Showing 15001 words to 18000 words out of 77913 words
hausa sanan dalilin girmanta da idanuwansa ke gani yasa yake kula jikarta Sahla don ba dan ita ba sam bazai saurari Sahlan ba don kuwa ita din bata cikin tsarin kalar matan da yake so , sam bata birgeshi sai dai dan dole don kuwa KO mubina da ta tafi tsere ta dan fita cikowa ( to fa 😳 )
Ci gaban labarin
Taku har kulun ..........sajidah
🇳🇪Belles écrivaines du Niger
*'YAR 👧🏻*
*MAHAUKACIYA👹*
*_Na SAJIDA_*
17
Dedicated to ♻ *EXCLUSIVE Forum* ku gane ina yinku irin da yawa din nan ,
*Ummy xeey*
*Aishan umma*
*Ruksad*
*Nabilancy*
*Bébé'arth*
*Phertimer Umar Abdallah*
*Aishat À muhd*
*Réal khady*
*Meelart Ahk*
*Sardy bash*
*Ummu khady*
*Billy Ladan* da da da ,,,,........,,,,,, da duk sauran da ban zano ba jinjina gareku *Muah*
Ci gaba
Yana tsaka da shan furarsa yaji takun takalmin Sahla ta nufo cikin gidan a ransa ya ce " oh Ashe taga zuwana KO wa ya fada mata , ? Wata zuciyar ta ce masa kanshin tiraranka manan tace ta shi take gane idan kazo ,, yana tsaka da tinanin yaji salamarta ya dago kansa a hankali ya ce " Amin wa'alaiki salam warahamatulah Sahla
Tana mugun jin dadin idan ya kama sunanta domin ji take duk duniya ba Wanda ya kaishi iya furta *Sahla* har wani sanyi sanyi take ji idan ya furta , cikin nutsuwa ta dauko farar kujera ta aje kusan sa ta zauna , kasa kasa yake kalon shigarta doguwar Riga ce ta atampa da wani zungureren takalmi mai kyau a kafarta sai dai ta tafi zumbal ba kibar komai ba inda ya dan ciko ya sauke ajiyar zuciya da yayi arba da jagirar da ta ja baka a goshinta domin harga Allah sai da ya tsorata
Cikin wata murya mai dadin sauraro ya ce " ki dena wanan abin a goshinki yayi yawa
Sahla tayi murmushi ta ce " huby a saloon fa akayi min
Cikin basarwa ya ce " basu iya ba
Ta kuma yin wani murmushin a ranta tace mutun sai shegen kushe mutane aman a fili tace " to zan dena
Yayi murmushi da yasa ta kuma narkewa ya ce " Masha Allah Allah yayi miki albarka
Tayi far da ido ta ce " Amin , aman a ranta tana fadin sai kace ubana ka ringa saka min albarka duk sai na rabaka da wanan shegiyar akidar ta mahaifiyarka ta saka albarka duk motsin da za'ayi
Mubasshir ya ce " ina son muyi magana da ke mai mahinmanci
Sahla ta ce " toh muje cikin gidan mom mana ai yafi siri KO?
Mubasshir ya ce " no muje cikin falon Hajiya hankalina yafi konciya da nan din
Ta mike cikin yanga tayi gaba har ta kusan shiga ta waigo ta Ganshi a zaunan ta juyo domin tasan abinda ya hana shi tashi ta dauki kwaryar furar tasa ta yi ciki , yayi bismillah ya mike yayi cikin shima
Suna shiga ta kara kakabe masa wajen da zai zauna ya karaso ya zauna ta juya ta nufi dakin Yar Mahaukaciya Wace ta gama sallah kenan da zumbulelen hijabinta mai hanu kalar blue mai duhu fuskarta ta kara haskawa a cikin hijabin , tana shiga ta ja tayi tsaye tana yatsina , taso taga wani abin fada sai dai bata ga komai ba domin dakin tas a gyare ga kanshin turaren wuta da yake ta ja tsaki ta ce " Ke yar talakawa tashi maza ki kawowa mijina abin motsa baki domin shi baya kyankyanin tsohuwar nan kiyi maza ina jira , ta juya kwas kwas ta koma falon bata cire takalmin kafartata ba
Yar Mahaukaciya ta mike tana fadin daman na sani yau tawace ta sameni , ta fito cikin nutsuwa ta nufi kicin din falon inda suke ajiye jus jus kalakala ta bude frij din ta ja ta tsaya , ita dai bata san wani kala yake sha ba ta rasa wane zata dauka kawai ta rintse ido ta dauko guda exotic karami dan naira dari uku ta dora saman faranti ta dauko abin zubawa ta juyo tana tafe tana adu'ar Allah ya taimaketa kar tayi laifi , ta kusan isowa cikin falon taji Sahla ta kwala wani ihu ta shiga rawa tana ta kakaba dariya Yar Mahaukaciya ta ja daidai kapet din ta tsaya ita bata karasa ba ita bata koma ba
Sahla cikin murna ta ce " wai dan Allah da gaske kake zaka aure ni? Dan Allah yaushe ? Wayo dadi kasheni Ashe daman kana son nawa?
