 - Yar Aikin Karuwai 2

22 Oct 2024

4705

gidansu Mata sunfi yawa namijj daya ne tal Kuma tambadadde ne ma namijjin gashi nan duniya duk tayi Masa Ruku'un Dila,Sa'ade tayi dariya ba shiri tace shegun Yara Baku da aiki sai bakar magana yanzu Baballlen kanin Uwa shine tambadadde duniya ta Masa Ruku'un Dila, Nazifa tace to mene shi dan kwaya bama gwara Mata masu tausayi ba mazan wasu duk gasu nan daga sunyi aure sai matansu da Dangin matansu mace ma me tausayi da Jin kai baza ayi Addua Allah ya bada dana gari masu Albarka ba sai maza maza mace ba mutum bace sabo da jahilci ku Kuma da kuke son maza wace ta haife ku idan ba mace ba,ku sai ku canja kanku ku koma mazan ai Jahilcin banza idan ance muku jahilai kuce ku ba haka ba,Omaira tana fari da rangwada tace mu da muke da baiwa ma iri iri mune fa farin cikin mazan su taba mu ma Dadi ne,Umma ta kwade Omaira tace ke a gaban namu ne,nace dan basu San Miracle bane da fitsara bane,haka ranar Suka yini suna Shige da fice a gidan suna tijara iri iri idan wannan tazo ta tafi gidan mijinta sai wannan tazo Uwa sai barin gidan tayi ranar sai dare ta dawo shima Abba guduwa yayi sabo da jarabar yaran nan,Umma Kuwa da tana Hana yaran ta gaji yanzu Ubansu Kawai zasu yiwa ta taka musu birki sabo da mahaifi mahaifi ne ko ne yayi musu basa ce Masa kala in Banda Cele itace kadai take fada Masa abinda taga dama shima da dalili abinda ya mata dole tayi.

Auta ne ya tambayi Mami ana gobe zata tare yace zai je Kaduna Birthday din abokinsa,da kyar Mami ta bari Suka tafi da abokinsa amma tace sai dai su tafi a jirgi Suka ce to,a ranar Suka Isa Kd da yamma da abokansu Suka hadu abokin Auta Afif a gidansu Suka sauka Suma masu kudi ne, da yamma yawo Suka fita a motar Yayan Afif su uku,Auta yace Wai ku baku da classy Girls ne haba gari kayau haka, Yana yarfe hannu Yana duba ogonsa da Wise ta bashi kyauta me tsada,Afif yace wanannan agogon yayi,Nawaf yace tsohuwar Babyna ce ta bani, tayi aure? Yace tayi aure Mana kanin Baffa ta aura,suka ce gaskiya kana Shan takaici,yace ba kadan ba Allah ya bani zuciya me karfi badan haka ba da tuni ciwon zuciya ya kamani,Suna ta dariya suna tafawa su a Dole samari,Afif ya danni pics din wata katuwar budurwarsa yace kalli wannan mugun so na take,Suka leka wayar,Wanda ke driving garin kallon pics Saura kadan ya make wata budurwa a gefen titi tana tafiya dauke da katon botikin markade, Auta yace ya zaka tafi Nura zaka kade Yarinyar mutane mutum ce fa a tsaya kaje ka bata hakuri gaskiya ai bai dace ba,Parking yayi Nura ya fita yace malama,ta juyo da sauri yace dan Allah kiyi hakuri,Murmushi tayi tace kaci sa'a yau birthday Dina wlh da sai ka Sha Mari yanzu,Nura ya saki baki Yana kallonta Omaira ce ta tafi da imaninsa Yara basu tafasa ba za
su kone,Auta yana mota ya dago ya ganta Ido ya zaro yace Aunty Rabi sak wallahi Kawai Rabi tafita fari da yawa ne,Auta mota ya bude ya fito yace ke kin San wata Rabi? tace wace Kuma haka,mu duk gidanmu ba rabi dama cewa kayi Rufaida sai nace tana makkah,Yace akwai wata wallahi irinku daya,Baki ta tabe ta juya zata tafi Auta yace ke ya ina Miki magana kina Raina min hankali bafa cewa nayi Ina sonki ba ya kamo pic din Rabi na biki yace kin ganta,dariya Omaira tayi tace wannan ai Cele ce,to ita Cele yaushe tayi aure ne wai, yace wace Cele Kuma ke wanne sunanta Rabi ana ce mata Miracle,Omaira tace Kama min na sauke markaden nan abin nan nayi ne,Auta ya Kama Mata Suka sauke tasa Hannu a cikin bra dinta ta dakko wayarta Vivo karama,Nawaf dariya ta kamashi yace maza cancer ta kamaki kyayi bayani ai waya a wajen abubuwa haka Allah ya kyauta,Omaira tace kaji mutum Ina ruwanka,tura min pics din kawai,ya tura Mata pics din Rabi,ta tura Masa pics din kaf Yan gidansu tace gashi nan ka nuna mata akwai wacce aka sace tun tana jaririya a cikin jini idan itace to ta neme mu,ga Number ta,Auta ya saka number,Omaira tace Dan Allah masifaffiya ce? Auta yace tab ai Yar kunama kenan Aunty Rabi wa ta kyale,sai yaga Omaira ta washe baki tace yawwa Kar ta bar ko ta kwana kowa ya mata ta Masa haka ake so amma wani salihancin nan ba cinyewa bane,Nawaf yace ke kin ganki karama dake to anfi son mutum me hakuri,Allah Yana tare da masu hakuri ba ko Baki sani ba,ai nima bance tayi tsokana ko taci zali ba Kawai nace idan an Mata ta rama Kai nawa kake da zaka ce min yarinya,Auta ya juya abinsa mota Suka shiga Suka wuce sun manta ma suna ta labarin Yan matansu.

