Showing 33001 words to 36000 words out of 77913 words

Chapter 12 - 'Yar Mahaukaciya

10 Oct 2024

15923

da shi a waje

Da Sauri mubasshir ya kaleta harda zaro ido gabansa yayi wani mugun faduwa idanuwansa suka wani firfito waje , ita kuwa wata irin kunya ta rufeta ta mike da sauri har tana hade kafafuwa wajen sauri ta shige kicin

Ya bita da kalo gabansa ya kara faduwa

Hajiya Fadimatu dake kalonsa tana nazarinsa ta ce " kana ji ?


Mubasshir ya juyo da Sauri ya ce " ohk toh zzzzan fada harda wata sabuwar inda inda da ta same shi , ya juya da Sauri ya fita ya nufi motarsa still gabansa bai dena faduwa ba


Hajiya Fadimatu tayi murmushi ta lumshe idanuwanta ita kadai ta san abinda take tinani sanan ta kuma yin wani murmushin ta mike ta nufi kicin dan ta dawo da yarta da taji kunyarta ta tsere





.


.





........................... . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . .
[11/19, 9:35 AM] ‪+234 909 534 8504‬: 🇳🇪Belles écrivaines du Niger



*'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*




39


Yana fita ya fada motarsa ya tayar ya kama hanya tafe yake kwakwaluwarsa tana cikin caji sai maimaita kalmar inalilahi wa'ina ilaihi raj'une yake ya rasa wanan wani irin tashin hankali ne ke tunkarar sa

Tun kafin ya isa kofar gidansa yake horn da gudu aka bude masa ya fada gidansa ya ajiye motar a nan ba tare da ya daidaita ta ba ya fito ya bar wayoyinsa a nan cikin motar ya nufi cikin gidan


Sahla dake zaune ta sha kananan kaya Wanda ilahirin jikinta a waje yake tana jin karar motarsa domin daman hankalinta gaba daya a wajen yake ,

Cikin yanga da karairaya ta Mike ta nufo kofar dan ta taro sa , kafin ta karasa har ya bude ya fado falon ja tayi ta tsaya gabanta na faduwa tana tinanin ta karasa ne KO ta juya ,balatana a irin yanda ya shigo


Tsayuwa Mubasshir yayi yana karewa Sahla kalo tun daga kitson atach din da aka yarfa mata kananuwa masu shegen kyau da yanayin tsarin halitarta da Allah yayi mata , sam Sahla a shafe take tun daga saman har kasan sanan abin haushin mamarta har sun dan fara faduwa daman gasu kananuwa hakan na nufin au haka halitarta take KO kuwa an zubar da su ne , yayi saurin rintse ido da ya Tina wai yayi taraya da matar da wani ya fara taraya da ita ,

Cikin bacin rai ya raba ta gefenta wani tirare mai karfin tsiya ya bige masa hanci take ya furta a'uzubilahi minan shaidanin rajim , yaci gaba da tafiyars ya nufi dakinsa

Da gudu Sahla ta bi bayan sa tana rungume shi ta baya ta saki wani irin kuka mai tsuma zuciyar duk wani mai saurare ,
Ta kai wajen minti biyar a haka sanan ya juyo da ita a gabansa cikin kakausar murya ya ce " Kuka? Sahla kina kukan jin kunyar halayenki ne, kina kukan irin dabi'unki ne, kina kukan kin banzatar da kanki ne KO kukan na share ki kike?


Cikin shashekar kuka Sahla ta ce " Haba Yaya Mubasshir mai yasa zaka yanke min irin hukuncin nan ba tare da kayi bincike ba ? Ka sani wly ba laifina bane kadara ce Wace ba Wanda yafi karfin ta afka masa, Haba Yaya Mubasshir dan Allah kai fa musulmi ne taya zaka yanke hukunci haka ba tare da bincike ba?



