Showing 81001 words to 84000 words out of 152911 words

Chapter 28 - Yar Aikin Karuwai 2

22 Oct 2024

4717

Washe gari Nawwar ya turo abokinsa Khaleel ya dauki Umma zuwa cikin wani katafaren gida na gaske yayi kyau matuka a unguwa me kyau Umma taga komai an zuba furniture da komai na more rayuwa tace gidan waye wannan kuma? Khaleel yace naki ne inji Nawwar ki dawo ciki ki zauna takardun gidan ya Mika mata,Umma harda kukan farin ciki da ta tuna irin wahalar data sha a rayuwa da haihuwa a gidan Abban su Omaira,Khaleel yace ai ba kuka zakiyi ba Umma sanda kuka ga dama ku tare,Umma tace wa? Dannan ai nazo kenan tace na dai yi waya yaran su kwaso kaya suzo nikam ban komawa cikin ukuba,Khaleel yayi dariya yace to Umma fito ki ga motarki, ta fito suka zaga ta baya taga mota lafiyayya ta kirki me kyau arsh,ta shafa motar tace Allah yayi masa Albarka tana goge hawayen murna tace mutumin kirki Zaki dauka driver ya dinga tuka ki,Umma zakwkura ce tace na koya dai ai Koya zanyi Dan nan da lafiyata da komai,yace me aikin gida fa? Tace sai na aurar da su Omaira kaf sai a daukar min me aiki,yace to shike nan yana gamawa ya tafi,Umma kin komawa tayi shuru Uwa suka ga bata dawo ba ga Yara su Bilkisu sun dakko kurkura suna ta kwashe kayan sawa Dana abinci sauran tarkacen kayan dakin Umma kuwa Omaira ta fito tasa kafa tayi ball da tukunyarsu ta girki ta daki wani bahon wankan su tace Dan ubanku ku lalace tace Uwa ga kwance ne Kya dinga yiwa danki girki tunda bakwa son mata mu Allah ya mana tashi,Ku tashi ku tafi gidan uban wa ai nan ne gidan ubanku dole ku zauna ita uwarku duk inda zata taje to taje cewar Abba yana bakin ciki yaji Umma ta samu gida hadadden ga Alheri daban daban,Omaira taje gaban Uwa ta buga skert dinta da hannaye biyu tace a kada Miki buje a haka Zaki kare ta juya tayi fatali da wani tire dinsu ta bar gidan,Abba yana kallo wato shi baza su iya masa rashin mutunci ba sai uwarsa, Su Rahma suka tafi su tuni sunbi motar kaya,Omaira kuwa ba rawar da bata yi ba a gaban su Abba harda galala da kafafu ta fice,sai kallon gidansu suke suna Murna,Aunty Rabi taci sunanta Miracle wallahi cewar Omaira, su Bilkisu a sabon gida suka yini suna ta kallon motar Umma.

