Showing 66001 words to 69000 words out of 152911 words
maka Omaira kanwar Rabia,Auta yace gaskiya Baffa a'a nasan Dan kyau tana da kyau ai ba kyau ne so ba,so ba a kyau yake ba kawai ni nasan ta cancanci a sota amma ta min karama,Mami Ido ta zaro tace Auta Omaira 19yrs ce tayi maka karama? Auta yace ae ni babba nake so a samo min kamar Wise matar Papa ko kamar Auntyn Nawwar matar Yaya yawwa irinsu nake so,why? Baffa ya tambaya,yace gaskiya Karka ku sa nayi rashin kunya amma kamar Omaira me zata bani, Baffa yace zaman kudu ya lalata min Yara da a Arewa ne yaushe Auta zai iya fadan haka Okay fine mu dai Omaira ce zabin mu,Auta ya mike yayi tafiyarsa, Mami tace Kar a takurawa Autana Honey a kyaleshi tukun ya samo,wannan yaron za a bari ai kuwa za a ga ba daidai ba tunda Allah ya hore ayi masa shine dai dai,Mami tashi tayi tace bari naje na lallashi Autana,ke kike shagwaba yaron nan wlh,Mami dai ta wuce bedroom din Auta.
Samun Auta tayi ya zauna yana kunci,tace Babyna,baki ya turo gaba tace ni na Daina kulaku tunda da abinda zaku Saka min kenan,Mami tace Auta abinda zan iya cewa mun baka sati daya ka kawo mace kana gani biki saura sati biyu kacal me kake Jira,Why are you so stubborn? Sai kace dole nace na fasa auren,wallahi baka Isa ba Auta aure zamu yi maka,Auta ya bude baki,wayarsa ce ta dauki Kara ya duba yaga Baso yace Mami zanyi waya,amma kafin nan ni a wanne gidan zan zauna? Mami tace gidan da ka zaba a Gina maka shi ake maka amma tunda dama yaro ne Kai ga part guda nan za a baku a gidan nan ku zauna da Amaryarka kafin muga kamun ludayin naka muga ya zaka rike yar mutane Idan munga normal sai a karasa gidan ku koma gashi yanzu Alhmdllh ranar da ba lecture kana zuwa Office har weekend Masha Allah saura matar muga yanda Auta zai riketa, dariya yayi ya furta 9 months dai dai ta haihu Mami Idan Ina sonta Idan kuwa bana sonta shekara Tara maybe Kya samu jikan Auta ya furta yana dariya,Mami dariya tayi tace Oh Auta ko kunya ai shike nan zamu gani ta mike ta fita,Baso ya Kira back yana dagawa ya jishi a cake ga Salma nan tana ta ihu a gefensa,yace kazo ka siyeta ko na aikata lahira ta isheni bana sonta tam,Auta yace Kai wanne hauka ne wannan muna da danganta ne da zaka dame ni ya ja tsaki ya kashe wayarsa.
Washe gari kuwa Salma ce ta durkusa a gaban Baso jiki na rawa yana zaune yana fushi ya harde hannaye a kirji,a Hankali tace kayi hakuri indai akan nace ka biya Sadakina ne kake wannan fishin kayi hakuri ga abincin Dan Allah Kaci,kayi hakuri na Daina cewa ka aureni Dan Allah Kaci abincin kaji,ya kalleta ransa a bace yace karki sake cewa kina so na Idan ba haka ba bazan sake cin abinci ki ba ko mutuwa zakiyi banza kidahuma ana soyayya dole ne? nace bana sonki ko dole ne mayya, Karar tsaiwar mota suka ji a kofar gidansu, Auta ne Yazo motar ma ta Abokin Nawwar ne ya karbo bayan ya sauka a jirgi,uban Swagga cikin kana nan kaya wando duk a farfashe pencil me shegen kyau da tsada arsh,sai Riga fara me dogon hannu ya dora top a Samanta marar hannu maroon and arsh,takalminsa Snickers me kyau arsh wandon nan harda sarka a gefe Daya gashi ya zazzago shi boxers dinsa a waje suma taci kudi sai sheki take an mata wani shegen gyara,yana kamshi ya fito da wayarsa a hannu ya mugun haduwa.