Mubasshir yayi tsai yana kalonta a ransa ya ce lale KO shekarunta nawa? Yarinyar da har tasan ita ba budurwa bace har ta san ta je wajen wani katon ya kara wangaleta yayi mata aiki dan ya mayar mata da abinda ta kau a titi wai itace zata yi tsaye ta kirayi kanta da kadara ? Tabas akoy na kadara kuma akoy na ra'ayi, ya lumshe idanuwansa a fili ya ce " Kadara? To Allah ya kare mu da mumunar kadara ya juya dan kwata kwata baya son wanan yawan dumin


Sahla ta kara shan gabansa ta ce " Dan Girman Allah , Dan Soyayarka da fiyayen Halita, Dan Darajar mahaifanka ka yafe min ka manta da komai muyi rayuwar mu cikin aminci dan Allah


Gaba daya ji yayi tamkar an dadaure masa gabobin jikinsa irin yanda ta hada shi da Allah , cikin kasalaliyar murya ya ce " Tabas ni musulmi ne , bazan so na kwana da haushin ki a raina ba , sanan du mai yafiya Allah yana yafe masa kurakuransa shi ma , ya dafa daidai zuciyarsa ya ce " Na Yafe miki , sanan zan ci gaba da rayuwar aure da ke aman fa bisa sharadi biyu zuwa uku idan kin amince


Cikin sauri Sahla ta ce " na amince koma mainene


Ya danyi murmushi ya ce " a yanzu na farko ina son ki dan nisanta kanki da ni na dan lokaci kadan dan na samu nutsuwa kafin na dawo gareki , a cikin gidan nake ba wani waje zan je ba , aman ina son nayi rayuwa da ibada har naji na ware da wanan , sai dai idan kin san kina da muguwar sha'awar da zata hanaki yin hakan


Wata irin kunya ta kama Sahla da dana sanin tarboshi a haka cikin sine kai ta ce" no aa ba komai Insha Allah zanyi iya yina dan ganin na kiyaye , mainene sauran sharadin?



Ya dan cije lebensa ya ce " idan lokacin ki san su yayi zan sanar da ke , sanan ya juya cikin nutsuwa ya fada tankememen dakinsa yana sakin ajiyar zuciya


Sahla ta bishi da kalo tana cije lebe domin ta dirki magunguna gudun yau ma kar ta sha wahalar da ta sha jiya sai dai a banza ga kuma maganin da aagaifiyarta ta ce shi kadai ma dubu ashirin ta baiwa boka sunansa malaka idan ya sadu da ita shikenan ta saye shi , haka ta juya tana mutsumutsutu ta nufi dakinta itama




Yana shiga dakin nasa ya nufi bayi ya dauro alwala ya fito ya kama nafillah yana karawa duk idan ya kai sujada sai yayi ta adu'a yana rokon sasaucin abinda ke damunsa , da ya gama ma ya mike ya cire kayansa ya saka na baci ya juya ya konta


Lumshe idanuwansa yayi yana adu'ar baci aman ina hotonta ya fado masa a idanuwansa ya mike tsaye ba shiri ya shiga zirga zirga a fili ya ce " anya kuwa Mubasshir baka sayarwa kanka tashin hankali ba?


Ya koma ya fada ya jawo filo ya rukumkume yana sakin ajiyar zuciya aman sam bacin ya kauracewa idanuwansa banda juyi ba abinda yake yana kokarin cire hotonta daga idanuwansa dan kuwa sam basu dace ba , wanan zancen idan ya fito ai kowa ma sai ya debe masa albarka dan wanan ai cin amana ne






To fah mai ya hana honorable baci? Hoton wacece yake kokarin cirewa daga zuciyarsa????????????????????????????????????????????????????????????????????

