Showing 72001 words to 75000 words out of 152911 words
harara ya zubawa Nawwar ya shige motarsa ya wuce,dariya ta kama Nawwar yace duk yanda akayi Amarya ta hana Auta kanta haka ya kwana Babu komai, haka nema ya furta tare da shiga bangaren Mami.
Mami tace Kai Kuma lafiya kake dariya Kai kadai yace ni da Auta ne kinga uwar hararar da ya min ya tafi fa school,Mami tace so soon haka har ya tafi? Yace ae Kuma yana fushi,tsokanarsa kayi maybe,Nawwar yayi dariya yace Anya kuwa Auta yana son yarinyar nan Mami,Mami tace Nima Ina ganin da wani abu kawai bazai fada bane sabo da Auta da aure amma ace gidan ma sai da na tasa keyarsa gaba yaje,Nawwar yace Allah? tace ae fa abin da mamaki wlh Kuma shi ya zabo abarsa bare ace mun takura masa,Nawwar yace lallaba shi zakiyi ya fada Miki ke Zaki iya jure iskancin Auta, kyale shi Idan haka yaci gaba da faruwa zan gane ai,Nawwar yace shi yasa na fada muku Auta ba wani hankali gare shi ba girman ne kawai kuka ki ji,da masifa Mami tace to munyi masa din kaji min yaro ka fa damu Autana,ai shi baya laifi dama,ae naji Dalla tashi ka tafi ni,Nawwar yace yau bazanje aiki ba fa Kuma Rabia na Kai Unguwa bata nan,Ina taje? Gidan Seraline wai zata yini a can,Salma tana gama karyawa ta wanke kwanikan ta yafa mayafinta ta taho part din Mami ko ta samu saukin tunanin Baso a ranta.
A hankali tayi sallama ta shugo ciki Nawwar ta gani taga suna kama da Auta tasan shine yayansa harda jin kunyar Yaya,a gaban Nawwar ta durkusa tace Yaya Ina kwana,ya amsa tace Ina Auntyn fa? Yace taje unguwa kuna lafiya? tace lafiya Alhmdllh, gaban Mami ta koma ta sake durkusawa tace Mami ga kwanikan Ina za a ajiye? Mami tana sani tace ya tashi kuwa? tace ae ya tashi,Nawwar yace wai wa? Salma tace me can wajen take nufi fa,Nawwar da hannaye ya dafe bakinsa dariya zata kamashi wai Auta ne me Can wajen sai kace tsohuwa ita baza ta fadi sunan Miji ba Babu kyau wai,dariyarsa ya boye yace ai ya tafi school tace ae,yace a gaishe ki Mami cewar Salma,Mami tace wa fa? tace shi din,Nawwar jaridarsa ya dauka tare da rufe fuskarsa yana dariya a boye,Doguwar kujera ta samu ta kwanta a kai sai bacci, Ya kwashe ta ta dinga bacci sai gani suka yi tana ta uban bacci sai da azahar tayi sannan ta tashi lokacin Nawwar har yaje masallaci ya dawo tana yin Sallah ta Kuma kwanciya a saman Sallaya sai bacci,Nawwar suna ta jira da Mami suna kallonta ta dunkule waje daya tana ta uban bacci,sai ga Auta ya shugo da Sallama ya ganta tana bacci,Mami ta kalle shi tace Yan Makaranta,yace Naam na dawo ya mikawa Nawwar hannu suka gaisa,ya nemi waje ya zauna yana satar kallon Salma yana Galla mata harara Mami tana kallonsa duk abinda yake Nawwar tayiwa signa da Ido Auta harda turo baki yana kallonta yana auna mata zagi a hankali,Nawwar da Mami suna ta masa dariya a boye har Salma ta Farka tana tashi taga Auta itama Ido ta faka ta zabga masa harara har da ce masa Yan Yan Yan kasa kasa a boye,ta murguda masa baki tayi fari ta masa wani up and Down,Mami suna ganin komai ga Auta ya nuna kamar baida hadi da Salma itama haka ba ruwan wani da wani,ganin Mami zata gane su sai Salma tace sannu da zuwa,Nawwar yace lallai yarinyar nan ta iya munafurci ta gama hararsa,Auta yayi murmushin dole sannan yace tashi mu tafi oya come come let's go,ta mike tace Yaya ka gaida Aunty yace to,Auta harda sakalo hannunsa ta wuyanta suna fitowa ya hankadeta saura kadan ta fadi,ta juyo a fusace tazo ta hankade Auta da karfi ta wuce tana tsaki.
