Showing 57001 words to 60000 words out of 152911 words

Chapter 20 - Yar Aikin Karuwai 2

22 Oct 2024

4701

tangadi yace zauna master,Auta ya zauna shi dai,Salma tana aikinta Baso ya daka mata uwar tsawa ta mike jiki na bari yace kawo masa ruwa,Auta da sauri yace na gode Dan Allah, kai ba a mana musu a nan yawwa ke kawo masa ruwa sai ka sha,Nawaf yayi shuru Salma ta kamfato masa ruwa a randa,Auta ya Dan dodana bakinsa a bakin kofin kamar yana sha yace yawwa Alhmdllh na koshi kai har naji Dadi kishirwa ta tafi,Salma tana kallon wayon da Auta yayi tayi shuru dai.

Auta yace wannan Mahaukacin fa? Salma tace ae a gari ya tsinto shi,Baso ya daka mata tsawa yace zan ballaki munafuka jibarki kina fama da koshoko me zan ci dake Baba ya mutu ya barmin masifa wlh bazan aureki ba bana sonki,Salma taji kuka ya taho mata tana son Baso matuka a duniya bata taba son wani ba face Baso,Auta shi dai Halin da ya gansu yaji Kuma Salma ba muharramarsa bace gata kyakyawa ta karshen karshe gata katuwa me shape komai ya fita a jikinta son kowa kin Wanda ya rasa fara da ita amma ba fara can ba normal normal dai sai kyawun tsiya kamar me,shi Kuma Auta bata dame shi ba Sam Sahar ce a ransa.
Tambayar Salma yayi yace baku da Iyaye ne?Salma idonta ya kawo ruwa tana kallon Baso tana jin tsoro tace ae bamu da su,Yaya na bashi labari? Baso yace cikin dabanci ku kuka sani ko ki bashi ko kar ki bashi duk daya.

Salma ta Kalli Nawaf tace mu yan asalin Ringim ne da babana da baban Baso uwarsu daya ubansu daya,su biyu iyayensu suka Haifa,tun suna Yara iyayensu suka rasu sai yan uwa Kuma suna can kauye,cikin maraici suka taso ba irin wahalar da basu sha ba a rayuwa har suka dawo Kano suna Sana'a suka samu gidan haya suka yi aure a cikin gida daya kowanne da matarsa suna zamansu lafiya kuma matan nasu duk Yan Ringim ne dangi ne,lokacin baban Baso shine Babban Haladu matarsa ta haife shi yaci suna Umar ana ce masa Baso,ni kuwa ko cikina Babu lokacin suna zaune har sai da ya shekara goma sha biyar sannan aka samu cikina,lokacin Kuma Maman Umar Baso ta rasu sai Babansa,ranar da Mamata ta haife ni anyi murna naci suna Salma,muna zaune lafiya har Baso ya cika shekara 32ni Kuma ina shekara 18, watarana Mamana Aisha tayi girki shinkafa da wake lokacin ina Makaranta, Baso kuma ya gama iya secondary an turashi almajiranta har ma yana Shirin dawowa ya zama saurayi sai aure,ni Kuma ina Ss3,Mama ta zubawa Haladu Baban Baso abinci itama ta zuba nata taci ta koshi,Sallar azahar tayi da kyar lokacin cikinta ya fara ciwo tana idarwa ta kwanta daga nan ko tashi batayi ba ta rasu,Ranar Kuma Baso ya dawo ganin gida ya zama saurayi ashe ba karatun yake ba kawaii Shaye Shaye ya koya a almajirantar shi,tun yana yaro a boye yake sha Idan baya gida yana can duk an zaci mutumin kirki ne ashe ya lalace illar tura yaro wata uwa duniya da sunan Almajiranta wasu dai ba karatun suke ba,sabo da Babu me daukan nauyinsu yunwa masifa ce ace yaro bara zaiyi yaci ya koshi,Babu tarbiyya Babu me lura da shi bare lafiyarsa duk sai abinda yaga dama.
Baso yana zuwa ya samu Haladu Babansa yana Shure Shuren mutuwa ina shigowa Nima da Uniform Dina na iske Mamata ta rasu bata motsi na fito da gudu na samu Baso gaban Haladu yana Shirin tafiya lahira.

