Showing 69001 words to 72000 words out of 152911 words
Kawai Baso mahaukacin ba Wanda ya bawa Amarya ba danginsu ya sulale ya fece,sai Nawaf yayiwa waya shi tuni ma fa yana hanya yabi mota,Nawaf yace to ya sake tura masa dubu talatin ya Kara kudin mota,Baso yayi ta godiya ya koma gidansa yana murna daga shi sai mahaukaci
Washe gari dare na yi Baso ya siyo manyan gasassun kaji da yogurt guda biyu ya bawa Mahaukacin guda da Madara shi ya dauki tasa yana ci yana cewa Alhmdllh na huta da jaraba haba ai na samu na Wala yarinya ta gallabeni da kyar na samu me siyanta sai shegen bakin jini.
Salma kuwa bayan Baso ya fece bata sani ba tana tsaye tana Shan kallon fitsarru muna ta rawa Auta rawa yake kamar me,Salma ta kalle shi tare da tabe baki tace kalle shi kamar Dan Iska aikin banza.
Zuwa dare aka Kai su Sultana Wise da Salma ta dinga tafiya sabo da taga bata da dangi,Mami ta dinga fada me yasa za mu dauki Amarya daga kawota mu tafi da ita Kai wasu Amaren,hakuri muka bayar.
Ranar Salma bata ga Ango ba Shima bai ganta ba a bangarenta suka kwana tare da Hamra,Sabreen da Iyamami sama sama suka yi bikin su ba ruwansu irin suna jin haushin su Mami,Iyamami Kuma wai an bari Auta ma ya auro musu bare ba yar dangi ba,gashi tana jin tsoron Auta wajensa ma baza ta je ba basa Shiri ko kadan gashi bashi da kunya wanke ta yake sol.
Yau duk Wanda Yazo biki na kusa da na nesa duk sun tafi sai iya Yan gidan,Hamra ita tasa masu aiki suka gyara part din Auta tsaf ko Ina yana kamshi ta hana Salma yin aiki ganin ta sawa kanta damuwa tunaninsu alhinin rabuwa da gida ne.
Mami har can taje tayi mata nasiha sosai karshe tace ki dauke mu Iyayenki Dan Allah ba babanci kuyi hakuri da juna aure sai hakuri,Idan ya Miki laifi kizo ki fada min kinji,Salma taji sanyi ko ba komai iyayen Nawaf mutanen kirki ne har mamakinsu take gasu masu kudi amma ba wulakanci,tana mugun son Wise da ni Rabi da su Star sabo da ta ganmu Yan harka ne har wasa muke mata muna tsokanarta.
Mami zata fice Salma tace ina matar Yayan me gidan nan? Mami tace waye megidan nan a kunyace ta kama Salma tana kasa da Kai tace Auta,Mami dariya tayi wai Auta ne ya zama me gida yanzu ta sake yin dariya tace tana gidanta,au ba a nan gidan take ba? Mami tace ae mana ku ma nan gaba zaku koma gidanku Idan an gama ginawa,Salma tace ina sonta wallahi ita da kawayenta da Wise take suna da kirki,Mami tace Wise Kanin Baffa take aure a takaice ta Dan bata labarin su,tace yanzu dama su Aunty Sultana sun girmi Me gidan nan,dariya ta sake kama Mami Idan tace wa Auta me gidan nan wani dariya ce take kama Mami,tace ai shine Auta,tace uhmm i see amma ya fisu girma ma kamar shine Babban, a ranta tace harda gemu da saje,Mami tace Dan Allah ku zauna lafiya,Salma tayi godiya sanye take cikin Atamfa super black and white tayi mugun kyau dama abinka da me kyau gata yar dagwas da ita matashiya.
Mayafinta ta gyara tare da rufe kanta ciki ta zauna a tsakiyar bed,Wise ce ta shugo tana mata turaren daki iri iri, Salma ita Baso ta tuna sai kuka take,Wise tace kyayi ma Kya gama Yan banzan Yara sai balagar zuci da Miji ya shugo za ajiku lakwas kuna karbar Antena, Salma tana kuka bata gane mene Antena ba.