Tafiyar gayu yake yana taku dai dai ana wani bubbudawa irin na Samari masu tashe, sallama yayi ya shiga gidan Kai tsaye,Baso yana ganin Nawaf ya mike yace bros yana ihun murna yace Oga chansa chansa Chau Chau sa'ade ya wani yin ta Yan daba,Auta dariya yayi ya mikawa Baso hannu suka gaisa sannan Baso ya jawo masa benchi ya zauna ya masa tayin abincin yace ya koshi,Auta yace na shugo ne ya deal dinmu? Baso ya sheke da dariyar murna yace yana nan Idan ka shirya,ya kwalawa Salma Kira yace baki ga abokina ba ne? Salma tazo tana murguda baki ita Baso take so ala dole ta durkusa tace ina kwana? Auta ya kalleta a banzance yace I'm good ya shareta,Baso sabo da kar a ji sirrinsu ya ja Nawaf kofar gida yace nawa zaka siyeta? yace Million daya a Hakan ma kafin na roki Baffa ya bani sai na sha wahala kasan ni dan Makaranta ne sai yanda aka yi Dani,Baso yace Allah mutumina to ka gane Kace Baffa ya baka dubu dari uku,Yayanka dari uku Mama ma dari biyu a haka Zaka hada kudin a saukake,Nawaf yace kamar ka sani haka nayi a Hakan ma da kyar kowa cikinsu ya bani,yanzu ya za ayi nan da sati fa za a daura aure ka samu manya ka sanar musu,amma kana ganin zata yarda Salman? Baso yace ita din banza na karyata kuwa,ai ka kwantar da hankalinka yanda nace haka zata bi kawai ayi komai na biki sai ka bani kudina ranar Kuma a Kai maka amaryarka,Auta yace Iyayena ne fa zasu zo bincike karka yi shaye Shaye please kar a samu matsala Dan ni taimakonta zanyi kaima na taimaka maka kawai ba wai sonta nake ba, Auta har ga Allah taimakon Salma zaiyi ba wai ko yana jinta a ransa bane kawai dukan da ake mata gata marainiya gashi Baso baya kaunarta abin ya mata yawa shine dalilinsa na aurenta amma shi Kam ba abinda zaiyi da ita ya fiso ya samu su Mami su kyaleshi tunda Idan yayi auren hankalinsu zai kwanta shi Kuma a hankali sai ya samu zabinsa katuwa nunanniya ya auro abarsa ya sha soyayya,haka suka gama tsare tsarensu da Baso da zai tafi har dubu ashirin ya bawa Baso,yana komawa gida yace wa Mami ya samu mata,tace har kayi wata budurwar? Karya yayi yace ai sun Dade tare kawai yaga karama ce 19yrs tazararsu ba yawa amma ya duba yaga tana da hankali,ya Basu Address,Baso tsabar bukatar kudin da yake baiyi Shaye Shaye ba,ya samu Salma yace Salma aure fa zan Miki,da mamaki Salma ta kalle shi,ya bata rai yace kinga karki zubar min da damata kudi zan samu sai na samu babbar sana'a na Gina mana gida daga baya yace zai sakeki sai ki dawo muyi aurenmu Muji Dadi,Shima yaron iyayensa ne suka takura masa sai yayi aure shi Kuma baya so a masa auren dole sai nan gaba zai sakeki ya auri zabinsa kinga Nima sai na aureki lokacin nayi kudi abinmu ya kika ce?