Haladu Hannuna ya kama ya kama Hannun Baso ya hada waje daya yace Baso gata nan ban muku dole ba amma zanso ace ka auri Salma,ka daure ka auri Salma Kaine kadai zaka rike min marainiya yar Dan uwana da Amana,Karka bari tayi kuka ka aureta ku zauna lafiya ka kula da ita,Karka sake komawa Makaranta ka zauna ka nemi Sana'a kuje danginmu su daura muku aure Karka Kaci Aman....kafin ya karasa rai yayi halinsa, ranar munyi kuka na fitar hankali ni da Yaya Umar Baso, bayan anyi bincike aka gano ashe waken da Umma tayi amfanin da shi ta dafa shinkafa da wake maganin kwarin da aka Saka masa guba ce wacce su dai tafi karfin jininsu tunda wasu sun dafa Kuma basu mutu ba amma su ta musu illa.

Salma taci gaba da cewa abinda iyayenmu suka mutu suka bari shi muka tattara muka siyi wannan Dan gidan muna zaune,tace Yaya Baso kayi hakuri zan fadi halinka,yace to yar iska sai kinci ubanki karasa ina ji,Salma tace ni da ka ganni bana jin magana ina da tsokana,shi Kuma Baso kullum Shaye shayensa yawa yake gashi ya iya gyaran machine sana'arsa kenan gyaran machine yana Shaye shayensa amma Kuma ba laifi kullum muna ci mu koshi ko ba Dadi,yana masifa yaki cikawa Mahaifinsa burinsa yace baya so na,ba wacce ya tsana Irina,kullum sai ya dake ni ya zageni ya tsine min ba muguntar da baya min...kafin ta rufe baki a labarinta Baso yace to bana sonki ko dole ne nace bana so, Salma taci gaba tace duk duniya ni ba Wanda nake so Irin Baso ina sonsa a duniya amma yaki aurena,ni ke masa wanki da guga,girki,ebo ruwa,komai da ka sani macen aure tana yi ina masa burina ya aureni,rannan daga tambayarsa yaushe zai kai Sadakina wallahi har targade ya ji min,gashi a haka yana da addini ga taimako,Kaga wancen mahaukacin tun muna Yara kowa ya sanshi a bola yana tsince tsince sai dai baya duka sannan haka zaka Ganshi a unguwa yana bin gidaje da kwanon barar abinci ana bashi sadaka yana ci,Kuma baka Isa ka wanke masa kwanon ba,sannan ko an masa wanka ya dinga ihu yana zubawa jikinsa kasa da bola,sannan baya magana,bashi da inda yake kwana haka zaka ga ruwan sama ya masa dukan tsiya a bola,sauro,sanyi rana duk a Kansa,amma Baso Baba yana rasuwa kaga wancen dakin zaka Ganshi kamar kango to dakine Baso ne ya dakko mahaukacin ya kawo shi,wallahi duk sati sai ya masa wanka,Idan bashi da lafiya shine yake Kiran mutane suna tayashi ya kaishi asibiti ayi masa Allurai,abinci Kuma kullum da kwanonsa ina dafawa zai fito har ya Saba ma.
Dakinsa ne leka ka gani har net ya Saka masa amma dake mahaukaci ne sai ya fincike net din ya kwanta haka sauro yayi ta cizonsa, Dan Allah ai ya cancanci a so shi ko?

