Showing 102001 words to 105000 words out of 152911 words

Chapter 35 - Yar Aikin Karuwai 2

22 Oct 2024

4713

aurenki da sati daya ya warke,sunansa ma Engnr Alhaji Mukhtar Dan asalin Adamawa ne amma a Kano suke zaune,a hanyar kano zuwa Adamawa yayi hatsari ba Wanda ya sani a danginsa ya haukace haka har ya fada gari gari har Yazo layinmu a cikin Kano,Yan uwansa sunyi cigiyar duniya ba a Ganshi ba,an zaci sace shi aka yi,yana da matarsa da yaransa biyu,yace a gaishe ki ma yace a bashi number dinki Kuma watarana zaizo,shine ya bude min shago na gaske a Kasuwar Kwari,ya siya min gida na million goma,mota ma shi ya siya min ita da kika ganta sannan ya kaini gidansa can dake Abuja a can nayi sati uku,duk zuwan nan da nakeyi nan Ina Abuja,ya dorani a hanya ya dinga min fada da nasiha har Allah yasa na Daina Shan komai,naga Shaye Shaye baida amfani a rayuwa face ya haukata mutum ya lalace ya zama dan Iska,Kalli yanda na dawo mutum kuma dake me kudi ne sai naji fadansa da wani talaka ne ko gaskiya ce bazan bita ba sabo da bashi da abin bani, kai duniya amma haka ya dinga zare min Ido yana fada yana min masifa Baso naki Salma shuru ban iya cewa komai ba,da ya warke fa a kan titi sai da Yan unguwa matasa suka bashi labarin abinda nayi masa amma shi bai iya tuna komai ba,Matarsa da Yan uwansa baki gansu ba Salma sai kin wanke hannu kafin ki tabasu.
Yace Kuma abinda kika masa kema har gida zaizo da iyalansa da Yayansa da Kaninsa,Salma tace Masha Allah Yaya na maka murna,yace iceko kin saita halinki? tace ae wallahi,wallahi Allah Yaya na canja Karka sa a bani wani aikin,murmushi yayi yace ai bazan sa ba Salma,ban zaci zan shiryu da wuri ba sabo da kar na aureki na cutar dake shi yasa na bawa Auta ke badan kudinsa ba ni Kam haduwata dashi naji ya kwanta min a rai kawai shine dalilin da yasa na dage sai ya aureki, ba wai dan bana sonki ba Babu Wanda zai ce bai sonki,yanzu Yaya dama kana so na? ya furta na dai soki ba Ina sonki ba,ki gyara zancenki ya soki a da banda yanzu ya daina babu ya kare cewar Auta yana gefe kishi kamar ya kashe shi, Baso yaci gaba yanzu sai dai Yan uwantaka tunda ni a tunanina na cire rai da zan shiryu ma amma wani ikon Allah Ina aurar dake sai Mahaukacin ya warke ba dadewa kuma Allah ya shiryar dani ta sanadinsa,amma bayan na aurawa Auta ke na dawo gida Salma naci Dadi na more kudin da Auta ya bani akan zai aureki Million daya Banda sauran hidima da ya min iri iri,nace sai ya bani million daya zan bashi ke na siyar masa ke tunda kin san lokacin kwakwalwar bata nan ni iya tunanina siyar dake nayi,Auta yace ai dan Adam yatsansa daya ma ko duk abinda ke duniya za a hada baza a iya siyansa ba sabo da Babu me yin wannan abin sai Allah,yace shi dai ba siyenki yayi ba aurenki yayi kudi kawai ya bani ne,bayan Kuma naci kudin nan a cikina nida mahaukacin nan nazo na dinga tunaninki kamar zanyi hauka duk karfin zuciyata sai da nayi kuka duk kayan gidan nan sai da na farfasa komai na gidan ba abinda na bari,har gado sai da babbala su,na fara cuta kamar zan mutu da kyar Allah ya taimakeni Kuma ban dawo nace Auta ya bani ke ba na Riga na aura masa tsakanina da Allah,na sawa zuciyata ko mene Dan Adam ya rasa to ya hakura ya barwa Allah tunda nayi tsakani da Allah Kuma Allah yasan dan shi nayi to nasan zai min canjin Alkhairi inshallah, haka Allah yaso dama,dama Yaya baka yi auren ba? Ba Aure nayi ba ni kawai Dan ki cireni a ranki na samo kanwar Saminu abokina Sayyada ai kin Santa to Sayyada ce ta Miki magana a waya ba Matata ba,ni kin san ban taba kula mace da sunan so ba kawai dai barni da Shaye Shaye na Kuma yanzu Alhmdllh ko taba sigari karya take ta sake shiga bakina Wanda ya kirkireta ma ubansa,ubansa ma ubansa,muka yi dariya muna jin Baso abin alkhairinsa ya taba mana zuciya, Auta ma yayi dariya wannan zagin ai sai Wanda ya taba Shaye shayen,Salma tace Yaya Allah ya baka ta gari,yace kin hakura da Baso kenan? Salma tace uhm Auta yace kiyi magana sai ki zauna gulma,Salma da karfi tace aeeeeeee....na hakura ni Kam tuni ni zan iya tayashi zaben mata ma,Baso yace ni na gani ma da idona wata ce me hankali ta nutsuwa a jikin bango,Baffa da Mami suka yiwa Baso godiya sosai suka ce gaskiya Idan kaga mutum a wani Hali Karka zage shi ko ka tsane shi,Baso yace Almajiranta ce ta jawo min nima Wanda sai kayi bara zaka ci ka koshi yunwa ba abinda bata sawa,wahala ba wacce Almajirai basa sha a duniya dole su dinga lalacewa a maimakon Karatu,a addini ba inda akace sai ka tura yaro Almajiranta sannan zai samu ilimi ,Iyaye mussamman na kauyuka wasu yaran marayu ne,wasu basu da Uwa sai matar Uba,wani Yan uwa ne zasu kasa rike shi su turashi Almajiranta da sunan Karatu gasu nan dai Wanda sai dai Idan ba Allah ne ya tsare ba duk kusan lalacewa suke musamman na yanzu in Banda siyan waya da jin wake wake ba abinda suka iya,Blue films a wayar Almajirai baza su irgu ba Yara kanana,su kunna kida suna yawo da speakers suna chashewa rawa iri iri,Shaye Shaye,sata, iskanci iri iri akan kawai a rike yaro a gida a bashi ilimi da tarbiyya baza a iya ba duk islmiyyoyi da makarantun allo na gida da sauran makarantun dare duk basu Isa mutane su Kai yaransu ba sai dai a dinga tura Yara bara wannan zubar da kimar addini ce,Baso baya jin hanya shi Kam ko tsoro ya mike yace tafiya zaiyi daga Abuja yake ya biyo ta nan sabo da yaji ya ake ciki.

