Showing 18001 words to 21000 words out of 152911 words
da ajiye Santana,sake daukan Santana tayi tana nishi,Sabreen ce ta shigo dauke da sallama,Baki ta saki me Zan gani haka? Santana ya karasa Mata Namiji da suna Hajara ko,soyayya ake ke tunda kin kasa,ke Yar nan rufawa kanki asiri ki samu Wanda zaiwa local government dinki aiki,Kinga ki kiyayi kwayar nan baza kizo ki maida matata ruwa ba gashi na samo kanta har goyani take karki zo ki dinga dagula min iyali ato,Sabreen dariya ma ya bata Zama tayi ta ajiye Jakarta a gefe Santana yace gata nan kuyi Hira Amanatun Amana wallahi idan Kika bata kayan maye yau sai kinci dan banzan duka a gidan Nan,Sabreen tana kallon ikon Allah ta saki baki.
Wise ce taje da sassafe part din Iyamami zata gaisheta sabo da ta hanata zaman lafiya duk da tana zuwa gaisheta gwara ta sake dagewa ko zata samu ta kyaleta ta zauna lafiya,ta sameta a Palo Baffa Yana gefenta shima Papa Yana zaune,Wise ta durkusa tace Ina Kwana Iyamami,kallonta Kawai tsohuwar tayi tana tabe baki tace yau Kuma kinibibi ne ya tashi wato sai da Kika ga Ina tare da yarana Kika Zo gaisheni sabo da suce kina da biyayya ke ta gari ce,Baffa yaji ba dadi Iyamami taki shiryuwa yanzu abin ya koma Kan Wise,tashi yayi ya bar part din ma Sabo da takaici,Shima Papa yaji haushin irin wulakancin da Iyamami ke wa matarsa tashi yayi kawai ya bar palon,Wise tana tsugune tace Dan Allah Iyamami idan wani Abu na Miki ki yafe min mu zauna lafiya...da wa Zaki zauna lafiyar? Karuwa ballagaza,na taba ganin marar tarbiyya irinki kinzo kin makale Mana a gida sabo da Kinga arziki ko? to abinda Kika Zo samu baza ki samu ba Karuwar banza Karuwar wofi,fasika,Wise ranta ya baci tace Ina ganin girmanki amma ki gyara kalamanki ni ba karuwa bace yanzu ba Kuma fasika bace aure nakeyi nan Kuma gidan mijina ne karki ga nazo Ina Baki mutunci kice Zaki takani wallahi bazai yuwu ba never ai ba aurenki nake ba Kuma ba zamanki nake Yi ba,sabo da kin samu ma na gaida ki sabo da fa mahaifiyar Mijina ce ke kema idan da Kara ai Mahaifiyata ce ....wani ihu Iyamami tayi ta dafe kirji tace ni na Zama uwarki Allah ya kiyaye ban haifi karuwa ba Kuma ki sani bana sonki tare da dana sannan bari kiji tunda Baki San muhimmancin uwa ba,Baki San zafin haihuwa ba dole ki fada min abinda kika ga dama sannan mu zuba ni dake Zan fito Miki da asalin ya nake kin daina Jin dadin aurenki,Wise tayi Murmushi tace to shike nan Naga yanda za ayi ni Kuma na kasa Jin dadin mijina tunda Yana so na Ina sonsa Ina jiranki ta juya tayi tafiyarta.
