Showing 75001 words to 77913 words out of 77913 words

Chapter 26 - 'Yar Mahaukaciya

10 Oct 2024

15844

haka ya dagata cimak ya nufi bayin da ita stilll ba'a daina buga kofar ba, harma an shiga danna Kira à waya, yana sane yayi bilis da su,

Suna shiga ya direta à bahon wankan cikin ruwan zapi , Yar Mahaukaciya ta rintse ido ta rike hannayansa hawaye na zirara daga idannuwanta, yana yi yana canza mata ruwan zapin har ya gamsu da gashin nata sannan ya koma gefe ya ce tayi wankan tsarki,

Yar Mahaukaciya ta kawar da kanta domin ta san KO mai zata yi bazai yarda ya fita daga bayin ba, hakan yasa kawai ta zagine tayi wankan ta duk da har à lokacin da zafin dan dai bai kai na dazun ba

tana gamawa ta Daura banban tawul a kirjinta tayi kokarin fitowa,

Da gangan ya tsareta da ido har ta fito daga bahon wankan, ta fara tafiya à hankali tana cije lebe, karasowa yayi ya dagata yayi tsakar dakin da ita, ita dai ba abinda ta ce masa shi kuwa sai leken yanayin fuskarta yake,

Haka ta zumbula doguwar rigarta ta saka hijab ta kabarta sallah,
Saï à sannnan tunanin karfa suyi tunanin KO wani abin ne ya same su ya saka shi mikewa Sam bai dauke zanin gadon da suka kwonta samansa ba,

Yana budewa ya gansu à tsaitsaiye, abin mamaki harda su Hajiya Hafsat maman Yar Mahaukaciya, Idannuwansa ya zaro ya ce" Au su aba kun karaso ? Dama kuna hanya kenan

Hajiya Fadimatu ta ce" son suna gidanku dai ba suna hanya ba, Ina yarinyata take ?

Elhaj Muhammad ya ce" Kai Hajiya ni dama tsorona KO jikin nasa ne Tunda naga kun daga hankali haka, ashe lafiyarsa lau, Dan haka ni kunga tafiyata, son Zo mu je akoy Yar tataunawar da nake SO mu yi

Mubasshir kuwa ya raba ta gefen mamarsa yana dan sine kansa dan kuwa tana iya zabga masa mari a kan y'arta,

suna sauka Su Hajiya Fadimatu suka nufi dakin inda Hajiya hafsat tayi gaba abinta duk da irin yanda zuciyarta take cike da mararin ganin y'arta aman wani abin da kunya,

suna shiga suka tarar da Islam à konce saman salayar da sauri suka karasa wajenta suna tambayar Lafiya ?

Hajiya Fadimatu ta dagota ta ji jikinta zapi rau, ta ce" subahanalah Yar Fadimatu zazabi ne KO meye jikinki zafi haka ?

Ita dai Yar Mahaukaciya Bata ce komai ba idannuwanta à rufe tayi lamo à jikin Hajiya Fadimatu tana sauke numfashi

hajiya Rafi'at ta matsa kusan bed din dan ta dauko abinda take hange à yashe, ido ta zaro ganin abinda yake saman bed din, à hankali ta furta ta faru ta kare, da ido ta yafito Aunty Habiba ta taso ta ISO itama Idon ta zaro aman ita tayi magana ta ce" Eyah AA ba'ayi hakurin ba kenan

hajiya Fadimatu ta dago ta zuba musu ido, yanayin fuskarsu kadai ya fasara mata abinda suka gani, tsam ta rungume Islam à jikinta, à ranta ta furta she is virgin, ya zama wajibi à mikata gidanta à gobe gobe dan haka al'adar take, ta kawar da kai cike da takaicin Mubasshir,

À hankali ta Mike da Islam ta nufi kofa da ita dan ta kaita dakinta ta kula da ita, su kuwa suka zagine dan gyara dakin

Sahla ce sai kai kawo take a tsakar tamkamemen falonta da waya à hannunta tana bugawa tana tsaki,