Su Mami suka yi suka yi ya kwana yace shi sai dai ya kwana a hanya suka masa Allah ya tsare,muka koma wajen kida,Nawwar yace to ko wa ya gani yake so Auta Idan ka raka shi kaji,yace ae zanga wace me hankalin nan suka fito suna hira da Baso sai Star ta wuce yace yawwa gata nan ita na gani,Auta ya dinga kyalkyala dariya harda rike ciki yace wannan tana da aure baka ga cikinta ba karami Kai baka gane ba,Baso Bai San Star rawa tayi taji Dan cikinta yana juya ta fita ta tsaya a jikin bango ta makale ta nutsu ta koma Yar kallo wai a haka shine yace nutsatsiya ce,Auta ya nuna masa Omaira dake tsaye a gefen Cele yace na zaci waccen ma ka gani,Baso yace naga kamar zata yi wulakanci ni Kuma ban son yanga da Iyayi yaran nan,Auta yace Allah tana da hankali ka aureta, Baso yace ba ruwana waccen matar manya ce Idan mutum zaiyi aure an Fi so ya auri dai dai shi amma Idan ka auri mace take ganin kamar alfarma ta maka to ka shiga uku ni ba yaro bane irinka,Auta ya dinga cusa masa Omaira Baso yace Kai rabu da ni da fetsararrun yaran nan,Auta yace inshallah sai ka aureta wallahi Kun dace itama a chake take Baso Hamra ya gani yace ga wata me kama da Kai can,yace Yaya ta ce yace ahh to wannan ma tayi amma waccen da ganinta Omaira kace ko to baza tayi mutunci ba,Auta yace Hamra yayata ai tana da Mijin aure itama ta kusa aure,Baso yace to bani da sa'a a gidan nan amma waccen omaira Idan na kalleta ma nasan ba sauki, yace bada ni ba ya bude mota ya shiga yace Allah ya hada kowa da rabonsa ba ruwana,Auta yace to shike nan tunda Kaki Omaira ta shiga uku tayi bakin jini,Wanda ma take so an hanashi aurenta,Baso har yaja mota ya tsaya ya Kira Salma tazo ya bata kudi dubu ashirin yace gashi nan Idan kina son wani abu ki fada min a waya zan tura miki,Salma tace to Yaya na gode ka gaida gida Allah ya tsare,yaushe Yan uwanmu zasu zo? Yace sai kin haihu,tace Allah ya kiyaye hanya yace Ameen.