Iyamami mikewa tayi ta bita har part dinta Wise bata sani ba ma tana shiga Papa yazo ya rungumeta ta kankame shi suna dariya tace murna nake Zan haihu,ai na fuki murna Zan sake samun yara Alhmdllh yayi kissing dinta suka sake rungume juna sai ga Iyamami ta shugo tana zuwa tsakiyarsu ta Shige tare da Jan hannun Papa tace muje Dana Ina son magana da Kai tana zuba Murmushi Kamar wata kishiyar Wise,Papa juyowa yayi hannunsa Yana cikin na Iyamami tana jansa Yana yiwa Wise signa akan tayi hakuri karta damu,ta bangaren Iyamami idan suka hada Ido sai ya washe Mata baki irin ba matsalar nan, sai da ta kaishi har bedroom sannan tace yaushe zaka kaini gidan Nawwar ne papa bai San me Iyamami zata Yi ba yace yaushe kike so? tace gobe,Allah ya kaimu ya furta sannan taci gaba da takalo hira, Wai dan Kar ya kula Wise,Wise tana tsaye sororo a palo tace hmm mu a gaya Mana bariki mu da Muka fito daga can tunda baza ki ja girmanki ba Zaki gani wlh na gaji, Papa ne ya fito Iyamami tana gefensa ya zauna a kujera itama Iyamami ta zauna,Wise Dining ta koma ta zauna tare da juya musu baya ranta in yayi dubu to ya baci,Papa ya juya ya kalli Wise data juya baya ransa ya sake baci da halin mahaifiyarsa, Wise tashi tayi ta ebo shinkafa sai ta zuba mai da yaji tana ci abinta,Papa yace Ya Naga kin San mai da yaji? Wise tace kasan cikin nan da kayi min ne yanzu abinci sai da yaji Iyamami hankali tashe tace ciki? Papa hankalinsa ya tafi Kan matarsa, Suka rabu da Iyamami suna hirarsu,Wise tace ya fara motsi ma,farin ciki ya ishi Papa ya manta ma Iyamami na nan yana washe baki yace ke ki bari dan Allah? Sosai fa hmm baka ji ba da alama Dan kwallon kafa zamu haifa akwai Chinese, Iyamami ji take Kamar bakin ciki ya kasheta ta mike tsaye da Niyyar tafiya tace dama ka haukace ta juyar maka da kwakwalwa, Papa yace Dan Allah kiyi hakuri Iyamami ba yanda na iya halittar Allah ce so,Kauna abin ne ba a iya Masa komai dagiya ,Digiyar ubanka haka na baka tarbiyya mutumin banza,ke Kam kinyi asara karuwa tirrr ta juya ta fice,Wise tace bana son sunan nan da take kirana da shi Karuwa,Amma ai ba ita bace ni na San ba karuwa bace ke cewar Papa Yana lallashin Wise yace karki tashi hankalinki akan wannan kina da ciki Kar a samu matsala please,shike nan ya wuce ta furta sannan ta mike Suka koma bedroom Suka tsunduma cikin rayuwar aure.
Washe gari Iyamami Driver ya kawota gidana,Ina Palo a tsaye Ina Shan ruwan sanyi,Nawwar baya gida Mami ma ta fita,ko sallama Babu ta fado nace a'a ai na zaci me gidan ne har zance Ina Islamiyyarsa take Naga Kuma shi ba jahili bane Dole zai min Sallama,Iyamami ce ta nuna ni tace ubanki ne Jahili Yar iska karuwan banza karuwan wofi asirin da kuka yiwa jinina sai ya karye algunguma duk kece kike hada jinina da kawayenki karuwai algunguma marar mutunci Yar cikin shege Yar tsuntuwa ai dama wacce aka tsinta a kwararo Ina zata Yi Albarka,ai cikin Shege shi ake Haifa a jefar sabo da gudun abin kunya,Ido na runtse sabo da maganar ta min zafi matuka har ban San ma me zance ba,nace Hmmm Iyamami kenan ai ke sai an Miki Uzuri tsufa ya kamaki dole ki dinga haka Sannu ke Kuma tsufan naki da hauka ya zo,uwarki ce mahaukaciya,nace a'a fa Kinga ya isheki karki jawo na fusata nayi sama dake na nunawa Allah,barikin Nan ba Gama sakina tayi ba mu bata sake mu ba har yanzu tana jininmu aure ne yasa ma muke hakuri dake ba yanda zamuyi Amma idan da