Showing 30001 words to 33000 words out of 152911 words
Sabreen ta samu Iklima sun hade kai sai sun kori Wise,sun hana Wise sakat a gidan nan tun bata damuwa har ta fara damuwa a ranta,Seraline ta Kira tace tazo Dan Allah sabo da Indai Shawara ce sai Seraline Allah ya bata fasahar yin abu cikin hankali idan Kuwa Star ce cewa zatayi Kawai aci ubansu a musu dukan tsiya,Nima Haka zance,Yar Zabil ma bare Mandula mijinta ne Kawai ya Isa da ita shima darajar so ne tana mugun sonsa shi yasa sai yanda yayi da ita,Seraline ce ta Kira Sabeer ya tafi Katsina wajen Yan Uwansa baya gari tace Baby dan Allah yau zanje gidan Wise,yace ban son yawo kin sani kullum fa sai Kun hadu a makaranta,da shagwaba tace kirana tayi fa matsala ce shi yasa yace to shike nan kije da motata karki kai dare tace to,da Yamma ta shirya taje,bayan sun dan taba hira Wise ta bawa Sera labarin komai,Seraline tace ki kyale su tunda uwarsa tana ciki kin San uwa tana da power zata iya yanke hukunci ko shi Mijin naki sai ya Mata biyayya ke me ya dameki suyi ta Yi miji shi Zaki rike duk abinda zasuyi a banza yaran dai idan Suka Miki kici ubansu wannan Sabreen din naga Alama bata daku bane,Wise tace zanyi bariki a gidan nan,Seraline tace a'a karki Yi please dariya Suka Yi tace kinga Iyamami da ace ba uwarsa bace da yanzu na canja Mata kamanni Mata da budurwar zuciya kullum zo kiga kwalliya ta wani saka jambaki harfa kitso ake Mata da Attach wallahi Rannan cewa tayi sai an sa Mata Attach,Seraline ta dinga dariya tace na gani ai,tace ni ai da dangin Sabeer sun Fara min wulakanci ya taka musu birki da Kansa ya kwatar min yanci shike nan ai Yana Jin harka a local government yaci ubansu kaf.
Wise da Sera suna Hira Suka ji hayaniya lekowa Suka yi Suka ga Auta da Iklima bakuwa matar da za a aurawa Papa suna kokawa, Namiji da mace karfi ba daya ba sai gashi Auta ya fasa Mata Hanci da baki jini Yana fita,Fitowa sukayi da Sera suna tafawa Auta wise tace Auta another punch Auta Kamar dan China haka yayiwa Iklima budu budu tana ta ihun agaji,Iyamami ce ta fito da gudu tana zagin Auta tace ubanka ta maka yanzu zaka Yi kisan Kai Dan iskan yaro marar tarbiyya dama uwarku bata muku tarbiyya ba,Auta yace ai ke shi yasa naga tarbiyar ce dake ke naki Iyayen tarbiyyar Suka Miki ai da sun Miki tarbiyya da baki abinda kike ba Kuma wallahi ta sake cewa zata aikeni sai na karyata baras,au au yanzu dama akan Kawai tace zata aikeka shine ka Mata wannan dukan,yace ae ni sa'anta ne ko kece bazan je ba bare wata kucaka kazama,ta kirani wai Kai yaron nan nine yaronta ko kanin ubanta ne ni,ko Papa kanin Ubana baya min wannan Kiran sai ita sabo da kin kawota Zaki cusawa Papa ya aureta baya so ta tafi gidan ubanta wallahi baza a sata a gidan nan ba ai ba gidanki bane kema Iyamami,Dan ubanka ko ubanka bai Isa dani ba bare kai,ai Ubana Yana tsoronki aljanarsa tana kafarki ni tawa a kafarki take? a kafar uwata take bazan biki ba idan Kinga dam ki tsine min ma,ai Kuwa idan na tsine maka sai ta kamaka yanda na Sha wahalar rainonka da goyaka a bayana ga shegen kukan tsiya haka nake goyaka kayi min fitsari da kashi duk na wanke maka,Auta yace Iklima take ko wa bata da waje a gidan nan baza a aureta ba, Iyamami tace to na gani idan ka Isa sai mu gani mace daya tayiwa Dana kadan wannan Karuwar ce zata bar gidan nan bana kaunarta.