Cele zobonta ta hada tasa a fridge,wuraren Nagriba duk kowa ya tafi gida sai iya su Cele da yan gidan kawai Yan aiki sun gyara ko Ina dake bai baci ba tunda ba wani taro akayi me yawa ba,ni me jego wanka nayi dake an gyara ko Ina gadona cike yake da gift na jariri Jakata ta cika da kudi gasu nan dai kyaututtuka daban daban gasu nan,Jaririn Cele tazo ta dauka nace wallahi bani abina,wanka zan masa ko ya huta nace bana so ki karya min yaro bada ni ba,fushi tayi ta bani abina,nace zo ki kwashe kudin nan ki gyara bed din Nawwar zai zo mu gaisa,Cele tace baza a gyara ba ta fice,nayi dariya na Kira Omaira nace gyara gadon nan ki kwashe kayan ki zuba a can ma'adanar kaya inda Babu kaya a ciki duk ki shiryasu a ciki,Omaira tace Aunty nima Allah ya bani Miji na gari nayi aure na huta,Na kalleta nace Ameen Omaira kema auren kike so kenan? tace ae wlh Aunty kina ganin Salma sai cikinku take shiga mu ana korar mu, Cele fa cewa tayi idan na shigar muku rawa sai taci ubana Ina son rawar na hakura sabo da nasan halinta,kiyi hakuri to ku dinga hakuri da Cele, Omaira tace jaraba ai gara ma tayi auren ta tafi mu huta,bari tazo na fada mata,Omaira ta hau magiya kar na fadawa Cele,nace to Allah kika Kara gulmarta sai na fada mata.
Shiryawa nayi cikin kayan baccinta Riga me siririn hannu da dogon wando blue da su,Mami ce tazo ta dauki yaron ta masa wanka ta kawo shi na shirya shi tsaf da pampers dinsa,nono na bashi ya sha duk yasha wahala sai bacci na kwantar da shi,Omaira duk suka tafi masaukinsu sun gaji suma Banda Cele tare muke kwana da ita,Mami ma tana part din Baffa. Nawwar sai waya ya min yace yana gida shi bacci yake ji da safe zaizo nace Allah ya kaimu yace ki gaida min Baby na,nace zai ji.