Nawaf yana gama ji yace ya cancanta gaskiya ta wani bangaren ma sai wannan ya zama silar shigarsa Aljanna wannan ba karamun jahadi yayi ba,Baso yana ciccijewa yace ke zan tattaka ki wallahi Allah bana sonta ni bana son kyakyawa,Auta dariya yayi ana Neman me kyau shi baya so,yace kai to sai mummuna? Yace ae ni mummuna zan samu na taimakawa,Nawwar yace lallai Shaye Shaye ya maka illa baka ganewa ka haukace ai wannan tayi gata da hankali kalleta fa chaschas chas da ita,Baso matashi son kowa kin wacce ta rasa da shi Shima yana nunawa da hannu yana magana bana so wallahi,Salma ta fashe da kuka tana cewa Idan baka aureni ba mutuwa zanyi Dan Allah ka cikawa Baba burinsa ka biya Sadaki na,a fusace Baso ya mike ya zare belt dinsa ya fara tafkar Salma,Auta ne ya kwaceta da kyar akan kawai tace ya biya Sadaki ta har da fasa mata gefen Ido tana kuka wiwi,Nawaf a ransa yace ya kamata a taimaki yarinyar nan gaskiya zai iya kasheta watarana gasu su biyu a gida Kuma ba muharramai ba wani abu zai iya faruwa gashi shi Umar din Dan kwaya ya fara haukacewa,Nawaf tashi yayi yace zai tafi Salma ta biyo shi tana kuka tana cewa Dan Allah duk da cewa baka da wasu shekaru kamar Yaya ka sa baki ya aureni,Auta yace karki damu zan taimakeki,ta fara murna ta goge hawayenta kamar ba ita aka gama zanewa ba, tace yau kawata Sumayya sai ta ji labarin nan Umar zai aureni tana tsallen murna,Nawaf yayi dariya suka fito har Baso.

Suna fitowa kofar gida Salma taga me siyar da madarar turare da yawa zai wuce da abinsa a Kansa,Salma tace tsaya me turare,ya kawo ya sauke kwandonsa na turare,Salma sai da ta samu Wanda zai wahala a samu a wajensa dama haka takeyi Idan taga me turare wai Dan ta samu na banza,sai ta Kira Wanda babu ma sunan turare haka wai malam kana Umarsal? Sunanta ta hada Dana Baso Umar ita Kuma Salma shine Umarsal,Bai taba jin sunan turare haka ba bashi da shi yace Hajiya Babu,tace a'a dole kana da shi Muji na wajenka,Me turare ya dinga Bude turarukansa tana dangwalawa a hannunta kala yafi talatin tace gaskiya Babu kayi hakuri jeka,shi me turare sana'arsu ce haka dole sai an dangwala kaji irinsa,yace to ya tattara tarkacensa ya tafi,yana tafiya ta murje a hannunta ta shafe hijab dinta da kayan jikinta har wuyanta ta shafe tace Alhmdllh naci banza ina fita za a ce na Faso gari,Auta yana tsaye yana kallon ikon Allah dariya ta bashi da son banza yace ke turare 500 baza ki iya siya ba? Salma tace rufa min asiri ban iya almubazzaranci ba shinkafa bata ishe ni ba ina naga ta kamshi ta wuce tayi tafiyarta ta bar Baso da Auta.

Baso yace yawwa ta tafi yanzu kai Dan inane? da Alama ku masu kudi ne Kalli shaddarka Kalli ma fatarka wallahi kayi hankali yan Hisba suna ganinka a Kano sai sun aske maka wannan gashin na kanka da ka masa wani aski mu a nan easy dai easy dai abokina Allah wallahi,Auta yayi dariya yace Sabreen tazo ga Dan uwanta wannan ya girmi kanta,Umar Baso yace yawwa wani Deal zamu yi,kai kaga da Alama kana da kudi,ni so nake na samu kudi na alkinta rayuwata gashi gyaran machine nake yi,Dan Allah Oga ko zaka lallaba ka rufa min asiri? Zabura yayi ya sake ja da baya yana gwadawa da hannu yace kaga master asiri zaka rufa min ya sake kankame hannayensa kamar me jin sanyi ya makale a jikin Katanga yace wani taimako zaka min kaga kullum sai na roki kudi wajen me duka kaga na roki trillion dari,billion bakwai,na dawo million talatin, na sauke farashin zuwa dubu dari biyar,dubu dari,dubu hansim har na dawo dubu biyar to abin sai godiya kudin sunki zuwa,jari nake nema Dan Allah ko zaka siyi Salma ni ka siyeta duk yanda zaka yi kayi da ita,Idan ma za a iya maka aure kazo na baka ita ka bani million daya gata nan.