a baya ne wlh da yanzu mun nuna Miki Alkibla,Nifa ba danki nake aure ba bare kice Zaki iko dani kinga ki juya inda Kika fito billahillazi Zan iya kina zagina Zan rama ba kunya ce dani ba,Sanda nake gida lokacin ne nake Rabi yanzu miracle nake bazai yuwu ki hanani zaman lafiya ba,bariki Kuma kiyi ta fada ki hau sama kiyi ihu ki sanar Rabi matar Nawwar karuwa ce,Iyamami tace dama nasan ba tun yau ba ke kinfi matar Yusufa fitsara baki da kunya,nace dama ni Ina Naga kunya ko nace Miki Ina da kunya ne ni? kullum jikanki Yana cin dadina ta ya za ayi nayi kunya ai kunya tayi nan munyi can, ba abin kunya bane in Miki zigidir a gidan nan....da sauri Iyamami ta bude baki tace ni din? ah ke dinfa Dan kina kakar mijina sai kizo ki dinga takura min kina zagina wlh bani da mutunci ki Kama kanki tun kafin ki kaini bango,ai dama ke ba Yar arziki bace Yar iska karuwa me bin maza,Nace ae awajen mijina ba Kinga ma ciki nayi wlh gashi har ya fito ai da jikanki nake yin iskancin ga sakamako kin gani na shafa cikina da ya fara girma,Iyamami ce ta juya ta fita tana Jan kwafa,nace ikon Allah sai kace uwar mijina kinbi kin dameni da zagi akan Kawai na auri jininki,Nawwar na Kira yana dagawa na fashe da kuka ya rude Yana tambaya lafiya? Ko cikin ne? Nace da ciki ne ai da sauki Iyamami ce tazo ta zazzagi iyayena tana ce min karuwa me bin maza ,fisabilillah igiyarka uku a dinga min kazafi ko a baya ban taba Iskanci ba sai yanzu tazo tana sheganta min dana tsakani da Allah an min adalci kenan, calm down ya furta ka dawo Kawai ka bi min hakkina na sake fashewa da kuka,Wai meke damun tsohuwar nan ne Ina ruwanta da Iyalina, nace Ni dai Kawai ka Mata magana Kar nayi loosing temper baza a ga da kyau ba Zan iya fasa motarka,yace ki bari dai idan kin siyi taki kya fasa amma ba tawa ba nasan halinki fa kece za a ciwa mutunci ki bari ai ba ke ba Kam na sanki Baby Kamar yunwar cikina,Haka kace ko? Yace nasan kin Mata rashin kunya na sani na sanki fa, tunda Kinga haka ya fi Miki shike nan kiyi ta yi,Iyamami fa Itace ta haifi Baffa ai ko Kara sai ki yiwa Baffa,ke baza ki dinga hakuri ba,kaji zagin data min kuwa,please aiki nake yi I'm busy ya kashe wayar,mamaki nayi nace iyye wato ni ba kowa bace nasa sune masu gaskiya gwara dana rama,na zauna saman kujera Ina dariya nace shegiya ni Rabi.
Dagaci tagumi ya zuba talauci yasa ya rame yayi Baki ya gama tashi daga aiki idan ka ganshi sai ka tausaya Masa,Gwaggo taji sauki suna gida amma har yanzu bata Fara tafiya ba tukun Gaji ce ke jinyarta,gaba daya sunyi baki sun rame sabo da wahala da talauci duk dukiyar Dagaci ta kare, Kuma Yana haka Dan albashin na Dagaci ya rasa sabo da hukuma ta sa an karbe Dagaci daga hannunsa an nada wani a garin sakamakon abinda ya dinga aikatawa a garin tuni hakimi ya tsige shi,sai aikin gona yake yiwa mutanen gari ana biyansa kudi wahalar duniya ta ishi Dagaci,nadama da kuka yayi ba adadi,Haka Gwaggo ana kwance ana nadama ga cuta ga yunwa,Gaji Sana'a ta Fara tana soya awara safe da yamma ba karamin taimaka musu kudin ke yi ba,Gaji ce ta kalli Gwaggo dake zaune tace Gwaggo iya hakkin Rabi ma ya ishe mu,ki duba dare Daya Allah ya Gama damu,yanzu ga auren ya gagareni aikin gomnati ma yanzu ba a bawa me diploma Matukar ba bangaren lafiya kake ba,Gwaggo tace ke dai bari nayi nadama na godewa Allah da ban mutu ba sai da nayi nadama Allah ya karbi tubanmu tashi ki jika Mana