Mairo zuwa yanzu a Hannun Mahmud ta jigata duk kuwa da abinci ta rame tayi duhu Dan man da take shafawa baya bari taje ko kofar gida ya kare tayi uwar Rama,yarinyarta kuwa tayi bulbul da ita,kullum Mairo a kuka take gashi ba dare ba rana sex yake da ita yana jin dadinsa kamar me,Mairo Addua ta koma Allah ya kubutar da ita ta huta,yau yana dawowa ko hutawa baiyi ba ya fara tube kayansa,Mairo hawaye ya zubo mata ko a jikinsa ya fara shafata Babu nutsuwa gagagaga ya shigeta,Mairo azaba tasa ta jawo kwalabarta data fasa ta boye a kasan gado tace sa masa a wuya tace sake ni Dan babarka suka fara kokawa zai kwace kwalabar Mairo ta Yanke shi da ita a Kansa,balarabe yaga jini ya saki Kara,Mairo ta fara Aljanun karya kamar gaske ta hau Aljanu ta barbaza gashinta tana ihu da hauka tana fari da Ido tana kafkafkaf kamar me fyarfyadiya tana gurnani,tsorata Mahmud yayi gashi da tsoron mutuwa Nan take ya saki Mairo duk da haka Sai da ta kafta masa yanka a hannu da kwalaba ya rike hannunsa yana Kara, ta dauki yarta ta fice da gudu Allah yasa yana sauri zaiyi sex bai ko rufe kofar ba,Mairo ta fito tana falfala gudu kamar za a kamata tana gudu tana kwarara ihu a gari ko wanne takari yaga Mairo sai ya kwashe da gudu Shima ya Kara gaba,tana gudu Cele tana siyayya taga mutane radada ga Mairo tana ihu fasa siyayyar tayi ta fito ta kwashe da gudu,Kaka Allah sarki ya dawo daga masallaci da sallayarsa yaga takari yuuuu suna uban gudu Shima yabi sahu sai ga Kaka cankal cankal da kafafu sirara, Yazo ya wuce su Cele,Cele ta tsaya cak tace Yasin bani da amfani tunda kaka ya fini gudu,Kaka kamar guguwa haka, taci gaba da gudu har cikin gida tace wlh sai mun bar garin nan wannan masifa da me tayi kama kullum mutum a gudu,Mairo kuwa sai da ta zo gaban askarawa ta zube a kasa tace da larabci Dan Allah ku kamani ku kaini Nigeria,dariya suka hau yi mata suka ce yau ba ranar kame bace ba a Basu umarni ba,tace Dan Allah ku taimaka wani ya boyeni ana baku damar kame ku fito Dani,suka ki yarda sai gidan Sadiya ta tafi tace wlh ko a kafa sai na tafi Nigeria,da kyar Sadiya ta lallaba ta tace ta bari tukun ayi aikin hajji sai ta tafi Mairo duk ta zauce, a zabure take ta cakumi Sadiya tace Allah ya Isa ke da uwarki tsinannu Kun jefa ni a masifa,kin san haka larabawan suke kika zugani nayi aure,Sadiya tace ahayye muka dai taimake ki,ke da kika gudu kika bar Iyayenki marar tarbiyya kinzo da cikin shege an taimakeki kina mana iskancin banza, Kuma larabawan an fada Miki kowa haka yake da sex da yawa ko a bakar fata ana samun irinsu Wanda basa gajiya sai kiga laifina wallahi sai na koreki Nima nan aure nayi gidan mijina ne kafin ya sakeni Ina caskar kudi zan Kara gaba,Mairo tace Allah ya hadaki da irin Mahmud suka yi kaca kaca daga baya suka shirya dai.

Gwaggo ta warke fes sai dai yanzu tana dingisawa baza ta taba komawa dai dai ba,Dagaci an murmure Rabi tana masa aike akai Akai gashi yana ta kasuwarsa yanzu Jira suke ta haihu suje kafin bikin Gaji,Gaji ta samu Miji a cikin Kano yana da mata da yaransa uku lecturer dinsu ne a da,bikinta saura wata uku kafin lokacin suna sa rai Rabi ta haihu suna ta Shiri, yaran Dagaci mazan suna ta karatunsa suma,Gwaggo kuwa an nutsu lokaci kadan sai ta sa an Kira mata Rabi a waya sunyi hira tace Idan ta haihu zasu je.
Rabi ta basu kabarin anga iyayenta ta fada musu komai tace zasu zo tare da su har gida,Dagaci sai yadawa yake a gari Rabi anga iyayenta,ance wacce Rabin? Rabi 'yata dana rike yar tsuntuwa iyayenta sun bayyana Alhmdllh zasu zo ma.
Seraline kuwa ta dauke uwarta Inna ta Maida ta gidanta bangarenta daban sabo da ita kadai ta rage mata, Inna ana can itama.