Auta yace ba ruwana ya juya zai tafi abinsa amma Umar ya tare masa gaba yana karkace baki yace ya haka yawa kake Oga haba abokina,haba Yayana to ka aureta ka bani dubu dari biyar,kai dubu dari uku ma ya Isa ai baza tayi tsada ba tunda ba a gidan masu kudi ta taso ba,Nawaf yace to naji kawai ya furta sabo da ya kyale shi ya tafi,yace Yayana bani number ka zamuyi Business din ko baka gane bane ey kar ka Yi mini ae yane ka gane,Nawaf ya bashi number dinsa suka rabu Umar Baso yana ta uban murna zai rabu da kaya ya huta ga kudi zai samu,Nawaf Kam Airport ya wuce yana tunanin lamarin Baso shi Kam ba ruwansa bazai iya ba zai Jira dai Sahar dinsa.
Bayan ya koma gida da kwana daya Baso ya addabi Nawaf da Kira a waya Nawaf kuwa yaki dagawa abinsa ya share Kiran yaki dagawa Sam.

Yana dakinsa a kwance Mami ta shugo tace gobe dai kasan zaka fara zuwa University an gama komai ko? Yace ae na sani Mami,kallonsa tayi tace ko tunanin Sahar dinne? Kai ya daga mata wai ae ya furta please Mami kije ki ji min ko zasu yarda ni nafi sonta,hmm amma Idan naje suka ce a'a shike nan ka hakura? Yace ae na hakura amma kije,to shike nan cewar Mami.
Bayan kwana hudu Mami ta shirya tare da Nasira da Sultana suka siyi kayan kwalliya masu kyau da turaruka driver ya tafi kaisu da yardar Baffa.
Mami suka ga gidan su Sahar masu kudi suma,iso aka yi musu,Sahar dince ma ta tarbe su tana Palo tana kallo dama Nawaf ya fada mata sun taho,taci kwalliyarta sosai ta sha Atamfa me tsada,har kasa ta durkusa ta gaishe da su Mami tace bari na Kira Hajiyanmu ta haura sama da sauri,tana uban murna Hajiyansu tace sun zo kenan? Sahar tace ae,shi yasa naga kina murna kamar Zaki tashi ki sani wallahi baza ki auri wannan yaron ba yaro karami wani aure zai iya rikewa,ga saurayi na kirki babban mutum me hankali me kudi na Kansa ba Wanda ya dogara da kudin Iyaye ba,wallahi Idris Zaki aura nutsatsen yaro ni da mahaifinki ma ki sani baza mu yarda da wannan yaron ba karki ce ban fada Miki ba.
Hajiya fitowa tayi wajen su Mami da fara'a suka gaisa sosai,sunyi hira Mami tace dama akan maganar Nawaf ne da Sahar...kafin ma Mami ta rufe baki tace ai an Riga anyiwa Sahar Miji Idris shi zata aure,ina Sahar ina Nawaf wannan ai yayi kankanta sai dai karatun ai,ya tafi Makaranta wannan ai Gigi ne na Yara haba Kuma sai ku biye masa shirme ne wannan,Baban Sahar ne ya fito zai fita Hajiya tace Mamin Nawaf ce yaron nan da aka dinga rikici da shi yana hurewa Sahar kunne,to...to.to Allah sarki ai kin fada musu anyi mata Miji Ina Sahar ina wannan,Sahar tana gefe ta labe tana kuka wiwi bata da bakin magana face kawai ta kyale Nawaf yayi kokari yayi iya yinsa,Mami ta gama jinsu irin rashin iya magana ta iyayen Sahar tace ba komai Allah ya hada kowa da rabonsa suka ce Ameen suka watse suka bar su Mami su kadai a Palo da ruwa da lemo a gabansu,Sahar ce ta fito tana cewa Dan Allah kuyi hakuri,ba komai wlh baki da laifi ke amma kinji abinda suka ce kiyi hakuri kiyiwa Iyayenki biyayya Dan Allah karki sake Kiran Nawaf ku hakura da juna Allah bai so ba.
Sahar tana goge Kwalla ta raka su Mami har mota suka bata abinda suka kawo mata tayi godiya ta koma ciki bata da bakin magana iyayenta sun gama da ita.