Dakin taji ana dannawa ta tashi da sauri ta nufi kofar dan budewa, tana budewa taga wani sécurite ne dan soja tsaye ya ce" Madame oga ne ya ce à sanar da ke Yar tafiya ta kama shi wayarsa à rufe aman ba zai jima ba

Sahla ta ce" What ? Kan uban cen karfa ya je ya ruguza min tsari, ba shiri ta nufi dakinta ta dauko dan gyalenta ta nufi gidan mahaifiyarta,

Daidai ta ISO Idriss ya ISO suna hada ido yaji wani irin haushinta da tsanar halayenta sun darsu à zuciyarsa, toh uban me ya fitar da ita daga gidanta à wannan tsohon daren, cikin Jin Haushi ya bude matarsa ya nufi tata da mugun bacin rai

to fa kardai garin bacin rai Idriss ya tona abinda AA ya ji ????? 😳😳😳😳😳😳

🇳🇪Belles écrivaines du Niger

*'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*

*Na*
*Sajida*

81

*Aunty Zainab kiyi ki gama min Docter deejart plz 😩*

*Sister Dee ya haka ? Gaskiya page daya yayi mana kadan, kawai ki karo mana page din bintalo domin ya dauko sugar😋*

wayarsa dake ajiye kasa ta kwashi ruri, à tare suka zabura, Mubasshir ya diro daga bed din Yar mahaukaciya tayi saurin mayar da kanta cikin bargon, yayi murmushi yana daga wayar

Idriss ya ce" kai wai ya haka Tunda safe Ina kiranka har karfe tara tayi mai kake ne ?

Mubasshir ya zaro ido yana fadin " what karfe 9 fa ? Ya Salam abokina bara muyi sallah

Idriss ya zaro ido ya ce" Ina gidanka

Mubasshir ya ce" gidana fa ? Haba bawan ALLAH da safiyar nan ?

Idriss ya ce " kasan ALLAH ka bude min KO Nayi maka aika aika à cikin gida

Mubasshir ya ce" aa yi hakuri, Bara na wurgo maka ky din falon kafin na sauko

Hakan kuwa akayi Mubasshir ya wulowa Idriss ky din falonsa ya bude ya zauna ya kuna TV domin yayi niyar fa bazai bar gidan nan ba sai da shi

Cikin nutsuwa ya dauki matarsa yayi bayi da ita inda ta dan sake da shi domin ta lura idan da taci gaba da nonokewa Mubasshir sai ta rame irin yanda yakeda takuran nan da son komai sai yayi mata,gashi ya mayar da lips dinta filin saukarsa du motsinsa sai ya mana mata kis

Haka suka gama ya jasu sallar asuba à karfe 9🤔,

Bayan sun gama Yar mahaukaciya ta duka gabansa cikin muryarta uwa ta yara ta ce" morning yayana

Mubasshir ya zuba mata ido yana kalonta yaki amsa gaisuwar tata,

Dago da kanta tayi tana kalon sa, yanayin kalon da yake mata sai da taji kunya, hudubar aunty habiba ce ta fado mata cikin ranta inda take fadin" karki baiwa mijinki damar wata ta waje ta birge sa, kiyi iya yinki dan ganin kin Wadata mijinki da dukan abinda yake bukata idan dai bai kaucewa hanya ba, sannan ki Kula da yannayin fuskar mijinki, Idannuwansa lebensa komai nasa yana iya yi miki magana da su, ki kasance mai gane kurmancin mijinki,

Yar mahaukaciya ta Mike ta cire dogon hijabinta, ta kuma cire abayar da ta dora saman Yar karamar rigarta fara tasss, tana sane ta duka kamar zata cire wani Abu à akaifunta,