Mami kuwa tace ka gani ko ji yanda suke harar juna,Nawwar baki ya tabe yace matsalarsu ce ki kyale su kawai.
Salma kitchen ta shiga ta dakko juice zata sha Auta yace mayunwaciya look at you kinga banza ta fadi kin wani dakkowa mutane lemo ya fisge ya Maida kitchen,tace ai Kai Kam baka gaji iyayenka ba wlh marowaci akan lemo kalleni tsaf na maka kama da yar yunwa,Kai kana da kudin siya ne? Ba su Mami bane suka zuba maka komai ba ina kaga kudin ko zaka iya siye ne? baza ka iya siyan ko tissue da kudinka ba komai sai an maka Kai tafi can Kuma lemo ne sai na sha sai dai ka mutu,ta Koma kitchen ta dakko, sai ga abincin Mami an kawo musu ,tace nikam na shiga uku komai sai anyiwa me gida bashi da ko taro,Auta ya tsaya kawai yana kallonta sabo da ta buwaye shi ta rainashi da yawa, ta jawo abincin tace mutum komai sai dai ayi masa na zama matar ladan Noma,flask din ya fisge yace ai ba daga gidanku aka kawo ba,hannu tasa itama zata fisge ya rike gam ta kama hannunsa ta gartsa masa cizo,Kara ya saki ya saki flask din ta kwace tace sai na ci to Dan bakin ciki sai dai ya mutu,Auta yana yarfe hannu yace hungry girl mayuwanciya ko kunya bakya ji,tun Ina yarinya na siyar da kunyata ni Kuma a gidana ba Wanda ya Isa ya hana ni cin abinda nake so gidana ne dole inyi abinda nake so yawwa ehe sai dai ka mutu,Auta ya rasa ma me zai ce sabo da haushi yace na tsaneki,Nima haka ta furta tana cin fried rice dinta da kaza tana wani zukar kemo harda wani Jan lemon yana Kara zuuuu zuut tashi daya ta shanye karamin kwalin guda tace Dan jeka kitchen ka dakko min wani,yace baki da kunya ya juya haura sama,sai da yayi wanka ya shirya cikin kana nan kaya marasa nauyi ya fito yana zuwa ya samu taci iya nata ta kwashe komai ta maidawa Mami sauran,tace ya naga kadan aka ci? tace yace ya koshi shi yaci a waje,Mami tace Autan? tace ae yace yaci a school,shike nan cewar Mami ta juya ta tafi ta iske Auta a zauna yana latsa waya yace Ina abincin? Na mayarwa masu shi tunda Kai komai sai dai ayi maka baka San ka nemi na kanka ba,Auta baki Bude yake kallonta yace Amma dai wiwin Baso ta taba Miki kwakwalwa kema? Karka dameni bani da lokacinka,kwafa Auta ya ja ya fita tace yaro karami kusan sa'ana sai Iyayi da nawa ya girmeni ta gyara zama tare da harde kafafu tana cewa wahala ma sai ta sa ka sakeni na koma wajen baso na.
Auta bai je wajen Mami ba tunda ta Riga ta fadawa Mami ya koshi sai ya shiga wajen Wise yace wai abinda baya so aka dafa taliya,Wise ta zuba masa abincin ya ci ya koshi yayi tafiyarsa ya bar gidan gaba daya.
Bacci taci ta koshi, kamar taci kafar Kare haka yamma nayi tayi wanka ta shirya cikin shadda ta tafi bangaren Wise suna ta Hira tana rage tunani.