Mami tana komawa Nawaf ya tareta a Palo yana tambaya Yaya? Mami ta Mika masa waya tace ji da kunnenka shi yasa na maka recording sabo da Karka dameni,Nawaf ya kunna ya gama jin komai a kunnensa Sultana tace sai kaga ma irin wulakanci da suka mana wallahi Auta amma Sahar bata da laifi,Nawaf yace sai na Riga yar tasu aure inshallah auren huce takaici zanyi,Mami tace ko kai fa kayi hakuri ka nemi wata amma tare da bikin su Sultana za a hada da naka tun wuri ka nemo mace wlh ko mu zabo maka ni da Baffanka,Auta yace yanzu Mami ai dai sai ku bari na huce ko ku sanda na hadaku kuka shirya haka nayi muku? Auta zaiyi hawaye yace Mami daga cewa ina son aure shike nan sai kuce ko ban samu wacce nake so ba zaku zabo min Hakan yayi kenan? Baffa Shima ai ba haka mukayi da shi amma Yaya Nawwar shi kuka kyaleshi ya zaba ya darje ni sabo da bani da kudi kune zaku min komai shine ni za a min auren dole,Shut up Baffa ya furta da shigowarsa kenan yana murmushi yace Auta kana bukatar aure bama so ka fada wani Hali ka nemo to mun baka zabi kafin bikin Su Sultana Idan ba haka ba mu munyi maka mata ma,Auta bedroom ya shige kawai abinsa ya bar Mami da Baffa baki Bude

Cele tunda ta sauka take garari tana zaga unguwar ta rasa ina zata shiga har gari ya waye inda taji Kiran Sallah nan ta nufa,masallacin bangaren mata tayi tayi fitsari ta fito tayi Alwala tare da Sallah sannan ta fito taci gaba da tafiya har rana ta fito mutane ana ta hada hada,Cele yunwa ce ta ciyota ta shiga wani Dan waje inda ake soya kwai da tea,tana shiga tace da me Kwan a soya mata guda biyar,shi dai yayi mamaki mutum shi kadai haka ya soya biyar ya cinye,tace a hada da dankalin turawa sai bread da tea aka zuba mata komai,inda aka tanada na cin abinci ga me ci a wajen, nan ta zauna taci ta koshi tayi tafiyarta,balaraben yana ta Kiranta da larabci Hajja amma ina tayi tafiyarta sai da ya fito da gudu ya riketa Cele tana juyowa ta mareshi gauuu ta fara masifa da Hausa aikin banza na zaci ma a kawo Kaduna nake,jiya ai ta malali na wuce na shugo ta unguwar sarki ashe nan a unguwar Rimi nake ma Dan wulakanci zaka rike ni Abuja zan tafi,ta kwaso kudi da yawa ta watsawa balaraben tana masifa tace ku dama yan kantin Kwari baku da mutunci indai aka zo sarin kaya sai kunyi wulakanci aikin banza kano dinma zan bari gaba daya tayi gaba,tana tafiya taga masu gasa kaji ta karasa wajen tace akwai kifi na sukunbiya? Ko yan gezu ba Wanda ya kulata,ta dauki hanyar harami tana Maheerah Kiji tsoron Allah,Kaka ya dawo daga masallacin kaabah ya kwana yana addua a hanya yaci karo da mutane sun rufe wani waje wai wata ce a Nigeria ta bata sannan bata da hankali mahaukaciya ce,Bai San Cele bace yayi tafiyarta yace su karanta sai naje askarawa suyi ram Dani yanda nayi kiba nayi jajir Dadi haka nada ni ba.
Mutane suna ta zuwa inda Cele ta fadi tana birgima da Shure Shure tace cewa wlh sai na soya Awara.
Haka ba Wanda ya saurari Cele sai wata mace wacce ta Dade a kasar ta dauki Cele tana zagawa da ita gidajen takari mata da maza ko an Santa har ta zo laying su Kaka,lokacin Kaka juya baya a layin yana siyen kwai

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login