Auta ya nuna Wise yace wannan da kike gani hadin Allah kenan mace Daya tamkar da dubu ai akan ki aurawa Papa Mata goma to gwara ki bashi Wise guda daya,baki ji sunan bane Wise ta ko Ina Wise ce duk ta cike gurbinsu su goman ,kainuwa dashen Allah ita da Papa sai Allah, yau naga dan iskan yaro haka ka koma cewar Iyamami, Auta yace Kuma sai ta haifo mana yara Papa ya samu yaran kirki masu Jin Kansa ba irin Sabreen ba ciwon Kai hawan jini da Kansa to Sabreen kenan, Auta ya kalli Wise yace kina haihuwa na zama Dan raino, ki share su Iyamami ba Arabic ba boko baza su gane ba ko Papa ya sakeki Ina nan zanyi ciki dake ni a haka ma Ina so,Iyamami salati ta saki tace au kwarto ka koma Kuma to wannan sai an sa Ido a kanka tunda ka Fadi haka zaka iya zagawa dama kaga Karuwa ce shike nan kwartonki a gida, Auta yace ke ma da kinyi wa ya san irin zalamar da Kika Yi a zamaninki, ki dai gyara tsufanki ko Kya samu ki cika da Imani yanzu mutuwa ma Yara dauke su take ba sallama bare ke da kin tafi gangara idan baki tuba ba sai yaushe, kin girma kisan kin girma,ki sani gadararki ke Kika haifi yara to suna da hakki a kanki wallahi sai Allah ya tambayeki tunda Amana ya baki,Dan Adam guda aka zabeki aka baki su gasu nan har Mata da maza aka hada Miki matan sun gujeki sai sunga dama suke zuwa daga su sai yaransu sabo da duk kinbi kin watsa Kan yaranki da kanki Aunty Rukayya da Aunty Binta ko gaisheki basa zuwa sai suyi shekaru sai da dalili suke zuwa Babu zumunci Sam yaransu basu sanmu sosai ba muma Haka to a haka kike so idan kin mutu muyi zumunci zuriarki su hada Kai a haka,yanzu Maman Sabreen duk kin jawo yanzu anyi baran baran,komai kin lalata Baffa ma da Papa badan Allah yasa ba da yanzu sun farrake to a haka ke son yaranki kike Yi? Ai ke ce ma makiyiyarsu,kina ta shiga hakkinsu kin hanasu zaman lafiya da matansu,takala na bala'i me kudi nayi mene amfaninsa sabo da koshi ya Miki yawa Zaki ci abinda kike so Allah ya bawa yaranki kudi, wani abin ma samun waje ne koshi ya Miki yawa da ace Zaki tashi ki wayi gari ace ta Yaya ma Zaki ci ki rayu kike da baki tsaya wannan abin baki da lokacin wannan abin,ta cikinki kike Yi,for God sake ki kyale mutane su sakata su wala Ki ja mutuncinki ki ja girmanki ke yanzu dadine Kamar mu ace mu zauna Muna fada Miki magana yanda muka ga dama,kin Sa surukai duk sun rainaki kowa ya tsaneki idan Kika mutu waye zai miki Addua me kyau ko yabon halinki baza muyi ba sai dai muce Allah raka taki gona wallahi sai na raka makara ina tsaye Ina latsa wayata Ina chat,kin San dai yanzu haka akeyi ana makarbata tsabar bushewar zuciya Zaki ga mutane ba ruwansu waya ma suke dannawa suna chatting abinsu,ko mutum ya hau tiktok akan kabari Yana kallon shirme da fitsara to yanzu haka akeyi,Ki kyale mu Dan Allah mu sarara,ki fadawa bakuwarki ba a aikena idan bata sani ba ta sani me aikena sai ya shirya ba kowa ba wlh sai Ina ganin mutuncin mutum bare tazo tana ce min Kai yaron nan sabo da ita bazawara ce wa ya san me tayi aka saketa maybe ma uwar mijinta tayiwa dukan tsiya ke kin kawota sabo da son zuciya danki ya aura kina nan za a aureta ta karyaki ta Miki buju buju ba ruwanmu Kuma Kuna Yi Muna Shan Ginger juice mu ba ruwanmu,har wani Galavanting take a gidan mutane.