🇳🇪Belles écrivaines du Niger



*'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*




40



Da kyar baci barawo yayi awon gaba da shi , baci marar dadi dan kuwa cike yake da mafarkai marasa dadi , a ganinsa domin mafarkinta ya kwana yi Wanda har wani zazabi ya zubo masa dalilin hakan dan kuwa damuwa bata daga cikin abinda ya sani , ba dai irin wanan damuwar ba





Konci tashi yau har kwana uku daidai da auren Mubasshir Da Sahla inda rabonsa da gidan mamarsa tun washe garin auren sa bai koma ba yana gidansa sanan shi da kansa ya cire dokar da ya dorawa Sahla KO ya rage tinanin abinda bazai fishe shi ba,





Kamar yanda ta saba ta farka da wuri tayi aikace aikacenta Wanda Hajiya Fadimatu tayi tayi ta rabata da su aman ina sai ta farka ta ga ta gama komai hakan yasa ta kawo ido ta zuba mata sanan tana matukar farin cikin irin yanda sam Yar mahaukaciya bata da ragonta sanan ga biyaya sosai take jin dadin yanda take kafakafa da duk abinda ya shafeta ,

Bayan ta gama aikinta ta koma dakinta ta tsala wankanta tana fitowa Hajiya Fadimatu ta fito cikin bakar abayarta ta sha nadinta tsaf masha Allah

Yar Mahaukaciya ta duka ta ce" barka da safiya mama


Hajiya Fadimatu ta amsa tana mikar da ita ta ce" yata zan fita , may be na dan jima , daga nan zan biya makarantar ku dan hutu kinga ya kusa karewa na ga abinda ya dace ayi KO?


Yar Mahaukaciya ta ce" to mama Allah ya kaiki lafiya ya maido ki lafiya


Hajiya Fadimatu ta amsa da amin ya Allah sanan ta juya tana mai adu'ar Allah ya sa wanan hadi da sukayi niyar yi alkhairi ne




Hajiya Hawau na hango cikin mota tana zaune da hijabinta zumbulele Hajiya Fadimatu ta karasa direba ya bude mata ta shiga sanan ta ce" unguwar yan baiwa zaka kaimu inda wakili ya sauka


Direba ya ce " toh Hajiya sanan ya harba motar bakin titi ya kama hanyar gidan wakili Elhaj Muhammad


Hajiya Fadimatu ta gaisar da Hajiya Hawau cikin mutunci sanan ta ce " tabas nima na yarda da tarbiyar yarinyar nan domin camera na laka a dakinta duk abinda take aikatawa ina kalonta sanan ina saurare , sai dai abu guda dake daure min kai ,


Hajiya Hawau ta ce " mai yake daure miki kai?


Hajiya Fadimatu ta ce " am akoy abinda ke damun Rahma domin ta fiya tinani KO haka Allah ya halice ta?



Hajiya Hawau ta ce " tabas nima na sha ritsata da tambayar shin tinanin mai take saï tace ba komai , sai nafi mayar da hakan kan KO dan yaronta ya rasu ne ?



Hajiya Fadimatu tayi shiru sanan ta nisa ta ce" hakane , Allah ya sa abinda zamu aikata alkhairi ne dan ni kam nayi ta rokon Allah kan isan har ba alkhairi bane to ya cire min wanan tinanin daga zuciyata aman cikin ikonsa a kulum kara sha'awar hakan nake



Hajiya Hawau ta ce" tabas alkhairin Kenan Allah ya biya mana burin mu sanan ya kade shetan


Daidai nan direban ya bubude musu kofa suka fito suka nufi falon inda wakili Elhaj Muhammad ke zaune yana jiran karasowar su




Bayan sun gaisa Elhaj Muhammad ya dago kansa ya gama nazartar Hajiya Hawau tabas daga ganinta ka ga tsohuwa mai kamala , sai dai ba a nan gizo ke sakar ba , shin da gaske ne abinda ta fada ?


A nitse ya ce " baba tabas na gamsu da bayananki sai dai wani hanzari ba gudu ba ,mai zai nunan shedar eh lale yarinyar nan mutuniyar kirki ce? Sanan shi yaron nan baba jininki ne kuwa?