Auta kuwa wanka yaci cikin wata Gezna ruwan Zuma ya tsula kyau yana kamshi ya gama Shiri ya zauna a bakin gado yana latsa waya a fili yace duk da cewar ba abinda zanyi wa Amarya amma da kunya yanzu kawai sai Mami taga na nufi part din Amarya ai da kunya sai da nace abokaina su rakani suka ce an Daina yayin raka Ango yanzu,Ina zan Saka kaina da kunyar Mami,yanzu Ina shiga shike nan ko banyi komai ba za ace nayi wani abu na zama Dan Iska,wayyo pillow ya jawo ya rungume yana cewa wayyo kunyar Mami waye zai rakani gashi ko kazar ban siyo mata ba ni ta Ina zan fara ne.
Tashi yayi yana gwada yanda zaiyi Idan ya shiga ya sha kunu ya bata rai ya furta kawai cewa zanyi Salamulaykum sannunki,da sauri yace nooooo Sallama zanyi da yanga na ajiye mata ledar kajin nace good night,a'a ai Kuma ba tsari kawai muyi fada tunda ba Sona take ba Nima haka,nooooo Auta nutsuwa zakayi Kaine fa namijin, mijinta a kasanka take behave well,yace uhmm hakane tabbas,yace yanzu zan fita Allah yasa kar na hadu da Mami,a hankali ya Bude kofar yana sanda yana lallabawa kamar barawo wai zai tafi part dinsa kar a Ganshi da kunya,da sauri ya dawo dakinsa kamar Wanda za a kama,sake gwadawa yayi har ya fita ya sake dawowa yana dariya yace wlh bazan je ba bazan iya ba,can Kuma yace haba karya ne Auta Kaine fa Dan zamani haba ka waye kunya ma tuni muka cillar da ita,kwanciya yayi a gadonsa ya ja pillow ya rungume
Mami ce ta banko kofar ta shugo dauke da katuwar ledar nama da kayan sha,uhm Auta Dan gata auren gata,Mami tace wai uban me kake Jira ne jiya fa baka je ba sai da Hamra suka kwana ko da matsala ne? kamar kana boye min abu,Auta duk zumudinka ka zauna jiya baka je ba yanzu uban me kake a nan ka bar yar mutane gashi har 10pm sai Wise na tura ta tayata zama,tashi ka tafi muje oya,Auta yace ni dai Mami wayyo yana yarfe hannu,dariya ya bawa Mami yace Mami zanyi kuka nima,muje Mami ta jawo shi ta rufe kofar tace kayanka an Kai can komai yana can muje,suka fito yana wani tirjewa yana sangarta,Mami tace zan mareka muje,suka tafi har bakin kofa ta kaishi tace kayi Addua ungo ta Mika masa ledar ya karba,ya juyo yana kallon Mami tace kaje,Rungume Mami yayi yace I love you Mami Babu kamarki,I will miss you gobe baza kizo ki tashe ni a bacci ba? Dariya Mami tayi tace ga matarka nan,mu kwana lafiya,tsokanar Mami yayi yace Mami ta juyo tace na'am yace hanyar ta Ina zan bi? zagi ta auna masa, ya shige ciki yana dariya har ya rufe kofa ya sake budewa yace Mami da karfi,ta juyo yace Good night kice Ina gaida Baffa,tafiyarta tayi,yana juyawa yaga Wise ta gama turaren tace Ango a bi yar mutane a sannu,Auta yace Mama karama karki bani kuka,Wise ta fice tana dariya ta musu sai da safe.