garin kwakin muci sai ki ragewa Baban Mairo nasa,Gaji tace to ta mike kenan taji ana sallama,amsawa tayi tace ya akayi ta saka hijab dinta ta leka Jin muryar Namiji Babba,Gaji anyi laushi harda gaisuwa yace dama Rabi ce ta Aiko da sako a kawo muku gashi a mota,ya nuna wata kurkura shake da kayan abinci ba abinda Babu na abinci shinkafa ma tafi buhu biyar,Gaji fita tayi tana murna taje har gona ta kirawo Dagaci,suna murna tare da me motar Suka sauke kayan Suka shigar dasu ciki su taliya macaroni manja man gyada Maggi,tarkacen girki daban daban harda buhun masara Dana gero Wai ko koko sai su dinga Yi da kunu, bayan an shigar da Kaya ya fito da kudi dubu dari biyu yace gashi tace kuyi cefane,Dagaci yace Dan nan daga can kudun ta turo? Yace a'a kudi ta turo ta accnt ta lissafa abinda za a siya gashi nan harda sabulan wanka da wanki da omo duk gasu nan,gaban motar ya sake budewa ya fito da shaddoji da atamfofi da leshi yace gashi nan ku dinka tace kafin ta zo sannan tace a fada muku ciki ne da ita wata hudu baza tazo yanzu ba tayi nauyi da yawa,Gaji ta Kama dariya tace wata hudun ne tayi nauyi lallai Rabi,Dagaci yace to ta Zama Yar gayu yanzu bata Saba da wahala ba,yaro an gode tsaya kaima a baka wani Abu cikin kudin,Me motar yace a'a ai ta sallameni nikam yaja mota ya tafi,Yau su Dagaci sun rasa inda zasu sa kansu sabo da murna,Gwaggo tace wannan kudin baza mu sa a gaba mu cinye ba ka daina aikin wahalar Nan na gonar mutane ka samu Sana'a ka fara,Dagaci yace ai dama za a cire dubu hamsim na cefane sauran na Kama sana'a, itama Aunty Amarya tana can gida wajen danginta tana jinya tana nadama taji sauki itama.
Bayan sati daya Ahsan kullum idan ya dawo sai yace baida lafiya baya taba kula Maheerah sosai sabo da Kar ma ta kusance shi,yau ya leka Office Maheerah kuma tana gida,Ina dakina a kwance abin duniya ya isheni na abinda nake ji a cikina kullum sai nayi kuka sabo da motsin kullum karuwa yake, Maheerah wayarta ce tayi Kara ta duba sai taga number Ahsan dagawa tayi taji muryar Kanin Baban Ahsan ne yace tazo asibiti an kwantar da mijinta yayi hatsari,a gurguje ta fice sai asibitin tana zuwa ta fada dakin ta hango Ahsan an manne Masa idanuwa da plaster, tace lafiya me ya same shi a Ido? Likitan yazo Yana Mata bayani cikin harshen larabci yace sakamakon hatsarin da yayi ya taba Masa jijiyar idanuwansa nan take sun samu matsala yanzu Kam ya daiba gani da idanuwansa sai dai ko Nan da wasu shekaru ana sa rai zasu dawo normal,za aci gaba kawo shi asibiti ana bashi magani amma jikinsa bai samu rauni ba Kansa ne da ya daki sitiyari nan take idanuwansa Suka tabu,Maheerah zata Yi kuka likita yace kiyu hakuri ki godewa Allah da ba kwakwalwarsa ta taba ba Kuma ana sa rai zai warke Inshaallah,Kanin Baban Ahsan sai hawaye yake Yana Kiran yan uwansu Yana fada musu,Cele bata San me akeyi ba taga dai Maheerah bata gida shima Ahsan haka har kwana uku,yau tana Palo ta zuba tagumi abinda take ji a cikinta ya dameta sai kuwa sallama taji taga Maheerah ta shigo rike da hannun Ahsan Wanda fuskarsa ke a cikin bakin glass,sai kanin Mahaifinsa da Yan uwan Ahsan da Dangin Maheerah suna ta Subhanallah,yanda cele taga Ahsan bai San inda yake jefa kafarsa ba gashi an rike Masa hannu ana Masa jagora yana duru duru Kansa a sama,ta kalli Yan Uwa Ana ta jimami da jaje ana Addua Nan take Cele ta gane Kamar makancewa yayi duba da yanda yake komai