Washe gari ma haka suka yini fada da Auta ba ji ba gani,har suka kwashe sati biyu a haka fada baya karewa, basa Shiri Sam ganin haka Mami tana fahimta taji tsoro tunda Yara ne kar azo ayi saki, Auta ta samu Yazo gaisheta,tace fada min uban abinda kake boyewa wallahi ko na fita harkarka,yace me kuma Mami? Karka raina min hankali nifa na haifeka nafika sanin waye Kai wallahi Idan baka fada min dalilinka na auren wacce baka so ba to ba ruwana da Kai Karka sake zuwa inda nake,Auta badan ya so ba kawai yace kiyi hakuri Mami ya bata labarin Salma kaf ya fadi gaskiya,Mami tace Auta baka da hankali ashe,Matar da bata sonka kasan kuwa kiyayyar mace Idan ba ta son mutum,me ya kaika wani biyan kudi ka aureta bayan kasan wani take so,Auta yayi mukus Mami ta dinga zazzaga fada,yace Idan kin yarda nan gaba ai zan rabu da ita ma,shut up zaka Raina mana hankali mu ai wasa muka maka ba cewa mukayi zamu yi maka auren dole ba shine ai gashi Kai ka yiwa kanka auren dole Mafi Muni ma,wacce zuciyarta wani take so,to ko da wasa ba saki kayiwa kanka wlh baka Isa ka sake ta ba sai kuyi ta zama a haka matsalarka ce,Mami taji zafin Salma bata son danta dama,amma Kuma Auta shi ya jawa kansa.
Zuwa Mami tayi tace Salma ta dawo part dinta kawai aka kwaso kayan Salma na sawa aka bata dakinta a kasan Mami,Shima Auta ya dawo part din Mami da dakinsa,Mami tace kowa yayi harkarsa muga abinda Allah zaiyi.
Salma kawai sai ta mike kafa kamar gidan ubanta a gaban Mami ma fada suke yi da Auta.
Yau Auta yana zaune Mami tana gefensa tana Yanke masa farcen hannu, Salma ta biyo ta saitin kafarsa tayi fatali da kafar Auta,Mami ta kalleta kawai harda shagwaba kamar uwarta ce Mami tace a canja min channel,Auta yace wai gidan ku ne kin fa ishe mu kina gani Mami ta min ball da kafa Autanki guda kisa ta bani hakuri,Mami tace ke Salma ki Daina haka Mijinki ne fa,Salma tana dire diren kafafu tace ni Allah Allah...shike nan sorry ta zauna ragwaf a kujera,Auta yace bata da kunya fa Mami shame on you ya furtawa Salma,tace na karbe hakuri na Dana baka nafi karfin na baka hakuri,yace ke Dalla kucaka,tace ai gwara ni kaifa kwaila da Kai zaka iya siyen tv ne ko tv Kana da kudinta ta fisge Remote din,Mami tana jinsu bata ce musu kala ba dariya ma take a ranta ana mata maganin Auta,haushi Auta yaji yace Mami kina jinta ko garin kwace hannunsa Mami ta Yanke shi kadan da razor Auta kamar Wanda aka kwadawa Adda ko wani takobi haka yake yana yarfe hannu,Mami tace Kai Kam Allah ya sawwake maka kamar ba Namiji ba,tissue ta sa tare da danne masa wajen,Salma tana masa dariya tace sai kace ba Namiji mu kayi mana shuru.
Yace Mami bani ruwa na sha ko na ji salama,Mami ta mike zata dakko masa ruwa Salma tace Mami da kanki kamar wannan ya aikeki ki zamanki ya tashi da Kansa ya sha ya dawo,ke da uwata Zaki rabani marar tarbiyya ya ja tsaki,Salma ta dauke Kai taci gaba da kallonta.