A dinga sharhi please shine godiyata ni
AsmaBaffa
08061929616
[8/15, 9:51 PM] AMINA KABIR CAPS: 🌼'YAR AIKIN KARUWAI 2 🌼
MATAFIYA
BOOK 2
51-55
Official
By
AsmaBaffa
SADAUKARWA GA
ZAINAB USMAN
*MISKI 3in1 Alfirdaus*🌹 Albishirinku💃 original miski daga *Egypt* miskin da koda yaushe Kuna yabawa dashi yana dauke 1.*Musk oil* ana shafawa agaba bayan gama al'ada inda hali za'a iya ringa sawa Koda yaushe yana maganin infection yana gyara gaban mace sosai 🙈ko yaushe gurin yakasance cikin kamshi 😇bayaga haka sunnah ne amfani da miski
2.*Musk cream* Ana shafawa ajiki gaba daya musamman wajan cinyoyi yana sa jikin mace koyaushe yakasance cikin kamshi kuma yana gyara fata, yasa tayi laushi
3.*Turaren tsarki* wannan turaren karshe ne 🔥 🔥 ba lallai se bayan gama period ba koda yaushe zaki iya rinka tsarki dashi yana gyara gurinnan🙈 sosai, kuma ana shafawa a hammata yana kawar da da wari karku bari abaku labari 🙍♀️👱♀️
Masu bukata ku ne wannan number
09065959708
Page naku ne
Sadiya Muhammad
Zakiyya Bello
Badimahd238
Gwaggonsu
Amina Maman Ibrahim
Dr Suhailat Hussein Armai.
Auta ciki ya shiga tare da haurawa sama direct dakinsa ya bude bata ciki ya dawo daya bedroom din ya tura kofar a hankali ya iske Salma tana uban kuka ita Baso take tunawa,Baki Auta ya tabe ya karasa ciki yace sannu da aiki ya bude ledar ya dauki abinda zai iya ci ya ajiye mata sauran yace ayi kuka lafiya,Salma wani takaici yasa tace sai anyi din Ina ruwanka dani, babu abinda ya shafeka da ni,juyowa yayi yace who even care about you kalleki Dan Allah ya ja tsaki, Salma kuma ta furta Karka sake ka shiga harkata,Ido ya tsura mata yace ni na Miki kama da ajinki? Salma ta juyo ta kalle shi tana yatsina tace Karka zo har dakina kace zaka fada min magana,dariyar yake Auta yayi yace Ina ya zama dakinki? Wa zai bawa irinki daki? Babu ni ba kai na fada maka Karka jawo Aljanuna su tashi na hada ma jini da majina, wani beran masallaci da Kai,Auta ya kalleta kawai wato tsabar lalacewa bera ne Kuma na masallaci ma.
Auta yace cikin fushi look at this dirty smelling local village girl, idiot ke Idan ban koma Santana naci ubanki ba shege nake useless girl yaja tsaki zai fice Salma tace Kai me nan wajen akuyarka ta kiyayi ramata wlh Nima tsagera ce Baso kawai nake wa biyayya,baki da aikin yi cewar Auta ya fice a fusace ya banko mata kofar kamar zai balla kofar, wani kallon banza ta bi kofar da shi ta ja tsaki ta mike tare da sawa kofar key tazo ta zauna ta baje kayan ciye ciyenta taci ta koshi,Alwala tayi da Sallah tana kallon dakinta a fili tace haduwa kuda a gefen gyambo Inama tare da Baso muke a nan wayyo Allah ta fada saman gadonta tana tunanin Basonta,Auta kuwa ya ja tsaki yafi goma yace Auta ka sa kudinka ka siyo problems da hannunka yace gobe Monday yana da lecture,Alwala yayi bayan yaci ya sha yayi Sallar Nafeela sannan yayi Shirin baccinsa cikin kayan bacci masu santsi Riga me dogon hannu sharara da ita da dogon wasu silver color,saman katon bed dinsa na alfarma ya haura ya jawo wayarsa ya hau Online,Nawwar yana kwance a jikin matarsa ni Rabiah muna danna waya dukkanmu muka ga Auta a Online yayi status ya rubuta Matata tafi ta kowa,Nawwar yayi dariya yace kaji Dan Iskan yaro a wajenka tafi ta kowa yo ta Isa ta fi miracle,nace never sai dai ta bi bayana,wani ya dora na biyu muka kunna muka ga yasa wasu suna chashewa an rubuta yanayi me Dadi,nace ba sabanba yau mun shiga uku,Nawwar magana yayi masa ta private yace Idan ana jin dadin a bar Online mana,Auta dariya yayi ya tura masa ya ranka mu babban Kai ne ba irinka ba an gama da Kai abu kadan sai ka rude mu kuwa sai an sha fama,Kai kuwa an wanke an baka ka shanye,Zanci ubanka wallahi cewar Nawwar sarkin masifa,Auta yayi voice yana cewa Yaya sai ya tsaya yace kashe light please sai Kuma yace sorry Yaya good night munyi can mu, waye yace kayi aure da wuri ka shanye dadinka kazo ka dameni ya kashe wayar gaba daya ya kwanta bacci abinsa..