Salma mamaki ya kamata da tsoro tace Idan kana so na Baso ta ya zaka bawa wani ni ya aura? Baso a ransa yace Dan baki sani bane siyar dake nayi,Gaskiya baka so na nidai bana son wannan yaron Kai nake so wallahi ta fashe da kuka,Baso ya hade rai yace wallahi zan karyaki ni na baki Umarni amma kice baza ki ba,nifa Zaki taimaka ashe karya kike bakya so na,Idan kina so na ai Zaki so farin cikina,kiyi acting kamar film karki sake ko ya aureki kice Zaki masa fitsara a hankali zai sakeki kawai ki bada hadin Kai kamar dama kina sonsa,Salma tana goge hawaye tana shesheka tace to zanyi sabo da Kai amma ka tabbatar zaka aureni nan gaba? Baso yace ya zama dole kawai kiyi abinda duk na tsara Miki,tana shesheka tace Allah bana son tafiya na barka,bana so nayi nesa da kai har kudu fa haba,Baso lallabata ya shiga yi abinda bai taba to ba yace kiyi hakuri zan dinga zuwa Ina ganinki kema Zaki dinga zuwa karki ji komai,haka ya dinga lallaba Salma da karya da gaskiya har dai ya samu ta amince zata Auri Auta amma Sabo da Baso Kuma da sharadin ana sakinta zata dawo ya aureta ba abinda Kuma Kuma zai shiga tsakaninta da Auta.
Mami,Baffa, Papa da Nawwar suka zo gidan su Baso sunga gidan sunga Salma Kuma sun basu tausayi matuka,Salma ce ta sauke su da girkinta da ruwa da lemo da Baso ya siyo,Baso harda basu kabarin tarihinsu amma sai yace muna zaman mu da Kanwata Ina ji da ita Ina matukar kaunarta Ina fata dama Allah ya bata Miji na gari Kuma Alhmdllh ta samu yaro yana sonta tana sonsa,Salma dai daki ta koma tana rusa uban kuka ganin da gaske fa auren zata yi,Baso da shi aka tafi cikin dangi can jigawa,bayan sun gama komai Baffa sai da ya sake bincike ya samu suna da asali me kyau Papa ne ya koma ya Kai kudin aure aka Yanke biki saura sati daya za a hada Dana su Sultana, abinka da talaka Wanda komai yi masa za ayi to fa sai yanda akayi da shi, lefe sai da aka kawo akwati goma cif kaya na kece raini komai me daraja aka yiwa Salma sabo da dama su Mami sun shirya dole da Auta za ayi auren shi yasa komai da shirinsa akayi,Auta sai gayya yake ba ruwansa da wani ba soyayya bai so a gane murna yake nunawa a fili yace ranar ma sai yayi rawa duk da Baffa ya Hana party yace suyi bikin da kidan a gida baya son taron nan.
Duk wani Shirin biki anyi shi Salma dangin uwa suna ta gyarata sosai ta Kara haske da kyau sai kamshi take,ana gobe biki aka mata lalle me kyau da gyaran gashi ita ba kawar data gayyata sai Hajara kawai,Hajara suna tare Amarya ta zuba tagumi Hajara tace wai mene ne haka ne ni wlh Banga abin so a wajen Baso ba da kika nace sai shi,mutumin da sai Shaye Shaye ya iya kullum ya Miki dukan tsiya ya zage ki tas zakunci iri iri mene abin so a Baso gashi kin samu yaro matashi kyakyawan gaske gasu masu kudi Kuma da Alama yana da hankali me kike nema.
Salma ta goge hawayenta tace aure kamar wasan Yara Hajara sabo da masu kudin su zasu yi mana komai ki duba yanda sati daya kacal aka sa bikina Kuma ni yanzu garin ya min nisa ya zanyi da Baso kullum Idan ban Ganshi ba bana jin Dadi,Hajara tace naga Alama baki San ciwon kanki ba Salma Allah ya Miki canji kina hauka,ni to yaro ne fa nawa yake,Hajara tace ke kika sani aure dai ba fashi gobe I yanzu kina gidan Mijinki,Salma tana ta kuka ita sai Baso Kuma baza ta cire shi a ranta ba,Ango kuwa ko a jikinsa mantawa ma yake da ita Idan ya aureta sai Idan yaga wata dai dai da shi irin kalar da yake so sai ya aura abinsa ya huta da su Mami,amma Idan suka bashi Omaira ta karfi zasu sa ya fara sonta ma yace baza a mallakeni ba ga yayarta nan ta mallake Nawwar daga taimako bada ni ba Autan Mami,yace su Aunty Rabi gadon soyayya suka yi sun iya love tunda ji yanda mamansu da Abbansu suka hadu sai soyayya, da sun aureka ka gama yawo soyayyar tsiya ce da su.