Mubasshir ya girgiza kai yana kalonta uwa zautata sai ihu take wai na murna ne
Tana tsaka da murnar tata ta waigo ta ga Yar Mahaukaciya ta zuba mata manyen idanuwan nan nata ya na mage tana kalonta saida gabanta ya fadi dan kuwa ba karamin kyau taga tayi ba cikin bacin rai na ganin jus din da ta dauko ta nufeta ta kifeta da mari cikin fada ta ce " ke jakar ina ce? Ki rasa jus din da zaki daukowa Honorable sai wanan? To yayi mai da jus din dari uku? Ke dan kin saba shan sa sai ki kawowa mijina? To bari ki ji KO karena yafi karfin ya sha kalar jus din nan bale Honorable
Yar Mahaukaciya da tunda ta mareta ta saki farantin gaba daya kayan saman suka zube kasa tayi Saurin tsugunawa tana kwashewa gaba daya jikinta na kyarma
Muryar Mubashir ta sakata dago da kanta cikin gagawa domin bata taba jin muryarsa a haka ba
Mubasshir ya ce """""""
😟😟😟😟😟😟😟😟😟😟
[9/20, 13:53] Umar Dalha: 🇳🇪Belles écrivaines du Niger
*'YAR 👧🏻*
*MAHAUKACIYA👹*
*_Na SAJIDA_*
18
Mubashir ya ce " ki guji batawa mutun rai a duk inda kike kiyi kokarin ganin kun wanye lafiya da mutun , ya juya wajen Sahla ya ce" ki je ki kawo min kalar Wanda kike si na sha din , Sahla ta juya tana matukar mamakin canjinsa na lokaci daya da da ne Hasan sai yayi mata fada tayi murmushi ta ciro wayarta dan tayiwa kawarta albishir mai dadi
Bayan tafiyarta ya dan kali wajen Yar Mahaukaciya Wace ta sala hanunta cikin kwalbar nan tana tsincewa tana ta hawaye domin ta tsorata da fadan da Sahla da mijinta suka yi mata a fada mana wanan ai shine a dakeka a hana ka kuka yanzu da hajiya tana nan ai da bata bari sun yi mata wanan wulakancin ba , aman ba komai zata kara hakuri har Allah ya bayana mata Yar Mahaukaciyarta su tatars su nemi wata bolar su domin kuwa konciyar hankali yafi kudi ,
Mubashir ya sauke ajiyar zuciya ya danyi murmushin abinda yake sakawa a ransa daidai nan muryar Malan yana salama Yar Mahaukaciya tayi Saurin dago kanta tana kalon kofar ta amsa salamar tare da yin kicin da sauri ta fito tana goge hanunta da tsuma ta nufi kofar falon ta bude sai ga Malan yunus yana murmushin sa
Yar Mahaukaciya cikin murnar ganinsa ta duka har kasa ta ce" Marhababika Malan ina yini an zo lafiya? Ya hanya?
Malan yunus yayi Murmushi ya ce" Lafiya lau Rahama ya na sameki ya kuma gida?
Ta ce" lafiya Alhamdulilah
Ya ce Masha Allah , Masha Allah , daman nazo na shaida miki zamu mayar da karatun mu da dare domin mai gidan yayi kirana ya fada min ya sama miki wata makaranta ta boko ita kuwa wuni ake a can , kin san kowane yana da anfani dan haka sai a maida hankali Allah ya kama mana
Yar Mahaukaciya cikin jin dadi domin harta manta marin da aka gaura mata ta ce" Alhamdulilah Allah abin godiya
Suka yi salama da Malan Yunus ya juya KO cikin dakin bai shiga ba dan kuwa sunyi da idriss sai na dare kuma daga gobe zasu fara ,
Ta Mike ta rufo daki sai murmushi take dokawa kuncinta na lobawa suka yi ido hudu da Mubasshir Wanda tunda ta bude dakin ya tsura mata ido , suna hada ido ya kawar da kansa a ransa ya ce" who is she??????? (Entouka i don't know)
Cikin nutsuwarta ta raba ta gefensa tayi shigewarta dakin hajiya ta rufo tana adu'ar Allah ya kawo hajiya lafiya tayi mata albishir
Sun jima shi da Sahla suna zance ba laifi yana observing dinta idan tayi tayi sai ta tambaye shi ya fahimceta? Shi kuwa sai ya gyada mata hakan kuwa sam baya damunta domin ta saba da rashin maganarsa ita dai ba aikin bokan mamarta ya ci bâ; maganar ma zai koya gaba gaba ( to fa )