Salma Allah ya yita da gasa sabo da yarinta da kuruciya Idan taga kusan sa'anta yana abu sai ta fara yi itama,Auta ta Raina an mata kananan kaya sunfi akwati biyu sabo da su can normal ne ana sawa bare Kuma matar aure,ganin Auta kullum cikin kana nan kaya yake sai itama ta koma sawa su normal ne amma sabo da ita ba a can ta taso ba tana ganin ko mace ce ta shugo sai taje ta Sako katon Hijab,komai Auta yayi sai tace sai tayi itama,Idan Mami ta masa abu itama fa sai anyi mata,daga gani Mami ta taje masa gashi,sai bayan kwana biyu tazo gaban Mami ta durkusa har kasa tace Mami kin iya kitso ki min Nima? Mami tace na iya,tace kalaba nake so,tace to bari ayi Sallar la'asar tace to,ita Salma tana birge Mami sabo da biyayyar ta da kunya sannan ga addini Sallah bata wuce,Auta 4pm ya dawo daga school ya shigo ya dora Kansa a cinyar Mami sai ga Salma ta fito ta bata rai tace matsa min,ko kulata baiyi ba,tace Mami kice ya matsa min ai kitso za a min tsaki ya ja ya tashi ya koma daya kujerar kasa kasa tace kwailan Miji kawai tana turo baki,Mami dariya ta kamata haka yake cewa Mata ko wacce yace kwaila ce yau gashi an ramawa su Omaira cikin ruwan sanyi,ran Auta Idan yayi dubu to ya baci kamar zaiyi kuka zaiyi magana Mami tace enough haba Enough of this nonsense ku kullum fada ke Salma Mijinki ne fa kike masa, haka kikaga anayi akan banzan tunaninki,sabo da bakwa son juna ku zauna lafiya mana,bana son rashin kunya Salma Mijinki ne fa ke ana lallaba Miji ana masa biyayya ke Banda ke kowa haka kika ga yana yi,Kai ma ba ruwanka da ita kowa yayi harkarsa, Auta yace dama matsalar da nake gudu kenan da auren kwailar yarinya indai ka hada harka da kwaila to ka shiga uku yanzu babba me hankali wacce tasan me takeyi zata yi abinda wannan sharar takeyi wannan tarkacen,indai mace ta mallaki hankalinta Ina zaka ga wannan shirmen,Ya Isa haka kayi hakuri kuyi hakuri da juna shi yasa fa na dawo daku nan gabana wato ban Isa ba ko bani da amfani,Salma zama tayi a kasa a gaban Mami tace kiyi hakuri Dan Allah tana so tayi kuka,Mami ta cire mata dankwalin gashinta dogo baki yala yala da shi ya bayyana yana sheki Mami tace Masha Allah Auta ya tabe baki tare da dauke Kai,Ita Kuma Salma dama ta Saba da kuka a gida tunda kullum sai tayi ita da Baso,Basonta ta tuna ta fashe da kuka wai an mata fada sabo da samun waje,Auta a ransa yace dama talaka bai iya samun waje ba,yarinyar da kullum sai an jibgeta na tausaya mata na aureta yau na zama kamar sa'anta ba komai kaima Allah ya Kara maka da Omaira ka aura da duk ba haka ba gadon soyayya tsaki ya ja yace a fili Wanda baiji bari ba ai yaji hoho rubbish ya tashi ya fice.
Nawwar ne ya shigo ni da shi cikina ya tsufa sosai,Mami tace daga Ina haka? Nace asibiti muka je muka biyo,Salma tana ta kuka,Nawwar yace lafiya take kuka? Mami tace gata nan tambayeta ta fada muku da bakinta,Salma tana kuka da shesheka tace sh...sh..shine...Nawwar yace shine wa? Shi....nace waye shi? tana goge hawaye tace Me can wajen, na kwashe da dariya nace Auta? ta daga Kai tace shine yake tsokanata har gori yake min,Mami tayi salati tace Salma kiji tsoron Allah Auta ba abinda ya Miki yana zaune kika ce sai ya matsa Miki ke Zaki zauna kina masa rashin kunya,kiyi ta kukanki tunda ke baza a fada Miki gaskiya ba,Nawwar yace to kiyi shuru za a masa fada kinji,ta goge hawayenta tace to,Mami tace bari na dawo ta nufi kitchen sai ga Auta yayi wanka ya dawo cikin 3qtr da Riga me gajeren hannu, hannunsa daya a aljihunsa daya Kuma wayarsa a rike yana latsata.