Cele ta hada zobonta tsaf ta fita ta samowa Ahsan take away yace ya shugo garin shi yasa ta samo masa kalar abincinsu da suka Saba ko zai iya ci, nace ta kaishi part din da Auta yake ta sa an Kara gyara ko Ina amma sabo da ta shiryawa Auta da Salma mugunta sai tace Salma Dan Allah muje can room din ki kwana a wajen Auta Ahsan zaizo sai mu dauki daya bedroom din Kuma ku dauki daya kunga shike nan bana so naje ni kadai kar yace zaiyi min wani abu nafi so sai an kaini dakinsa kinga Idan yasan a gidan wasu yake dole ya hakura,Salma tace to,Cele tace yawwa tayani Kai abincin can,Salma ta tayata komai suka gama shiryawa a bedroom din da Ahsan zai kwana,suka dawo part din Mami Cele ta shiga kitchen ragowar zobon ta tsiyayi nata me kyau ragowar ta zuba masa maganin sha'awa kadan yanda Mandula tace bata wuce ka'ida ba,ai kuwa Salma ta dakko nata a glass cup ta kurba sau uku sai na Salma yafi nata yawa tazo ta zauna a Palo ta kwalawa Salma Kira zo,Salma tazo tace ga zobo ki shi Salma tace na gode ta dauka tana faman chat da Auta suna soyayya,Zobo na Hannun Salma bata sha ba,Cele tana sha Ahsan ya kirata akan ta fada musu gidan Ina yake, sabo da tasan nata yafi kadan sai ta mike ta ajiye a saman center table ta tafi wajena na fada mata address na gidan,bata San Salma da kwaikwayo ba,ita Salma tunaninta na Cele yafi dadi sabo da haka ita nata zata sha,Cele tana tashi Salma ta shiga kitchen ta rage nata a sink kadan ya zama Kai Daya Dana Cele sai ta fito ta canja kofi tace naki zansha Nima watakil yafi dadi ta ajiyewa Cele nata ta dauke na Cele ta shanye tas,Cele tana dawowa ta gama waya murna ta kamata Salma ta sha masifa, taje kitchen ta dakko ragowar me maganin a glass cup tace ki kaiwa Auta Shima yasha,Salma tace kamar kin sani bana so naci Abu bai ci ba ta mike tana murna ta fita,Cele tace Yar banza taki ta Kare ta dauke zobon Salma ta shanye tas a cikinta,Salma ta taho da cup zata kaiwa Auta sai Auta yace ya fita Nawwar ya aike shi,ta juyo zata koma sai zobo ya subuce ya fadi cup din ya tarwatse,Salma tazo ta share glass din ta kwara ruwa a wajen yabi ruwa tace kar mutum ya maka kyauta ka kifar aga kamar wulakanci ne gwara nace mata ya sha,Salma ta koma tace Aunty ya sha baki ji yanda yaji dadinsa ba an gode sosai,Cele taji Dadi tace ba komai ai an zama Daya ta mike ta koma dakin Miracle.
Tana shigowa nace Cele shirya kudin nan mu irga Cele ta zauna a kasa ta baje kudi tana irgawa Salma tana tayata sabo da tana jiran Auta ya dawo,Can Cele sai muka ga tana motsa cinya,tace wash...taci gaba da irga kudi,,gashinta ta Sosa,sai ta cire dankwali ta ajiye gefe,ta tale kafa ta tsuke bata magana irgan kudin ma ta kasa,dubu ashirin,ashirin da Daya,da gudu,sittin,tsaki ta ja ta dawo baya da irga daya,biyu,uku, takwas sai taja tsaki ta dawo baya, na kalleta duk ta rasa sukuni ta hada zufa sosai,nace Cele kalau kuwa? Cele tace Ina fa lafiya, Salma ajiye kudin nan ki Dan bamu waje,Salma ta ajiye kudi ta fita,Cele tace yarinyar nan na sawa maganin sha'awa a zobo sabo da Auta yayi maganinta amma kinga zobon Dana bata daban Wanda na sha daban amma ita gata lafiya ni Kuma yanzu wallahi Sha'awa nake ji ta bala'i,da Ahsan dinma zai zo shike nan, Rabin kauye yau zan iya yiwa mutum fyade,Nace kin tashi da kika bata lemon? Ae da ya kirani na kawo miki waya kin masa kwatancen,nace kinga kaikayi koma kan mashekiya Kai Cele da