Hajiya Fadimatu ta dauko wayarta ta ciro wata memori ta jona jikin TV daram sai ga vidion Yar Mahaukaciya tun zuwanta gidan da yawancin maganarta harda idan tana tare da kawarta Fati , da komai sanan ta ce " Yaya ka yarda da maganata ka jagoranci daurin auren nan domin yarinyar nan yar Amana ce ceton rai zamu yi , Allah shi zai bamu ladan mu



Elhaj Muhammad ya aa numfashi ya sauke Sanan ya ce " toh babu damuwa Allah ya sa alkhairi ne , yanzu su liman din suna can dakin bakin KO?



Hajiya Hawau ta amsa da eh suna can


Ya ce " sunan yarinyar Rahma wa?


Hajiya Hawau ta ce " lokacin da tazo daidai da sunanta ta manta hakan ya sa mukayi duk yanda ya dace a musulunce muka saka mata Rahma


Elhaj Muhammad ya kuma kalonta shi dai yana dan kokonto aman bashi da wani iko a nan Dole ya aiwatar da umarnin hajiya fadimatu haka ya mike ya tafi wajen su liman din da niyar daura auren Rahma da agonta ..................................................................................🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀



🇳🇪Belles écrivaines du Niger


*'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*

41

Sun jima zaune sunyi shiru kowa da abinda yake sakawa a zuciyarsa jiran vilowar Elhaj Muhammad suke ,

Bayan kamar minti arba'in sai gashi ya shigo da damin goro a hanunsa yayi salama

Suka amsa masa a tare suna kalonsa

Waje ya samu ya zauna ya fuskance su ya ce " cikin ikon Allah an daura aure a gaban shedu sanan kuma ga goro na samu Kiran sarki na shaida masa ya ce eh aure taya shi ake Allah ya sanya alkhairi,

Hajiya Hawau ta ce" kana nufin *Rahma* ta zama matar *Dan Aljannah*?

Elhaj Muhammad ya ce " Kwarai kuwa ni na wakilce ta liman ishak ya wakilci Mubasshir Allah ya sa alkhairi aka hada

Hajiya Hawau ta ce " Alhamdulilah Allah abin godiya tabas alkhairi aka hada Allah ubangiji ya fi karfin su Allah ya kare duk wani mugun abin da za'a jefa dan a bata wanan taraya sanan Allah ya hada Hankalinsu

Hajiya Fadimatu ta amsa da Amin ya Allah

Haka suka gama suka tatara suka nufi gidan Hajiya fadimatu

Suna shiga suka tarar da Yar Mahaukaciya konce saman doguwar kujera tana bacinta , cikin nitsuwa Hajiya Hawau ta karasa ta tataro gashin kanta ta daidaita mata shi sanan ta dora mata dan kwalinta da ya fadi a hankali ta ce " ina ji a jikina ke Yar Halak ce, sanan ke ba mutuniyar banza bace , hakan yasa na gommaci ki auri bawan Allahn nan tun kafin su saka rayuwarsa a garari, jinina ne Idriss sai dai kash bashida mahaifiyar kirki , sam bai yi dace da uwa ba , haka yar uwarsa tayo halayar mahaifiyarta Wace ta raba soyayar da da uwa,
Ni na san Ilyasu baya cikin hankalinsa shi yasa nake yi masa uzuri Allah ya yaye masa abinda ke damun sa ya haskaka rayuwarsa, kema Allah ya baki hakuri da juriya kan rayuwar da zaki tsinci kanki nan gaba

Hajiya Fadimatu dake zaune tana kalon Hajiya Hawau tayi Murmushi ta ce " Baba tabas ance zamani ya canza kana iya haihuwar yaro ka kasa tankwasa shi , na sani ne bi'izinillah gata muka yiwa Mubasshir l'a zai gode mana kan hakan , aman fa ina neman wata alfarma