Ranar da Mami zata tare walima Baffa ya hada da abokansa da Kawayen Mami da Yan Uwa na kusa aka ci nama aka more amma ba kida ba komai daga wajen Walimar ya dauke matarsa sai gidansu Wanda yaji gyara an canja abubuwa da komai gida ya dauki gyara,Iyamami ko leke bata leko ba ko a jikinta.
Amarya da angonta kayan makulashe Suka ci sannan Mami wanka tayi ta fito suka yi Nafeela tayi shirinta cikin rigar baccinta me Jan hankali,Baffa ko da yayi wankan ma kasa shiri yayi sabo da zumudi Kamar yau ne ya santa,Mami Kuma sai yanga ake ana Jan aji,Baffa inda take zaune a gefen bed ya dawo a kunne ya rada mata Babyna haba Sahiba,kiji tausayina Ni rayuwata sai da ke,Ki duba Allah ki duba manzo ki tausaya min,ki agaza min,Ki bani dama please,ni rayuwarki ma kadai tare dani na godewa Allah,Dan Allah ki bani ta biyu ki saki ranki,Mami tana Jin dadi a ranta tayi kasa da kanta tace da Kai na saba in babu Kai zuciyata baza ta zauna kalau ka daina rokona,Kawai ka rike ni Amana,da sauri Baffa yace yace nayi Alkawari ga zuciyata ma karbi idan yaso ki sata a cikin kwalaba ko keji,dariya Mami tayi yanda Baffa ke zuba abin kunya matuka Kamar yaro,ko yaran ma wasu baza su iya wannan magiya da kalamai haka ba,Kumatun Mami ya sumbata yace gaki Yar farata,yau Ina cikin murna za nayi kwanan farin ciki,Mami tace nima haka, ni ai Dadi ma ya isheni ko rungumeni kayi to ya isheni nishadi ma,Baffa yace Shedan sai dai ya mutu yau sabo da bakin ciki suka Yi dariya Mami ta mike Baffa ya jawo ta jikinsa yace Ina kuma Zaki je yau Ina ango na, jikinsa ya jawota Yana bin jikin Mami da shinshina yana kissing wuyanta,Light Mami ta kashe Suka koma tsakiyar bed.

Bayan sati uku Cele ta dage tana ta faman koyon larabci idan Hajiya Hauwa tazo har Ahsan ake koyawa Hausa sosai yanzu Cele tana tsintar abubuwa da dama dama ba wuyar iyawa idan kana zaune da masu ji, Maheera tunta ta bar gidan bata dawo ba tana can tana cin duniyarta da tsinke ita da Kwartonta, tunda Cele ta tsaga Masa Duwawu ko unguwar Ahsan Bai sake bi ta wajen ba a hakan ma Maheera ce mayyarsa da kyar ta shawo Kansa itace take Kama musu hotel a zuwan mijinta ne Watarana kuma idan matarsa bata nan sai ya kirata taje gidansa a boye, wani bangare na zuciyarta Kuma tana son Ahsan dinta,taga kwartancin bazai Kai ta ba gwara idan tana gidan mijinta yafi safe,Iyayenta ta dinga yiwa kuka tana fadar karya da gaskiya suzo suyiwa Ahsan magana ya daina kula Cele,Kuma sun yarda zasu je.