mugunta kike ashe Yara Zaki cuta ki sawa mutum maganin sha'awa Idan yayiwa yarinya Illa fa lallai Cele baki San Antena da azababa a farko wallahi da baki sawa yarinya karama irin Salma ba Kuma wai kika sake bata ta kaiwa Auta Kuma tace Auta ya sha lallai to Allah ya Ceci Salma kuma dan baki San Salma bane shegen rashin ji ne da ita da kwaikwayon tsiya yanzu haka naki ta gani kin sha tace itama shi zata sha ai haka take da kwaikwayo Idan wani yayi Abu tace zata yi saukinta ma bata kwaikwayon Halin banza sai na shirme ko gayu ko abinci ko wani abu dai na shiririta shi take kwaikwayo wlh ko raba Daya biyu karki yi naki ta gani ta shanye,Cele tace wash ta baje ta kwanta a kasa ku kunna min ac,idon Cele yayi kwal kwal kamar zata yi kuka,murya a sanyaye tace ni ki koya min soyayya ki Daina damuna da Surutu wlh yau abin kunya zanyi a nan gidan zanyi first night,Naci dariya nace wayyo Allah Cele zata mutu Ahsan maza ka karaso,Cele ta Miko min wayarta tace ungo Idan ya Kira ki daga Shima da shegen iyayinsa yaki ya karaso tun dazu a Ina ya tsaya ne oho,nace Cele tashi na koya Miki love,Cele ta mike zaune tana fifita local government da hannu tace inda kisan nayi Zigidir Rabi,Allah wadaran Halin su Star Yan bariki banza Yan barikin wofi ai sai su fada min Illarsa mugayen banza shegiyar Mandula tana tafiya kamar tsohon kunkuru duk sai naci ubansu daya bayan daya,Allah ya tsine musu mutanen banza mutanen wofi,dariya nake Cele tace harda ke Yan iska kwartaye ba abinda kuka iya sai iskanci,waccen kinibabbiyar Star harda da wani cewa suna sha ita da Abhulkhairi,Ita Kuma Wise tana make murya yana da kyau ai hakane kyan maganin ya Isa wlh in aka Saba akwai dadi sai ayi ta soyewa shegiyar murya kamar ta tsakuwa,ita Kuma Sera ko ba maganin nan ba ai Sabeer yana matukar sonsa,Yar Zabil nawa mijin dake yare ne ai bama free da shi, shegiya da murya kamar ta Devido,Kwartayayen banza wannan Mandula ta Daina ciniki daga yau Babu me sake siya zata gani,dauke biro da takarda ki zana local government din nan da Antena ki bani hadda bazan iya ba yau wlh abin kunya zanyi,mikewa Cele tayi tana Jan skert tana karkada skert dinta da hannu,sai da naji tausayinta yanda ta rasa sukuni nace da haka kike so Salma tayi? Cele tace wlh ko ba yau ba sai na bawa yarinyar tunda jifa ya fada kaina ya fada kan uban kowa wallah kika sake kema sai kinyi wani cikin kafin arba'in gwara ki kyaleni Idan Zaki koya min ki koya min,Mami tsaf zan iya bata ta sha Baffa ya kwashi gara,muka yi dariya tace to tsofaffin sai soyayyar tsiya wai harda ce mata honey a gaban mutane ku da suruka duk Yan bariki.

Nace to ni yanzu Cele me zan koya Miki? Uwarki Zaki koya min Idan iskanci ne ai Kun iya ,Nayi dariya nace Ahsan ne zai koya Miki Nima mijina ne ya koya min,ko me kika ga yanayi kawai ki masa,inda kika taba kika ga yaji Dadi shi Zaki yi har ku Saba,Cele tace to da biyayya, ta shiga wanka tace bari na shirya kafin Yazo naci dariya kamar me,na Kira Star na bata labarin ta tab reshe Ya juye da mujiya ta dinga dariya Nace yau kuna ta Shan zagi tace ai gobe zamu zo gashi rai fess wlh ko a jikina,Cele tayi wanka ta fito na bata Yan magungunan mata na niima da sauransu na hada mata da Madara ta shanye kuwa ta shirya ta zaro sabuwar rigar baccinta gantalalliyar rigar bacci me kyau dark green ta Saka na

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login