Mubasshir dake zaune ido ya zaro yana kalonta, kafin yayi wani yunkurin ta Mike,, ta juyo gabansa, cikin dabara ta dan ja rigar tata kasa, saman mamarta suka dan bayana à fili, nufo shi take, shi kuwa ya tsura mata ido yana son ganin abinda zata aikata

tana isowa daidai shi ta mika hannayenta biyu ta zagaye wuyansa da su, ta Haye saman cinyoyinsa ta hade idannuwanta da nasa tana kashe shi da wani Shu'umin kalo, à hankali take matso fuskarta da tasa har ta ISO Daidai lebensa, inda Idannuwansa ke rawa ya kali idannuwanta ya kuma kali lebenta, gaba daya ya kunce ya zama wani sususu, maimakun ta mana masa Kiss sai ta fitar da harshenta ta lashi gefen fuskarsa wajen sajensa sannan ta Isa Daidai kunnansa ta hura masa iska cikin wata murya wace ni kaina sai da na zaro ido domin ban san Islam da ita ba ta furta" *Morning My Blood*

Mubasshir bai san lokacin da ya rintse Idannuwansa yana Jin saukar leben islam à kunansa da kuma sunan da ta nada masa, gaba daya tsikar jikinsa tayi wani irin tashi, bai san sanda yayi saurin jawo ta gaba dayanta jikinsa, jikinsa na mugun Bari ya lalubi lips dinta ya shiga kissing dinsu cikin zafafan Kiss,

wayarsa ta Kuma kwasan ruru tamkar an kara mata sautin kidan


Bai saki bakinta ba ya lalubo wayar sannan ya saki cikin kasalaliyar murya ya ce" Haba Idriss, haba Idriss ya zaka yi min haka, haba mana, shin mai Nayi maka da farar safiyar nan kazo kana shigar min haki haka ? Ka tausaya min mana kana katseni

Idriss ya ce" la la la, lale ma Mubasshir jarabarka tafi karfinka, toh wly au ka bude kofar nan ka fito ka raka ni zance au na hanaka koma meye kake bazaka yi shi ba wly

Yar mahaukaciya banda dariya kasa kasa ba abinda take, ta Mike a hankali daga jikinsa tayi gaba abinta

Mubasshir ya ce " baby plz karki tafi

Idriss d'à bai katse wayar ba ya ce" tafi ke karki kula shi

haka dai à dole ba dan ya SO ba ya bude kofar bayan ya saka shadarsa maroon ya sauko inda ya bar Yar mahaukaciya tana shafa mai

yana saukowa ya nufe Idriss d'à maseefar taya zai adabi rayuwar amare, ba'a yiwa ango sauko haka

Idriss yayi murmushi ya ce" nawan wly ban rintsa ba, dama na samu Nayi hajiya traitement dinta na dawo dakina dan yin baci abin ya gagara, dole na tashi na shiga fadawa ALLAH kan ya kwata min zuciyar Rafi'at

Mubasshir ya ce " abokina baka da dama, yanzu dan iya shege ka tsalake ka diro kan auntyna ?

Idriss ya ce" au yaushe kuma ka yarda da auntynka ce ?

Mubasshir ya ce" Tunda ta haifi My Islam

Idriss yayi dariya ya ce" ai kuwa nima na zama uncle dinka daga yau

zaiyi magana wayar Idriss ta kwashi kara, ya daga da sauri yana salama

Elhaj Ilyass ya ce" kaga fa abin arziki Idriss insha ALLAH yau za'a daura aurenka, yanzu haka zancen da nake maka muna gidan à zaune, ga su elhaj da mamana, da su hajiyar, Elhaj ya ce Tunda yau juma'a ne kawai mu je gidan liman mu shaida masa sai à daura idan an gama sallah

Idriss ya Mike da sauri yana ta wara ido murna ta cika masa ciki ya rasa ma mai zai ce hakan yasa ya mikawa Mubasshir wayar yana ta hamdallah,

Mubasshir yayi godiya ya ce" su din ma gasu nan tafe gidan

hakan kuwa akayi islam banda murna ba abinda take

Suna Isa ta bude ta fice da gudu inda Mubasshir ya zaro ido ya ce" ya Salam, islam no karkiyi ki fadi