Auta Yana gamawa ya karkade rigarsa yace sai nayi wankan tsarki ta shafa min najasa,Dariya su Wise Suka yi Wise tace ni da Kai Amana ne Auta you be better person,Auta yayi gaba abinsa ya bar Iyamami a tsaye Kamar gunki,yaro ya zage yaci mutuncinta haka ashe fadan ma duk wannan bala'in da yake Dan ance Masa yaro ne za a aike shi,Amma maganganun Auta na karshe sun taba zuciyar Iyamami,wa'azin Auta ya shigeta tabbas abinda ya fada gaskiya ne iyaye da dama suna raba Kan yaransu su watsa zumuncin zuriarsu da kansu gashi kowa ya tsaneta babu me sonta sai yaranta su ma Dole ce ta sa.
Sera dai tace to ke Auta ya Gama Miki aiki Saura naki idan basu hakura ba ki karasa da kanki,Wise sai Murna take Yi tace ai Dole nayiwa Auta kyauta.
Umma Umma na dawo fito ki sauke min markaden geron,matar ce ta fito da sauri,dittujuwa ce Fara kyakyawar gaske ta saukewa budurwar da baza ta wuce 18yrs ba katuwa da ita kyakyawar burdurwa zankadaziya son kowa kin Wanda ya rasa Yar jajir da ita,markaden aka sauke Mata,tace Umma Aunty Cele Ashe sunfi wata uku ma da tafiya ita da kaka,Umma Murmushi tayi tace Omaira kyale Rufaida bata Jin magana amma ni Banga laifinta ba ko kadan mahaifinku ne da uwarsa sune da laifi duk abinda tayi tana da hujja laifinta Daya da take hadawa dani,dariya Omaira tayi tace kin San Rannan daga naje nace Cele ta bani awara da kudina fa Umma wallahi ta kamani da kokawa Wai ubana nane ya bata jarin nima kin San bani da hakuri naki kyaleta Muka Yi ta kokawa a titi shine ta fasa min goshi ta min dukan tsiya Wai na rainata shike nan duk inda ta gani sai taci ubana har bana so mu hadu a hanya da Cele sabo da bata gajiya da fada Allah ya taimaka ma ta tafi makkah,Umma tayi dariya tace ku dai na rasa inda kuka yo gadon masifa sai dai ubanku kuka yo, ku goma na Haifa cif duk Mata Kuma duk Babu me sauki duk da ban San dayar ba tana raye ko tana mace oho ko tana gidan marayu Ina aka jefar min da ita oho sabo da Kawai Ina haifar Mata amma ai Alhmdllh tunda dai Ina da guda Tara na suna nan bazan yiwa Allah Butulci ba akan daya ta bace,Cele ai Dole tayi masifa an cuceta ne bana ganin laifinta wlh,Nima Kuma an shiga hakkina an yiwa Allah shishigi,Omaira tace karki damu Umma gamu dukkan mu zuciyar maza ce da mu mace daya ma gayya ce a cikinmu dan ma duk sunyi aure yanzu mu hudu ne Kawai a gabanki Banda Cele da taki aure yanzu maga shegen da zai taba Mana uwa da anyi tsiya.