Gidan su Cele wasu dakunan da suke Empty sai gani tayi an kawo Yan daudu su wajen takwas gasu da Jallabiya ta maza, can babu zani baza a barsu a garin ba sai dai sunyi bleaching kwalliya suke irin ta mata duk gasu nan a Makkah Yan daudu shekara da shekaru sai su tafi can da sunan neman kudi suna daudu a can suna luwadi sun cika gari suna ta batawa mutane suna,wasu ma sunfi shekara ashirin a can.
Cele tace ya zama dole na bar gidan nan wallahi wannan zama a wannan gidan bala'in zunubi sai ya shafeka,wannan wacce masifa ce haka,dole a raina mu wlh dole a daina ganin Takari da mutunci,wasu ne suke bata wasu akewa takari kudin goro amma akwai na gari, Driver ne yayi Sallama da Cele ta fito ta ganshi da kantamemiyar mota ya juyata yanda baza ta Kalli gaban glass ba,Ahsan yana ciki yana kallonta,suka gaisa tace Kaine ka siyo min botikin Awara? Sannan kana ta min Aiken kudi? Hammad yayi murmushi yace ae nine,a gaskiya na ganki Ina sonki,Cele ta kalle shi tsaf tace kayi hakuri ni zuciyata ta Saba da ganin me haske balarabe nake so ga Wanda yake jajir kullum idona Idan Ina kallonsa zasu Kara haske,Hammad yayi murmushi yace kiyi hakuri ki bani dama,Cele tace bafa zan soka ba ni Karka takura min wani nake so ni,Hammad yace larabawan nan basu da kirki,Cele tace Allah ya kona me karya Karka harzuka ni,ko Ina akwai na gari akwai na banza,Wanda nake so na gari ne,Hammad yace kiyi hakuri naga har kin harzuka,please Idan ba damuwa zan canja miki gidan zama,Cele ta kalle shi tace bada ni ba ka hada Kai da wasu larabawan a siyar dani yanda suka yiwa kaka,Yace haba dai Ina muamula da larabawa amma na kirki tace Kai ka kiyayeni munga Abila habee ma karewar tuggu,mu fa a tafin hannu mu kuke muna da tarihin garin nan abinda suka aikatawa masu Imani nasan akwai burbushin su Abu jahal har yanzu ba ruwana a Africa ma akwai nasu,ka kyaleni na bar garin nan lafiya ana aikin hajji zan tafi Idan na sauke farali,driver Hammad yace ni dai Ina rokonki Idan kina so ma zan hadaki da Yan sanda su ai baza su cuceki ba,Cele tace amma ba mutun daya ba a taho da bataliya guda ayi min kwambo da su sannan na je,yace to na gode ya juya ya mata Sallama,Cele tace jibe shi wani guntu da shi Dan banza suffa kamar gajeren wandon Kaka ta juya ciki,yana komawa mota ya fadawa Ahsan yanda sukayi yayi dariya yace ai Yan Makkah suna Shan gori a wajen baki sabo da Annabin Rahma yayi Hijira sun Kori Dan uwansu.