Ahsan ganin Cele yanzu tana dan tsintar abubuwa sai yace yanzu cikinta ya Kai wata hudu,baki Cele ta bude tace ciki a Ina na samu ta tambaya da larabci,yace bata San anyi dashen ba? to bata Yi nisa da larabcin ba bata fahimtar wani wani Abu,Kawai sai ta karbi wayarsa ta Kira Hajiya Hauwa ta roketa dan Allah tazo, ai Kuwa tazo yace tayiwa Cele Maganar cikin ya bawa Hajiya Hauwa labarin Kan zancen da komai,Hajiya Hauwa ta dinga salati tace da Ahsan ai Cele budurwa ce bata San namiji ba Sam Kuma bata San ma tana da ciki ba ko sisi ba a bata ba bata San ma an Mata dashen ciki ba sato ta akayi shigowart Saudiya,Nan take fuskar Ahsan ta canja ya shiga matsanancin damuwa,wani tausayin cele ya kamashi abinka da Balarabe harda hawaye Yana kallon Cele Yana tausayinta,Yace dan Allah Hauwa ta fadawa Cele komai ta bata hakuri,Cele taga Ahsan yana hawaye tace mene Kuma lafiya ko solobiyoncin ne ya motsa,Hajiya Hauwa tace ke dalla ki tsaya kiji Maganar gaskiya Cele ciki ne fa dake wallahi dama na fada miki ta kwashe zancen komai ta fadawa Cele,Cele mikewa tayi tsaye tace na tuna ohhhh shine ta kaini asibiti nayi kwananki a can ya min Allura hankalina ya gushe,Cele ta taba local government dinta tace shi yasa na tashi naji Nan ya canja ashe abinda aka zuba min kenan, Hajiya Hauwa tace kinji shi Ahsan baida laifi, Kara Cele ta kwalla ta dafa kai ta sake kwala ihu sai da tayi sau uku sannan tace bazan Yi kuka ba tana Kuma share hawayenta tana cewa karki kuka bazan Yi kuka tana goge hawayen dake sintiri a kumatunta,tace na yarda da kaddara,Kaddarata ce Allah ya rubuta ba komai Zan zauna na haihu ba damuwa,Ni yanzu ta Kaka nake yi burina na hadu da kaka wannan ya Riga da ya afku amma tabbas Maheerah sai Allah ya saka min ko ban Mata komai ba,to me ma Zan mata ni Wanda zai huce min zuciyata babu shi a duniya ko me nayi Mata ban rama ba batawa kaina lokaci ma zanyi, cuta ce ta rigada ta cuceni Allah ya Isa wallahi Allah ka isar min na kai file Dina gaban Allah Kara ta na daukaka ta wajen Allah tana kotun Allah, Allah Kuma yasan yanda zaiyi dani wani bala'i ya Kare me zan ce,Ina budurwa ban San Namiji ba tasa aka sa min ciki a jikina Allah ya Isa wallahi tana kuka wiwi Cele abinda bata taba yi ba,tace yanzu mutane idan zan kwana Ina cewa ban namiji ba waye zai yarda,ya zanyi da kunyar mutane me zance, Ni tuni nasan wannan Dan iskan shi na kirki ne Dan banza ta daki Ahsan a kafada tace kai karamin alhaki ne a wajena bare ma ba Kaine da laifin ba tana goge hawaye,Ahsan Yana kallonta shima sai hawaye yake.
Cele tace kice yaushe zamu Fara zuwa awooo ta karasa da kuka ?