Gyaran muryar me gidan suka ji ya shugo Yana muzurai wani fari dogo me Dan jiki tun kafin ya karaso ya fara tsawa Kai Kai....hayaniyar me nake ji ne haka ne baki da aiki sai dai kisa Yara a gaba kina zance gashi Nan duk yaranki ba na gari aikin banza wannan ba tarbiyya bace ki dinga munafunci da yaranki,duk Wanda yaci namana ban yafe ba nasan gulmata kuke yi,Umma tace na rasa gulmar Wanda zanyi sai Kai Ina abin gulma a wajenka,Hanifa ce ta shigo sanye da uniform ta dawo daga school tayi sallama ta wuce dakinsu,Can sai ga Rahma da Raheema sun shugo su biyu Yan matasan mata sun shugo suna fada akan biro daya ta sacewa daya biro,Omaira ce babba a ciki tsawa ta musu Kai dalla kuyi Mana shuru muna fama da talaucin mu Kun dame mu,Abbansu ne yayi magana yace ai ni rabon da naji dadi a duniya tun kafin nayi aure gaba daya banyi dacen mace ba,gashi yaran ma banyi dace ba gaba Daya an cika min gida da gwari Mace ai gwari ce, Ni kenan kudina su Kare a siyen gado da katifa kullum a bikin Yara nake har an gaji da zuwa daurin aure gidana,gaba Daya Kuma ba wacce ta auri me kudi duk talakawa suke kawo min ko wacce da kyar take Sha a gidan aurensu Ina za a iya taimakon Iyaye, Uwa ce ta fito daga dakinta mahaifiyar Abba kenan tana wani gadara tace Kai Kam sai dai Allah ya biyaka a lahira mace bata da aiki sai haifo Yara mata da wannan haihuwar ai gwara babu, sai da tayi Yan biyu a jere sau uku sabo da bala'i, su yaran ma da suna da kashin arziki da sai ace da sauki amma duk talakawa suke kawo mana, gashi duk wacce ka aura Suma duk matan suka haifo ta Gama cinye su da baki, Abba yace ai gashi nan wlh sai an aurar dasu tas Zan dinga ciyar da ita tunda haihuwar Mata ta zaba to sai dai su ci da kansu abinda Naga dama shi zan bayar a gidan,Umm ta kalle shi tare da tabe baki tace jahilci yafi hauka ciwo Allah ya ganar da ku, dake Umma itama bata da tsoro bata barin ko ta kwana Indai aka Mata.
Maheerah tayi tayi ta fita Cele ta tare hanyar haka ta juya ta koma Palo ta zauna tace Kuma Ni Zan fita ba ke ba gantalalliya Albakaratun,Al Himarun jaki to ke jaka ce me kawo mazan banza tana jinta Maheerah tayi Shuru tana saka muguntar da zata hadawa Cele,Cele Kuwa shiri tayi cikin Abaya tayi rolling ta bude kofa ta fice tare da cire key din kofar ta kulle Maheerah ta baya tayi ficewarta daga gidan gaba daya, ta fito taga hadadden gari ta bude hannaye tare da daga Kai sama tace iskar yanci haba har naga rana ai na samu sinadarin vitamin D a jikina,ta Fara tafiya tana nishadi tana zaga layin gashi layin manya ne tana tsoro Kar ta bace sai da ta gama yawonta mutane sai dai daiku ta gaji da yawon ma tace bari na koma gida Banga kowa ba ta juya kenan taji ance ke daga ina,sai data tsorata ta zaci gamo tayi ta juyo da sauri taga mace dattijuwa bahaushiya baka da ita tana yawo da katuwar jaka,harshen larabci ta juya taga Cele Fara ko ruwa biyu ce bata Jin hausa,Cele tace Sannu bakuwa ce ni ban fara Jin larabci ba,matar tace kin San a state din nan kazamin kame suke Yi idan Baki da sheda wallahi ki daina fitowa,Cele tace asibiti nake so naje wallahi bani da lafiya Kinga cikina kullum sai Naga ya Kara girma Kuma ayi ta motsi a ciki,Matar tace ni kin ganni Yar Jigawa ce ni mijina ne ke aiki a nan ya taho Dani muke zaune Amma