Salma tana ganin shine ta mike tsaye taga ya nufi kujera ya zauna komawa tayi wajensa tana kallon kitchen kar Mami ta ganta tace tasar min ni nan wajen nake so a nan zan zauna,Auta iya kulewa ya kule amma ya shareta ya tashi ya koma dayar ya zauna Salma ta zauna tayi irin zaman Auta ta harde kafafu ta fito da vivo dinta tana dannawa itama,yana cin chewgum kawai ita ba chegum a bakinta ta fara tauna itama,ni da Nawwar muka zuba Ido muna kallo kamar Film,dariya kawai suke bamu,Auta yana da abin hannu a tsintsiyar hannunsa na Samari Salma ta gyara nata na mata, juyowa tayi Shima ya juyo suka hada Ido gwalo ta masa,Hannu ya Kai zai dauki Remote ta Riga shi daukewa tana sani ta Kai tashar cartoon,Auta ya zuba tagumi da hannu Daya ya ajiye wayar a gefe ji yake kamar ya lakada mata dukan tsiya.
Nawwar ne ya Kalli Auta suka hada Ido Nawwar yace Matata tafi ta kowa ya rike hannuna,yasan da shi yake sabo da status dinsa ranar da ya shiga dakin Amarya,tashi yayi a fusace ya shiga kitchen yace Mami ki wa Yaya Nawwar magana tun dazu ya zuga matarsa sai Kallona suke suna min dariya,Mami ce ta fito tace waye yake taba min Baby,Nawwar yace ba ruwanmu daga nace Matata tafi ta kowa,Auta yace wlh da ni yake ai na sani, Mami tace ku tashi ku bar mana gida ta Kori su Nawwar.
Mami tana shiga kitchen ya zo ya zubawa Salma rankwashi tare da furta marar tarbiyya yar Namiji,dama tunda Baso ne ya rike ki Ina Zaki hankali,oho maka dai .
Bayan kwanaki kadan Salma ganin Auta yana ta zuwa school sabo da kwaikwayo sai da taje gaida Baffa bayan sun gaisa tace Baffa dama alfarma nake nema,yace Ina jinki,Salma tace tunda na gama secondary Kuma result Dina yayi kyau Dan Allah ko yar college ce ka sani,Baffa murmushi yayi yace ki kawo min takardun naki ta dinga murna,dama ta taho da abinta,Mami ta samu itama ta fada mata,tace kinyi hankali Salma Kuma kin birgeni,taje ta dakko takardunta ta kaiwa Baffa Wanda ya kamata a nema aka Nemo mata aka mata registration a Makarantar da Auta yake zuwa bai ko sani ba sai da zata fara zuwa Baffa ya sanar masa,ransa ya baci akace Kuma tare zasu dinga tafiya su dawo,amma department din Salma daban ita microbiology tace tana so shi Kuma Business time table dinsu kusan lokaci Daya ne,har waya Mami ta siya mata me tsada Samsung.
Yau Monday da wuri ta shirya cikin Arabian gown peach tayi rolling ta sa jaka arsh da takalmi me Dan tufu Arsh, 9am suna da lecture har Auta,ta fito da wuri ta tsaya a jikin motarsa tana waya da Baso yana masifa karki dameni da Kira fa haba jiya kin kirani yau ma haka wanne naci ne wannan ya kashe wayarsa,Nan take idonta ya cika da hawaye sosai ta kasa cire Baso a ranta sabo da Baso take ta yiwa Auta rashin mutunci ko zai gaji ya sake ta ko ya koreta amma yaki,Auta ne ya fito cikin wankansa na farin jean rigarsa silver yayi kyau ya sa glass me kyau a fuskarsa,ganinsa da Glass Salma hankalinta ya tashi da Mami ta bata kudin Makaranta taki karba amma ganin glass din Auta ta koma ciki da gudu,Sai da Mami taji tsoro tana haki tace Mami bani kudin school din na tuna zanga abin ci, Mami murmushi tayi ta bata dubu Daya,ta fito da gudu,Auta har yayiwa motarsa key