Hajiya Hauwa ita dai tausayin Cele take ji ta fadawa Ahsan tace ta hakura tace babu laifinka Kuma ta karbi kaddara yaushe zaku fara zuwa awo? Ahsan yaji Dadi sai Allah yake godewa Yana Addua yace ko yaushe ta shirya,tausayi yasa Hajiya Hauwa tace Zan tabi yaushe Zan dawo karatun? Cele tace bana so bazan koya ba suje da yaren kasar su,Hajiya Hauwa tace yanzu ne ma yake da amfani,tace bana so ni na fada miki,Hajiya ta kyaleta tace idan kin huce ma Zaki neme ni tace ni dai Ina Kara Baki hakuri ta tashi ta musu sallama ta tafi tana cewa maganin Matan mu hausawa kenan da matan aure da zawara da Yan Mata burin kowa ya tafi kasar waje,gani ake kana zuwa ka Zama me kudi kawai.
Cele zaman dabaro tayi ta dinga uban kuka sosai,Ahsan ya dawo kusa da ita ya dafa Kafadarta Yana lallashinta yana bata hakuri amma Cele taki yin shuru,yayi yayi duk masifar lallaba irin ta balarabe yayi ya hakura karshe ma daki ta koma ta kulle kanta da key tayi zaman Yan bori tana rusa kuka tana cewa yanzu ya zanyi da Kaka da mutanen dunuya Maheerah ittaqillah Maheerah Ittaqillah haka Cele take fada,Ahsan Yana jinta cike da tausayawa,ta koma sai kinci kwalabar ubanki Maheerah Dan Kan uwarki me gashi Kamar Audugar Rimi wayyoooo ta Danna min kabiri Ashe ba miciji bane kasurgumin da ne a cikina da aka sa min me katon kai me suffar fatalwa....Tsit tayi Jin larabci na tashi Ahsan Yana ta masifa,ashe su Maheerah ne da iyayenta Suka Zo bada hakuri Maheerah zata dawo sunzo saji,Maheera tayi mugun girgiza ganin Ahsan ba makaho bane gashi ras dashi,Cele tashi tayi ta fito a hasale.

Kwanan Auta Uku Mami tace idan bai dawo ba wallahi sai taci mutuncinsa ba shiri Suka dawo,Ko hutawa baiyi ba ya shiga wajen Mami suna tare da Baffa Wanda sai kace sabon ango Wai ya dauki hutun angwanci na sati uku,yace Mami na dawo tace ko kaifa ni bana son yaro da yawo yaje ya hadu da abokan banza kana tarbiyya wasu suna lalata maka Yara a gefe.
Ko hutawa baiyi ba ya taho gidana Ina Shan kunun tsamiya ya shigo yace Aunty zo kiga yan gidanku,dariya nayi nace Kamar ya? yace Allah wannan Kuna da danganta yazo ya nuna min pics harda na cele a gaban kasko tana suyar awara,Nace Kai a Ina ka gansu? ya kwashe labari ya fada min, nace tab Amma wannan Kamar tayi yawa wlh muna Kama musamman me suyar awarar nan irin mu Daya,Auta yace wlh ki nunawa mayenki ku tafi tare kuji Kuma sunce wata ta bata tana jaririya,waye mayenta Nawwar ya furta Yana sakkowa daga steps,Auta yayi dariya yace Sorry,Wayar Nawwar ya karba yace mu gani ni Kuwa na kasa magana,dariya Nawwar yayi yace ah ai sai nace kece Baby,to ka kula Kar Watarana ku hadu ka rungume matar wani cewar Auta,Nawwar kunnensa ya ja yace Wai ni sa'an ka ne? nace kai hankalina ya tashi mu tafi dan Allah naji su waye,to ai kya bari dai gobe tayi ko,Auta yace ni Ina da number ma Zan Kira su bamu address din gidan,Nace shike nan Alhmdllh.
Washe gari daga ni sai Nawwar sai Auta Muka tafi can a sirri muji mene gaskiya.