Hajiya Hawau ta kaleta ta ce" Alfarmarki KO maicece fada min ita insha Allah zanyi kokarin ganin na cika miki

Hajiya Fadimatu ta ce " bana son su san an aura musu juna nafi son na kara wanke yata ta goge da ilimi ta yanda zata kwaci kanta koda za'a cutar da ita, ina son yaronki da kansa ya nuna yana so dan kar yaga an bashi kyauta yayi kokarin banbanta darajarta da ta Sahla du da ita bazawara ce aman itama mutun ce so plz hajiya ki taya ni mu boye musu

Hajiya Hawau tayi shiru ta ce " to aman hajiya kar mu taka dokar musulunci fa , kar aje ta kula wasu samarin bayan ita ga mijinta

Hajiya Fadimatu ta ce " tabas wanan shi na fara tinawa aman kuma zan saka ido sosai a al'amuran ta , l'a komai zai tafi daidai

Habiya Hawau ta ce " Toh Allah ya kama mana

Sun kusan minti talatin sanan Yar Mahaukaciya dake sheka bacinta ta farka da adu'a a bakinta tana rike dan kwalinta dake kokarin koncewa ,

Ido ta zaro ganin Hajiya Hawau zaune , ta mitsika idanuwanta ai bata san lokacin da ta tashi da Sauri ta fada jikin Hajiya Hawau ta saki kuka ta rukunkumeta

Itama kukan take na yaushe gamo sai da Hajiya Fadimatu ta ce " ya isa hakanan sanan suka sasauta

Hajiya Hawau ta talafo fuskar Yar Mahaukaciya ta ce " kiyi hakuri yata , kiyi hakuri

Yar Mahaukaciya ta girgiza kai ta ce " Haba hajiyata ki dena bani hakuri kan laifin da ba naki ba sanan wly ni na yafe har cikin zuciyata ,

Hajiya Hawau tayi murmushi ta ce " Allah yayi miki albarka ,

Ta amsa da amin sanan ta juya wajen Hajiya Fadimatu ta ce " Mamana tun yaushe kika dawo? KO tare kuka zo?

Hajiya Fadimatu cikin murmushi ta ce " Mun dan jima da shigowa kina dan hutawa shi yasa naki na tashe ki dan na san halinki sarkin aiki ta karasa tana murmushi

Haka sukayi ta labarin su har yama tayi direban Hajiya Fadimatu ya mayar Da Hajiya Hawau gida cike da kewarsu Yar Mahaukaciya

Gidan Mubasshir ,

Zaune suke saman diner suna cin abinci Sahla ta sha ado sai zuba kamshi take tana iyayi shi kuwa gangar jikinsa kawai ke tare da ita aman zuciyarsa ta tafi aikinta tinani wata can daban

Sahla ta ce " konci tashi yau har munyi kwana biyar da aure , husby yaushe zaka kaini na ga momyna?

Mubasshir ya kaleta ya ce " au har kinyi kewar gidan ne?

Sahla tayi fari da idanuwanta ta ce " eh to ba sosai ba aman momyna nafi kewa

Mubasshir ya ce " Sahla ba fa mu kadai bane a cikin gidan nan

Sahla ta tsayar da cin abincinta ta ce" eh man husby akoy masu aiki KO?

Mubasshir ya ce " no banda masu aikin akoy iyayena a cikin gidan nan

Sahla ta ce wasu iyayen naka bayan Hajiya

Mubasshir ya kaleta a ransa ya ce *Hajiya* au bazata ce mata mama ba? A fili ya ce " eh banda maman Mubasshir inada iyaye da nake kyautatawa suna saka min albarka dan gamawa da duniya lafiya kuma ina son matata ta koyi halayana na kirki

Sahla ta dan yatsina fuska a ranta ta ce lale ma har wasu bare Kenan ka yayubo min a gida tabas zanyi août da koma su waye su , aman a fili ta ce " oh ohk

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login