sai an ja shi,dangi suna gama jajensu Suka tafi ya rage sai mu a gidan Ayusha ta dafa Kai da hannaye biyu tana Jimami Oga ya makance,Cele ta zura Masa Ido maheerah ta zabga Mata uwar harara ta mike tana cewa Ahsan ya tashi yaje yayi wanka ya huta taja hannunsa tana Masa jagora,suna shigewa bedroom ganin ba kowa Maheerah ta zaunar dashi a saman bed ta tsaya a gabansa tana dariya kasa kasa,ta juya ta Masa gwalo,ta kalle shi ta tabe baki ta tsura Masa Ido sai ta nuna shi da yatsa tana Masa gwalo tana zaginsa da hannu yanda larabawa ke yi a nasu salon,ya zaci bata kusa tunda ba gani yake ba ya kirata da Habibty sabo da rainin hankali a gabansa tayi taku irin na gudu raf raf tana tsalle ta furta Noorul Qalb gani nazo Ina Palo ne me kake kayi hakuri bari na maka wanka ta rike hannunsa ta jashi toilet tana tabe baki tana Maganar zuci Ina Zan zauna nayi bauta kana makantarka Ina da saurayina wayyo Zan Shana tana washe baki,Haka ta Masa wanka tana zaginsa da zancen kurame a gabansa tana Masa gwalo har ta Gama Suka fito ta shiryashi taki gyara Masa cola din rigarsa ta barta a Haka a mike,gashinsa ma tana tajewa ta barbaza shi yanda zaiyi muni ta barshi a haka sabo da baya gani,ta dakko jagira ta Mata ta dambara Masa baki a girarsa duka biyun,ta zana Masa katon bille a goshi,Yana tambaya me take sa Masa ne? tace Wai goge Masa wani bakin Abu tayi yaji Dadi matarsa na kula da shi, jambaki ta dakko tace bari na shafa maka man lebenka,dama Yana da manlebe ba maza Ashe jambaki ta dambara Masa ja tace an gama noor ta jawo hannunsa ta fito da shi Palo da glass dinsa ta zaunar da shi,Cele ce ta fito daga kitchen sai data tsorata ganin kwalliyar Ahsan,Maheerah tana gefe kuma,Cele ce tazo tace na gaji dole na tofa albarkacin bakina,Maheerah ta kalleta ganin tana magana da masifa,ta nuna Maheerah da yatsa tace sabo da bashi da lafiya baya gani shine kike Masa wulakanci haka dama nasan ba sonsa kike ba munafuka annamimiya,Maheerah ta gane Annamimiya sun sani kalmarsu ce,Cele tace kiji Ni da kyau majnoon....Maheerah ta nuna kanta Cele tace ae ke fa ta Mata ambola tace Umminki, Maheerah ta Kama Cele da kokawa Cele ta shaketa to Maheerah ba karfi Cele ta wanketa da Mari ta jefar da ita tare da take ruwan cikinta,Maheerah ihu take,Ahsan Yana tambaya meke faruwa da larabci,Ayusha ce ta fito tana ganin haka ta koma kitchen ta buya tasan cele da karfi,Cele ta dage ta zauna a Kan Maheerah ta dinga naushin bakinta Kamar ta samu gardi,bakin Maheerah ya fashe sosai jini na fita,Ahsan Yana ta masifa daga Zaune su bari yasan da Cele akeyi,cikin harshensa karyayye yake furta Celei Celei,ya koma Rufaida,sai lokacin Rufaida ta kyale Maheera dake kwance tana kuka,gashi ita ba abin ta kiri cele ba cikinsu dake jikinta shine hope din Maheerah tunda bata haihuwa wannan ce damarta ta samun da jininta,da kyar Maheerah ta tashi ta koma daki tana kuka tana wanke bakinta.
Cele Kuma hannun Ahsan ta riko tunda baya ganinta taji tausayinsa sosai har hawaye ya zubo mata,hannunsa ta Dora ta fuskarta Wai yaji kukan tausayinsa da takeyi tace Sannu kaji kuka nake Ina tausaya maka Allah ya baka lafiya wayyo me kamshi na ta fashe da kuka yau ko turaren ma da nake shaka ba a saka maka ba Amma gashi a makale a kayanka kamar ka saka,Me kamshina ta sake fada tare da durkusawa a gabansa,hannunsa ya Dora a kanta Yana lallashinta da hannu, Dan karamin towel ta dakko