Karfe shida da rabi ya mike domin yaga alamar Hajiya ba dawowa zata yi ba suka fito tayi masa rakiya har wajen motarsa ya shige ya tafi ita kuwa ta nufi wajen mahaifiyarta dake jiranta su tatauna
[9/20, 13:53] Umar Dalha: 🇳🇪Belles écrivaines du Niger
*'YAR 👧🏻*
*MAHAUKACIYA👹*
*_Na SAJIDA_*
19
Tana shiga Hajiya Marhaba ta ce " tun dazu ina zaune ina zuba idon ganin kin dawo fada min nawa ya ce za'a kawo kudin tambayar
Sahla ta ce " Momy bamu yi wanan maganar ba kin sani sarai tuwon girma miyarsa nama kin san abin mamaki za'a kawo mana ya ce fa a cikin satin nan yake so a kawo komai tunda na fada masa Dad zai dawo gobe kinga kawai sai ayi ayi a amshi kudin muma mu shiga shirye shiryen mu
hajiya Marhaba ta ce" Ohk tohm ai ba damuwa sai muyi jiran dawowar Elhajn
Ba Hajiya Hawau ta dawo ba sai karfe Takwas Idriss ya biya ya daukota suna tafe yana mitar ta bar yarinya ita kadai a gida tun tana kyale shi har tace" yo to kaji ubana ai sai ka kawo min duka , yanzu ayi mana mutuwar ka hana ni zaman makoki dan kin Allah? To KO ubanka bai isa ya hanani balatana kai ehe , nan da jikana ya rasu har kwana tayi a gidana tana tayani jaje dan ita ta isa da iyalanta ba Wanda ya bi sayunta ya titsiyota a gaba ya korota gida sai ni da aka raina , ni dai Idrissu ka fita a idona na rufe Aradu tohm
Idriss yayi gum da bakinsa sai a lokacin yayi mata maganar ya samawa Yar tata makaranta har an gama uniform dinta da komai sai dai direct secondry ya kaita aman da masu yi mata lesson dan dai kawai ta kara wayewa ne ta san wani abin
Hajiya ta washe baki kamar ba itace yanzu take fadan an dameta ba ta ce" Allah yasa ka gama da duniya lafiya yanda kake kokarin faranta min ni da yata Allah ya baka mai faranta maka Allah ya jikan kakanka kuma sai hawaye aka ci gaba da fadin sak irin halayensa ne ka dauko Allah ya sa ya huta
Idriss ya gumtse dariyarsa don kuwa lamarin na Hajiya yanzu dariya yanzu kuka kai Allah ya sa muyi tsufa mai anfani , ya Mike yayi mata salama ta rufo dakin nata ta kashe komai itama ta yasu sai barcin gajiya .
Tunda asuba bayan sunyi sallah Yar Mahaukaciya tati wanka Hajiya ta miko mata kayanta dogon wando ne da riga daidai gwuiwa da fararen safa kayan ma farare ne tas sai bakin hijabi mai hanu da kuma bakin takalmi mai dan tudu mai igiya , makarantar ta yayan manya ce shima ta kan Mubasshir ya bi aka dauketa sanan aka daukar mata malaman da zasu kula da harkar karatun ta ya kasance tayi gagawar iya turanci KO test baza'ayi mata ba dan ya fadi gaskiya bata iya komai ba .
Cikin minti talatin ta gama shiryawa ta daure gashin kanta da kyar ta saka hijabin Wanda yake da tsayi sosai domin har ya fi rigar tsayi ta juyo cikin nutsuwa ta fito wajen Hajiya Hawau da ta gama mata abin kari da kuma zuba mata wani a kwano ta saka mata a jakar da kudin abinci idan ta cinye wanan abincin , tana fitowa ta gaisar da Hajiya
Hajiya ta ce" kai kayan nan sun karbeki Ramatutu wly sunyi miki kyau nasan duka sai kinfi yaran kyau
Yar Mahaukaciya tayi murmushi ta ce" Hajiyata kings hijabin harda wajen fitar da hanu
Hajiya ta ce " kema kya fada zamani , tashi mu je muyi jiransa kar ya tafi ya barki ga abincinki komai da komai harda kayan hada shayi idan kinje ki zauna ki karya sanan ki shiga ajin kinji KO?