Nawwar yana jin muryar Auta yace lallai yaron nan ya rainani yana magana da ni yana wani ce mata kashe light ya rainani na Daina wasa da shi,Nace chill man mene abin raini,dariya Nawwar yayi yace Allah Yan Makaranta abu kadan yanzu sai turanci nan gaba ma naga Alama Hausa Zaki daina,dariya nayi tare da makalewa a jikinsa,yace ga cikina yana ta girma Allah yasa a haifo min mace na fi son mace,Nace Ameen Allah ya bamu me albarka.
Washe gari da asuba Auta ya tashi mutumin da kullum sai an tasheshi ya tafi masallaci Sallar asuba indai Mami bata je ba bazai tashi ba sai rana ta fito yawanci yake Sallar safiya amma yau harda tashi da asuba,Light ya kunna yace to ya zanyi na zama Mijin wata Idan ban tashi ba ace banyi hankali ba,brush yayi da Alwala ya fito sanye cikin jallabiya harda rike carbi fari ya tako dakin Salma ya Murda handle kofar ta Bude ya Dan tura kofar a saman Sallaya ya isketa zaune yace cab duk sammakon ka wani a tafe ya kwana munafuka itama Dan tayi aure ne wai ita ta gari bayan mata da yawa basa Sallah akan lokaci wasu ma sai suce sai su gama ayyukansu suke hadawa,juyawa yayi ya rufo mata kofar tana jinsa domin a fili ya furta maganarsa tace Dan kawai Addua nake ne da na rama amma zamu hadu ne.
Yau Mami tana sa Ido ta Samanta ta leka part din Auta ta gani ko zai fito Sallah ko uban baccin nasa zaiyi sai kuwa ta Ganshi ya fito harda carbi da jallabiya,Baffa ta Kira tace zo kaga Auta me gida,window din ya karaso tare da rungume Mami ta baya suna kallon Auta suna dariya,Baffa sahu daya suka yi da Auta yau,sai da aka idar da Sallah ya tsaya harda azkhar sannan suna fitowa yace Baffa barka da asuba Ina kwana? Baffa yace sai kazo ma gaisa a hanya zaka gaishe ni,yace ni fa yau bazan zo ba bacci zan koma 12pm Kuma ina da lecture,au yau ma baza ka hakura da school ba kana Angon,yace me zan mata to shike nan sai na dinga zama,Baffa ya Kalli Auta yace Auta Anya kuwa kana son yarinyar nan duk mugun son aurenka,Ina sonta mana ya furta a ransa yana cewa karya nake bana sonta,sai da zasu rabu kowa zaiyi bangarensa yace ka gaida Mami,Baffa yayi dariya yace to zata ji ya tafi,Yana komawa bacci ya kwanta ya dinga bacci,Salma kuwa tuni ta koma bacci,sai 10am tashi tayi ta gyara gidan tace wallahi bazan gyara masa daki ba,wanka tayi taci kwalliya cikin leshinta na lefe brown and golden color tayi kyau,mayafi ta yafa ta fita taje part din Mami ta isketa a kitchen a kasa ta durkusa tace Ina kwana Mami,Mami taji Dadi taga hankalin Salma,ta amsa da fara'a,bayan nan ta fice tace zata je ta gaida Sauran tana mikewa Baffa ya fito cikin Shiri zai fita,ta sake zubewa a kasa guruf tace Ina Kwana ya amsa tace an tashi lafiya ya amsa da fara'a dama Baffa ya tsani gaisuwar zamanin nan da akeyi mussamman yaran yanzu ana ganin wayewa ce ko wacce Ina kwana wasu ma kafin ka amsa sunyi gaba Babu mutunci ba girmamawa Ina kwana kawai sai yarinya ta wuce ta barka nan,Baffa yace Honey zan fita,Salma kunya ta kamata a ranta tace bariki