BA EDITING AYI HAKURI




AsmaBaffa.
[8/9, 10:59 PM] +234 806 192 9616: 🌼'YAR AIKIN KARUWAI 2🌼
MATAFIYA

BOOK2


31-35


Official

By
AsmaBaffa


SADAUKARWA GA
ZAINAB USMAN


MASU AUDIO WANNAN BOOK NA SIYAR DA SHI BAN YARDA A JUYA MIN LITTAFI AUDIO BA



Ina masu bukatar unique kitchen utensils . fabrics adult and children's wears shoe's and bag's.
Da masu bukatar ahada musu lefe ko masu bukatar iya luggage's din kawai duk inkazo
R&U EXCLUSIVE KITCHEN AND MORE.
Zaku samu duk abinda kuke bukata ko a awanne state kake zaa kawo

Masu bukata ga number. 0703 455 9202

https://chat.whatsapp.com/LAizQA6PofSLoFhQ7XeaQx


PAGE NAKU NE
Mum Basma
Hafsa Abdullahi
Faeeza
Sumayya Auwal sa'id
Ummu Lateefah
Maryam T Baliya
Murjamashi
Fatima Bintu
Mmn Mubeen
Khadijah/mashi
Aneesat
Mrs A
Hussaina S Alsn






Ina kusa da Auta Nawwar ya dawo ya kori Auta sit din baya shi ya zauna a kusa dani,Auta yace ni na huta ma matar taka da duk yawu gareta,nace Auta Inshaallah sai ka auri mace tana samun ciki kullum yawu da amai suna hanya yace ba Amin ba.
Muna sauka Auta dama ya Kira abokinsa Afif shi ya dakko mota Nawwar yace wlh bazan shiga tukun wannan yaron ba yaje yayi hatsari da mu,nace dan Allah kayi hakuri muje ba abinda zai faru Auta Kuwa har ya Shiga gaban mota ya kame,da kyar Nawwar ya yarda Muka shiga baya,Auta Wayar Omaira ya kira ta daga,yace ke gamu nan mun shigo gari Ina ne gidan naku Omaira ta musu kwatance,Umma da sauran Yan Uwa kaf an taru ana jira a gani wacece ake tunanin jaririyar da ta bata oho,Abba Yana zaune a kusa da Uwa Babarsa suna cewa wallahi baza su kawo tsintacciya a hada jininmu da ita ba ace wata Yar uwa ce bazai yuwu ba,Abba yace yanzu haka ma irin Kama ce da Allah yake halittar bayinsa da ita zamu gani ai,su Bilkisu da Umma duk suna Palo a zaune suna jira,Omaira kafin mu karaso ta fito kofar gidansu wani ginin bulon siminti tsoho tukuf da shi dama unguwar tasu gata ga irinta,Nawwar Yana ganin Omaira yace gaskiya jininku ce wannan ba sai an tambaya ba ma,Omaira ta rike kugu a kofar gida tana tsaye sanye cikin riga da wando ta dora hijab maroon ya wuce gwiwarta, suna parking Nawwar ya fito ta bishi da kallo tace tace amma daga madagaska kake ko bawan Allah,Nawwar Bai shirya dariya ba sai da yayi yace a'a daga Masadonia nake,Miracle ya zaga ya budewa kofa,Omaira tace hamshakiya mandiya kofar ma Sai an bude Mata,Kafar Miracle Omaira tabi da kallo Tasha takalmi me tsada da tsini ta fito sanye ciki wani danyen leshi me tsada Golden and White jaka da takalmi da mayafin Golden tayi kyau na mamaki sai kamshi suke na musamman,Auta ya fito tuni ya harde hannaye a kirji Yana jingine jikin mota anyi tsaiwar samari,Jakar Miracle Nawwar ya daukar mata Wai baza ma ta rike jaka ba,Omaira tace sannu Alhaji Bawa sunan wani wai Bawa to ai da Kai aka sawa sunan ma,Auta Murmushi yayi,Miracle tace ke dan Allah kin ishe mu ki Kai mu gida sai shegiyar magana.

Omaira gaba tayi tace ku biyoni a bayana suna tafiya tana juyowa tana kallonsu tana sake juyowa ni Miracle na Mata ambola nace kanwar uwarki,Omaira ta juya tana dariya Suka shiga gidan ta kwala Sallama Salamu Alaykum Umma ga yarki marar mutunci ta zo,Nace Mijin uwarki ke Omaira kike ko wa nace Mijin uwarki,tace ai an saki Umma bata da miji Nace to tsohon mijin uwarki,Abba yana zaune ya saki baki yace Kai na yarda wannan 'yata ce babu tantama,Uwa Mahaifiyar Abba tace gayyar tsiya naji mace daga zuwa sai zagi kana zaune tana zaginka,yace ai bata San nine ubanta ba shi yasa duk yarana basa ci min mutunci suna daraja ni banda Cele kam Yar banza me Kai

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login