Ina bata ma jinsa ta tura kofar ta shige tana ta murna sai dai Bata kai ga karasawa ba ta ja ta tsaya tana kalon ikon ALLAH, Aunty Rafi'at ce sai kuka take shekawa an kewaye ta

Turo kofar suka yi suka shigo inda suma suka ja suka tsaya suna kalon ikon ALLAH

Rafi'at ta ce" haba aunty, haba hajiya, kawai dan yaro ya ce " ga abinda yake SO sai à biye masa, haba dan Allah yanzu da girmana à hada ni Aure da yaro karami ? Nafa girme masa fa kuma wly tausayina ne yake ba wani sona ba

hajiya hafsat ta ce " sister wai meye haka ne ? Haba taya za'a zauna ana nuna miki gabas kina kalon yama ? Sunar ce bakya SO ? Idan har baki godewa ALLAH kan ni'imar da yayi miki à yanzu mai zaki yi ? Taya zaki fasara kyautar da Allah yayi miki adu'arki da ya amsa da wata fasarar ? Rafi'at à da inai miki kalon kinyi hankali ashe dai da sauran ki,

hajiya hawau ta ce " aa hajiya ku tashi ku barni da y'ata mu zanta kun ji ?

Hakan kuwa akayi sai da suka tashi suka ga su Mubasshir sunyi cirko cirko da hanu suka yi musu nunin su fice karta gansu

hakan kuwa suka shige inda hajiya hawau ta dage wajen kontarwa da hajiya Rafi'at hankalinta kan auren ta da idriss

ya kasa tsaye ya kasa zaune, du labarin da suke yana dai jinsu ne aman baya fahimtar abinda suke fada,

Hajiya hafsat ce ta fito da faranti da abinci à ciki, ta ajiye ta dauko ta shiga zubawa kuskus ce ta sha muryar jan nama sai kanshin kayan yaji ke tashi, ta mimika musu,, har ta kai kan Idriss ta mika masa ta ce" Idriss ka dawo cikin hayacin ka mana,

Idriss ya juya à hankali ya shiga cacakar abincin

Yar mahaukaciya ta shigo da jus jus ta ajiyewa kowa à gabansa, ta juya ta dauko nata farantin ta zauna Kusa da hajiya Fadimatu tayi bismillah ta debo ta kai bakinta

Wani irin Abu taji ya bigeta à hancinta na kanshin kayan yajin nan da tafarnuwa, kafin ta Ankara tayi wani abin sai kawai taji cikinta ya fara hautsina mata sai ga amai

da gudu ta mike zata nufi Bayi aman Ina dole ta duka à nan tana kwara amai tun karfinta, dan kwalin kanta ya fadi kasa haka mayafinta domin wani irin tukota aman yake

da gudu Mubasshir ya rigayi kowa isawa wajenta ya kamata yana tambayarta Lafiya ? Mai ya sameta ? Wani abin ta hadiye ?

Da kyar ta samu ta gama aman du ta galabaita ya dauketa yayi bayi da ita dan ya wanke mata wajen da ya baci à jikinta, ita kuwa hajiya Fadimatu sai sintiri take tana tambayar ta shigo ne bayin ? inda hajiya hafsat ta shiga gyara wajen

Idriss ya Mike ya fice dan dauko kayan aikinsa domin yana Docter gida har uku hakan ya sa baya tafiya ba malet dinsa mai dauke da yan abubuwan da ya dace domin aikinsa

Daidai zai fita suka yi karo da Hajiya Rafi'at, da sauri ta zaro ido tana yi masa kalon mamaki domin Bata san shigowarsu ba, ido Hudu suka yi inda gabanta ya fadi, tayi saurin sada kanta kasa shi kuwa yaki dakin hanyar balatana ta fice,

Hajiya hawau ta taho tana fadin lafiyarku kuwa yayanan ? Naga kun tsare hanyar ficewa

hajiya Rafi'at ta ce " hajiya shine ai ya tsare hanyar fa

Idriss ya ce" to hajiya ta shige mana ?