Washe gari motocin Yan Sanda sun Kai hudu ga mota Ahsan ya bada suka zo kofar gidan su Cele ba Ahsan a wannan karon,Yan gidan suna ta murna anzo kama Cele wai ta tsokani wani balaraben za ayi maganinta,sai suka ga ta hado kayanta ta fito tsakar gida tace na gaji da kwasar zunubi kullum Ina gidan fasikai,Boobs dinta tallafe tace abuna ya huta da kawo hari yanzu zai Kara bulbul,shegu inshallah sai an kamaku Daya bayan daya sai kunyi bursuna a kasar nan,suna jinta tana masifa tace Allah yasa na hadu da wata a hanya ta min magana ko ta nuna ta sannu wallahi sai na mata daga daga,in ance a fita filin badar Kun kasa sai madugo matsiyatan banza baza Kuga Annabi ba ta fice ta barsu,tana fita suka ce Alhmdllh haba jaraba ta tafi yau zamu huta.
Kaka aka biya ya fito da kayansa Shima zai shiga gefen Cele yayi Bismillah yace Ubangiji ka rabu da sharrin Yan uwan kafiran zamanin baya ya shiga mota suka tafi,Cele tace kaka muyi alkunutu tun a mota suka fara karanta alkunut ita da kaka har aka kaisu dai wani gida a unguwar takari ne amma gidane dogo a hawa na biyu Cele take ita da Kaka,gidane hadadde na glass da Glass gidan glass takari suke Kiran gidan,2bedroom and Palo sai kitchen kowanne daki da toilet komai sabo ne a ciki me kyau Palo yasha kujeru da center carpet,Hammad yace Alhmdllh kuyi zamanku a nan Kuma ku daina wata sana'a zan dauki nauyinku,Cele tace Masha Allah,Allah yasa na soka a haka,nidai ba ruwana Idan ban so ka ba Karka kace na yaudareka ko na cuceka naci kudinka,bani na Saka ba ato,Kaka yace kwarai kuwa,Hammad yace sabo da Allah nayi suka masa godiya.

Washe Gari Ahsan shopping yayi na suturu masu tsada da kyau harda agogo Rolex ya bawa Hammad yace gashi ka kaiwa Cele a matsayin Kaine,Hammad ya tafi gidan su Cele suna ta kallonn film da Kaka,Kaka ga lemo a gabansa yana korawa yace Ina goge duniya Alqur'an bana son barin garin nan,kinji Ko ciwon Kai banyi ba har yanzu,Cele tace to komai me kyau ake ci ba cuta,Kaka yace da a Nigeria ne da yanzu na shanye paracetamol yafi carton guda,maganin ma baya aiki duk kamfanunuwan mu sun gurbata maganin basa aiki Idan cuta ta kamaka ayi ta gabza maka kwaya da Allurai basa aiki,komai namu Babu me kyau,asibiti ma abinda aka ga dama akeyi,sai ayi ta shirme ga inda ya dace a gyara baza ayi ba Kai muna Shan wahala a Nigeria kawai rayuwa muke,muma da halinmu muyi ta sabon Allah ana jika kasa da jinin bayin Allah Wanda jinin mutum Daya mumuni ya Isa ya haifar da masifa a kasa yau mutane million nawa aka kashe,a kama wasu a gana musu azaba,a kama wasu masu aure mata a auri matan wasu aure kan aure su haihu da wasu,cin Amana,yaron me gida ya kashe me gidansa,a danne hakkin marayu,zinace zinace,luwadi ga lasbiyalizim wai yan Lesbian inji Kaka alkalai zalunci kowa zalunci,masu siyar da kayan masarufi zalunci awo ma baza a baka dai dai ba,Yan kasuwa su boye kaya su tashi abinsu kullum sai an Kara kudin kaya,daga an fitar da doka kafin ta fara aiki mutanen kasar sun karawa kayan Abinci tsada, awannan zunubin da zalunci Ina zamu kaishi,Cele tace kyale su Kaka Allah zaiyi hukunci ga shugabanni sabo da suna da ikon su sa baki a gyara baza su ce komai ba su suna da kudinsu ba abinda ya dame su komai tsadar Abu zasu iya siya ba ruwansu,mutane Yan kadan sun jefa milliyoyin mutane a mafisa.
Hammad ne ya shigo yayi knocking Cele ta Bude masa ta gaida shi ya amsa yace gashi ya Mika mata,tace Kuma ma dai? gaskiya kana kashe mana kudi mun gode fatan dai nan gaba Idan banji sonka ba baza aji haushina ba? yace ba damuwa tace to na gode Allah ya Kara maka so na ya links shi sai dari indai hakane ni kuwa na sha kyauta,dariya Hammad yayi yace kefa baza kice Allah ya sa Miki so na ba,tace wayyo bana mararin samunka yayi dariya ya juya yace na tafi tunda babu Kara abin,tace yo ai gaskiya na fada.