Ta ce " toh suka fito kofa wajen mai gadi suka zauna suna jiran fitowar Idriss Wanda KO daga baci bai farka ba
Sai karfe bakwai da rabi ya fito shima dan kar aje bata shirya ba suyi lati ranar zuwanta ta farko bai dace ba , yana fitowa ya hangosu Hajiya a zaune a yar tayani tsegumi ita kuwa a tsugune a gefenta ai besan sanda dariya ta kufce masa ba ya ce " aiki ga mai kare ka
Haka ta Mike ta shiga ya tayar suka haura titi suna tafe yana yi mata bayanin yanda zata yi dan karta sha wahala sosai, ya ciro wani kati mai walwali ya Mika mata ya ce" wanan katin cin abincin ki ne na biya na shekarar gaba daya sanan na zabi na biya idan kinje kinada damar duk lokacin da kika ji yunwa ki shiga restaurant ne part VIP ki shiga can ki zabi kalar abinda kike sha'awar ci a kawo miki ki ci ki dan huta kiyi sallah sai ki huce wajen karatun ki , karkiyi wasa da karatun nan naki domin kafin ki fahimci lesson sai kin sha fama tunda baki iya rubutawa da karantawa ba aman da yardar Allah zaki iya harma ki koya min , ya karasa yana murmushi '
Tayi murmushin itama ta miko hanu ta karba tana godiya ta ce" ai kuwa kaga Hajiya har ta zuba min kayan abincina a jaka
Ya kwalalo ido ya ce" to kaji yo ai baza'a barki ki shiga da wani abinci ba gudun karki zo da abinda zai bata miki ciki kuma a tsayar da karatun KO wani ya ci ya bata masa ciki a samu matsala , makarantar nan akoy shegen tsaro dan haka ki kiyaye ki dena zuwa da komai wanan din ma ki juye shi a nan idan kin shiga kya karya , hakan kuwa akayi ta juye komai ya rakata har kofar shiga daidai nan aka tsayar da shi ita kuwa aka caje Jakarta aka rage litatafan aka ware na ranar abinda zasu yi sai wani litafin aka saka mata dan saboda karatun da zata ringa dauka da wasu malaman bayan aji .
❤
🇳🇪Belles écrivaines du Niger
*'YAR 👧🏻*
*MAHAUKACIYA👹*
*_Na SAJIDA_*
20
Haka Yar Mahaukaciya ta shiga cikin makarantar ta nufi office din da aka nuna mata taje ta ja ta tsaya ta shiga rapka salama ta kai wajen minti biyar a nan a tsaye sai da wani dalibi ya zo ya dana wani jan abu sai taga kofar ta bude ya shige ta kwalalo ido tana nan tsaye ya fito yayi tafiyarsa ta lumshe ido tayi bismillah hanunta na karkarwa ta dana jan abun kofar ta ce wani guiui ta bude ai uwa an hankadata ta fada sai zazare ido take tana kifkif da ido
Mutumin dake zaune ya hakimce da shigar manyan kaya a jikinsa gefensa kuwa da wasu mutane sai dadana computer suke gaba kadan da shi kuma jerin wasu mutanen ne suna observing dalibai a computer ita dai tayi tsai tana kalon su yayi gyaran murya ya mika mata hanu da nufin ta bashi takardarta Wace idan tazo zata gabatar a kaita aji a nuna mata komai
Ai gaba daya takardun hanun nata da litatafen da jakar ta ajiye masa saman table din nasa na glass ta ce" wly sun caje ni kosan ma yaya ya juya da shi KO karyawa banyi ba
Nan da nan suka shiga kalon juna , banban na zaune Wanda ke hakimce ya ce" ur name?
Yar Mahaukaciya tayi Kifkif da ido tana kalonsa fuskarta bayane da tsoro kafin tayi magana téléphone din saman table din yayi ringin ya Mika hanu ya daga
Daga dayan bangaren ya ce " tazo KO?
Abdallah mai kula da makarantar ya ce" aa dalibai dai suna ta shigowa har yanzu bamu ga mai sunanta ba aman ga wata tsaye inajin bata iya turanci ba ma
Mubasshir ya ce" what? Na fada maka yar gidana ce kuma akoy abinda ya tsayar da ita ba'a kula da karatunta ba kayi mata hausa idan tazo shine zakana cewa baka sani ba ? Look idan kaga bazaku kula kan karatunta ba na tura a dauko mini ita , karatu KO a Wace kasa take so sai na kaita kuma KO wani kalar malami sai na sama mata ya koyar da ita
Abdallah ya ce " kayi hakuri abin du bai kai nan ba yaya sunanta ne?
Mubasshir ya zaro ido yayi Saurin rufe kan wayar ya kali idriss da ya saka shi a gaba kan a kula kar su banzatar da ita ya ce" kai sunanta fa?
Idriss ya dane dariyarsa ya ce" *RAHAMA IDRISS*
Mubasshir ya yatsina fuska ya kara a kunan sa ya ce" Rahama idriss
Abdallah ya tambayi Yar Mahaukaciya dake tsaye da hausa ya ce" kece Rahama Idriss?
Da Sauri ta gyada kanta ta ce " eh Nice
Abdallah ya ce" sir itace a kara hakuri zata samu kyakyawar kulawa