Hajiya hawau tayi murmushi ta juya tama daina shigan balatana su fake da ita

Rafi'at ta juya itama zata bar wajen da saurinsa ya riko hannunta ya jawota tamkar wata beby ya hadeta da garun dakin

Idannuwanta ta rintse tana mutsukmutsuk da baki, Idriss ya tsurawa bakin nata ido Yana kalonta

Jin yayi shiru ne t'a bude idannuwanta ta sauke su à cikin Idannuwansa, ta kasa janye idonta daga NASA

Idriss ya saki murmushi à hankali ya ce" hei *I Love u*

Aunty Rafi'at ta zaro ido ta kasa dauke idannuwanta daga fuskarsa gabanta na dukan uku uku

Idriss ya kashe mata ido daya ya ce" Yaya dai madame, kalon fa ?????

Da sauri ta sada kanta tabi ta kasa hannun NASA tayi dakin da gudu tana ajiyar zuciya

Yayi murmushi y'a ce " she love me too, yayi gaba abinsa

Yana dawowa dauke da kayan aikinsa ya shiga aune aunensa inda ya bukaci fitsarinta, bayan tayi ta bayar ya kuma daukan jininta ya fice, ita kuwa tayi lamo à cinyar hajiya Fadimatu, inda Mubasshir yake zaune rike da hannunta daya yana dan murzawa, hajiya Rafi'at tana dan shafa gashin kanta ita kuwa hajiya hafsat sai cin abincinta take domin juna biyu ne da ita mai shegen sakata kwadayi du da ba Wanda ta fadawa har shi kansa mai abin,

Hajiya hawau ta kare mata kalo ta ce" wai y'ata watansa nawa ?

Hajiya hafsat ta zaro ido domin ta san da ita hajiya hawau take, ba shiri ta Mike tana fadin " Wa ?, tayi gaba ba tare da ta tsaya an fada mata Wa din ba,

ai kuwa hajiya Fadimatu tayi dariya ta ce" haba kin rigani à fili na rigaki à badini hajiya, Allah ya raraba Lafiya

Yar mahaukaciya ta zaro ido zata Mike Idriss ya shigo da result yana ta murna ya ce" an daura auren

Hajiya Fadimatu ta ce" oh yaren zamani idriss to barka

Idriss ya dan sine kai yana mikewa Mubasshir takardar gwajinsa yana hangen Rafi'at da ta sada kanta kasa tana share hawaye, wannan karen kam kukan dadi take( Wa ya fada miki)

Hajiya hawau ta shigo tana fadin" an daura Aure ba ango, ya akayi baku je masalaci ba ?

Mubasshir da ya buda takardar bayan ya yiwa Idriss barka yayi saurin cewa what ? Yana zaro ido ya kali Idriss yace"docter baka fasara min abinda nake gani ba ?

Idriss ya ce" congratulation, abinda ka gani hakane

Mubasshir yayi saurin kai kansa kasa yayi sujada yana ta murna, yana dagowa ya dagota ya rungume à gaban su hajiya Fadimatu wace itama murnar ta hanata zama, à tare suka yi gaba suka bar masa dakin domin kara rungumeta yake yana lalubar cikinta dake shafe yana fadin"beby boy or girl hi, dadyne, how are u ? Kana cin abinci ? Kana jina ?

Yar mahaukaciya sai sine kai take a ranta tana mamakin rashin kunyar AA

Alhamdulilah , Alhamdulilah, dukan godiya ta tabata ga ALLAH buwayi gagara misali da ya bani ikon ganin Karshen novel dina *Yar Mahaukaciya* Ina fatan du Wanda ya karantashi ya karu da abin karuwar dake ciki sannan Ina neman gafarar du Wanda na batawa sanadiyar wannan novel nawa na biyu bayan *Duk karyar kada na ruwa ne* , Allah ya hada mu à novel dina na gaba mai suna *Daga tafiya daukan soja* Na gode taku y'arku, kanwar ku, yayarku *Sajida* Y'ar mutan Niger,...


Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login