Bangaren gidan Baffa Yan uwa da abokan arziki sun zo,Aunty Rukayya da yaranta haka Binta ma da yaranta duk Yayan Iyamami ne basa zuwa sai da dalili sabo da Halin uwarsu Iyamami,Wise kuwa uwar Ango da ita Nawaf yake shawarar bikin,Umman Rabi,NazifaNazira sai Bilkisu sunzo bikin Hadi da ganin gidan auren yar uwar su daga baya Kuma su Omaira zasu zo hutu suma,Wise ma wasu sunzo bikin Auta a danginta,gida ya cika an gama Shiri Auta uban abokai kamar me ko Ina sune a gidan ana ta Dj Su Sultana Amare suma komai tsaf an shirya sun sha gyara,tun ana gobe suka Fara Dj a gidan.
Auta ne ya shugo Ina kallonsa a Palon Mami nayi dariya nace Angon gobe,Kallona yayi yace fadi ki Kara,su Bilkisu ma suna tsokanarsa,Duk inda Auta ya juya tsokanarsa akeyi,Nawwar ne ya shugo Shima Ido muka hada ya kashe min Ido daya Nima na kashe masa nawa,Auta yana kallo yace Allah ya kyauta,Autan Mami Ango Dan banza wallahi sai munga rukonka ya za a Kare cewar Star da shigowarta kenan,kowa yace Auta kaza kaza ana ta dariya,Kasa kasa yace da Wise Mama karama an goge min kayan angwancin nawa? Wise itama kasa kasa tace tun yaushe yace karku min dariya wlh kwaila ce matar itama,nayi gudun gara na afka zago,muka dinga dariya muka ce ai kowa zai gani da idonsa,Seraline ta furta ka shiga uku duk karyar Ina ta Kare gaskiya Auta ka fado,yace ya na iya da kaddara danya ce to ta dai fara alamun bura zata Dan fara nuna kadan,Auta yana ta bamu dariya har shewa muke,Wise tace na siya maka man power Auta,Auta da sauri yace Natural.... Natural... Mama karama ni Natural ne ba sauki,Muka dinga dariya, Nace Auta ya kaga shaddojin? Yace sunyi Aunty ai kin iya zabe akwati guda kika min fa na kayan angwanci nima kin hada min lefe tnx,nace Auta namu ai kadan ne ma,Wise kuwa takalma masu tsada ta siyawa Auta sun Kai set goma,ga su Star an siya masa agoguna da huluna na angwanci komai anyi,Part din Auta a cikin gidan aka canja masa komai da tsari 3 bedroom ne sama 2rooms kasa bedroom Daya,Palo kitchen komai an zuba an kashewa Auta kudi sosai,Mami tace guiding danta zata yi sai ta ga kalar zaman nasu, amma sai take ganin kamar Auta yana boye mata wani abu.
Washe gari daurin Aure Auta wanka yaci ubansa ranar Shaddarsa fara Kal komai fari tas har hular ya sheka kyau yana zuba kamshi,babbar rigar ma ta matasa Yan gayu cass da shi,wasu ma a can jigawa suka kwana wasu Kuma a jirgi suka tafi can Jigawa a gidan Iyaye na gado cikin dangin Salma a nan aka cika aka daura Auren Salma da Nawaf akan Sadaki dubu dari uku,ana daurawa Auta sai murna kamar yana son matar ma haka yake murna,
Baso Kuma ana daurawa yaja Nawaf gefe yace Alhmdllh saura kudina Nawaf ya masa transfer kudinsa Million Daya chas sai murna Baso yake.