Salma tana ta aikinta kullum bata hutawa,Mami ce ta shigo kitchen ta iske ta tana girki tace sannu Mami,Mami tace yawwa kawai ta shareta,kamar tayi kuka tunda Auta ya fara ciwo basa zuwa school dukkansu,jinyar Auta take fama.
Washe gari da sassafe ta tashi ta tafi barruwan flowers tana sanye da Doguwar Riga yar fitted me siririn hannu dark blue me layin layin fari tana aikinta Auta yana zaune a garden din yana latsa waya yana kallonta tana rike tiyo tana fesawa flowers ruwa tana bi layi layi ta bata rai kamar zata yi kuka,ta Kalli Auta ya dago ya kalleta ta dauke kanta yaci gaba da kallonta ta sake kallonsa ta gasa masa harara,tana gamawa ta wuce gate ta budewa Baffa zai fita ta yafa Dan karamin mayafinta,tana rufewa na shugo da motata ta Bude min gate ta kalleni na kalleta nace Masha Allah gaskiya Allah yayi halitta itama,Ina fitowa ta karaso da gudu tace Aunty Ina kwana,nace lafiya Alhmdllh nayi wucewata,Salma ta tsaya tace kowa ya tsaneni ta fashe da kuka ta koma kujerar me gadi ta zauna,dakin Auta ta shiga yace ki kaini Palo,ta rikeshi tana dafa bayansa yana dogarawa da sandunansa suka fito Palo,ta karbi sandunan ta jingine gefe,Mami tana kallo tace Auta bai karya ba,Salma ta fada kitchen da gudu ta fara girki,tana jin Karar mota ta fito da gudu ta fice ta bude gate aka fita ta rufe ta dawo kitchen da gudu ta iske Auta yana kwance a cinyar Mami sai shagwaba yake,Ina wajen Wise sai daga baya na shigo bangaren Mami na samu Salma ta fito daga kitchen da tire ta jerawa Auta komai a dining tazo tace ka taso,Mami tace jeka ka karya, tace ke a baki Zaki bashi sometimes baya ci da Kansa,Salma kamar ta fashe tace to ta koma dining tayi serving nasa ta hada masa tea tace Bude bakin ko Shima sai an bude maka? yace ae,Hannu tasa a kumatun Auta ta matse masa baki ya saki Kara tace to ka bude ance,ya Bude kadan tana bashi a baki,yana ci yace nifa Idan Ina cin abinci ana shafa min gashi fa inji Auta,Salma tace nidai mutuwa zanyi kowa ya huta kawai ta saci kallon Mami taga tana kallonsa hannunta ta sa a cikin gashinsa tace ko kunyar Iyaye Babu a gabansu za ayi wannan aikin ni wlh Ina da kunya ba a nan na taso ba, Auta yace ko a Kira Baso ne? tayi shuru taci gaba da bashi a baki tana shafa masa gashi,Mami ce tace dani Rabi Idan cikin ya cika watan haihuwa ki dawo nan sabo da gudun matsala,nace ae haka yace me gidan can Shima nan zamu dawo,Mami tayi murmushi tace so kike ta rainaki ko kina tsokanarta kema.

Auta yana koshi yace na koshi a goge min bakina,Salma tasa tissue ta goge masa,yace zan kwanta a kaini kan gadona,harara ta watsa masa tace tashi ta rike shi har da yin tangal tangal zai fadi, tayi sauri ta ruko kafadunsa tare da Mika masa sandunansa suka tafi.



Masu Audio kar a juya littafi Babu izinina na siyar da shi,





Masu sharhi Ina godiya aci gaba Dan Allah





AsmaBaffa
08061929616🌼'YAR AIKIN KARUWAI 2🌼
MATAFIYA


BOOK 2


61-65



Official

By
AsmaBaffa

SADAUKARWA GA
ZAINAB USMAN



*👭GARKUWAR MATA👭*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login