unguwar da muke ba irin wannan bace ta manyan larabawa unguwa ce ta Yan fake fake, Cele tace okay Ashe kina Jin larabci? Matar tace ae Ina ji ni,tace Dan Allah ki Zama Aunty na Zan dinga zuwa kina koya min,Matar tace hmm baki da shedar Zama a kasar su wlh kamaki zasu yi matsayinmu na hausawa Zan dai dinga zuwa duk sati Ina koya Miki ki tanadi biro da takarda Cele tace na gode,Matar tace Sunana Hajiya Hauwau,Cele tace Rufaida Cele sunana,Zo muje na nuna Miki inda nake aiki Ni Yar aiki ce,Hajiya Hauwa tace to Suka taka Cele ta nuna Mata gidan,Matar ce tace muji cikin naki da yake girma ta taba cikin Cele tace Kan Uba ai ke ciki ne dake,waye ya Miki ciki Yar Nan? Cele tace ban gane ciki ba nifa bani da lafiya wallahi ban san da Namiji ba ma Sai dai idan ciwon koda ko Hanta ne ya kamani ko ciwon sanyi,Hajiya Hauwa tace wanne irin ciwon koda haihuwata bakwai nasan ciki nasan komai haba yarinya
Me yasa kuke zubar Mana da mutunci a idon duniya ne gashi nan kasashe duk sun Raina mu kadan ne ake samun na gari a takari me yasa haka da kuruciya da komai ki kwanta ki bawa Namiji kanki haba gaki wayayyiya,Cele tace ahhh karki kaini inda banje ba nace Miki na rantse da Allah ban San Namiji ba,Watanki Nawa rabon da kiyi al'ada? Sai lokacin Cele ta tuna rabonta da period ta Kai wata uku tunda tazo garin Saudi bata yi jini ba,tsoro ya kamata tace sai dai idan Aljani ne ya min ciki ai Rannan dama nayi mafarkin Ina sex Aljani ne idan cike ne to Aljani ne ya min wallahi bazan yafe musu ba Indai Aljanu ne idan ba su ba waye to.
Hajiya Hauwa ta kalli Cele Kawai tace muje ciki na rubuta Miki wasu kalmomin ki rike kafin na dawo,suka Shiga ciki tare Maheera ranta idan yayi dubu ya baci Cele ta hanata fita,sai ganin Cele tayi ta shigo da mace gidan Kuma ta sake kulle kofar ta cire key,tana kallonsu,Hajiya Hauwa tayiwa Maheerah magana da larabci tana gaisheta, Maheerah ta samu me Jin larabci sai zagi Kawai Wai ta shugo musu gida ba Izini,Cele tace kyale banza muyi abinda ya kawo ki ta shiga daki ta dakko littafin data gani Diary din Maheerah da take rubuta tarihin rayuwarta kaf ta dakko ta bude page din da ba rubutu ta mikawa Hajiya Hauwa tace rubuta nima tarihin koyon larabcina nane, Hajiya Hauwa tayi dariya ta Fara rubutu da Hausa larabcin ma da Hausa take rubutawa yanda Cele zata gane kalmomi masu ma'ana Wanda ya Dace mutum ya iya su ta koya Mata sabo da Zama da masu yare,Cele tace ya sunan ciki da larabci ciki na haihuwa ta rubuta mata,tace cuta fa Nan ma aka rubuta mata tana ta tambayoyi ana rubutawa sai da Suka Yi da yawa sannan Maheerah ta lura Diary dinta aka lalata Mata,tazo tana masifa da bala'i,Hajiya Hauwa tace wannan gidan naku bana zuwa bane Rufaida idan nazo Zan shigo na kiraki mu dinga haduwa a iya tsakar gida,Cele tace to ba damuwa ta rakata ta tafi ta dawo ta dauki Remote ta kunna channel din da ake nuna dakin Ka'abah ana ibada,Maheerah wani Tsaki ta ja ta fisge remote tare da canja channel ta Kai tashar larabawa masu rawa da damammun kaya, data gaji ma tashar turawa ta Kama me saka wakokin disco ta tsani a kamo Mata tashar Dake nuna wani addini.
Cele shareta tayi har Ahsan ya dawo driver ya shigo da shi har ciki,Yana shigowa Cele ta mike ana cewa marhabah marhababika ya Ahsan dariya yayi ba shiri