kan Uba tsofai tsofai a gabana cab wai honey,tana tsugune taga Mami ta rike hannayensa tana kwarara masa Addua,Salma tana satar kallon su ta mike sum sum ta fice kunya ta isheta ita Kam,part din wise ta shiga dauke da Sallama a bakinta Papa ya wani kwantar da Kansa a kirjin Wise suna Palo kuma,Baffa ganin surukarsa ce ashe ya tashi da sauri,Shima durkusawa tayi ta gaida shi ya amsa da fara'a ya tashi ya koma bedroom,tace Aunty Ina kwana? Wise tace ai ni kawarki ce yarinya tashi ta jawota saman kujera tace da Alama kalau kike wlh Auta ba abinda yayi gaskiya Ina Jira nazo gashi,Salma tana jin kunya tace sai kace wata kaza,bata Dade ba ta tafi wajen Iyamami Sabreen ta koma can da kwana ta gansu tare suka mata wani kallon banza suka watsar da kyar ma suka amsa gaisuwarta,Iyamami tace ashe da sauran hankalin da kika San kizo ki gaida manya Allah ya kyauta ko a Ina Auta ya kwaso Sabreen ta karasa da oho masa,Salma ta kalle su ta balla musu harara ta juya fiya fiya ta fice, Iyamami tace Iyye kaga yar iskar yarinya to dama tun kafin a aurota an zuga ta,lallai an sanar mata mune shegun gidan nan zata ci ubanta,Sabreen tace kyale banza can zata yanka.
Salma part dinta ta koma tana shiga ta samu Mami har ta Aiko musu da abinci,Auta ta gani ya fito daga shi sai wando 3qutr ya fito da mopper da tsintsiya ya gyara bedroom dinsa tsaf da toilet,tazo zata wuce yace dadin abin Allah ya mana hannu Kuma ya bamu lafiya mu bamu Saba kazanta ba,binsa tayi da kallo gaba daya ta shagalta da kallon surar Auta Dan dagwas har ta manta ma a Ina take ta shagalta ta tsura masa Ido,yace Hello,hankalinta ta dawo tace ai kasan ba Kai kadai bane a gidan da mutane to baka birge ba ka Maida rigarka ka Saka ya fiye maka na gaji da ganin muninka,Auta yace sannu uwata Mami ya ja tsaki yaje ya ajiye mopper ya dawo ya wuce sama abinsa wanka ya fesa ya sha kana nan kaya ya dakko yar jakarsa ya ratayota ta wuyansa ya fito Dan gaye anci swagg, Salma ta zuba abinda take so tana ci,ya fito ko kulashi bata yi ba tana Shan tea tana danna wayarta karama Vivo,cup ya dakko ya zuba tea ya hada abinda ya sha yaci chips kadan ya dauki chegum me tsada ya jefa a bakinsa,ta kalle shi ta tabe baki tace Iyayi mu ayi mana Iyayi mene bamu sani ba Mami Son kawai, komai sai an baka ai Kai a garin nan baza ka taba samun aikin yi ba,ga mate Dinka nan suna Neman na kansu kaje gari ka gani Yara kanana sun zama attajirai Kai kuwa sai dai a baka ka dogara da kudin Iyaye,a haka Zaka iya daukan nauyina,Auta yace Allah ya baki lafiya naga Alama baki da hankali,Salma ta mike tare da rike kugu tace Kai waye da zaka fada min magana,tsaki ya ja ya fice ya barta tana kwafa,cikin fushi ya fito a fusace yana cewa yarinyar nan naga Alama bata da hankali,Nawwar ne ya juya kan kan motarsa yayi parking ya iske Auta yana Shirin shiga motarsa da Baffa ya siya masa gaf da aure,yace Ango Makaranta Kuma? Auta ya kalle shi kawai ransa a bace,yace Auta kalau Ango Kai da za a ga kana nishadi,Auta