A lokacin dangin Salma suka tattara kayanta da lefenta da abubuwan bukata aka hada Salma da mata uku wanda zasu rakata can kudu gidan mijinta,Salma kuka take kamar ranta zai fita ita duk abinda ya dameta Baso ne,zata Daina ganinsa,shi kuwa Baso kiransa akayi a matsayinsa na uban ya Wanda ke rike da Salma akace ya mata nasiha,ya Kalli Salma dake uban kuka cikin lafaya me kyau da tsada,tana kamshi tana kuka,Baso yace kiyi hakuri Dan kutmar....ya duro mata ashar su kadai ne a daki yace ki min shuru ko na farfasa Miki baki,Kuma na fada Miki wallahi kiyi abinda nace kiyi abinda ya dace Idan ba haka ba sai na kusa kashe ki,na rigada na aurar dake ki nutsu ba a wasa da aure karki masa ae yane ko baki gane bane,Nawaf abokina ne yanzu Ina sonsa wallahi karki sake naji an kawo min kararki sai na sassaba Miki kamanni,saura Yazo yace ki Dan buda masa kika ki yarda sai naci ubanki shegiya me suffar aljanu ki min shuru munafuka,Salma tana goge hawaye Umarnin Baso kamar Umarnin Allah haka take jin maganar Baso sabo da so,yace kar naji kar na gani fito na rakaki mota,Ango yana bayan mota a zaune suna jiran Amarya zasu wuce Airport
Kwayar Baso ce ta motsa yace da matan da zasu raka Amarya Dan uwar kowacce gyatuma ta koma gidan mijinta uban waye ya rike min ita Idan bani ba to baku da amfani sai ranar aure sanda muke wahala akwai Wanda ya taba zuwa gidanmu ya tambaya Yaya muke ci muna koshi wanne Hali muke ciki Babu,sabo da bani da kudi ko gidanmu bakwa zuwa ziyara sai Idan mu munga dama mu neme ku,yanzu na aurar da ita lafiya mun rabu lafiya Kun kwaso tsofaffin kafafunki zaku tafi kaita gidan Miji uban me kuka taba taimaka mana,to ba shegiyar da zata Kai min kanwa gidan Miji ni zan kai abata da kaina na damkata Amana,Anji jirgi an taho za aci baza naga shegiyar da na gani a jikin motar nan,ya juye ya Kalli Salma yace ke shiga muje,Salma ita murna take da farin ciki Baso zai kaita har can ko banza ta dinga kallonsa taji Dadi, daga Baso sai Amarya sai Ango da wasu tsirarin abokai tunda har Baffa duk an koma ana daura Auren Sultana da Nasira suma akan Sadaki dubu dari biyu biyu,ana ta shagali ana ci ana sha ga Selfie ana yi ga kida na tashi munyi rawa har mun gode Allah.
Baso da Salma a jirgi har garin aka kawo motoci aka dauki Amarya da Basonta ita kadai Ango yana motar Afif suka nufi gida wajen Mami,suna shiga kida na tashi duk angwayen su Sultana anyi hotuna sun tafi, Abokan Auta suna jiransa ga Motar Amarya a baya,suka shugo bayan anyi parking Auta ya fito da zugar abokai duk suka taho ga Kida na tashi ana Dj Auta ba kunya ya shige ciki ya dinga cashewa muna ta masa liki ana dariya,Baso ne ya fito da Amarya Shima ya shige cikin filin rawar yace a kashe,aka kashe kidan kuwa, yace bani kidan Na aurarta lafiya na huta da kaya,Dj da mutane aka dinga dariya ana tambaya waye haka akace ai shine ya kawo Amarya shi ya riketa,Kowa mamaki a haka ma Dan baiyi Shaye Shaye bane sosai,Baso yace ku sa min Kidan na jefar da kwallon Mangoro na huta da kuda,akace Shima Babu yace to wai sai Uban me Allah ya gani dama ba a so na taka,Nawaf ne ya jashi gefe yace zaka bata deal za ace ba tarbiyya please,yace chansa dai chansa dai na hakura ko Dan kudina su tsira,Wise ce ta budewa Salma mota ta fito da ita tana guda ga Amarya ga Amarya.